Fiddausi Musa (2020). A Yankinmu. Muhalli, Sutura (Labaran Da Suka Samu Nasara a Gasar Gajerun Labarai a Kan Muhalli Ta Arc. Ahmed Musa Dangiwa, 2020). Darma Digital Prints.
A
YANKIN MU
Na
Fiddausi
Musa
GIDAN HAYA
Nan take raina ya yi mummunan ɓaci, wasu
hawaye masu ɗumin gaske suka soma sintiri saman kunci na.
“Kaico.! Na faɗa a fili, na janyo haɓar zani
na share hawaye.
A raina nake tunani,
Shikenan a haka zan
cigaba da rayuwa babu wani ɗan uwana da zai tako ya zo wurina mu sada
zumunci? Sai ace babu wanda zai zo wurina ya ƙwana don
taƙamar muna zaune a gidan haya mai ɗaki ɗaya tilo? Shin aƙwai wanda ya taɓa
zuwa na
ce mashi ban
da inda zan aje shi
ya kwana? Koko sun yanke hukunci ne
da hasashe? In kuwa
haka ne ba'a yi mani adalci ba domin ina buƙatar inga nawa in ji daɗi.’’
A take na janyo wayar tarho na danna lambar
yaya Hadiza. Bugu ɗaya ta ɗauka ta rangaɗa
sallama.
Ban amsa mata sallamar ta ba, cikin ɓacin
rai na soma faɗin "Yanzu fisabillillah yaya Hadiza kin kyauta? Shekara
nawa bamu haɗu ba? Amma a
ce ki shigo Nijeriya
sai dai in ji gurin Inna har kin koma?"
Ta tausasa murya
tace, "Haba Batula
kin
san dai babu yadda
za
a
yi inzo garinku in
koma a ranar, tafiya ce mai ɗan karan nisa tsakanin Jibia a zuwa Kaduna.
Na ƙara harzuƙa
"Dole ne sai kin koma a ranar?
Idan kika kwana wajena laifi
ne.?
"In kwana
a ina Batula? Dan
Allah ki rufa ni ki sakaya! Ina ce ɗakin
ɗaya ne a gidan? kuma Inna ta ce
daga ke har ɗiyanki da mijin ki a nan
kuke kwana."
Na yi tsit na kasa cewa komai, ya yin da
hawaye suka cigaba da bin saman kuncina, ke nan daga ni sai yarana ake so mu yi
rayuwa?
Muryarta na tsinkaya tana tambayata "Ya
jikin Ahmadun? Inna ta ce
bai ji ɗadi ba."
"Da sauki."
"To Allah ya daɗa sauƙaƙawa Batula, insha
Allahu idan na dawo zan ƙumo safko inzo in ganki ko da sa’a ɗaya ne, sai
in koma, kuma ban
da
abun ki ai Inna ta ce tsohon ciki ne da ke, kin ga dole idan kin haihu in
zo."
A sanyaye na ce “Allah ya
kaimu."
Shigowar Sailuba riƙe da ciki sai murɗe-murɗe
take ya sa na yi sallama da ita tare da yanke wayar ina
tambayarta "lafiya Sailuba.?
Muryarta na rawa ta
ke faɗin "Mama
bahaya nake ji, wallahi kamar zai
kubto.’’
Na rafka mata harara "Sai akayi ƙaƙa?
"Naje makewayi na tarad da shaddar ya daɗa
cika, ga tsutsotsi a sama suna yawo babu inda zan raɓa in tsugunna." Ta
ƙarashe maganar ta kamar za ta
yi kuka.
Na miƙe na durfafi madafi, na ɗebi toka na je
na watsa ma shaddar, na rungume hannuwana ina jiran ya lafa in
ce ta shigo ta
yi.
Ganin bashi da alamun lafawa ya sa na fito ina
faɗin "Zo ki ɗauki leda ki shiga ciki ki raɓa bakin ƙofa kiyi, idan kin
gama ki ƙulle sai ki yar bayan gida kafin Baban ku ya dawo a san yadda za
a
yi."
Na juya na koma ɗaka da
tunani barkatai a zuciya.
Ko da Babansu
ya
dawo na sanar da shi halin da ake ciki,
sai ya soma hargowa yana faɗin "To ni ya zanyi Batula? Kina dai gani a gabanki
na kira mai gidan nan tun kwanaki
na faɗi ma shi shadda ta cika,
maimakon ya aiko a ƙwashe amma don rashin daraja sai ya aiko mani da wata baƙar
hoda yace a zuba ya lafa."
Na kalleshi cike da takaici "Kai ba za
ka
iya kiran masu ƙwasar ba, su ƙwashe mana ba.?
"Wa? Raba ni da zubama ungulu ƙwan zabuwa! Kawai
ku cigaba da yin abunku a leda, tunda dududu baifi sauran mako biyu ba mu bar
gidan." Ya faɗa kai tsaye.
Cikin mamaki na tambaye shi "Kenan baka
biya shi kuɗin shi ba.?
"Zan bashi babu ne
Batula.?
Ban ƙara cewa komai ba na miƙe tsam na bar
ma
shi ɗakin. Allah ya
sani na fara gajiya da wannan gantalallar rayuwar! Na ja siririn tsaki ina
ƙoƙarin tsaida hawayen da ke niyyar suɓuce mani.
***
Washegari da hantsi ina zaune tsakar gida ina
tsintar shinkafa sai ga Safara'u maƙwabciyar mu ta shigo kamar an
jeho
ta, ta ja kujera ta
zauna haɗe da miƙe ƙafafu tana faɗin "Maman Ahmad zuwa nayi ki lallaɓe
mani kai. "
"To ki ɗan yi hakuri
in ƙarashe tsintar
shinkafar tukun."
Ta kalli Sailuba dake tsugunne bakin magudanar
ruwa tana wanke-wanke,
ta juyo ta dube ni "Ni kam me ke hana Sailuba zuwa makaranta Batula? Allah
shi sa ba hidimar gida ba?
Na waiga na kalleta, na ƙaƙalo murmushin yaƙe
" An kai ta nan firamari da ke kusa da mu,
shugaban makaranta ya ce ba zasu amsheta ba, saboda suna tsakiyar
zango ƙarshen na karatu, sai dai mu jira idan an shiga sabon zango.
"
Ta riƙe haɓa " Kai jama'a! Batula ba
ku san an yi hutu ba
har an koma sabon zango. ?
A sanyaye na ce "Na sani! mun
dakata ne sai mun
koma wata unguwar, tunda a wannan watan kuɗin hayar mu ke ƙarewa, kin ga ko sun fara
zuwa dole a datse a canza wata."
"Asha! Shi
ya sa bana son yawon haya wallahi, ilmin yaranka a
gantale! wai ni kam ajin
ta
nawa.?
"Firamari aji biyu. "
Zunzurutun mamaki ya bayyana ƙarara a fuskar
ta, ta zaro ido waje "Na shige su! Aji
biyu ki ka ce?Ai na zaci a tare
suke da Mustafa
na
tun da sa’annin juna
ne."
Na girgiza kai "Shi ajin shi nawa.?
"Ajin ƙarshen"
Na ce" Eh da a ce babu canje-canje
makarantu da duk kusan tare suke, ita duk lokacin da muka sauya muhalli dole a
sauya masu makaranta mafi kusa damu, sannan mafi akasari sabuwar makarantar da
za a kai ta ba zasu ɗauke ta ajin da ta ke ba, sai sun maishe da ita baya."
" Asha! Allah ya kyauta.!
Shiru ya ratsa gurin na 'yan daƙiƙai kafin ta
numfasa ta ce mani, "ni kam Batula mai zai hana kiyi ma magidan ki magana
ya fara adashen gata da bankin bada lamanin gina gidaje.?
‘’Kayya ba zai yi ba! Ko kwanaki ya ce mijinki
ya ma shi maganar.’’
Ta gyara zamanta
"Saurara ki ji! Ki same shi ki masa magana, wata ƙil tunda ke
matar shi ce ya saurare ki.’’
Haka ta zauna ina mata
kitson tana yi mani bayani dalla-dalla game da banki.
Ko da Baban Ahmad ya dawo, na yi ma shi
gamsashen bayanin da Safara’u tayi mani tare da ba shi shawara a kan yaje ya buɗe
asusun, sai ya hau ni da faɗa ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, shi ba
zai je ya dinga zuba kuɗin shi banki ba tun da ba aikin gwamnati yake ba, shi
bai iya tattali ba? Idan ajiya yake so ai ya san inda ake siyar da asusu, ni
dai bance ma shi kome ba har ya ƙare faɗan shi, ya janyo kwanon tuwo ya soma
ci, sannan na kaɗa baki na ce "Ni zan iya buɗe asusun?
Ya yi watsi dani, na dube shi na ce , “Dan
Allah kayi ƙoƙarin biyan Alhaji Haladu kuɗin shi tun kafin yazo ya ci mana
mutunci."
"Ya jima bai zo ba!
Bani maganin ko anini, Alhaji Babba na ke jira ya shigo garin ya samman wani
abu.!
Tun da na ji haka sai na kama bakina na gumtse
na miƙe tsam na fita tsakar gida, na samu gefen tabarma na zauna na rafka
tagumi. Ji nake gaba ɗaya duniyar ta juya ma ni baya! Allah ya sa ni na gama
ƙosawa da halin shi, ba zai taɓa sauyawa ta ɗaɗin rai ba, ba zai taɓa miƙe wa
ya nemi sana'ar da zai dogara da kan shi ba, bare har ya mallaki muhallinsa, ya
gwammace ya sayi ƙatuwa wayar ya buɗe fesbuk, shi ne yabon wannan mai ɗan siya
san, ya koma ya zagi wannan, a bashi abun da bai taka kara ya karya ba.
Ga
yawon bin gidajen masu hannu da shuni maula, zuciya ta mutu, ba a san ayi aikin
ƙarfi ba a nemi na kai, da anyi magana zai fara faɗin DIGIRI gare shi! Aikin
gwamnati yake jira! Alhaji ya ce zai samo ma shi aikin banki, wane yace zai
samo ma shi sojan ruwa, da matakin farko ya fita.
A raina na ce
"DIGIRI ɗin ƙaniya! Ina amfanin ƙwalin da zai kashe ma
ka
da zuciya? Ina amfanin zaman jiran gawon shanu.?
Muryar Ahmadu naji yana faɗin "Mama kuka
kike.?
Baban su da ya fito wanke hannu ya yi karaf ya
ce da shi
"Kukan
daɗi ne Ahmad."
Bance ƙala ba har ya
gama ɗauraye hannun sa, ya matso kusa dani ya ce" Ki shigo ciki muyi
magana."
Ganin yaran suna kallon mu ya sa na koma ɗakin
na zauna bisa kujera ina kallon ƙofa, cikin lallami ya tambaye ni " Haba
Batula menene na ɓacin rai yanzu?
Na ce, “Dole raina ya ɓaci muddun ba za ka
sauya hali ba Jamilu, yanzu fisabilillahi ta ina ka nakasa da ba za ka iya
neman aikin ƙarfi ba ka huce ma kanka takaici? Amma kai kullun cikin jiran a
baka ka....’’
Ya dakatar dani “Ki ƙara hakuri, Alhaji
Abubakar ya ce, in jira shi, idan aka fara ɗaukar ma'aikatan banki zai saƙala
sunana, haba Batulata! Uwargidan Jamilu kuma amarya, ki ƙara ƙwantar da
hankalin ki, na maki alƙawarin da na fara aikin zan sayi ƙaton gida a unguwar
sarki."
`Nayi watsi da shi, ya kuma sassauta murya
‘’Haba Batulata da kuɗin da zaki dinga zuba wa a bankin bada lamani, me zai
hana ki tara ki bani in jujjuya maki? Ya cigaba da mani ɗadin baki har ya samu
na aminta zan dinga tara ma shi duk sadda nayi kitso.
****
Yau baƙar rana ce a gare ni domin bayan fitar
Babansu Ahmadu ba da jimawa ba sai ga ƙugin babur ɗin Alhaji Haladu, gabana ya
faɗi ras! Na kai duba na ga Sailuba da yaran maƙwabta dake tsakar gida su na
hidindimunsu, idan ka cire Ahmadu dake ɗaka yana makyarkyatar ɗari.
Kai tsaye ya faɗo mana babu ko sallama ya fara
wurgi da kayan amfanin da ya gani a tsakar gida yana faɗin "Wallahi yau
sai kun bar wannan gida ko gadon uwayenku ne! Mutum da gida nai amma a maishe
shi shashasha..!
Jikina ya fara ƙyarma "Ka dubi girman
Allah ka rufa mana asiri Alha...."
Maganata ta datse lokacin da ya ke umurtar
yaron sa da "Hankaɗa uwar ɗakan ka finciko mani wancan lalatacce yaron da
na ke hangowa ƙwance. "
Na runtuma da gudu "Karka taɓa shi dan
Allah, baya da lafiya. "
Bai saurareni ba ya finciko Ahmadu ya fitar
waje, na bi shi da sauri na amshi yarona na kwantar gefe, na dawo na cigaba da
ba shi haƙuri amma a banza an yankawa
kare ciyawa.
Bai ƙara bi ta kaina ba har sai da ya gama
facali da kayanmu, sannan ya taso ƙeyar mu muka fito bakin ƙofar gidan muka yi
cirko-cirko.
A sanyaye na dubi Ahmadu dake ƙwance tsakiyar
hanya yana ƙwarara amai, ga tsohon ciki dake jikina ɗan kimanin wata shidda da
'yan satuttika, na tallabe kumatu ina kuka ƙasa-ƙasa lokacin da ya ƙarasa watso
mana tarkacen kayan mu da ke hannun shi.
Cikin muryar kuka na ce "Ka rufa mana
asiri dan Allah, na maka alƙawari nan da kwana uku zan sayar da kujeruna in haɗo
maka kuɗin hayar, kaji tausayinmu Alhaji, ko dan darajar wancan yaron dake
ƙwance tsakar hanya yana amai." Na nuna Ahmadu.
Ya watsa mani harara tare da busa karan
sigari "An ƙi a bari ɗin! Tun yaushe nake fama da
lalataccen mijiin ki ya bani kuɗina amma ya ƙiya?
Sau nawa ina aiko wa? Wallahi ba zan ƙara maku ko da daƙiƙa biyu, wanda ma ba ku
biya ni ba, Allah ya isa."
"Ka taimaka, wannan karan ni zan
baka kuɗinka, ka rufa mana asiri."
Watsi ya yi da ni, ya janyo
marfin ƙofar gidan ya saka ƙwaɗo, ya hawo babur ɗin shi ya buɗe mu da ƙura.
A hankali na kalli dandazon mutanen dake tsaye
suna kallon mu cike da tausayawa, na sadda kai na ƙasa domin ba wannan ne karo
na farko da aka tozarta mu irin haka ba, na share hawayena. Allah ya sani na
gaji da yawon hayar nan, kullun cikin tozarci da wulaƙanci muke ga kuma karatun
yaranmu dake koma baya saboda yawan canje-canjen makarantu, kayana kullum a
lalace wasu ma sun ɓace, 'yar sana’anar kitson da nake taƙama da ita babu
cigaba, domin duk sadda muka canza unguwa sai nayi sabon kiran kasuwa, wani sain
kafin a gama sanina mun sake unguwa.
Cikin sauri na janyo wayar tarho, na kira
Babansu Ahmad na sanar mashi halin da ake ciki, amma cikin halin ko in kula ya
amsa "Gani nan tafe, sai ku shiga maƙwafta kafin in ƙaraso."
Haka na tattara komatsai na muka shigar dasu
zauren gidansu Safara'u da taimakon yaran maƙwabta, mu ka bar kujeru da katifa
saboda na san babu mai taɓa su, tunda hanyar wucewar mutane ce, kuma aƙwai mai
shago a kusa damu ko shi zai duba mana.
Ko da ya iso babu abun da ya dame sa sai ma
banbami da ya hau yi, bai da ko sisin a hannu shi, shi bai san yadda za ayi ba,
wa ya mutu wa ya dawo! Ganin ba mafita ya sa na ce ya ɗauki kujeru na a siyar a
samu wani gidan.
***
Tunda muka doshi layin unguwar da zamu ko ma
naji hankalina bai kwanta da ita ba, na ja zanina sama, saboda ruwan kwatar da ke
malale ta ko'ina da alama babu ta in da zai fita saboda cunkuson gidajen da ke
yankin, lungu na ko ta ina amma basu ɓullewa, hanya ɗaya ce tal a yankin, ta
nan ruwa da mutane ke fita, ga kuma gidajen har da na sama. Duk da marece ne
amma haka nake jin kukan sauro ya karaɗe mani kunnuwa, gashi duk in da ka
dira ƙafa to tabbas cikin ruwan datti za ta sauka, haka muka nufi gidan da zamu
zauna babu ko ƙyaure a ƙofar sai buhun da aka saka aka rufe ƙofar da shi.
Har ila yau ɗakuna ne har guda goma sha huɗu
rairas, ɗakuna baƙwai na kallon baƙwai, na runtse ido lokacin da wani inyamuri
ya fito daga shi sai gajeran wando da fo a hannun shi, daga cikin ɗakin dake
kallon na mu, ya nufi wani ɗan sirɗaɗo da alama makewayi ne.
Na kai dubana ga Sailuba da ta bi shi da
kallon mamaki, domin ko Ahmadu dake shekara baƙwai ban cika barin shi yana yawo
haka ba, bare wannan garjejen.
Gefe guda kuma maza da mata ne zazzaune
kowanne a bakin ƙofar ɗakinsa ana ihu da shewa ana labaran duniya, kuma matan
aure ne da mazaje su, ga shi yawanci su ba cikakkun kaya bane na mutunci a
jikin su, masu mutunci ne ke sanye da ‘yar shimi, wasu kam daga su sai ɗaurin
ƙirji, kawuna babu kallabi.
Muryar babansu naji yana faɗin "Ki
shigo mana Batula."
Na sauke ajiyar zuciyar tare da
ƙarasa cikin ɗakin "Gaskiya bazan iya zama a wannan gidan ba.!
Ya ɗaure fuska "Akan me.?
"Ko saboda tarbiyyar ‘ya'yan mu! Yanzu
fisabillahi baka ganin yadda lamarin gidan yake ba? Ina
tarbiyya a nan? Har ga Allah wannan
ba gidan zama bane Babansu Ahmadu."
"Haba Batula? Idan ba wannan ba ina ki
ke son mu zauna? Kuɗin
shi garemu, ko kin
manta nawa aka siyar da kujerun ki? Dubu sha biyu ne
fa? Kuma ko sisi ban ɗauka ba haka nazo na biya kuɗin wannan ɗakin."
Daga haka ya juya ya fice ya
barmu tsaitsaye, na kunna fitilar tarho ina haska ɗakin, ɗan ƙarami ne sosai ko
gado bazai ɗauka ba, kuma a haka za mu yi rayuwar ni, mijina da yaran mu guda
biyu ga tarkacen kayan mu! Nan take Sailuba ta taimaka mani muka kakkau da
kayan mu da a ka kawo ɗazu da safe, na ƙwantar da katifar ƙasa na yabuɗa wa
zanin gado.
Haka na kwana ina korar sauro, su kansu yaran
sai bubbuge-bubbuge suke yi, sannan ga maƙwabtanmu da suka raba dare suna
kallon talabijin.
Da Asubahi na fita domin ɗaura alwala, sai dai
layin da na gani a bakin makewayin ya sa hankalina ya ƙara tashi, domin maza da
mata ne baligai tsaye suna jiran na ciki ya fito su shiga, sannan kowannen su
riƙe yake da ƙaton fo a hannu da alama bisa shi ne za ka zauna kayi abun da za ka
yi sannan ka zubar. Idan na fahimta dai-dai makewayi ɗaya tal a cikin gidan da
ke dauƙe da kimanin mutane hamsin maza da mata da yara.
A sanyaye na juya zan koma sai tsinkayar murya
wata mata nayi tana faɗin "Baiwar Allah ki tsaya su fito mana ki shiga,
domin ko kin koma wannan baƙin layin da kike gani ba zai taɓa yanke wa
ba."
Wata tsamurmurar mata da ke kusa da mai
maganar ta rafka tsaki "rabu da ita Hauwa, ta daɗe bata koma ba, kina gani
ko da ta zo jiya babu wanda ta kula, ni wallahi tun da na ganta na san ba za mu
shirya ba."
Na juyo na dube ta, ta
kuwa gallah mani harara ta finciki fo ɗinta ta faɗa
makewayi. Ni kam mamaki ya ishe ni, na ga dudu jiya da
marece muka dawo gidan, yaushe har na gama kintsawa, na bisu ɗakunan su muka
gaisa? Ni a nawa tunanin sai yau da safe nake niyyar shiga.
Na yi tsayuwar sa’a guda sannan layi ya zo
kaina, na raɓa ƙartin mazan dake tsaye dako-dako na shiga ciki, ya yin da
zarni, wari, ƙarni, hamami suka dakar mani hanci, na kai duba na ga ɗan ƙaramin
makewayin da a ka cika da ledojin ƙazamta, shi kan shi shadda a cike yake fal
har yana tumbatsa, abunka da mai juna biyu nan take wani amai ya taho mani, na
doɗe hanci na fito da gudu na shiga sheƙa amai a bakin 'yar ƙaraman magudadar
ruwan da ta ri ga ta toshe.
Kan kace ƙwabo an karaɗe gidan da cewa sabuwar
baƙuwar da tazo ta ce mutan gidan ƙazamai ne, ta shiga makewayi ta fito tana
sheƙa amai, maganganu iri-iri. Ni kam Allah ya sani, bance ma kowa kanzil ba.
*****
A mako guda na gama fahimtar halayyar mutanen
cikin gidan, sun ƙware wajen gulma, sa ido, munafurci, faɗace-faɗace, bin
bokaye kuwa basu ɗauke shi a bakin kome ba, a tsakar gida ma za ki ji ana faɗin
malam yace kaza-kaza, sannan hatta mazajen su basu raga ma wa , don ka ji matar
wancan ta ƙwada ma mijin wata ashariya ba baƙon abu bane. Sannan kaf ilahirin
gida babu wanda ya kai matan dake jingine da ɗakina, ma'ana hagu da dama iya
munafunci, da haɗa husuma,wato Hauwa'u da Asabe.
Yau ma kamar kullum ina wanke-wanke a bakin
kofar ɗakina sai ga Asabe da Hauwa'u kamar haɗin baki sun fito, Asabe ta raku ɓa
ta zauna gefe na tana faɗin "Su Batula aiki ake.?
Nayi murmushin
da iyakar sa laɓɓa na ce
mata "A’a bacci ni ke!
Banda rainin wayo me ta taras da ni ina yi bayan
aikin.
Suka kwashe da dariya
sannan ta kalli Hauwa ta kanne mata ido tana faɗin "Dama ‘yar shawara ce
muka zo mu baki."
Na ɗaure fuskanta tamau domin na tabbata babu
wata shawarar kirki da su ka zo min da ita, babu yabo ba fallasa na ce
"Ina jin ku."
"A kan mai gidan ki ne, dan Allah ki
mashi magana ya dinga sanya gajeren wando na ciki.." Asabe ta fada idon ta
kur a kaina.
Gabana ya faɗi ras! Na ɗago na kalle su ɗaya
bayan ɗaya, ban taɓa tunanin jahilcin nasu ya kai har haka ba, na miƙe a fusace
na ce dasu "Wallahi ban taɓa sanin har yanzu a kwai jahilai irin ku ba! Ni
za ku kalli tsabar idona ku faɗa wa wannan lalatattar maganar? To ahir ɗinku
wallahi! idan kuna cin ƙasa ku kiya yi ta suri!
Nayi masu kaca-kaca sannan na shige ɗaki na
barsu tsaitsaye don basu taɓa zaton ina da baki har haka ba.
A yinin ranar mamakin
maganganu su ya hanani sukuni,
domin ban taɓa ganin marasa kunya iri su ba, sa
idon har ya kai ga kallon haramci. Ko da baban
su ya dawo ban sanar ma shi
ba, illa da safe na tambaye shi zan je kasuwa,
ya kuma barni, na je na ƙaro ma shi
gajerun wanduna a gwanjo tun da dama ɗaya gareshi idan kuma aka wanke bai da na
canza wa.
***
Wata irin bahagguwar rayuwa ake a gidan, ba
kome ba ne ka ji matar wani da mijin wata suna cacar baki, wani sa'in ma sai ka
ga kamar za su dambace sai ana rirriƙesu, sannan ga kuma wani hatsabibin boka
da ɗakinshi ke ƙarshen gida, a nan mafi akasarin matan gidan ke lalacewa ga
neman asiri, kaɗan ne ke fita waje, nima babu kunya babu tsoron Allah Hauwa
take bani shawarar in fara zuwa gurin shi ta yadda zan mallake mijina ya
kasance sai abun da nace zai yi, sannan duk abun da ya samo ni zai mallaka ma
wa.
Na ce ma ta ta ji tsoron Allah, ni kam ko kwabona
ba zan yi asarar shi ba gurin kaima boka, haka ta miƙe sanyaye ta bani guri.
Ranar Asabar ina zaune in wanki ya yin da
Sailuba ke mani ɗauraya sai ga Ahmad sun fito wanka shi da Habibu, na kalle shi
sosai na tabbatar a tare suka shiga suka yi wankan, na miƙe tsam na ja kunne
shi muka shiga ɗaki, na zaunar da shi na tambaye shi dalili da ya sa ya shiga
wanka mutun biyu.
Kai tsaye ya sanar dani wai Maman su Habibu
tace su yi a tare tun da akwai layi, nace ƙarya yake domin mamansu bata nan, da
ya ji matsa sai cewa, ya yi Habibun yace su shiga tare ya dinga riƙe mashi
al’aura zai ba shi alawa shi ma sai ya riƙe ta Ahmadu, hankalina ya tashi na
tambaye shi ina suka san haka, tunda daga shi har Habibun babu wanda ya haura
ma shekara takwas, sai ya ce wai haka Auwalu yake masu kullum da daddare sai ya
ja su ɗakin shi ya kunna masu kallo yace su dinga taɓa mashi ko’ina na jikin shi,
da safe ya siyar masu alewa.
Hankalina ya tashi sosai na tsoratar da shi,
sannan nayi ma shi dubara nace idan na kuma ganin shi ya shiga ɗakin Auwalu (tunda
matar shi taje goyon ciki), ko na ƙara ganin shi da Habibu sai na haɗa wuta na
turmutsa shi, haka na dinga tsoratar da shi da azabobi masu yawa nan da jiki sa
ya hau ɓari.
Da Baban su ya dawo na sanar da shi halin da
ake ciki sai ya nuna abun bai dame shi ba, wai in bar kama zancen yaro, ya
cigaba da sabgogin shi. Ban hakura ba na samu Maman Habibu na sanar da ita halin
da ake ciki amma sai cewa tayi ƙarya nake ma yaronta, sharrin zan masa, ta samu
Auwalu ta sanar da shi na ce yana lalata da yaran mu, shi kam ya hau ya yi ta
tsine-tsine har yana barazanar kaini kotu na ɓata masa suna, da ƙyar aka kashe
maganar aka ba shi hakuri.
Ni kuma tun daga ranar na kulle dukka mutanen gidan,
iya ka ta da su gaisuwa a hanya, na daina barin yarana fito wa ko ƙofar ɗaki
sai idan dole, na soma koya masu karatu iya sanina a cikin ɗaki.
Matsala ta gaba da ta kunno ma na shi ne ciwon
sanyin mara da ya kama Sailuba, ta shiga fidda farin ruwa masu ƙaiƙayi daga
al'aurar ta, ga ƙuraje da suka feso mata a gaba, na kai ta asibiti likita ya ce
amfani da makewayin da mutane barkatai ke amfani da shi ne mai ƙazanta ya janyo
haka, ya rubuta mata magunguna da allurai ya ce mu kiyaye amfani da makewayi
mai ƙazanta. Tun da lokacin muka koma fitsari daga tsaye, ba dan mun so ba sai
don babu yadda za mu yi, domin ko ka wanke makewayi kafin ƙyaftawar ido an ɓata
shi.
****
Ban ƙara sanin illar unguwar ba sai da damuna
ta kama, domin kullun cikin zullumi muke muddun ana ruwa…
Yau ma
tun da safe ake makaka
ruwan sama kamar da bakin ƙwarya, babu alamun zai ɗauke har kusan la'asar,
gashi hankalina ya gagara ƙwanciya bare ma da
na
leƙo waje naga yadda gidan ya cika maƙyil da ruwa, har ya fara hawan tudunkar ɗakunan
mu, domin babu inda zai fita, sai idan an gama mu fita mu ƙwalfesu,
mu kai waje mu zubar.
Na cije baki ina dafe
cikina, saboda azabar ciwon marar da na yini da shi a yau.
Babansu na kalla yana zaune bisa kujera 'yar
tsugunno na ce "Tun da safe nake faɗa maka naƙuda nake a tsaitsaye amma ka
ƙi
taɓuka komai."
"Ya kike son in yi Batula? Ai kin
san yanayin unguwar
muddun ana ruwan sama babu damar fita, bare kuma abun hawan, ki tashi ki leƙa
da kan
ki ki
ga yadda ruwa ya
cika unguwar maƙil."
Na dafe marata tare da haɗa
kaina da guiwa ina cije leɓɓa, Sailuba dake zazzaɓin cizon sauro ta matso kusa
dani jikinta zafi rau tana faɗin "Sannu Maman."
Na gyaɗa mata kai kawai.
Wasa-wasa ciwo ya turnaƙe ni, ga kuma ruwan da
ake kwararawa babu alamu zai tsagaita, ga ciwo na ƙara tsananta. A nan ne
hankalin shi ya fara tashi, ya miƙe ya leƙa waje sannan ya dawo ya rufa buhu ya
fita da gudu.
Da ƙyar ya samo aron babur gurin mai shagon
dake bayan mu, ya turo shi da niyya kawo shi bakin ƙofar gidan, sai dai a bakin
‘yar ƙaramar hanyar shigowa yankin mu ya tokare! Ya yi ya yi amma babur ya
gagara motsawa, har sai da ya samo matasa suka taimaka mashi suka ɗaga babur ɗin
aka fidda shi ƙwalta sannan suka ce sai dai ya shiga ya kamo ni, amma babu
yadda za’ayi babur ɗin ya ƙarasa ƙofar gidan kamar yadda yaso.!
Ya komo cikin gidan a ruɗe a lokacin har na
soma fita hayyaci na, ya samu da ƙyar ya ɗagani ya sagala hannuwa na a
ƙafadarshi, muka fita ina cije baki gashi duk matan dake gidan babu wacce ta
leƙo bare su taimaka mani, haka muka fita yana jefa mani "Sannu batula, cije.!
Ina sauka daga tudunkar ƙofar gida ruwa ya
kawo mani har guiwa, santsin ruwa haɗe da taɓo ya ƙwasheni ji kake timmmm ƙasa!
Nan da nan jini ya balle mani.
Ni dai ban ƙara sanin inda kaina yake ba sai
farkawa nayi na ganni bisa gadon Asibiti, Innarmu riƙe da hannuna tana share
hawaye, ga Sailuba da Ahmadu cirko-cirko, ga kuma tiyatar likita a jikina, amma
babu jariri a gefena.
Sai dana wartsake aka bani ruwan shayi na sha,
sannan Inna ta ke faɗi mani sai da aka mani tiyata aka fidda yaron saboda faɗuwar
da nayi wuyanshi ya karye, su kansu likitocin faɗa suka yi, wai da an ƙara
daƙiƙa goma ba a kawo ni ba, to ba iya yaron cikin ba har ni za a rasa rayuwa
ta, take hawaye suka zubo mani.
Mako na biyu aka sallemi ni daga asibitin inda
Babanmu ya rantse da Allah ba zan ƙara komawa wancan gidan ba, idan yanzu an
rasa jinjiri gobe ni da yarana za a rasa, don haka yace zai tattara ni da
yarana mu tafi gida katsina duk lokacin da mijina ya yi muhalli mai inganci
yazo ya ɗauke mu.
Hankali Babansu Ahmad ya yi ƙuloluwar tashi
ganin za a raba mu da gaske, ya shiga bada hakuri haɗe da alƙawarin zai nemi
wani gidan daban, Babana ya ƙeƙeshe ƙasa yace shi gidan hanyar ma gaba ɗaya
baya buƙatar zamana.
Da ya tabbatar da gaske ake sai cewa ya yi zai
maishe mu garin iyayen shi Kankia ta Katsina tun da a cikin gidan su yana da ɗaki
ɗaya, dama abun da ya sa bai zauna ba saboda bai son zama a ƙauye, amma yanzu
sai mu ko ma can ni da yaran, alabash shi idan ya kama sana'a ya samu muhalli
mai inganci sai mu dawo Kaduna shi kuma duk bayan sati biyu zai dinga zuwa yana
duba mu.
Haka aka yanke kuwa muka tattara ni da yarana
muka koma Kankia da zama, kuma ko wata ɗaya ba mu cika ba, aka sanya su
makarantar boko da ta muhammadiyya.
Cikin ikon Allah watan mu uku da dawowa shi ma
Babansu Ahmad ya tattara ya dawo nan Kankia, domin zaman shi kaɗai aƙwai
matsala, ga abincin shi ga na mu, ga kuma Babana da ya gargade shi idan ya
gagara ciyar da mu to babu makawa raba auren zai yi, shi ya sa ma ya sayar da
babbar wayar shi..
Bayyi mako biyu da dawo wa ba ya soma aikin
kanfani, ya yin da ya tattara kwalin shi na digiri ya soke ƙarƙashin katifa, ya
fahimci ba dole sai da aikin gwamnati ba za ka iya rayuwa mai kyau, a kwai
ayyukan ƙarfi da za su haskaka maka goben ka, ya fahimci girman darajar dake
tattare da mallakar muhalli, babu zullumi bare tunanin yaushe kuɗin haya zasu
ƙare, ka sakata ka wala, babu takura, hankali kwance babu sa ido bare tsegumi.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiyar mana hankali
ƙwance ni da yara na, babu takura bare fargabar sauye-sauye muhalli, ga karatun
su yanzu lafiya lau Alhamdulillah, kuma cikin Ikon Allah ba mu shekara huɗu ba
ya gina mana wani gidan madaidaici, ɗakuna ciki da falo guda biyu har da
makewayi ga kuma ɗakin yara maza a bakin ƙofa.
Yanzu kam ‘yan uwa da abokanan arziƙi su kan
zo mana zumunci har da kwana gidan mu, ga sana'a ta da nake ta kitso da ƙunshi
ta ɗaure kowa ya san ni, ba kamar da ba, kafin mutane su gama sa ni na mun bar
unguwar in da za mu koma kuma sai na canza sabon kiran kasuwa, yau ma tun da
safe sai ga yaya Hadiza har da shirin kwanan ta.
Alhamdulillahi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.