Ticker

6/recent/ticker-posts

Aron Kalmomi Daga Wasu Sassan Harsuna: Nazarin Hausar ‘Yan-Tashar Mota a Garin Sakkwato

Citation: Umar, M. M. and Sharu, Y. (2025). “Aron Kalmomi daga wasu Sassan Harsuna: Nazarin Hausar ‘Yan-tashar Mota a Garin Sakkwato.” in Ɗunɗaye Journal of Hausa Studies, Vol. 03, No. 02, Pp. 20– 27. www.doi.org/10.36349/djhs.2025.v03i02.003.

ARON KALMOMI DAGA WASU SASSAN HARSUNA: NAZARIN HAUSAR ‘YAN-TASHAR MOTA A GARIN SAKKWATO

Na

Muhammad Mustapha Umar

Department of Nigerian Languages, Usman Danfodiyo University, Sokoto

And

Yusuf Sharu

Goɓernment Day Secondary School Wamakko, Sokoto State Teachers Serɓice Board, Sokoto

Tsakure:

Manufar wannan takardar ita ce, a aiwatar da nazarin kalmomin aro a Hausar ‘yan-tashar mota a garin Sakkwato. Haka kuma, takardar ta yi amfani da ra’in da ya shafi yadda mutane suke amfani da harshe ta fuskar ma’anar kalmomi, wato Ra’in Fiɗar Zantuttuka (Discourse Analysis Theory)’ wanda Harris (1952) ya assasa. Sannan, an yi amfani da hanyoyi biyu wajen tattara bayanai waɗanda suka haɗa da tattaunawa da kuma lura ta kai-tsaye. Takardar ta gano ‘yan-tashar mota a garin Sakkwato suna sarrafa kalmomin aro wajen ambaton direbobi da yaran mota da ‘yan kamasho da ‘yan dako da fasinja da tashar mota da motoci da jami’an tsaro, ko kuma don su bayyana wani hali da suka tsinci kan su a cikin tasha ko a halin tafiya.

Keɓaɓɓun Kalmomi: Aron Kalmomi; Hausar ‘Yan-tashar Mota; Harsuna; Sabuwar Ma’ana; Sakkwato

Gabatarwa

Babbar manufar wannan takarda ita ce, fito da sabbin ma’anonin kalmomin aro da ‘yan-tashar motar garin Sakkwato suke amfani da su a cikin sadarwarsu, tare da fayyace alaƙar da ake samu tsakanin maana ta asali da sabuwar maana.Daga cikin muhimmancin harshe ga al’umma akwai sadarwa, wadda ita ce ƙashin bayan aiwatar da kowace irin hulɗa. Tasirin zamantakewa da hulɗa a tsakanin wasu jama’a yakan haifar da taimakon juna da wayar da kai da haɓakar arziki da kuma bunƙasar sadarwa. Yakasai (2020:26) na ganin, ai wannan ne ma dalilin da ya sa ake samun wata rajista wadda ta keɓanta ga wani rukunin jama’a, wadda ba kowa yake iya fahimta ba daga cikin masu magana da harshe ɗaya. Irin wannan tasiri ya bayyana a cikin rukunin jama’ar tashar mota a garin Sakkwato.

Farfajiyar wannan bincike ta taƙaita ne ga wasu tashoshi na cikin garin Sakkwato; waɗanda suka haɗa da Babbar Tashar Motar Sakkwato da Tashar Alu da Tashar Filayi-oba da Tashar Bafarawa da Tashar ‘Yan Lemu da kuma Tashar Кwannawa ta shigowa cikin garin Sakkwato.

Hanyoyin da a ka bi don tattara bayanai sun haɗa da hira da waɗanda bincike ya shafa (‘yan-tashar mota) da lura ta-kaitsaye da ziyarar tashoshin mota da kuma tattaunawa da malamai don samun dalilai na ilimi. Haka kuma, an yi amfani da hanyar tace bayanai wajen zaɓar sumfarin da aka buga misalai da su.

A wannan maƙala, an yi amfani da ra’in fiɗar zantuttuka, wanda ake kira ‘Discourse Analysis Theory. Ra’in yana da manufar nuna yadda mutane suke amfani da harshe wajen fito da ma’anar zantuka ta la’akari da ayyukansu. Haka kuma, ra’in ya samu karɓuwa tun a farko-farkon shekarun ‘1960s’ da ‘1970s’. Daga cikin masana da manazarta da suka fara aiki da shi domin bayyana yanayin zamantakewa sun haɗa da: Janos (1971) da Teun (1972) da Teun (1977) da Joseph (1975) da kuma Tom (1979). Ra’in ya yi fice sosai musamman ta fuskar fiɗar zantuttuka. Saboda haka ne ma ko a baya-bayan nan Isah (2018) da Zailani (2019) da Sharu (2023) da kuma Mode (2024) A ra’ayin Knapp da Daly (2002) “Discourse Analysis is the systematic study of naturally occurring communication in the broadest sense, at the leɓel of meaning”. Fassarar marubuci: Ra’in fiɗar zantuttuka, wani tsararren fannin ilimi ne da yake nazarin zantuka ta fuskar ma’ana. James (1991) kuwa cewa ya yi: the Discourse Analysis analyses spoken and written language as it is used to enact social and cultural perspectiɓes and identities”. Fassarar marubuci: Ra’in fiɗar zantuttuka, yana nazarin harshe a magance da rubuce, musamman wajen bayyana fahimtar al’adu da ɗabi’u ko halayyar mutane.

Hausar ‘Yan Tashar Mota

Tashar mota wani fitaccen wuri ne na sufari da mutane daban-daban suke haɗuwa domin gudanar da harkokinsu mabambanta; babban aikinsu shi ne sufarin al’umma da kayansu (Abdu, 1991:2; Abubakar, 2023:16; Abraham, 1977:856; Bargery, 1934:1002; CNHN, 2006:431; Manir, 2010:16; Newman da Newman, 2020:235; Yero, 2017:3).

Hausar tashar mota wata rajista ce ta daban, wadda ba kowa yake iya fahimta ba. Ma’anar kalmominta da sassan jumla ko jumlolinta sun bambanta da na sauran rukunan al’umma. Hausar ta ƙunshi faɗaɗa ma’ana da sarrafa kalmomin aro da ƙirƙira sababbin kalmomi. Hausar ta ƙunshi maganganun azanci da sarrafa harshe iri-iri, da uwa uba samar da wata nau’in Hausa ta musamman a huldar zamantakewa da sauran ma’amaloli a tashar mota a garin Sakkwato.

Aron Kalmomi

Masana da dama sun bayyana ra’ayoyinsu a kan abin da ake nufi da aro a harshe. Daga cikinsu akwai Sapir (1921:23) da Bargery (1934:34) da Garba (1977:33) da Imam (1978:27) da Rufa’i (1979:33) da Kabir (2004:65) da Yakasai (2005: 2, 3) da CNHN (2006:18-19) da Chamo (2011:27) da Umar da Shehu (2017:13) da Umar (2019:62) da Rufa’i (2021:3) da kuma Yakasai (2023:280). La’akari da ma’anonin masanan za a iya cewa, ana aron kalma ta ɗaya daga cikin hanyoyi uku; ko dai ta fuskar cikakken aro (wato aro kalma tare da lafazinta da ma’anarta) ko ta fuskar yi mata kwaskwarima ko kuma a aro lafazin kawai.

Aro daga wasu Sassan Harsuna a Hausar ‘Yan-tashar Sakkwato

‘Yan-tashar Sakkwato suna amfani da dabarar aron kalmomi daga wasu Harsuna da suka haɗa da harshen Larabci da Ingilishi da Fulatanci da Zabarmanci da kuma harshen Yarbanci.

1. Aron Kalmomi daga Harshen Larabci

Harshen Larabci yana ɗaya daga cikin harsuna iyalan Afro-Asiya wanda ya ƙunshi harshen Larabci da Hibru da Aramaik da Ƙurdish da Berber da dai sauransu. Fagge (2004:25) ya nuna tun a shekara ta 1194-1294 Larabawa suka zo ƙasar Hausa domin kasuwanci da yaɗa addinin Musulunci. Sakamakon haka, ya haifar da cuɗanya mai yawa ta hanyar koyon addini da saye da sayarwa tsakanin Larabawa da Hausawa. Harshen Larabci ya yi tasiri har a cikin Hausar tashar mota a garin Sakkwato. Daga cikin ire-iren waɗannan kalmomin Larabci da ‘yan rukunin suka aro akwai:

Jadawali na 1. Misalan Kalmomin Aro Daga Larabci

m

Kalma

Ajin Kalma

Tushen Kalma

Sabuwar Ma’ana a Hausar Tashar Mota

1.                   

Sáahíbúl-sáfár

Suna

مسافر

Fasinja wanda ya zo cikin tasha za ya yi tafiya

2.                   

Láabá’ásà

Suna

لابئس

 

Direban mota na cikin tasha wanda ba ya kulawa da wasu ‘yan gyare-gyare ƙanana, waɗanda kan iya haifar da babbar matsala ga motarsa

3.       

Háràamún

Sifa

الحرام

Kuɗin balas waɗanda direba yake bayar wa ga mai mota bayan kowane wata. Wato waɗanda ake kula da mota ko sake saya ma direba wata motar idan ta tsufa ko lokacin inshora ya ƙare da su

4.       

Káulàasân

Suna

الكاف

Rashin tsaya wa da wasu direbobi suke yi a cikin daji, domin su taimaka wa wani direba da matarsa ta samu matsala

5.       

Mádíinà

Suna

المدينة

Arewacin Nijeriya, inda ake bin tafarkin addinin musulunci

 

Háràamún: dangantakar ma’ana ta asali da subuwar ma’ana ita ce, ta fuskar aikinsu. Wato samun hukunci mai taɓa zuciya.

Mádíinà: dangantakar ma’ana ta asali da sabuwar ma’ana ita ce, ma’anonin sun yi maganar gari ko muhalli ko wurin zama.

Sáahíbúl-sáfár: dangantakar ma’ana ta asali da sabuwar ma’ana ita ce, duk suna bayyana wasu mutane da za yi tafiya.

2. Aro daga Harshen Ingilishi

Harshe.3n Ingilishi yana ɗaya daga cikin harsuna iyalin gidan Indo-European. Kalmar Ingilishi kwaskwarima ce daga kalmar Turanci ta ‘English’ kuma harshe ne na Turawan Ingila (Hornby, 2000:206). Turawan yamma sun shigo ƙasar Hausa a lokuta mabambanta domin cim ma wasu manufofi. Sidi (2023:27-37) ya bayyana Turawa sun shigo ƙasar Hausa a karon farko domin leƙen asiri da manufar gano irin tarin arzikin ma’adanai da Allah ya azurta yankin da shi. Akwai kuma waɗanda suka shigo domin yaɗa addinin Kirista da kuma waɗanda suka shigo da nufin mulkin mallaka. Daga cikin ire-iren kalmomin Ingilishi da ‘yan rukunin tashar mota suke amfani da su akwai:

Jadawali na 2. Misalan Kalmomin Aro Daga Ingilishi

 

Kalma

Ajin Kalma

Tushen Kalma

Sabuwar Ma’ana a Hausar Tasha

6.

Àláabúkúu

Suna

 

Yaron mota mai shaye-shaye

7.

Ângùul

Suna

Angle

Ƙarhen sama da ake yi a saman mota domin ɗaukar kaya masu nauyi sosai, (wato babban lodi)

8.

Búkîn

Suna ɗan aikatau

Bucking

Sa mota layin lodi a cikin lis tun kafin ta iso (Wannan kuma wata cuwa-cuwa ce da ake ƙulluwa tsakanin direba da ɗankamisho mai wannan aiki)

9.

Câmbàa

Suna

Chamber

Ofishin ƙungiyar direbobin cikin tasha

10.

Dáawùn

Suna

Down

Kuɗin fita daga tasha, waɗanda ake bayar wa ga ƙungiya mai kula da tsaftar cikin tasha

11.

Dísfíláa

Suna

Discipler

Alƙalin tasha, wanda ake kai wa koken wata matsala domin a warware

12.

Dóojìn

Suna ɗan aikatau

Dodging

Fasinja da ba ya biyan kuɗinsa na tafiya sai mota ta cika, don ka da a ɓata masa lokaci. Da zarar ya fahimci babu fasinja, sai ya wuce zuwa wata tashar, ko kuma ya tsaya a kan hanya ya jira direbobi ‘yan haɗa-haɗa

13

Dìròs

Suna

Drugs

Jami’an hana sha da fataucin ƙwayoyi, waɗanda suke tsaya wa a hanya

14

Ésbîn

Suna ɗan aikatau

Eɗ being

Saƙo mai hatsari, wanda kan iya saka masu ajiyar kaya cikin wata babbar matsala. Kamar ƙwaya ko hodar ibilis

15

Éskút

Suna ɗan aikatau

Escort

Rakiyar da ɗan kamisho yake yi domin ya karɓi sallama daga direba

16

Fàatìròl

Suna ɗan aikatau

Patrol

Yawon da shugabannin ƙungiyar yuniyon suke yi, don hana direbobin da ba su bin layi a tasha ɗaukar mutane a kan hanya

17

Fíi’è

Suna

P. A

Yaron mota mai zama a ƙofar mota domin kula da shige-da-ficen fasinja

18

Fúlóogùu

Suna

Floogoo

Jigon tasha, dattijo mai shekaru wanda ake girmama wa a cikin tasha

19

Hózíláa

Suna

Hosler

Direban da ba ya hutu, wanda kodayaushe yana kan hanyar tafiya

20

Káagòo

Suna

Cargo

Lodin da ake yi wa mota na kayayyaki a sama da ƙasanta

21

Kwámándáa

Suna

Commandant

Shugaban ‘yan kamisho

22

Kófúràa

Suna

Corpral

Mai tsaron mashina na ƙofar tasha

23

Léebúr

Suna

Lebel

Direba mai gudu sosai, wanda kan haddasa hatsari a hanya

24

Máakàa

Suna

Marker

Ɗan kamisho mai rubuta sunan direbobi a layin lodi

25

Máajàa

Suna ɗan aikatau

Marger

Haɗe fasinja na mota biyu a cikin mota ɗaya, musamman idan wata ta samu matsala a hanya

26

Mís

Suna sifantau

Miɗ

Tsohuwar mota, akwala wadda ba ta da ƙarfi ko lafiyar yin doguwar tafiya

27

Nétìwòk

Suna

Network

Direban da ke yawace ƙasa baki ɗaya, wato kowace jiha yana tafiya (Bisa al’adar direbobin mota, kowane direba da irin garuruwan da yake tafiya waɗanda ya yi sabo da su har ake alaƙanta shi da sunansu kamar Ɗan kano ko Ɗan Kaduna)

 

Ângùul: dangantakar ma’ana ta asali da sabuwar ma’ana ita ce, bayyana wani bagire ko muhalli.

Búkîn: dangantakar ma’ana ta asali da sabuwar ma’ana ita ce, ta fuskar aikinsu, wato kama layi ko shiga layin jiran wani abu.

Dísfíláa: dangantakar ma’ana ta asali da sabuwar ma’ana ita ce, ladabtarwa da tabbatar da bin doka da oda.

Dóojìn: dangantakar ma’ana ta asali da sabuwar ma’ana ita ce, ta fuskar aikinsu.

Éskút: dangantakar ma’ana ta asali da sabuwar ma’ana ita ce, ta fuskar aikinsu, wato daga rakiya.

Fàatìròl: dangantakar ma’ana ta asali da sabuwar ma’ana ita ce, ta fuskar aikinsu, wato daga zagaye don kama mai laifi.

Fíi’è (P.A): dagantakar ma’anonin ita ce, ta fuskar aikinsu. Wato hidimar da wani yake yi don taimakawa wani mutaum.

Fúlóogùu: dangantakar ma’ana ta asali da sabuwar ma’ana ita ce, ta fuskar aikinsu, wato daga tasiri a kan wani abu.

Hózíláa: dangantakar ma’ana ta asali da sabuwar ma’ana ita ce, ta fuskar aikinsu, wato daga neman na kai wurjanjan.

Káagòo: dangantakar ma’ana ta asali da sabuwar ma’ana ita ce, ta fuskar aikinsu, wato daga ƙarfin iya ɗaukar kaya masu yawa.

Kwámándáa: dangantakar ma’ana ta asali da sabuwar ma’ana ita ce, ta fuskar aikinsu, wato jagoranci ko ikon sa wa da hana wa.

Kófúràa: dangantakar ma’ana ta asali da sabuwar ma’ana ita ce, ta fuskar aikinsu, wato daga tsaron kayan al’umma.

Máakàa: dangantakar ma’ana ta asali da sabuwar ma’ana ita ce, ta fuskar aikinsu, wato daga rubutu..

Nétìwók: dangantakar ma’anonin ita ce, kamar yadda kimiya ta netiwok na sadarwa yake game ko’ina, haka direban yake zagaye ƙasar nan domin kai fasinjoji garuruwansu.

3. Aro daga Harshen Fulatanci

Harshen Fulatanci harshe ne iyalin gidan Niger-Congo. Masu magana da shi ake kira Fulah a ƙasashe irin su Mali da Senigal da Gambiya da Guinea da Guinea-Bissau. Ana kuma kiran su Fulani a Nijeriya da Nijar. Duk da yake harshen Hausa shi ne harshe mafi girma da ake magana da shi a cikin garin Sakkwato, harshen Fulatanci ya zama na biyu (Kokoshe, U. 07/01/2025). Fagge (2004:20) yana da fahimtar lokacin da Haɓe suke mulkin ƙasar Hausa Fulani suna zaune a rugogi, sai dai ba su cusa kansu cikin harakokin mutanen wurin ba. A kwana a tashi sai addinin Musulunci da ƙasaitar sarakunan Hausa ta sanya cuɗanya tsakanin waɗannan mutane da Hausawa. A dalilin haka ne Hausawa suka samu damar aro waɗansu kalmomin Fulatanci suka mayar da su na Hausa. Ga wasu misali, akwai:

Jadawali na 3.  Misalan Kalmomin Aro Daga Fulatanci

 

Kalma

Ajin Kalma

Tushen Kalma

Sabuwar ma’ana a Hausar Tasha

28.

Árɗóo

Suna

Arɗo

Shugaban ƙungiyar direbobin cikin tasha

29

Dèesá

Suna ɗan aikatau

Deysa

Ajiyar kaya a cikin tasha

30

Fíllèrí

Suna

Feelire

Sunan tashar mota

31

Jáhò

Suna ɗan aikatau

Jahoo

Tafiya mai nisa wadda ta kai zuwa wata jaha

32

Ján Héeɗí

Suna

Jaheeɗi

Masu satar mutane a hanya

33

Jéháiɗò

Suna

Jahoo

Fasinja mai jiran mota a hanya 

34

Jífìnò

Suna ɗan aikatau

Jifinol

Aikin dako da wasu suke yi a cikin tashar mota domin neman abinci

35

Lílál

Suna

Lilall

Saƙon kaya waɗanda ba su da yawa da za a tafi da su zuwa ga wani wuri

36

Sírbáajóo

Suna

Surbajo

Fasinja ƙaramar yarinya

 

Árɗóo: dangantakar ma’ana ta asali da sabuwar ma’ana ita ce, ta fuskar aikinsu, wato jagoranci.

Dèesá: dangantakar ma’ana ta asali da sabuwar ma’ana ita ce, ta fuskar aikinsu, wato ajiye wani abu. 

Jéháiɗó: dangantakar ma’anonin ita ce, duk suna nufin mutumin da ya zo tashar mota da nufin tafiya zuwa wani wuri. Ma’ana ta gama-gari tana nufin kowane irin matafiyi, ba tare da bambance wa ba.

Lílál: dagantakar ita ce, dukkan ma’anonin sun shafi aike daga tashar mota ko kasuwa zuwa wani wuri. Ma’anarta wadda sauran jama’a Fulani suke ba ta ita ce, tana nufin bayar da sautun wani abu a kasuwa (Mayanci, B.M. 06/09/2024).

4. Aro daga Harshen Zabarmanci

Harshen Zabarmanci shi ne ake kira Zarma. Harshen yana ɗaya daga cikin harsunan kudancin Songhai a cikin iyalin gidan Nilo-Sahara. Zarma harshe ne da aka samu masu magana da shi sosai a wasu ƙasashen Arewa masu yammacin Afirika kamar Nijeriya da Nijar. Jamhuriyar Nijar ƙasa ce da ta yi iyaka da jahar Sakkwato da take Nijeriya, ta garuruwan Illela da Tangaza da Gudu da kuma Gada. Bugu da ƙari, Sadiƙ (2019:13) yana ganin tasirin hulɗar kasuwanci da auratayya da take aukuwa tsakanin al’ummomi biyu takan haifar da aron wasu kalmomi domin ambaton wasu baƙin abubuwa da suka ci karo da su. Daga cikin waɗanda ake amfani da su a tashar motar garin Sakkwato akwai:

Jadawali na 4.  Misalan Kalmomin Aro Daga Zabarmanci

 

Kalma

Ajin Kalma

Tushen Kalma

Sabuwar Ma’ana a Hausar Tasha

37.

Báazùm

Suna

Báazùm

Direban Nijar

38.

Màtánóo

Suna

Màtánóo

Mai ajiyar kaya na cikin tashar mota

39.

Tìisámbèeríi

Suna

Tìisámbèeríi

Gama-garin sunan tashar mota

40.

Tíyáanìi

Suna

Tíyáanìi

Gma-garin fasinja

 

Tìisámbèeríi: dangantakar ma’ana ta asali da sabuwar ma’ana ita ce, duk suna nuni ga wurin ajiye motocin hawa, don haya ko jigila.

Tíyáanìi: dangantakar ma’ana ta asali da sabuwar ma’ana ita ce, dukansu sunaye ne da ake kiran wani mutum da shi.

5. Aro daga Harshen Yarbanci

Yarbanci harshe ne na ɓangaren Volta-Niger iyalan harsunan Niger-Congo. Al’ummar Yarbawa suna daga cikin baƙin mutane mazauna babban birnin Sakkwato. Cuɗanya tsakaninsu da al’ummar Hausawa a garin ta yi tasiri matuƙa. Fagge (2004:22) ya bayyana Yarbanci wani harshe ne da ake amfani da shi wajen hulɗa tsakanin mutane kuma waɗanda suke magana da shi su ake kira Yarbawa. Ga misalan wasu daga cikin kalmomin da ake amfani da su a tashar motar garin Sakkwato kamar haka:

Jadawali na 5.  Misalan Kalmomin Aro Daga Yarbanci

 

Kalma

Ajin  Kalma

Tushen Kalma

Sabuwar Ma’ana a Hausar Tasha

41.

Áríirí-áajóo

Harɗaɗɗen suna

Áríirí-áajóo

Fasinja

42.

Áwáakòo

Suna

Áawáakòo

Direban mota na cikin tasha

43.

Fíifíifáanóo

Suna

Fíifíifáanóo

Masu ajiyar kaya na cikin tasha

44.

Íbúutíi

Suna

Íbúutíi-ókóo

Sunan tashar mota

45

Ísérírán

Sifa

Ísérírán

Saƙon kaya waɗanda ba su da yawa da za a tafi da su zuwa ga wani

46

Tíníbù

Suna

Tùníbù

Man fetur

 

Íbúutíi: dangantakar ma’ana ta asali da sabuwar ma’ana ita ce, duk suna nuni ga wurin ajiye motocin hawa, don haya ko jigila.

Tíníbù: dangantakar ma’anar kalmar asali da sabuwar ma’ana ita ce, cire tallafin man fetur da tsadar rayuwa.

Kammalawa

A wannan takarda an yi nazari tare da fito da irin yadda rukunin jama’ar tashar motar garin Sakkwato suke sarrafa kalmomin aro a cikin sadarwarsu. Inda aka fito da wasu kalmomi daga wasu harsuna a cikin jadawali, aka kawo ma’ana ta asali da sabuwa, sannan daga bisani aka yi fashin baƙin wasu daga cikinsu don a nuna alaƙar da ake samu tsakanin ma’anonin biyu.

Daga cikin da sakamakon da takardar ta gano sun haɗa da:

1.   Takardar ta gano cewa, ‘yan rukunin suna amfani da wasu kalmomi a cikin Hausarsu, waɗanda ba kowa yake iya fahimtar ma’anoninsu ba kai-tsaye.

2.   Haka kuma, takardar ta gano cewa, ‘yan rukunin suna sarrafa kalmomin aro daga wasu baƙin harsuna a cikin sadarwarsu.

3.   Bugu da ƙari, takardar ta gano ‘yan rukunin suna amfani da dabarar sarrafa kalmomin aro  don ambaton direbobi da yaran mota da ‘yan kamasho da ‘yan dako da fasinja da tashar mota da motoci da jami’an tsaro, ko kuma don bayyana wani hali da suka tsinci kansu a cikin tasha ko a halin tafiya.

Manazarta

Abbas, Y. (2012). Hausar Masu Ƙwallon Ƙafa a Garin Katsina. Kundin Digiri Na Biyu. Jami’ar Bayero.

Bargery, G.P. (1934). A Hausa-English Dictionary and English-Hausa Ɓocabulary. Ahmadu Bello University Press Limited.

Bature, A. (1995). Nazari kan Ƙirƙira Sababbin Kalmomi a Hausa. 5th Intertional Conference on Hausa Language, Literature and Culture. CSNL. Bayero University.

Bature, A. (2002). Nazari kan Ƙirƙirar Sababbin Kalmomi a Hausa. In Bichi, A.Y, Yalwa, L.D, Hausa, A.U.K (Eds.). Studies in Hausa Language, Literature And Culture. (5th ed., 129-146). Kano: Benchmark Publishers Limited.

Bello, A.K. (2021). Kwatancen Ƙwayoyin Ma’ana a Ƙirar Kalmar Hausa da Fulfulde. Unpublished M.A. Hausa Dissertation. Department of Nigerian Languages. Usmanu Danfodiyo University.

Chamo, I.Y. (2011).Language and Identity: Hausa Language of Youth Generation in Northern Nigeria. Studies of the Department of African Languages and Cultures, University of Warsaw, Poland, 45, 23-38.

CNHN. (2006). Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero. Ahmadu BelloUniversity Press.

Fagge, U.U. (2004). Ire-iren Karin Harshen Hausa na Rukuni. Benchmark Publishers Limited.

Garba, A.B. (1977). Nazari  a kan Ararrun Kalmomin Hausa Daga Larabci.  Unpublished B.A Hausa Project. Department of African Languages and Culture. Ahmadu Bello University.

Harris, Z.S. (1952). Discourse Analysis. Language, 28, 1 – 30

Hornby, A.S. (2000). Oɗford Adɓanced Learner’s Dictionary. Oɗford University Press.

Imam, B.B. (1978). Ɗafi a Ararrun Kalmomin Hausa a Harshen Kambari. Unpublished B.A Hausa Project. Department of Nigerian Languages. University of Sokoto.

Isah, F.H. (2018). A Sociolinguistic Analysis of The Jargons Used by Town Serɓice Tricyclists (A-daidaita-sahu) in The Kano Metropolis. Unpublished M.A Dissertation. Department of Liguistics. Bayero University.

James, G.P. (1991). An Introduction to Discourse Analysis: Theory and Method. London: Electronic Media Diɓision of Bloomsbury Publishing Plc.

Janos, P.S. (1971). Transformations Grammatiken and Eine Ko-Teɗtuelle Teɗt Theories. Frank Furt Publishers. Athenaeum: Germany.

Joseph, G.E. (1975). The Thread of Discourse. Paris: Hague Mouton Press.

Kabir, B.U. (2004). Nazari a kan Hausar Mata Matasa a Cikin Garin Kano. Kundin Digiri na Biyu. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Jami’ar Bayero.

Knapp M. & Daly J. (2002). Hand Book of Inter Personal Communication (3th Ed., 102-129). Sage Global Academic Publishers. U.S.A: New Bury.

Mode, A. (2024). Nazarin Hausar ‘yan Koli a Garin Sakkwato. Kundin Digiri na Biyu. Sokoto: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Newman, P. & Newman, R. (2020). Hausa Dictionary: Hausa-English/ English-Hausa. Kano: Bayero Uniɓersty Press.

Rabi’u, A.M. (2019). Tasirin Harshen Larabci a kan Hausa. Unpublished M.A Hausa Dissertation. Department of Nigerian Languages. Usmanu Ɗanfodiyo University.

Rufa’i. A. (1979). Principal Resouces of Leɗeme-formation in Hausa. Unpublished B.A. Hausa Project. Nigerian Languages Department. Bayero University.

Rufa’i, A. (2021). Aron Kalmomin Ingilishi Cikin Hausa a Ƙarni na 21: Nazari a Ma’aunin Ilimin Walwalar Harshe. Unpublished M.A. Hausa Dissertation. Department of Nigerian Languages. Usmanu Danfodiyo University.

Sadiƙ, F.Y. (2019). Tasirin Hausa a kan Zabarmancin Bankanu ta Fuskar A ro. Unpublished M.A. Hausa Dissertation. Department of Nigerian Languages. Usmanu Danfodiyo University.

Sani, M.M. (2019). Matsalolin Furuci ga Ibo da Yarbawa Majiya Harshen Hausa. Unpublished m.A. Hausa Dissertation. Department of Nigerian Languages. Usmanu Danfodiyo University.

Sapir, E. (1921). Language: An Introduction to the Study of Speech. New York, Harcourt, Bruce and Company.

Sharu, Y. (2023). Hausar ‘yan Agwagwa-da-buje a Garin Sakkwato. Kundin Digiri na Biyu. Sokoto: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

Sidi, M. (2023). Bature a Idon Marubuta Waƙoƙin Hausa. Unpublished M.A Dissertation. Department of Nigerian Languages. Usmanu Danfodiyo, University.

Teun, A.Ɓ. (1972). Some Aspects of Teɗt Grammar. A Study in Theoretical Linguistics and Poetics. The Hague: Mouton.

Teun, A.Ɓ. (1977). Teɗt and Conteɗt. Eɗplorations in the Semantics and Pragmatics of Discourse.  NewYork: Longman.

Tom, G. (Ed.) (1979). Syntaɗ and Semantics. Vol. 12: Discourse and Syntaɗ. New York: Academic Press.

Umar, M.M. da Shehu, M. (2017). Aro da Ƙirƙira: Nazarin Samuwar Sababbin Kalmomin Kimiyya a Hausa. YOJOLLAC: Yobe Journal of Language, Literature and Culture, 5, 11-19.

Umar, M.M. (2019). Nazarin Hausar Wasu Rukunan ‘Yankasuwa a Garin Sakkwato. Kundin Digiri Na Uku, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Jami’ar Usamanu Ɗanfodiyo.

Yakasai, S.A (2005). Aro da Ƙirƙira: Nazarin Samuwar Sababbin Kalmomin Hausa a Jami’a da Kuma Garin Sakkwato. Maƙalar da Aka Gabatar a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Yakasai, S.A. (2020). Jagoran Ilmin Walwalar Harshe. Amal Printing Press.

Yakasai, S.A. (2023). Aro da Ƙirƙira a Hausa. Amal Printing Press.

Zailani, A.A. (2019). A Study of Communication Strategies in Hausa Reƙuest Act. Ph.D. Thesis. Department of Linguistics and Foreign Languages. Bayero University.

 Dundaye Journal

Post a Comment

0 Comments