Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda ya shar'anta ma bayi hukunce-hukuncen da suka dace da hali da yanayinsu, don su iya bauta ma Allah cikin sauki, don rayuwarsu ta inganta, kuma ya yi musu sakamako a Ranar Lahira.
Tsira da amincin Allah su tabbata
ga Ma'aikin Allah, Annabi Muhammadu, wanda ya zo mana da wannar Shari'a mai
sauki, da iyalan gidansa, da Sahabbansa da wadanda suka bi su da kyautatawa.
Idan bayin Allah sun cika
Azuminsu na watan Ramadhan Allah ya wajabta musu Zakkar Fidda Kai, wacce za a
fitar a Ranar Eidi, don yawalta mabukata da abinci.
Zakkar fidda kai ibada ce da take
da alaka da Azumin watan Ramadhan.
Da Larabci ana kiranta
"Zakatul Fidir". An kira ta da sunan Zakkah ne saboda tana gyara
halin mutum, ta habaka shi, ta sanya shi cikin masu kyauta da karamci.
Sababin shar'anta ta shi ne shan
ruwa daga Azumin Ramadhan.
Hikimar shar'anta ta ita ce don
ta tsarkake mutum daga abubuwan da ya aikata na yasassun maganganu da na batsa
a lokacin da yake Azumi. Ya tabbata daga Ibnu Abbas (ra) ya ce:
«فَرَضَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ زَكَاةَ الْفِطْرِ طُهْرَةً لِلصَّائِمِ مِنَ اللَّغْوِ وَالرَّفَثِ،
وَطُعْمَةً لِلْمَسَاكِينِ،
[السجستاني، أبو داود، سنن أبي
داود، ١١١/٢]
((Manzon Allah (saw) ya farlanta
Zakkar fidda kai don tsarkake mai Azumi daga yasasshiyar magana, da magana ta
batsa, kuma don samar da abinci ga miskinai)). Abu Dawud (1609), Ibnu Majah
(1827).
Ita Zakkar Fidda kai tana rataye
ne a wuyan mutum kansa, ba da dukiya take rataye ba. Shi ya sa aka wajabta ta a
kan kowa, ba ta takaita kan masu dukiya kadai ba. Don haka ita wannar Zakka ta
wajaba a kan kowane Musulmi, mace ko namiji, babba ko karami, da ko bawa.
Saboda ya tabbata daga Ibnu Umar (ra) ya ce:
«فَرَضَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ زَكَاةَ الفِطْرِ صَاعًا مِنْ تَمْرٍ، أَوْ صَاعًا مِنْ شَعِيرٍ
عَلَى العَبْدِ وَالحُرِّ، وَالذَّكَرِ وَالأُنْثَى، وَالصَّغِيرِ وَالكَبِيرِ مِنَ
المُسْلِمِينَ، وَأَمَرَ بِهَا أَنْ تُؤَدَّى قَبْلَ خُرُوجِ النَّاسِ إِلَى الصَّلاَةِ»
[البخاري، صحيح البخاري،
١٣٠/٢]
((Manzon Allah (saw) ya farlanta Zakkar fidda
kai za a bayar da sa'i daya na dabino, ko sa'i na sha'er, wajibi ne a kan bawa
da da, namiji da mace, karami da babba daga cikin Musulmai. Kuma ya yi umurni
da a fitar da ita kafin mutane su fita Sallar Eidi)). Bukhari (1503), Muslim
(984).
Zakkar tana wajaba a kan kowane
Musulmi ne idan yana da sa'i daya da ya karu a kan abincinsa tare da iyalinsa
na ranar Eidi da darensa. Haka kuma ko da rabin sa'i ne ya saura, to sai ya
ciyar da shi, saboda Allah ya ce: {Ku ji tsoron Allah iya abin da za ku iya}
[al-Tagabun: 16].
Kuma wannar Zakka tana wajaba a
kan Musulmi ko da kuwa bai yi Azumi ba saboda wani uzuri, kamar wanda tsufa ya
hana shi yin Azumin, ko mace mai jinin haifuwa, wacce tsawon wata gudan ba ta
samu ta yi Azumi ko daya ba, ko yaro, ko da kuwa jariri ne. Saboda fadin Annabi
(saw) a Hadisin Ibnu Umar (ra) wanda ya gabata:
وَالصَّغِيرِ وَالكَبِيرِ مِنَ المُسْلِمِينَ
[البخاري، صحيح البخاري،
١٣٠/٢]
((Karami da babba daga cikin
Musulmai)). Bukhari (1503), Muslim (984).
Bashi ba ya hana fitar da Zakkar
Fidda kai ta kowace fiska, saboda bashi yana rataye ne da Dukiya, amma ita
Zakkar kuma tana rataye a wuyan mutum kansa.
Asali Zakkar ta wajaba a kan kowa
ne da kansa, amma idan wani ya fitar ma wani bisa yardarsa, kamar mai gida ya
fitar ma iyalansa, da 'ya'yansa to ya wadatar. Saboda aikin Sahabbai ya
tabbatar da haka, Nafi'u Maulan Ibnu Umar ya ce:
فَكَانَ ابْنُ عُمَرَ «يُعْطِي عَنِ الصَّغِيرِ،
وَالكَبِيرِ، حَتَّى إِنْ كَانَ لِيُعْطِي عَنْ بَنِيَّ»
[البخاري، صحيح البخاري،
١٣١/٢]
((Ibnu Umar ya kasance yana fitar
da Zakkar ga yaro da babba, har ya kasance yana fitar ma 'ya'yana)). Bukhari
(1511).
Don haka wannan ya nuna cewa;
yaran da ba su da dukiya fitar musu za a yi, haka aikin Sahabbai ya nuna.
Zakkar fidda kai tana wajaba ne
da zaran rana ta fadi a ranar karshe na Ramadhan, in an shiga daren Eidi.
Dalili a kan haka shi ne Hadisin Ibnu Umar (ra):
" فَرَضَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ
صَدَقَةَ الفِطْرِ - أَوْ قَالَ: رَمَضَانَ - عَلَى الذَّكَرِ، وَالأُنْثَى، وَالحُرِّ،
وَالمَمْلُوكِ صَاعًا مِنْ تَمْرٍ، أَوْ صَاعًا مِنْ شَعِيرٍ «فَعَدَلَ -[132]- النَّاسُ
بِهِ نِصْفَ صَاعٍ مِنْ بُرٍّ،
[البخاري، صحيح البخاري،
١٣١/٢]
(Manzon Allah (saw) ya farlanta
Zakkar fidda kai a kan mutane ga Ramadhan, za a bayar da sa'i daya na dabino,
ko sa'i na sha'er, wajibi ne a kan da da bawa, namiji da mace daga cikin
Musulmai)). Bukhari (1511), Muslim (984).
Fadinsa (saw) cewa: ga Ramadhan
shi yake nuna da zaran Ramadhan ya zo karshe, rana ta fadi a yinin karshe na
Ramadhan to Zakkar ta wajaba.
Bude baki daga Azumin Ramadhan
yana tabbata ne da zaran Rana ta fadi an shiga daren Eidi. Wannan ya sa duk
yaron da aka Haifa a daren Eidi, bayan faduwar rana to Zakkar ba ta wajaba a
kansa ba, saboda bai riski Ramadhan ba. Amma da a ce za a haife shi kusa da
faduwar rana, kafin a sha ruwa, to Zakkar ta wajaba a kansa.
Lokacin fitar da Zakkar shi ne
ranar Eidi da safe, kafin a fita Masallacin Eidi. Saboda ya tabbata daga Ibnu
Umar (ra) ya ce:
«فَرَضَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ زَكَاةَ الفِطْرِ صَاعًا مِنْ تَمْرٍ، أَوْ صَاعًا مِنْ شَعِيرٍ
عَلَى العَبْدِ وَالحُرِّ، وَالذَّكَرِ وَالأُنْثَى، وَالصَّغِيرِ وَالكَبِيرِ مِنَ
المُسْلِمِينَ، وَأَمَرَ بِهَا أَنْ تُؤَدَّى قَبْلَ خُرُوجِ النَّاسِ إِلَى الصَّلاَةِ»
[البخاري، صحيح البخاري،
١٣٠/٢]
((Kuma Manzon Allah (saw) ya yi
umurni da a fitar da ita kafin fitan mutane zuwa ga Sallar Eidi)). Bukhari
(1503), Muslim (984).
Don haka wajibi ne Zakkar ta isa
hanun Fakirin da za a ba shi Zakkar ko wakilinsa kafin a fita zuwa Masallacin
Eidi.
Ya halasta a fitar da Zakkar
kafin ranar Eidi da rana daya ko biyu, saboda Sahabbai sun aikata hakan, sun
kasance suna bayar da ita kafin ranar Eidi da rana daya ko biyu. Nafi'u ya ce:
وَكَانَ ابْنُ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا
«يُعْطِيهَا الَّذِينَ يَقْبَلُونَهَا، وَكَانُوا يُعْطُونَ قَبْلَ الفِطْرِ بِيَوْمٍ
أَوْ يَوْمَيْنِ»
[البخاري، صحيح البخاري،
١٣١/٢]
((Ibnu Umar (ra) ya kasance yana
bayar da ita ga masu karbanta, kuma sun kasance suna bayarwa kafin ranar Sallar
da kwana daya ko biyu)). Bukhari (1511).
Haramun ne fitar da ita bayan
Sallar Eidi, kuma ba ta isarwa ga wanda ya fitar, saboda Hadisin Ibnu Umar
wanda ya gabata, cewa; Annabi (saw) ya yi umurni da fitar da ita kafin fita
Sallah. Da kuma Hadisin Ibnu Abbas (ra) ya ce:
: «فَرَضَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ زَكَاةَ الْفِطْرِ طُهْرَةً لِلصَّائِمِ مِنَ اللَّغْوِ وَالرَّفَثِ،
وَطُعْمَةً لِلْمَسَاكِينِ، مَنْ أَدَّاهَا قَبْلَ الصَّلَاةِ، فَهِيَ زَكَاةٌ مَقْبُولَةٌ،
وَمَنْ أَدَّاهَا بَعْدَ الصَّلَاةِ، فَهِيَ صَدَقَةٌ مِنَ الصَّدَقَاتِ»
[السجستاني، أبو داود، سنن أبي
داود، ١١١/٢]
((Manzon Allah (saw) ya farlanta Zakkar fidda
kai don tsarkake mai Azumi daga yasasshiyar magana, da magana ta batsa, kuma
don samar da abinci ga miskinai. Wanda ya bayar da ita kafin Sallah ta zama
Zakka karbabbiya, wanda ya bayar da ita bayan Sallah ta zama sadaka daga cikin
sadakoki)). Abu Dawud (1609), Ibnu Majah (1827).
Wannan Nassi ne a kan cewa;
Zakkar ba za ta wadatar wa mutum ba idan ya bayar da ita bayan Sallar Eidi,
kuma ba za a karbe ta a matsayin Zakkar Fidda kai ba, ta zama sadaka ce kamar
sauran sadakoki.
Amma idan wani uzuri ne ya sa bai
fitar a kan lokacinta da ba fa, misali ya yi tafiya, ya wakilta wani ya fitar a
kan lokacinta, amma sai da ya dawo daga tafiyar sai ya samu mutumin bai fitar
da ita a kan lokaci ba, to ba shi da laifi a wajen Allah, amma zai fitar da ita
ko da kuwa bayan Eidin ne da kwanaki. Wannan kiyasi ne a kan rama Sallah ga
wanda ya yi bacci ko ya manta ta.
Ya halasta mutum ya bayar da
Zakkar ga Kungiyoyin Agaji masu rijista ko amintattu. Sai su zama wakilai ga su
fakirai da za a ba su wannar Zakka. Saboda haka idan mutum ya bayar da Zakkar
wa kungiyar a kan lokaci, amma ita kungiyar kuma ba ta raba ba har sai bayan
ranar Eidin, to shi dai Zakkarsa ta yi. Ta yiwu su kuma wani uzuri ne ya hana
su raba ta a safiyar ranar Eidin, ko kuma wata Maslaha ce ta sa suka jinkirta.
Wajibi ne a fitar da Sa'i guda na
abinci, a kan kowane Musulmi. Saboda Hadisin Ibnu Umar (ra) ya ce:
«فَرَضَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى
اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ زَكَاةَ الفِطْرِ صَاعًا مِنْ تَمْرٍ، أَوْ صَاعًا مِنْ شَعِيرٍ
عَلَى العَبْدِ وَالحُرِّ، وَالذَّكَرِ وَالأُنْثَى، وَالصَّغِيرِ وَالكَبِيرِ مِنَ
المُسْلِمِينَ، وَأَمَرَ بِهَا أَنْ تُؤَدَّى قَبْلَ خُرُوجِ النَّاسِ إِلَى الصَّلاَةِ»
[البخاري، صحيح البخاري،
١٣٠/٢]
((Manzon Allah (saw) ya farlanta
Zakkar fidda kai za a bayar da sa'i daya na dabino, ko sa'i na sha'er, wajibi
ne a kan bawa da da, namiji da mace, karami da babba daga cikin Musulmai. Kuma
ya yi umurni da a fitar da ita kafin mutane su fita Sallar Eidi)). Bukhari
(1503), Muslim (984).
Malamai sun yi ittifakin a kan
cewa; Sa'in da ake nufi a nan shi ne Sa'in Annabi (saw). Ana kaddara shi a
wannan zamani da kilo biyu da gram 40.
Abin da ya wajaba a fitar shi ne
sa'i na irin abincin mutanen gari, kamar shinkafa, masara, gero, dawa da
makamancinsu ko garinsu. Dalili a kan haka shi ne Hadisin Abu Sa'eed (ra) ya
ce:
«كُنَّا نُخْرِجُ فِي عَهْدِ
رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَوْمَ الفِطْرِ صَاعًا مِنْ طَعَامٍ»،
وَقَالَ أَبُو سَعِيدٍ: «وَكَانَ طَعَامَنَا الشَّعِيرُ وَالزَّبِيبُ وَالأَقِطُ وَالتَّمْرُ»
[البخاري، صحيح البخاري،
١٣١/٢]
((Mun kasance a zamanin Manzon
Allah (saw) muna fitar da sa'i na abinci a ranar Eidi. Ya ce: abincinmu ya
kasance shi ne sha'er da zabib da cukui da dabino)). Bukhari (1510).
Don haka cewa da ya yi abinci, ya
nuna jinsin abinci ne ya wajaba a fitar, ba dole sai nau'in abincin da aka
ambata a cikin Hadisan ba, saboda su ne abinci a wancan lokacin. Don haka sai
ambaton nasu ya zama tamkar misali ne, ba wai an ayyana su ba ne a matsayin
dole su za a fitar. shi ya sa ya gabata a Hadisin Ibnu Abbas (ra) ya ce:
زَكَاةَ الْفِطْرِ طُهْرَةً لِلصَّائِمِ مِنَ
اللَّغْوِ وَالرَّفَثِ، وَطُعْمَةً لِلْمَسَاكِينِ،
[السجستاني، أبو داود، سنن أبي
داود، ١١١/٢]
((Don samar da abinci ga
miskinai)). Abu Dawud (1609), Ibnu Majah (1827).
Wannan ya sa Malamai suka ce;
wajibi ne a fitar da abinci, ba kudin abincin ba.
Ana bayar da zakkar ce ga
talakawa; Fakirai da Miskinai. Babu laifi a bayar da zakkar mutum goma ga
Fakiri mutum daya, ko kuma a bayar da zakkar da ta fito daga bangare daya ga
Fikirai goma a raba musu, saboda Annabi (saw) ya yi bayanin iyakacin abin da za
a bayar din ne, wato sa'i daya, amma bai kayyade yawan wadanda za a ba su ko
yawan abin da za a bai ma kowa daga cikinsu ba.
'Yan'uwa ku yi kokari ku yi da'a
ma Allaha a wannar Zakka, saboda farilla ce, Allah ya wajabta ta ne ta harshen
Manzon Allah (saw).
Allah ya karba mana Ibadunmu, ya
gafarta mana zunubanmu, ya shiryar da mu hanya madaidaiciya. Ya sa mun dace da
daren Lailatul Qadr.
Allah ya jikan iyayenmu, ya yaye
mana matsaloli da fitintinu da suke damun kasarmu, na kuncin rayuwa da rashin
tsaro da aminci, ya ba mu shugabanni na gari, masu tsoron Allah da kishin
al'umma da tausayin talakawa.
Dr Aliyu Muh'd Sani
(Hafizahullah)
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.