𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam mene ne hukuncin wanda yake wasa da azzakarinsa maniyyi ya fito? Ko Kuma matar da take sanya yatsa a cikin farjinta? Malam gaskiya Allah ya jarrabe ni da wani halin wasa da gabana lokacin da na ji sha'awa takamani. Yau nakai shekara biyu ina yinsa Na yi kokarin dainawa daga nadaina kwana biyu zan koma.

𝐀𝐌𝐒𝐀

Alal-Haƙiƙa wannan wata Mas'alace da ana iya cewa ta yawaita sosai awannan zamanin, musamman tsakanin Samari da 'Yammata, harma da Matan-Aure da kuma Mazan-Aure.

Yin haka bai halatta ba kuma yana daga cikin manyan laifiu a musulinci. Yana janyowa mai yin hakan fushi da kuma tsinuwa daga ubangiji ( S.W.A).

Ibnu Katheer Rahimahullah ya ce Imamush-Shafi'i da waɗanda suka goyi bayansa ya kafa hujja da haramcin wasa da gaba da faɗin Allah maɗaukakin Sarki:

وَالَّذِينَ هُمْ لِفُرُوجِهِمْ حَافِظُونَ ۝ إِلَّا عَلَىٰ أَزْوَاجِهِمْ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُمْ فَإِنَّهُمْ غَيْرُ مَلُومِينَ ۝ فَمَنِ ابْتَغَىٰ وَرَاءَ ذَٰلِكَ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الْعَادُون

Bayin Allah nagari Sune waɗanda dangane da farjinsu suke kiyayeshi. Face a kan matan aurensu, ko kuwa abin da hannayen damansu suka mallaka (kuyanginsu) to lalle sũ ba waɗanda ake zargi ba ne. Saboda haka wanda ya nemi abin da ke bayan wancan, to, waɗancan sũ ne masu ƙetarewar haddi. (Suratul Mũminun 5-7)

Imamush-Shafi'i a cikin littafin Aure ya ce sai ya kasance Allah ya bayyana kiyaye farjin su sai fa a kan matayen su ko abin da damar su ta mallaka, sai ya zama haramun idan ba matar ka ba ce ko kuyangar ka sai Allah ya karfafi maganar da cewa " wanda ya nemi koma bayan hakan yana cikin masu taka dokokin Allah"

Bai halatta amfani da azzakari ba sai a kan matar ka baiwar ka, bai halatta jin daɗi da shi da hannu ba wallahu A'alamu kitabul ummu na imamu shafi'i.

A Sunnah kuwa sun kafa hujja da hadisin Abdullahi dan mas'ud Yardar Allah ta kara tabbata a gare shi yace: Mun kasance tare da Annabi sallallahu Alaihi wasallam muna samari ba mu samu komai ba sai Annabi sallallahu Alaihi wasallam ya ce damu "ya ku taran samari duk wanda ya samu halin ɗaukar dawainiyar iyali ya yi aure, domin ya nasa kamewa daka gani, yana kuma tsare farji, wanda kuma bai samu dama ba to na hore shi dayin azumi domin azumi yana kariya daka faɗawa haram. Bukhari 5066.

Sai shari'ah ta shiryar lokacin da mutum ya gajiya wajen yin aure sai ya dunga azumi domin azumi yana kariya daka faɗawa haram. Bukhari 5066.

Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana cewa "Mutum bakwai, Allah ya tsine mu su. Kuma ba zai dube su da rahama ba ranar al-ƙiyamah. Zai ce mu su Ku shiga wuta tare da masu shigar ta:

1. Wanda yake yin luwaɗi

2. Wanda ake yin Luwaɗin da shi

3. Mai yin zina da dabbobi

4. Mai yin zina da Uwa/Mahaifiya

5. Mai yin zina da 'yar ta

6. Mai yin zina da hannayensa (wato mai yin wasa da azzakarinsa da kuma....

7. mace mai yin hakan ga al'aurar ta)

sannan shi kuma wannan aiki yana daga cikin irin laifukan da mutanen Annabi Lut ( A.S) suka aikata. Sannan kuma an Ruwaito cewar duk masu yin hakan idan har basu tuba ba. za su tashi a ranar al-ƙiyamah Hannayen su ɗauke da ciki ( wato juna biyu)

Sannan kuma Likitoci masu ilimin sanin lafiyar jikin Bil-adama sun fadi wasu illoli da dama wadan da yin hakan yake haifarwa:

1. Zai sa Gabanka Ya Koma Ɗan Karami Kamar Na Kananan Yara. Ko da daga baya idan kayi Aure. Ba za ka iya Cika Mace Ba. Sabida Jijiyoyin Wannan Gaban Naka za su Saki. za su Sami Disfunction.

2. Zai ɗauke Maka Karfin Sha'awar da Allah ya Halicceka Akan ta. za ka zama Baka da wani Sha'awa Na Mace. Duk ka tafiyar da Sha'awarka kai kaɗai.

3. za ka Sami Ƙuick Release. Ma'ana Saurin Kawowa. Idan kayi Aure Ba za ka iya Gamsar da Matarka ba. Domin Nan da nan za ka ke Kawowa, ko Second Ukku Ba za ka iya yi ba. Daga nan Kuma ka Gama. Domin Ba za ka iya Komawa Ga Matarka ba. Wanda a Dabi'a Ansa Namiji da Komawa na biyu wani ma har na Ukku. Sabida Faɗin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam inda yake Cewa idan ɗayanku ya biya bukatarsa ga matarsa, sannan yake nufin zai sake komawa karo na biyu, sai ya yi alwala bayan karo na farko ɗin, kafin ya koma ba biyun. Malamai Suka Ce, Sabida Hakan Yana samarwa Namiji Nishaɗi. Ka Gwada ka Gani. za ka Tabbatar da hakan In sha Allah.

4. Lalataccen Maniyyi zai Daskare maka a Cikin Mararka. A haka zakake ta yawan ciwon Mara. Domin Wannan Maniyyin da yake fitowa da Daidai lokacin da kake yin Istimna'in Domin Biyan Bukatar Kanka da kanka, baya Fita Gabaki ɗaya, Sannan Kuma Ba zai Koma Asalin inda Aka Halicceshi ba. Sabida haka ke nan Zai Tsaya Maka a Mararka. Sabida haka zai Baka Matsala ba Karama ba.

5. Rashin haihuwa: wannan daskararren maniyyin yana kashe kwayoyin halitta daga jikin Namiji ko Mace.

6. Mantuwa mai tsanani ( mantuwar karatu e.t.c)

7. Raunin idanu masu yin hakan idan basu daina ba, suka makancewa kafin wani lokaci mai nisa.

8. Ciwon hauka da Kuma kaskanci.

Wannan kaɗan na tsakuro daga cikin irin illolin da yake haifarwa. A jikin Namiji ko Mace.

Duk wanda ya saba Aikata Irin wannan Al'amari yana tattare da waɗannan Matsalolin da na Ambato. Kuma Tabbas Sai Bayan Aure Mutum zai Tabbatar da Waɗannan Abubuwa da na Lissafo Su. Sabida haka idan har baka yi Nisa ba. To Kayi Gaggawar Denawa. Shi ne Abin da Ya fi Alkairi a gareka. Tin kafin ka Tsinci kanka Tattare da waɗannan Matsaloli da na Kawo.

Allah Shi ne Masani.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

 

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam