Ruƙayya Ibrahim Lawal (2023). Wutar Kaikayi. Ɗaukar Jinka (Labaran Da Suka Samu Nasara A Gasar Gajerun Labarai Ta Arc. Ahmed Musa Dangiwa, 2022). Kangiwa Multimedia and Communication Company LTD
WUTAR
ƘAIƘAYI
Na
Ruƙayya
Ibrahim Lawal
Da
hanzari na bar yin safa da marwan da nake yi a ƙofar
ɗakin
da aka shigar da mijina don ba shi agajin gaggawa cikin asibitin, ganin babban
likitan da yake duba shi ya fito tare da tawagar masu taimaka masa. Na tari
gabansu a rikice ina ƙwalla
ina tambayarsa,
“Likita
yaya jikin nasa? Me ya same shi?” Sai dai a maimakon ya ba ni amsar tambayar da
na yi masa shi ma tasa tambayar ya watso mini.
“Mijinki
yana shaye-shaye ko?”
Sai
da na ji wani bargon kunya ya lulluɓe
ni, har na sunkuyar da kaina zuwa ƙasa.
Sanin cewa ba a ɓoye wa likita komai ya sa na
ɗaga
masa kai alamar ‘eh’, don sosai kunya nake ji a ce wai mijina ne ɗan
shaye-shaye. Sai da ya yi gyaran murya sannan ya ce.
“Bayan
kammala gwaje-gwaje mun tabbatar da cewa zuciyarsa na gab da daina aiki,
yanayin bugawarta ya yi rauni sosai, wanda kuma duk silar shan kayan mayen da
yake yi ne. Shi ya sa yanzu duk lokacin da ya ga wani abin da ya firgita shi
irin yadda ya ga na yau, komai zai iya faruwa.
Ba
iya zuciyarsa ba, hatta hantarsa ma tuni ta fara taɓuwa,
don haka rayuwarsa a yanzu dai sai yadda ta yiwu naƙuda a ɗakin
mayya.” Yana gama faɗin hakan ya kewaye ni ya yi
gaba tawagar ɗaliban jinya suna take masa baya.
Abin
mamaki sai na ji duk firgicin da nake ciki ya kau a zuciyata, a halin yanzu
kuma tausayinsa nake ji kawai na irin yadda silar shaye-shaye ya rasa komai na
rayuwarsa...
Kasancewar
a I.C.U (Ɗakin
ba da kulawa ta musamman) yake, kuma sun hana mu shiga. Sai na je ina leƙa shi ta gilashin tagar ɗakin.
Yanayin yadda na gan shi a ciki ya firgita ni ainun, yana kwance ne kawai
tamkar gawa. Na tsare shi da ido ina kukan zuci da na sarari, daga hawayen da
ke tsiyaya a gefen fuskarsa na fahimci har a lokacin wutar nadamar da take hanƙoro a zuciyarsa ba ta lafa ba. An saka
masa wata na’ura da take taimakawa wajen dai-daita bugawar zuciyarsa, saboda
yanayinsa ya ta’azzara.
Da
na kalli zanen bugun zuciyar tasa a jikin na’urar, sai ya zamar mini tamkar
majigin da na fara hango silar faruwar komai...
“Inna
lillahi, wayyo!” Na furta a gigice tare da farkawa a firgice, na miƙe a kan gotaccen gadon da nake kai a
kwance, ina rarraba idanu. Da fuskar Sayyid na yi tozali yana huci tamkar
kumurci. Kamar mai jira, ya ci gaba da tsula mini bel ɗin
hannunsa.
Na
shiga tsalle-tsalle ina kare jikina da hannayena, gami da ƙaraji, gangar jikina tana zuƙo raɗaɗin
dukan.
Ƙururus! Na jiyo sautin karyewar abu da
nake kyautata zaton katakon gadon ne, lokaci ɗaya
kuma na ji sautin kukan yara yana tashi cikin wani firgitaccen yanayi.
Sai
a lokacin sha’afaffiyar ƙwaƙwalwata ta tuna mini cewar ina kwance ne
a kan gadon tare da yarana uku.
Shau!
Na ji saukar bel a cikin ƙwayar
idanuna, ba shiri na buɗe baki cikin galabaitacciyar
murya.
“Wayyo
Allahna! Zai fitar mini da ido!” Take idon ya fara tsiyayar da ruwa tamkar
famfon da ya birke.
Yayin da shi kuma yake ta bambamin cewa na raina shi da na yi bacci ban jira
dawowarsa ba, sai faman ba shi haƙuri
nake.
Na
dafe idon da hannu ɗaya ina sauraren yadda yake
zogi tamkar an baɗa masa niƙaƙƙen
barkono.
Ihun
yara ya ci gaba da mamaye ilahirin ɗakin.
Na juya yamutsattsiyar fuskata ina ƙare
wa yamutsattsen mijin nawa kallo.
Ya ɗaga
hannu da niyyar sake jibga ta ga yarana a cikin wani yanayi. Ganin bai san zuru
ba, sai na saka ɗaya hannun na ture shi ya
baje a ƙasa, na yi kan yarana.
Safna
‘yar shekaru biyu da rabi ce riƙe da
hannu tana kuka, ashe ƙarar
karyewar ƙashinta na ji, kuma
ni ce na taka mata hannun lokacin da nake tsalle-tsalle.
Sautin
kukan Sabir ɗan shekaru huɗu da
ya ratsa masarrafar jina ya sa na bar wurin Safna na shiga neman sa. Na yi
nasarar gano shi a bayan gadon ne sakamakon wadataccen hasken wutar lantarki da
ya mamaye ɗakin, wanda nake kyautata zaton mijin
nawa ne ya kunna ta.
Ɗago yaron ke da wuya maganaina suka
sauka a kan goshinsa da ke fesar da jini. Na janyo shi, kafin na yi wani yunƙuri na ceton su Sayyid ya yi nasarar miƙewa yana zage-zage.
“Ke
Jaka! Lallai kin isa. Ni kika ture? Za ki kawo mini abincina ko sai na ɗora
daga inda na tsaya?” Ya yi zancen cikin sautin ‘yan maye.
‘An
kuma, wai mace ta haifi mace.’ na faɗa a
raina.
A
zahiri kuwa ban ce masa kanzil ba, na fice zuwa madafa ina masa fatan shiriya.
Bayan
na kawo masa abincin ne na shiga lallashi da kula da yarana wanda suka yi bacci
da ƙyar. Karim ɗan
shekara ɗaya
ne kaɗai
Allah Ya kare bai samu rauni ba. Hasalima duk abin nan da ake shi bacci yake
abinsa.
Shi
ma watsattsen mahaifinsu yana gama cin abincin ya mimmiƙe ya fara jan rago, cike da takaici nake
tuna silar komai.
Kamar
yadda huɗubar
Liman ke tasiri a zuciyar masu tsoron Allah, haka huɗubar
aboki ta yi tasiri wurin samar da gurɓatacciyar
ɗabi’a
ga matashin mijina.
Wannan
ne dalilin da ya sa a rayuwata ba abin da na tsana sama da zaman majalisa da
abokai. Me yiwuwa hakan ya samo asali ne a dalilin illar da abokantakar ta
haifar mini.
‘Aboki
fitilar sharri ko ba mai kina kai safe, wake ɗaya
mai ɓata
iri, macijin sari ka noƙe,
gayyarka daban ce.’
Wannan
ne kirarin da nake yi wa aboki dalilin matsalar da ya jaza mini a gidan aurena.
Aboki
ne ya ɗora
mijina a makauniyar hanya a dalilin zaman majalisa, biyo bayan korarsa daga
wurin aiki da aka yi. Yayin da ya kasa riƙe
gidansa, damuwa ta samu matsugunni a zuciyarsa, gurɓataccen
amininsa ya yi nasarar ɗora shi a keken ɓera
ta hanyar ba shi fatawar cewa tsotse-tsotsen kayan maye yakan wanke baƙin ciki da damuwa, shi kuwa ya riƙe wannan huɗubar
gam.
Tun
daga wannan ranar farin ciki ya ƙaura
a gidan aure na, tashin hankali ya maye gurbinsa.
Har
sai da ta kai da zarar mijina ya dawo daga majalisa to fa tawa ta same ni wai
kura da hatsin gandu.
Don
haka na ci alwashin raba shi da miyagun abokanai har ma da mummunar ɗabi’ar
da ya koyo a wurinsu.
A taƙaice dai ranar a haka na ƙarasa sauran awanni ukun da suka rage na
daren ina kukan zuci, sai gab da asuba bacci ɓarawo
ya sace ni.
Washe gari Sayyid ya farka a wartsake bayan ya fahimci
komai da ya faru ya yi kuka sosai, musamman da ya kasance shi mutum ne mai
tsananin tausayi da nuna zallar so da ƙauna ga iyalansa.
Bayan dawowarmu daga nemawa yaran magani ya tasa su a
gaba yana hawaye da faɗar “Ku yi haƙuri yarana duk
laifina ne, ban san wane laifi na yi wa ƙaddara ba ta saƙale ni a haka.”
Na matsa kusa ina lallashin shi tare da ƙoƙarin janyo hankalinsa, “Kada ka
zargi ƙaddara a cikin wannan al’amari, domin wannan ba aikinta
ba ne, aikin son zuciya ne, son zuciya kuma shi ne ɓacinta. Ya kai
mijina ka ji tsoron Allah ka daina tu’ammuli da kayan maye tunda har ya bayyana
a gare ka cewar ba ya daga cikin ɗabi’un nagartattun bayi. Ko ma don lafiyarka
da kare martabar ‘ya’yanka ya kamata a ce ka daina. Dubi yadda ka zamo sanadin
illata lafiyar ‘ya’yanka da matarka, maye ya tagayyara rayuwar ahalinka, ta
yadda ka kasa riƙe
amanarmu da ta rataya a wuyanka...”
Har
zuwa lokacin bai tamka ba, hakan ya ba ni ƙwarin
gwuiwar ɗora
igiyar zancena da faɗar, “A suratul Ma’ida aya ta
90, Allah Maɗaukakin Sarki ya ce, Ya ku waɗanda
suka yi Imani, haƙiƙa giya da caca da gumaka da kibiyar
neman sa’a, ƙazanta ne daga cikin
ayyukan shaiɗan, ku nisance su ko da za ku samu rabo.
Ka
sani fa, dukkaninmu makiyaya ne kuma za a tambaye mu a kan ababen kiwonmu. Wace
amsa ka tanadarwa wannan ranar mai zuwa duk daren daɗewa?”
Ina
zuwa nan a zancena sai ga hawaye suna tsere a kan kyakkyawar fuskarsa. Na yi
shiru ina nazarin yadda jikinsa ya yi sanyi tamkar kazar da aka jefa da
gishiri. Kamar da gaske wai karuwa ta ga noman Ɗan
koli. Take a wurin Sayyid ya yi mini alƙawarin
daina shaye-shaye da kuma rabuwa da abokin da ya shirya masa wannan gadar
zaren.
Zamanmu
da Sayyid ya yi daɗi a cikin satin da na yi
masa nasihar. Ya daina dawowa gida a buge, haka ya fara sana’ar adaidaita sahu
da yake karɓar sojan haya, yana neman na sayan gari
a cikin gari. Har ma ya kai ni asibiti aka duba mini idona da ya ci gaba da
tsiyayewa a hankali har ya ƙanƙance.
Bayan
cikar awanni ɗari da sittin da takwas da suka bayar da
kwanakin mako, giyar mamaki ta fara ɗawainiya
da ni. Ina zaune na samu labarin cewa mijina yana tsare a hannun jami’an tsaro
sanadiyyar kayan maye da ya sha ya kifar da wasu bayin Allah har suka ji
raunuka.
A gigice na ƙarasa caji ofis ɗin na same shi
zaune ya yi tsamo-tsamo tamkar kazar da ta faɗa ruwan zafi, muna
haɗa ido ya kautar da kansa.
“Yanzu
Sayyid ka yi mana adalci kenan? Da ma tuban muzuru ka yi?” Na yi zancen ina
goge guntuwar ƙwallar da ta zubo
mini.
Haka
na yi ta yi wa jami’an magiya suka yi kunnen uwar shegu da ni, har sai da na
kira yayansa Bilal, nan ma da ƙyar
da jibin goshi suka ba mu
belinsa da alƙawarin cewa zai biya
kuɗin
sabuwar adaidaitar da ya ɓata da kuma kuɗin
jinyar mutanen da ya raunata, duk da cewa shi ma ya samu raunin.
A haka muka ɗauko shi zuwa gida aka ci gaba da yi masa maganin
gargajiya, na ci gaba da jinyar su shi da yarana biyu da nake kan jinya, ni ma
ga nawa jikin. A raina na ce, ‘Wannan shi ne haihuwar guzuma
ɗa
kwance uwa kwance.’
A
lokacin da muke tsaka da tunanin mafitar inda za a nemo musu kuɗinsu
kafin wa’adi ya cika, bayan cewa cikinmu ma a ɗamfare
suke da yunwa. A lokacin ne kuma ciwon sikilar Sabir ya motsa fiye da koyaushe,
jikinsa sai zafi yake yi, yana faman kuka da faɗar
Mama hannuna ciwo, wayyo ƙafata!
Guiwata!!
A
haka ciwon ya ci gaba da cin ƙasusuwansa
yana shanye masa ɓargo ba tare da mun iya yin
wani yunƙuri na ceton shi ba.
Ranar
Lahadi da dare Sayyid ya shigo gidan a dame, ya zauna a kusa da ni kansa a
sukunye ya ce, “Matata ki yi haƙuri,
na sani cewa ban zamo nagartaccen miji a gare ki ba, na tauye yardar da kika ba
ni, kika zaɓe ni a cikin jerin taurarin da suke son
haska rayuwarki a wancan lokacin, sai ga shi na ƙuntata
duniyarki da duhu mai tsanani. Daga ƙarshe
ma na yi silar mayar da ke nakasasshiya mai ido ɗaya
a lokacin da kike ganiyar ƙuruciyarki.”
Ya sauke ajiyar zuciya.
A
lokacin ni kuma hawaye ya ɓalle mini.
Ya ɗora
da cewa “Mun yi shawara ni da Inna cewa zan siyar da wannan gidan nawa, mu koma
can gidan da take mu raɓe...”
Na
yi saurin ɗago ɗayan
idon da ya rage mini na kalle shi, a take ya ɗauki
haske cewa ina neman ƙarin
bayani ne, don haka bai jira cewata ba,
“Na
san me kike tunani, amma ina amfanin baɗi ba
rai? Siyar da gidan shi ne kawai mafita, domin Oga Goje bai san me ake kira
mutunci ba.”
Sai
a lokacin na harhaɗo kalmomi da ƙyar “Amma ina kuɗin
da na ba ka a watannin baya? Me ne amfanin zinari idan ba zai biya buƙata ba?”
Ya
juya mini baya yana yunƙurin
tashi, “Na tattare su na saka a wani kasuwanci mai matuƙar riba, kayan na sauka za ki zama matar
Alhaji.”
Na
yi ‘yar dariyar farinciki, “Allah ya tabbatar mana da alkhairi.”
Duk
da jikina bai ba ni ba, sai dai ko ba komai an samu zaftarewar ɗaya
daga cikin matsalolin da suka gurgunta mana rayuwa.
Washe
garin ranar, Sayyid ya haɗa takardun gidan ya fita ya
bar ni ina hawaye, ba wai don an sayar da gidan ba, sai dai an ce sabo turken
wawa.
Wata
rana da ba za ta taɓa gogewa a ma’adanar taskace
shuɗaɗɗun
abubuwa da ke ƙwaƙwalwata ba.
A
tsakiyar wannan daren ne, da na riski kaina a cikin matsanancin tashin hankali
da ya yashe dukkanin nutsuwata.
Sheɗar
Sabir ta zo iya maƙogwaro,
a lokacin da yake fafutukar ƙwato
numfashinsa daga mutuwar da ke ziyartarsa a lokacin ne watsattsen mahaifinsa ya
shigo a bige.
‘Mai
hali ba ya fasa halinsa.’
Na
faɗa a
raina ina kallon shi cike da tsana. Na yi kan yarona da yake ta faman kokawa da
numfashinsa, amma na kasa dakatar da shi daga ci gaba da tunkarar ajalinsa.
“Ke
ba ki ga na dawo ba ne? Uban me kike dubawa a wurin da kika zauna kamar an dasa
ki?”
“Kana
gani fa mutuwa yake yi, kusantar ajali yake yi.” Na faɗa
cikin sautin kuka.
A
maimakon Sayyid ya tauyasawa halin da nake ciki, a cikin hamagancinsa da
shirmensa kawai sai ya bushe da matsananciyar dariya.
“Hahaha!
Kamar fa Azara’ilu yana jinkirin ɗaukar
ran nan bari na taya shi.”
Rufe
bakinsa ke da wuya ya fisgo yaron da ke kwance a kan cinyata da ƙarfi ya maka shi da ƙasa.
Tamkar
bulo ya faɗo daga hannun magini haka salwantaccen
yaron ya faɗo daga hannun bugaggen ubansa da wani
sauti ‘Tim!’.
“Innalillahi
wa Inna ilaihir raji’un!” Na faɗa a rikice, na miƙe a kiɗime
na yi kan yaron tare da ɗago shi ina jijjiga shi faɗar
nake, “Sabir! Ɗana! Sabir ka motsa,
ka yi mini magana!”
Sai
dai ina! Tuni ruhinsa ya yi bankwana da gangar jikinsa.
Da
na fahimci hakan cikin kuka na shafe idanunsa, na shimfiɗar
da shi a ƙasa kan shimfiɗarmu
na rufe shi da zani, na koma gefe ina ruzgar kuka na fitar hankali.
Shi
kuwa Sayyid ya koma gefe sai tsala dariya yake cikin ficewar hayyaci, “Wai har
ya mutu ne? Dalla ki daina kuka, ba ga ni nan ba, za ki samu wani lafiyayyen ɗan
da ya fi wannan ma.”
Tun
da nake a duniyata ban taɓa jin na tsani wani ɗan’adam
ba kamar yadda na tsani Sayyid a ranar. Na tsine wa kayan maye da wanda ya ƙirƙiri
shan su sau ba adadi, duk a wannan ranar.
Ba
don alƙawarin da na ɗaukar
wa margayiyar mahaifiyata ba, da a ranar ba abin da zai hana ni neman takardar
sallama, ko na huta da ƙunci
da azabar gidansa.
Washe
gari da Sayyid ya tashi ya fuskanci abin da ya faru a daren jiya, ya sha kuka
har da birgima, daga ƙarshe
ma bai samu damar zuwa maƙabarta
ba tsabar baƙin cikin da yake ciki
na kashe babban ɗansa da yafi soyuwa a ransa.
A
wannan ranar ne kuma bisa ga tilas muka bar gidan, ba tare da mun samu damar
yin makoki a cikinsa ba.
Sama
da sati biyu ina fushi da mijina a dalilin wannan abu, na jima ba na iya bacci
sakamakon tunawa da waccan baƙar
ranar da nake yi.
Wata
rana da misalin ƙarfe
shida na yamma na dawo daga ziyarar ahalina, na shiga sabon muhallin namu. Tun
daga soro nake ganin hayaƙi
yana tashi, wannan dalilin ya sa na ƙara
sauri kamar zan wuce ƙafata.
A
tsakar gidan na ci birki ina ƙare
wa fasassun kwalabe da ƙonannun
takardun kallo, hayaƙi
duk ya turniƙe gidan.
Sautin
shessheƙar kuka mai ƙarfi ta fara kawowa kunnena ziyara,
‘Waye
mai wannan kukan?’
Tambayar da ta ziyarci zuciyata kenan. “Inna!”
Na faɗa a
razane, ban san lokacin da na sake hannun Safna ba na nufi ɗakin
Inna gadan-gadan, domin kamar daga can sautin ke fitowa.
Zuwana
tsakankanin ƙofofin guda biyu ne
ya raba mini hankali gida biyu, domin sai na ji kamar a duka ɗakuna
biyun kukan ke fitowa sau bibbiyu.
Ban
tsaya dogon nazari ba, na shige ɗakin
Inna da ke bangaren hagu.
A
kwance na same ta cikin jini tana mayar da numfashi.
“Inna
me....me ya same ki?” Na faɗa cikin tsinkakken sauti.
Na
kai hannu zan kama ta cikin kuka ta ce “Kada ki taɓa
ni, ki tafi ki bar ni, raɓar ku zunubi ne a gare ni,
ki bari na tafi a wanke.”
Na
kalli cikin idonta da ruɗaɗɗiyar
fuskata, a take na karanto damuwar da ke zane a allon fuskarta. Kawai sai na
fice da gudu cikin damuwa na yi ɗakinmu,
Safna ta bi bayana a ɗimauce.
A
lokacin kuma magariba ta kawo kai don haka ɗakin
ya yi duhu. Shessheƙar
kukan da na jiyo ce ta alamtawa ƙwaƙwalwata cewar Sayyid yana cikin ɗakin,
hakan ya saka ni ƙarasawa
ciki a hanzarce.
Na
tarar da shi ya haɗa kai da guiwa yana rera
kuka tamkar yaron goye. Cike da ƙarfin
hali na juya na ja hannun Safna na kai ta maƙwafta,
a can na ajiye Karim na juyo zuwa gida yayin da nake karanta wasiƙar jaki. ‘Meke faruwa? Ruwa fa ba ya
tsami banza.’
Ɗakinmu na koma na same shi cikin tausasa
harshe. “Me ya ƙuntata
rayuwar mijina da yake yi mini asarar hawayensa haka?”
Ya ɗago
kansa tare da zuba mini jajayen idanunsa da suka canza launi, ya sake fashewa
da kuka. Da ƙyar na lallashe shi.
Cikin
sautin kuka ya ce, “Na shiga uku Zainab! Na ɗebo
ruwan dafa kaina, ni da albarka mun yi hannun riga, ni tsinanne ne, ba zan sake
haɗa
hanya da alkhairi ba a rayuwa.”
Kalamansa
sun gigita duniyata, sun yi tsauri a sikelin auna fahimtata, sai kawai na zuba
masa kadarar mujiyata, alamun neman fitilar da za ta haska mini ma’anar
kalamansa.
“Na
fasa wa Mahaifiyata kai da kwalba...”
Kuka
ya fara cin ƙarfinsa, ya ja dogon
numfashi ya ce “Na yi wa Mahaifiyata fyaɗe.”
“Na
yi wa Mahaifiyata fyaɗe.”
“Na
yi wa Mahaifiyata fyaɗe.”
“Na
yi wa Mahaifiyata fyaɗe.”
Wannan
sautin ne yake ta yi mini amsa amo a kunnena, kafin lantarkin da ke janyo
sautuka zuwa ga masarrafar jina ya ɗauke.
Na
yi faɗuwar
‘yan bori a ƙasa.
‘Ya
Ilahi! Wannan wace irin makauniyar rayuwa ce?’
Ko
bai faɗa
ba, hasashena ya hakaito mini komai da ya faru.
Idan
na kintata dai-dai ranar ma kayan mayen nasa ya shawo ya dawo gida a bige, shi
ne giyar mayen ta ɗebe shi zuwa ɗakin
Inna da tunanin nan ne muhallin da ya dace da zuwansa. Za ta yi yunƙurin dakatar da shi sai dai wanda ya yi
nisa ba zai ji kira ba, hankalin da ya gushe bayani ba zai dawo da shi ba. Shi
ne ya afka mata a tsammaninsa ni ce.
Kafin
na gama farfaɗowa daga shokin ɗin
da kalamansa suka ba ni na jiyo shi yana faɗar, “Allah
ya tsine wa giya da duk wani nau’in kayan maye. Wallahi daga yau ba zan sake taɓa ko
da sigari ba, na ga izina.”
Cikin
wani irin yanayi yake zancen sannan ya sake cewa “Ka cutar da ni Habib, da ka
sanya ni a halaka ka yi amfani da dukiyarka wurin siya mini giya, ga shi ka taɓar
da rayuwata.”
Sai
a wannan lokacin ne mutuwar Sabir ta dawo mini sabuwa, tsanar halayen Sayyid ta
linku a zuciyata.
Na ɗago
idona na watsa masa mugun kallo.
“Da
ma tsalle ɗaya ake yi a faɗa
rijiya, idan an shiga kuma sai a yi uku ma ba a fito ba. Irin wannan ranar ce
nake jiye maka zuwanta, amma da yake mai rabon shan duka ba ya jin kwaɓo
sai ka yi biris da kalamaina. Yau wa gari ya waya?”
Ranar
a haka hargitsattsen mijin nawa ya raba hargitsattsen daren yana kuka,
hargitsattsiyar fuskarsa ta bayyanar da hargitsin da ke cikin hargitsattsiyar
zuciyarsa.
A
safiyar wannan ranar ne na tashi da matsananciyar faɗuwar
gaba da kasala. Sai wuraren ƙarfe
tara na safe na fito daga ɗakina jiki a sanyaye, na
nufi ɗakin
Inna ina takawa a hankali tamkar kazar da ƙwai
ya fashewa a ciki.
‘Ko
da wane ido zan kalli wannan baiwar Allah?’ Da wannan tunanin na daure na sa
kai a ɗakin.
“Assalamu
alai...”
Sallamar
ce ta maƙale a ƙasan
maƙoshina sakamakon yin arba da
sandararriyar gawarta a kan gadon da na yi. A hanzarce na ƙarasa na ɗora
yatsana a saitin mazuƙan
iskarta, don na tabbatar da zargina a kanta.
“Innalillahi
wa Inna ilaihir raji’un! Mun shiga uku, Sayyid!” Na faɗa
ina ƙwala masa kira da ƙarfi.
Kafin
na gama rufe bakina ya faɗo ɗakin
tamkar wanda aka ingizo.
“Me...
Me ya faru?” Ya tambaya a dabarbace.
Ko
da na labarta masa abin da ke faruwa sai gani na yi ya zube a ƙasa ‘sharaf!’ Kamar tsohuwar katanga.
Silar
zuwan mu asibiti kenan, wanda kuma ga abin da likita ya gama faɗa
mini game da rashin lafiyar tasa.
Nan
take ƙwaƙwalwata
ta tafi tunanin Ziko, wani matashi da ke yankinmu wanda ya jima yana
shaye-shaye lokacin ina budurwa. Amma zuwa yanzu labarin ya zama tarihi a
sanadiyyar faɗakarwa a kan illar sha da fataucin
miyagun ƙwayoyi da tallafin koya sana’a da wani ɗan
kasuwa mai kishin al’umma ya ƙaddamar
ga wasu ƙididdigaggun matasa na yankinmu, Ziko
yana daga cikin waɗanda suka samu horon. Yanzu
haka ya nisanci shaye-shaye da abokan banza ya zama nagartaccen mutum har ma ya
yi aure yana zaune ƙalau
ga sana’ar ɗinki da yake koyarwa wasu matasan abin
da ba a taɓa tsammani ba.
Gatan
da mijina bai samu ba kenan, shi ma na san wataƙila
da shaye-shayensa ya zama tarihi.
Ina
ma ace gwamnati ko masu hannu da shuni za su samar da wani tsari na tallafa wa
masu shaye-shaye a unguwanni, da kuma sama musu sana’ar dogaro da kai. Tabbas
da za a samu sassauci sosai na yawan shaye-shayen da yake neman ƙone ƙasata
kamar wutar daji.
Da
ma in dai ba zaman banza, ba a ƙunci
a banza, muddin ba ƙunci
ba shaye-shaye a banza.
Yau
dai ga inda rashin abin yi da biyewa abokan banza ya kai mijina.
Da a
ce ya samu irin wannan tallafin kafin ya yi fargar jaji wataƙila da bai shiga wannan yanayin da
koyaushe zai iya tafiya ya bar ni da ƙuncin
da zai zame mini lumbu-lumbu wutar ƙaiƙayi da
za ta ci gaba da zurɗar zuciyata har zuwa
numfashina na ƙarshe ba.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.