Citation: Rabiu BASHIR (2020). Zuga Da Yabau A Bakandamiyar Ibrahim Narambaɗa. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. .8 Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660
ZUGA DA YABAU A BAKANDAMIYAR IBRAHIM NARAMBAƊA
Rabiu BASHIR
Tsakure
Waƙoƙin fada waƙoƙi ne na musamman da ake shirya su cikin harshe nagartacce mai kama jiki
tare da sanya karsashi domin a wasa tare da fayyace isa da muhibba ta wani
basarake. Bakandamiyar Ibrahim Narambaɗa ɗaya ce tamkar-da-goma a
ire-iren waɗannan waƙoƙi domin ta haskaka tare da
fayyace asali da kwarjini da kuma cikar iko na sarkin Gobir na Isa Amadu Bawa.
Wannan maƙala ta yi ƙoƙarin nazartar tubalan zuga da yabau ne daga cikin bakandamiyar Ibrahim
Narambaɗa domin ta fayyace yadda makaɗin ya sarrafa su ya yaba maigidan nasa. Maƙalar ta tabbar da cewa makaɗin ya yi nasara wajen taskace nau’o’in zuga da
yabau tare da sarrafa su wajen bayyana martaba da asali da buwaya da kuma
jarumtar sarkin.
1.0 Gabatarwa
Waƙa ɗaya ce daga cikin ɓangarorin adabin
harshen Hausa, wadda a cikinta ne fasihai ke ɓarje guminsu cikin harshe mai yalwa da
kama jiki domin ganin sun isar da wani saƙo cikin armashi tare
da burge mai saurare. Tubalan zuga da yabau wasu ne daga cikin tubalan da makaɗan fada ke sarrafawa
domin su gina waƙoƙinsu cikin harshe mai burgewa gami da zalaƙa. Tarihin waƙoƙin fada a ƙasar Hausa ba zai
cika ba har sai an fayyace matsayin makaɗa Ibrahim Narambaɗa, wanda ya ba da
gudummuwa isasshiya wajen waƙe sarakunan ƙasar Hausa da dama,
tare da haɓakawa gami da taskace
al’adun Hausawa, musamman kasancewarsa makaɗi mai tarin hikima da azanci, wanda waƙoƙinsa kan taɓoɓangarorin rayuwar
al’uma mabambanta, kuma kasancewarsa wayayyen makaɗi wanda ya san ciki
da wajen zamanin da yake ciki kamar yadda Bunza (2009, sh. 22) ya tabbatar.
Bakandamiyar Ibrahim Narambaɗa kuwa kamar yadda masana irin su Muhammad (1981), da
Bunza (2009), suka tabbatar ita ce waƙar makaɗin mai gindin
“Gwarzon Shamaki na Malam Toron Giwa Baban Dodo ba a tam ma da batun banza”,
wadda waƙa ce da suka tabbatar cewa duk waƙoƙinsa bai yi kamar ta
ba, domin waƙar tana cike da tarin azanci da hikima tare da nuna
baiwar da Allah ya yi wa makaɗin a sarari.
An haifi makaɗi Narambaɗa a wajajen shekarar
1890, a unguwar Dembo, da take garin Tubali cikin gundumar Jangeru a ƙaramar hukumar
Shinkafi ta jahar Zamfara a wannan lokaci. Cikakken sunan mahaifinsa shi ne
Buhari amma an fi saninsa da Maidangwale, Gusau (1987), da Bunza (2009), wanda
ake ganin ya samu wannan suna ne daga sana’arsa ta alewa wadda a cikinta ne ya
yi fice har aka san shi, baya ga kokawa da kuma sana’ar noma da yake taɓawa. Asalin mahaifin
Narambaɗa Kambarin Barebari
ne, wanda ake ganin asalin garinsu shi ne Katuru kafin ya koma garin Galadi da
zama, inda a can ne ya auri mahaifiyar Narambaɗa mai suna Riba (Bunza, 2009, sh. 12),
wadda ake ganin ta samu wannan suna ne kasancewar ita kaɗai ce ta rayu a
hannun mahaifiyarta sakamakon rasuwa da sauran yayyenta kan yi bayan
haihuwarsu. Asalin Riba mutumiyar Badarawa ce, kuma mahaifinta shi ne Sarkin
makaɗan Badarawa na wancan
lokacin. Ke nan a iya cewa Narambaɗa ya yi gadon kiɗa ne ta wajen
mahaifiyarsa. Cikakken sunan Narambaɗa shi ne Ibrahim kamar yadda mahaifinsa ya raɗa masa, amma da ya
taso sai wasu na kiransa da ‘Iro’, kafin daga bisani ya samu laƙabin ‘Narambaɗa’, wanda ake ganin
ya samu wannan suna ne a sanadiyyar wata karyarsa da yake wa laƙabi da ‘Rambaɗa’ wadda yake yawon
farauta da ita, (Bunza, 2009, sh. 15-16).
A wajen iyali,
Narambaɗa ya auri mata guda
uku da suka haɗa da Hana, wadda ita
ce ta haifi babban ɗansa (Namori). Sannan
daga baya ya auri ‘Yaƙƙaya, sai kuma matarsa ta uku da ya aura mai
suna Kande. Allah ya azurta makaɗin da ‘ya’ya da dama maza da mata, da kuma
jikoki. Narambaɗa ya shahara sosai a
fannin kiɗa da waƙa, wanda har ana
ganin yana daga cikin makaɗan fada na ƙasar Hausa da Allah
ya yi wa tarin hikima da zalaƙa. Makaɗin ya rasu a ranar juma’a 30 ga watan
Junairu, 1963, bayan jinya da ya yi fama da ita, (Bunza, 2009, sh. 10-18).
1.1 Bakandamiyar Ibrahim Narambaɗa
Bakandamiya ko
makandamiya kamar yadda aka fi cewa a yankin Sakkwato, kalma ce ta Hausa tilo
kuma mace, wadda aka ciro daga kalmar aikatau ta ‘Kandama’ wadda take nufin
kwashe abu gaba ɗaya, ko shiga cikin
wani abu (kamar ruwa ko matsala). Kalmar ‘Bakandamiya’ tana da alaƙa da waƙa, kuma a nahawunce
sukan daidaita da juna kasancewar kalmar ‘Waƙa’ ita ma kalma ce ta
suna tilo kuma mace, (Muhammad, 1981, sh. 1-2) da kuma (Bunza, 2009, sh. 274).
Bunza (2009), ya bayyana cewa Bakandamiya ita ce waƙar da ake jin shi
kansa mawaƙin na jin waƙar, yana son ta kuma
bai da kamarta a duk cikin waƙoƙinsa, jama’a kuma sun
aminta da hakan. Sannan ya ƙara da cewa irin wannan waƙar takan kasance ne
wadatacciya wadda za a iya saurara a ko’ina kuma a gaban kowa. Ke nan a taƙaice a iya cewa
Bakandamiya ita ce wata waƙa mai tsawo da yalwa wadda wani makaɗi ya shirya kuma a
cikinta yake zuga kansa ya kuma yaba wa wanda yake so, sannan ya zambaci wanda
ya ga dama, kuma ta kasance shi kansa yana sauraron ta yana kuma son ta domin
azancin da ke cikinta ya zarce na dukkan sauran waƙoƙinsa.
Babu shakka masana
sun tabbatar da cewa waƙar Narambaɗa wadda ya shirya wa uban gidansa sarkin
Gobir Na’isa Amadu Bawa ita ce Bakandamiyar makaɗin, kamar yadda shi kansa ya tabbar da
hakan a cikin waƙar, inda ya ce:
Jagora: Kowa ya zaka kallo ya karkaɗe kunne nai
Yara: Ga bakandamiya za ni yi cikin manyan waƙoƙi
Jagora: Na jiya Jankiɗi
Yara: Ya yi tai uwar waƙar sai nai tau
Jagora:Na jiya Zamau
Yara:Ya yi tau uwar waƙar sai nai tau
Jagora:Na jiya Gurso
Yara:Ya yi tai uwar waƙar sai nai tau
Idan aka dubi ɗan waƙar Narambaɗa ya kira sunayen
wasu fitattaun makaɗa ne waɗanda ya tabbatar duk
suna da tasu Bakandamiyar, wanda a daliln hakan ya ƙarfafa shi ya ƙirƙiri tasa, watau ita
wannan waƙa ta ‘Gwarzon Shamaki’. Haka kuma Bunza (2009), ya kawo ƙwararan hujjoji duk
domin ya tabbatar da cewa ‘La shakka’ wannan waƙa ita ce bakandamiyar
makaɗin, inda ya tabbatar
da cewa waƙar ta fi dukkan waƙoƙin Narambaɗa tsawo, kuma salonta
ya bambanta da salon dukkan waƙoƙinsa, haka kuma
hikimomi da falsafar da waƙar ke ƙunshe da su, babu
kamar ta, (Bunza, 2009, sh. 276-277).
2.0 Nau’o’in Zuga A Bakandamiyar Narambaɗa
Zuga a cikin waƙa ta ƙunshi amfani da
kalmomi da jumloli waɗanda ke kambama tare
da koɗa wanda ake waƙewa, ta yadda za a sa
kansa ya kumbura har ya rinƙa jin ya fi kowa, a wani lokacin har
ta sa ya aikata aikata wani abu na bajinta, ko kuma ya yi wata kyauta wadda ba
dole ba ne ya yi irinta idan ba zuga shi aka yi ba.
Bello (1976), ya
bayyana cewa zuga tana kama da yabo wajen faɗin abubuwa na ƙwarai da mutum ya yi,
sai dai a wajen zuga ana ƙara gishiri a faɗi abin da ba haka nan yake ba, amma babu
wanda zai damu tun da an san niyyar ta a kumbura kan mutum ne. Ya ƙara da cewa babban
harsashin da aka gina zuga a kai shi ne, a nuna wa sarki ya fi kowa, babu kamar
sa kuma yana iya yin abin da kowa ba zai iya yi ba, (Bello, 1979, sh. 29). Shi
kuwa Gusau (2002), cewa ya yi zuga wata magana ce da ke ɗauke da wasu kalmomi
da ake amfani da su a koɗa wani a cicciɓa shi, a nuna
fifikonsa kan wasu. Dumfawa (2004) kuwa, ya fayyace ma’anar zuga ne ta fuska
biyu, inda ya ce ta fuskar harshe zuga na nufin hurawa. Sannan ya ce a magana
ta yau da kullum kuwa zuga tana nufin rura ko hura mutum ko kumbura shi, ko
harzuƙa shi. Sannan kuma sai ya kasa zuga zuwa gida uku, inda
ya ce a kwai zuga Kumburau, da zuga Kariyau da kuma zuga Ingizau (sh. 223-225).
Ataƙaice za a iya cewa
zuga ta ƙunshi zaɓo kalmomi masu kumbura mutum a yi amfani da su a cikin waƙa domin a ɗaukaka matsayin wanda
ake waƙewa a nuna ya fi kowa, har shi kuma ya rinƙa jin ya fi kowa ɗin, kuma zai iya
aikata komai, a wani lokacin har a ingiza shi ya aikata wani aiki na isa ko
bajinta, wanda haka kawai ba zai yi shi ba idan da ba a zuga shi ba.
2.1 Zuga Kumburau
Wannan ita ce nau’in
zuga da mawaƙan fada suke amfani da ita domin su kumbura wanda suke waƙe wa har ya ji yana
cika yana batsewa tamkar ana hura shi. Haka kuma idan zugar ta kama wanda ake
yiwa ita, zai ji zuciyarsa na kumbura, ya ji cewa ya kai wani matsayi. Kuma
irin wannan zugar ce sukan sa zuciyar wanda ake yiwa ita ta dunga yi masa wasu
saƙe-saƙe, (Dunfawa, 2004,
sh. 225).
Watau zuga kumburau,
zuga ce da makaɗan fada ke amfani da
ita a lokacin da suke waƙe wani basarake, inda za su yi amfani da kalmomi masu taɓa zuciya su tsokalo
zuciyar basaraken ta hanyar kirara shi da cicciɓa shi, har kuma zuciyar tasa ta rinƙa raya masa cewa ya
buwaya kuma ya zarce kowa, don haka sai kawai ya shiga faɗi yana kumburi.
Kasancewar Narambaɗa fitaccen fasihi a
kiɗan fada, ya yi amfani
da irin wannan nau’in zugar tun daga gindin Bakandamiyarsa inda ya ce:
Jagora: Gwarzon Shamaki na Malam Toron Giwa
:Baban Dodo ba a tam ma
:Da batun banza.
Idan aka duba tun
daga gindin waƙar, za a iske cewa Narambaɗa ya fara ta ne da zuga gwanin nasa,
wato sarkin Gobir Na’isa Amadu Bawa, inda yake nunu cewa shi fa gwarzo ne ko a
cikin sarakuna, kuma shi toron giwa ne, wanda sai namijin giwar da ya riƙa kuma da ma ko a
garken giwa guda ɗaya ake samu ba a yin
biyu. Sannan sai ya nuna cewa ba fa a iya tunkararsa da zancen banza, wanda da
zarar basaraken ya ji wannan zugar, zuciyarsa za ta rinƙa gaya masa cewa
lallai ya buwaya kuma ana shakkarsa, don haka sai kawai ya rinƙa faɗi yana kumbura.
A wani ɗan waƙar cewa ya yi:
Jagora: Amadu ɗan Alu gida nai na Isa
Yara:Ya yi sarki kuma ga ɗiyan da yah haifa sun
yi,
:Kuma yau ga ta nan ga ɗan jika nai ya hau,
:Dangi sai ku hanƙure shi na har Mahdi
A nan, Narambaɗa ya zaɓi ya zuga gwanin nasa
ne ta hanyar kumbura kansa ya nuna cewa ya fa gaji sarauta ne tun daga kakansa,
haka kuma babansa ma ya yi sarki, wanda ko da mutum ya zama sarki kamar sa, to
kila shi babansa ko kakansa ba su yi sarauta ba, don haka bai kai shi ba, domin
shi ɗan gado ne. Haka kuma
don ya sake kumbura masa kai, sai ya bayyana cewa, duk fa wani mai jiran
sarautar Gobir ta, Isa to fa ya haƙura, domin gwaninsa
ne a kan karagar mulki, kuma shi ne zai yi ta yin sarautar har Mahadi ya
bayyana. Babu shakka ko da mutum bai san daɗin sarauta ba, aka ce masa mutum ne yake yin
wani abu, kuma a na so kowa ya haƙura don shi zai ci
gaba da yi har tsawon rayuwarsa, to wannan magana ta isa ta sa mutum ya yi
doro, ya kumbura tare da ƙara jin shi shi ne, kuma dole a sa masa ido a kuma bi
shi.
A wani ɗan waƙar kuwa da Narambaɗa ya tashi zuga
gwanin nasa, ta yadda zai ƙara jin lallai fa ya isa, kuma dole a
dama da shi, sai ya ce:
Jagora: Ai dag ga Kaduna har Gusau ƙarewar Hausa.
Yara: Yau kowace shawara ta zamanin Turawa,
:Amadu ba a yin ta sai ya sa hannunai,
:Zan kau ƙoƙari garai da sanin
hujjoji,
:Gwarzon Shamaki na Malam Toron Giwa,
:Baban Dodo ba a tam ma
:Da batun banza.
Makaɗi Ibrahim Narambaɗa ya zuga sarkin
Gobir Amadu Bawa ne ta hanyar yin fyaɗan ‘ya’yan kaɗanya, ya nuna cewa duk sarakunan ƙasar Hausa tun daga
Gusau har zuwa garin Kaduna babu wanda ya fi shi sanin makamar mulki da iya
aiki da kuma iya tafiyar da jama’a, saboda haka wannan ya sa duk wani abu da za
a yi sai an nemi shawararsa da sa hannunsa. Lallai kam wannan zuga ta isa ta sa
zuciyar basaraken ta rinƙa gaya masa cewa lallai fa ya isa sarki, kuma duk wani
mai sarauta a bayansa yake domin kuwa yankin da makaɗin ya ambata cike
yake da manyan sarakuna, amma kuma sai ga shi an nuna duk ba su kai shi ba.
2.2 Zuga Kariyau
Ta ƙunshi nau’in zuga ce
wadda makaɗan fada ke sarrafawa
musamman domin samar da kariya ga wanda suke waƙewa daga abokan
hamayya da kuma sauran mabiya. Irin wannan zugar ita ce Dunfawa (2004), ya nuna
cewa makaɗan fada na amfani da
ita don kare wanda suke yi wa waƙa daga hawan ƙawara na abokan
hamayya. Sannan ya ƙara da cewa, a wani lokacin sukan yi amfani da ita don
kare wanda suke yi wa waƙar daga waɗanda yake wa shugabanci, a kan kada su
kuskura su yi wata jayayya da shi. Dumfawa (2004), ya ƙara nuna cewa a cikin
irin wannan zugar, makaɗan kan bayar da tsoro
game da shi basaraken ta hanyar nuna cewa shi ɗin gagarau ne kuma wandara. Sukan kuma
nuna cewa duk wanda bai ji bari ba zai ji woho, domin duk wanda ya ja da shi to
shi ne a ƙasa. A wani lokacin har sukan ambaci irin nasarorin da ya
taɓa samu a kan wasu
abokan hamayyarsa da suka yi jayayya da shi. (Dumfawa, 2004, sh. 227-228).
A taƙaice dai zuga kariyau
nau’in zuga ce da makaɗan fada kan sarrafa
domin su zuga basarake da nufin ba shi kariya daga dukkan wani mai sha’awar faɗa masa ko haye masa,
ta hanyar bayyana ƙarfinsa da nasararsa a kan duk wanda ya nemi jayayya da
shi. Babbar manufar irin wannan zugar ita ce, sarkin ya samu damar tafiyar da
sarautar tasa ba tare da samun wata matsala ko tarnaƙi ba daga wurin wani
abokin hamayya ko mabiyi, inda za a karya zuciyarsa ya ji tsoron haye wa
basaraken tare da yi masa biyayya ko da kuwa ba ya so.
Irin wannan fasahar ta zuga kariyau ce
Narambaɗa ya sarrafa a cikin
Bakandamiyarsa, inda ya ce:
Jagora: Arna sun san halin Alu Maisaje na
Isa,
Yara: Amadu kakanka na mazajen gaba an nan.
Jagora: Sun san Bello yac ci Gawon Gazau,
Yara: Da yac ci Alƙalawa Atiku yad
darzaza Bauchi,
:Iro na Kwantagora yac ci mutanen Gwari,
:To dut martabarsu na nan gun hannu nai.
Narambaɗa ya zuga gwanin nasa ne ta hanyar kawo
jarumtar kakanni da iyayen sarkin da kuma ire-iren nasarorin da suka ci na yaƙi ga abokan
hamayyarsu, da irin garuruwan da suka mamaye a lokacin sarautunsu. Haka nan
kuma, ya nuna cewa duk irin jarumta da ƙarfin waɗannan sarakunan yanzu
yana nan ne a wurin gwanin nasa domin daga gare su ya yi gadon sarautar. Da
zarar abokin hamayyar basaraken ya saurari makaɗin, zai ƙara firgita da kuma
razana da sarkin, sannan ya ji tsoron faɗa masa, domin an fayyace jarumtarsa a fili
wadda ya gada tun kaka da kakanninsa, wanda hakan wata kariya ce ga basaraken
da kuma mulkinsa.
A wani ɗan waƙar kuwa, Narambaɗa ya zuga sarki Amadu
ne ta hanyar fayyace rinjayen basaraken a kan sauran sarakuna ‘yan uwansa, inda
ya ce:
Jagora: Bana Amadu Hausa ka yi rinjaye ni na
yi,
Yara: In an ce Isa ba ka jin an ce wani sarki
:Ni kau dut Hausa ba ka jin waƙa bayan tau.
Makaɗin na ƙoƙarin zuga sarkin ne
ta hanyar fito da rinjayensa da girmansa a kan sauran sarakunan ƙasar Hausa, inda ya
nuna cewa duk wani sarki fa a fagen sarauta da jarunta bai kai gwanin nasa ba,
kai hatta shi kansa da yake makaɗinsa babu wani makaɗi da zai iya jayayya
da shi duk ƙasar Hausa. Tabbas da abokan hamayyar sarkin sun ji
wannan ɗan waƙar, za su ƙara karaya su shiga
taitayinsu, tare da amincewa kansu lallai sarkin Gobir na Isa ya fi ƙarfinsu, wanda hakan
wata kariya ce ya samu.
A wani wurin kuwa da Narambaɗa ya tashi zuga
sarkin Gobir na Isa, sai ya fito da ƙarfin mulkinsa a fili
da yadda yake aiwatar da hukunci ga duk wanda ya so ya kawo wargi a cikin ƙasarsa. Inda ya ce:
Jagora: Yanzu Amadu izni garai na ɗaure ashararu,
Yara: Yau ƙasatai babu ko guda
sun ce sun tuba.
Duk wani talakan da ke ƙasar
sarki Amadu Bawa, da ya saurari Narambaɗa a
wannan gaɓar zai ji tsoron aikata wani aikin
laifi, domin kuwa ya tabbatar da makomarsa gidan maza, kamar yadda basaraken
yake da izni na ɗaure duk wani mai ƙoƙarin
tayar da zaune tsaye. Haƙiƙa wannan wata babbar kariya ce makaɗin
ya ba sarkin ta hanyar zuga shi, wadda za ta sa duk wani mai niyyar faɗawa
ga aikata wata ɓarna, ya shiga taitayinsa.
2.3 Zuga Ingizau
Wata nau’in zuga ce damakaɗan fada ke amfani da
ita su ingiza sarki ya kai ga aiwatar da wani abu wanda ba shi da niyyar yi, ko
ya fasa aikata wani abu wanda da ya yi niyyar aikatawa. Dunfawa (2004), ya
bayyana irin wannan zugar da cewa ita ce mawaƙa suke amfani da ita
domin su tunkuɗa ko su ingiza
basarake ya aikata wani abu wanda da ba domin zugar ba, da ba zai aikata shi
ba. Ya kuma ƙara da cewa, ana kuma iya amfani da irin wannan zugar a
sa Basarake ya fasa aikata wani abu wanda da ya yi niyyar aikatawa. Ya kuma
nuna cewa, ana aiwatar da irin wannan zugar ne a wasu lokuta ta hanyar danganta
ta da wani abu na tarihi, sai ta zama kamar an yi wani fami ne ga wani rauni
wanda ya kusa warkewa, (Dunfawa, 2004, sh. 229).
A taƙaice dai zuga ingizau
ta ƙunshi
sarrafa wasu kalmomi ne a waƙa waɗanda za su iza sarki tare da sa shi ya
aikata wani abu kamar kyauta ko wani alheri ko rangwame ga wani, ko da kuwa bai
yi niyyar yin hakan ba. Haka kuma, amfani da irin wannan zugar takan sa sarkin
ya fasa aikata wani abu wanda ya ƙudiri aniyar
aiwatarwa kafin a zuga shi.
Irin wannan zuga ce Narambaɗa ya yi amfani da ita
a cikin bakandamiya ya nuna wa Amadu Bawa cewa, ba domin shi ba da kuma irin ɗaukin da ya kawo
masa, bai san inda zai sa kansa ba a yayin da ruwan sama ya cinye musu dukkan
amfanin gonar da suka shuka, inda ya ce:
Jagora: Mui ta kiɗiɗiya,
:Kamar mu yi borin botso.
Yara: Bana shi za mu yi,
:Ruwa sun canye gero.
Jagora: Gulbi ya tattaro ruwa,
:Fadama dut ta sha.
Yara: Ya kashe gero,
:Ya kashe dawa,
:Balle wake.
Jagora: Ba don taimakon da sarkin Gobir yai
ba,
Yara: Da mai dogon cikin ga
:Ya watce mun kaya.
Jagora: Sarki ya ban sule ɗari,
:Ya ban kyankyandi.
Yara: Ba don mu kashe ba,
:Don mu san damma yab bayar.
Narambaɗa ya yi zuga ne ga uban gidansa ta hanyar
ingiza shi domin ya yi musu kyauta ta kashe ƙishi, inda ya nuna
cewa bana cinsu da shansu ya dogara ne gare shi, domin duk abin da suka shuka
ambaliyar ruwa ta lalata shi. Don haka sai ya umarci yaransa da su yi kiɗa kamar za su yi
hauka saboda cin su da shan su a nan ya ta’allaƙa. Jin wannan zugar
ta sa sarkin Gobir ya yi musu kyauta mai tarin yawa ta kuɗaɗe waɗanda da su ne za su
yi amfani su sayi abincin da za su ci a wannan shekarar.
A wani ɗan waƙar bakandamiyar kuwa,
makaɗin ya zuga sarkin ne
ta hanyar ingiza shi, inda ya nuna wa duniya yadda sarkin ya gyara masa
gidansa:
Jagora: Sai kui mani godiya
:Ga sarkin Gobir na Isa,
:Bana ya gine gidanmu
:Duk ya sa a yi soro,
:Duk da maginan da sunka
:Gine gidan nan.
Yara: Ga sallama fam ashirin da shidda
:Sarkin Gobir yab bai,
Jagora: Bai sa jan sule ba
:Duf fefa yab bayar.
Wannan hikima ta zuga sarki, ita ce har ta
ingiza sarkin Gobir Amadu Bawa ya sa aka gine gidan su makaɗi Narambaɗa, wanda ƙila da bai yi azanci
ya nemi duniya ta yi masa godiya wurin uban gidan nasa ba, to ba dole ba ne
hankalin sarkin ya kai ga tunanin ya kamata a gyara gidan makaɗin ba kamar yadda ya
yi.
3.0 Yabau a
Bakandamiyar Ibrahim Narambaɗa
Kalmar Yabau ‘Euloƙues’ kalma ce ƙirƙirarriya a Ingilishi,
kuma wanda ya fara ƙirƙirar kalmar shi ne wani masani da ake kira Kunene (1971),
inda ya ce “Daga yau za ariƙa amfani da ƙirƙirarriyar kalmar
‘Yabau’ domin bayyana dukkan kalmomin da suka shafi yabon wani gwarzo, ko da
kuwa sun kasance suna ne ko dangantawa”. Wato a nan kalmar ‘Yabau’ za ta
kasance baddalawa ne ko faɗaɗawa a kan kalmar yabo
ko yaba, ko yabi, ko yabe, ko kuma yabawa, da nufin bayyana ko dai Kalmar yabo,
ko yankin yabo ko kuma yabo a cikin jumla gaba ɗaya. Yabau a cikin waƙa shi ke siffanta
jarumi da ayyukan jaruntarsa ta hanyar amfani da kwalliya ko alamta shi da wasu
abubuwa, haka kuma akan yaba wa gwarzo tsurarsa, a wani lokaci kuma a danganta
shi da wasu mutane. Irin muhimman kalmomi da aka kwarzanta barde da su a cikin
waƙa
su ne ake nufi da ‘Yabau’ ba yabo ba. (Tsoho, 2002, sh. 2-143).
Tsoho ya jaddada cewa yabau a Hausa ya ƙunshi kalma ko yankin
magana ko jumlar da aka yi amfani da ita wajen yaba wa gwarzo cikin kwalliya ko
alamci, musamman danganta shi da ƙarfafan dabbobi ko
abubuwa ko yanayi mai tsoratarwa da ake yi. Ya ƙara da cewa yabau kan
siffanta zatin jarumi ya cicciɓa shi, ya kuma ɗaga kimarsa a idon duniya, haka kuma yabau
kan fayyace kimar sarakuna da manoma, ya bayyana kyawawan halayensu da ɗabiu’nsu, saɓanin yabau a waƙoƙin ‘yan tauri da ‘yan
dambe da ɓarayi, (Tsoho 2002,
sh. 145-146).
Har wa yau Tsoho (2002), ya ci gaba da cewa
Umar (1985), ya zayyano fitattun abubuwan da mawaƙa suka fi amfani da
su wajen yaba wa iyayen gidansu, inda ya ce sun haɗa da Giwa, wadda ke
nufin ƙarfi da kammalallen iko, sai zaki, wanda ke alamta
jaruntaka da dattijantaka, sai doki, mai alamta arziki da tasiri, sai kura, mai
alamta handama da zalunci da barazana, sai jaki, mai alamta wawanci, sai raƙumi mai alamta
juriya, sai dila, mai alamta wayau, sai biri mai alamta ɓarna, sai mujiya mai
alamta baƙin jini, sai launin ja, mai alamta matsala ko jaruntaka,
sai launin kore mai alamta ƙaruwa, sai launin baƙi mai alamta rashin
sa’a, sai kuma ruwa mai alamta tsafta da tsarki da ƙarfi da kuma cigaba.
A ƙarshe
sai Tsoho (2002), ya ƙare da cewa yabau tamkar kayan ƙawa ne a kirari da waƙa, kuma kirari da waƙa su ke taskace yabau
su kuma cicciɓa jarumi, su
kwarzanta shi. Sannan ya tabbabatar da cewa a Hausa za a iya raba yabau a ƙalla zuwa gida biyar,
inda ya ce a kwai yabau na kwalliya da yabau siffantau, da yabau aikatau da
kuma yabau na yankin magana ko na jumla, (Tsoho, 2002, sh. 150-159 da 159-202).
A taƙaice dai a iya cewa
yabau wata hikima ce da ake amfani da ita a cikin waƙa ko a kirari domin a
kwarzanta ko kuma a koɗa wani mutum ta
hanyar sarrafa kwalliya ko alamci ko kuma a danganta shi da wasu mutane masu
kima da daraja, domin shi ma girmansa da martabarsa gami da jaruntakarsa da
kuma asali da muhibba su bayyana tare da ɗaukaka a idon duniya.
3.1 Yabau Dangantau
Bahaushe kan ce ‘Sarki baban kowa’, wato a
wurin Hausawa an ɗauka cewa sarki shi
ne gaba da kowa, bisa ga wannan dalili ne ya sa kowa ke girmama shi tare da yi
masa biyayya, kuma da wannan ya sa aka amince masa dangane da yadda yake
gudanar da mulkinsa. Iyaye da kakannin sarki kuwa, an ɗauka cewa yana cin
darajar su ne don haka suke da wata daraja da kima ta musamman, babu ma kamar a
ce sun shahara sosai, kila ga mulki ko ga jarunta ko kuma ga malanta.
Tsoho (2004), ya bayyana cewa baya ga iyaye
da koyaushe akan danganta sarki da su a yaba masa, akwai kuma ‘yan majalisarsa,
waɗanda sukan haɗa da ‘yan uwansa da
kuma wasu daga wasu gidajen sarautun, wani lokacin har da wasu daga cikin
talakawa, kamar su Liman da Alƙali da kuma waɗanda ke da kima a
idanun jama’a. Baya ga ‘yan majalisar sarki, akan danganta shi da abokai ko
wasu aminansa, sannana akan danganta sarki da fadawansa da kuma barorinsa,
(Tsoho, 2004, sh. 8-9).
Makaɗi Ibrahim Narambaɗa ya sarrafa wannan
hikima ta yabau dangantau a bakandamiyarsa domin ganin ya yaba girma da
martabar sarkin Gobir Amadu Bawa. Misali inda ya ce:
Jagora: Amadu Allah ya baka albarkar Shehu
Usmanu,
Yara: Yadda ya yi zaman duniya da imani yaƙ ƙaura.
Jagora: Amadu Allah ya baka albarkar Bello ɗan Shehu,
:Amadu Allah ya taimake ka ya Atiku ɗan Shehu,
:Amadu Allah ya baka albarkar Nana Uwa Daje,
:Amadu Allah ya taimake ka wa Mu’azu ɗan Bello,
:Amadu Allah ya baka albarkar Ummaru ɗan Atiku,
:Amadu Allah ya taimaka maka wa Hassa irin
Mu’azu gidan Bello.
Yara: Shi da yay yi zaman duniya da imani yaƙ ƙaura.
Idan aka duba waɗannan ɗiyoyin waƙar, za a ga cewa
Narambaɗa na ƙoƙarin yaba gwanin nasa
ne, don haka sai ya danganta shi da iyaye da kakanni, inda ya ɗauko tun daga kan
mujaddadi Shehu Ɗanfodiyo ya gangaro kan wasu fitattaun sarakuna, makaɗin ya yi haka ne
saboda ya ƙara fito da kima da darajar Sarki Amadu Bawa ta hanyar
danganta shi da sarakunan musulunci waɗanda suka gabata, sannan ya roƙa masa daraja da
martaba irin tasu.
A wanin wurin kuwa cewa ya yi:
Jagora: Lura arna sun san halin Nagwamatse
Dodon Gwari,
Yara: Amadu kakanka na mazajen gaba an nan.
Jagora: Maza sun san Maiturare Gogarma ɗan Amadu,
Yara: Amadu kakanka na mazajen gaba an nan.
Jagora: Arna sun san akwai Zarto ɗan Shawara,
Yara: Amadu kakanka na mazajen gaba an nan.
Jagora: Arna sun san halin Mua’alleyiɗi na Birni Ƙaya,
Yara: Amadu kakanka na mazajen gaba an nan.
Jagora: Arna sun san halin Alu Maisaje,
Yara: Amadu kakanka na mazajen gaba an nan.
A waɗannan ɗiyoyin waƙar, Narambaɗa ya ya jero sunayen
wasu fitattun sarakunan ƙasar Gobir ne, ya yaba wa sarki Amadu Bawa ta hanyar
dangata su da shi ya nuna cewa dukkan su kakanni ne wurinsa. Yin hakan zai ƙara fayyace daraja da
martaba da kuma kimar gwarzon nasa.
Baya ga iyaye da kakanni da Narambaɗa ya danganta ya yaba
gwarzon nasa da su, ya kuma ce:
Jagora: Tun da nig ga Muhammadu ɗan Shehu,
Yara: Ba ni kwana ban ga Majidaɗi ba.
Jagora: Jiyan Majidaɗi,
Yara: Bawan namijin duniya’
:Toya matsafa Sadauki na Abdu,
:Baban Isa baban Buwai,
:In don nan ka gama lafiya.
A cikin wannan ɗan waƙar, makaɗin ya yaba gwarzon
nasa ne ta hanyar danganta shi da wasu fadawansa irin su Majidaɗi domin ya nuna yadda
sarkin ke zaune da su lafiya. Sannan kuma ya danganta shi da wasu daga cikin
‘yan uwansa da danginsa, sai kuma wasu daga cikin ‘ya’yansa. Yaba wa sarkin ta
hanyar danganta shi da su zai ƙara fayyace girma ne da darajar sarkin
da kuma nuna cewa kowa nasa ne kuma yana zaune lafiya da kowa.
3.2 Yabau Na Kwalliya
Babbar manufar waƙoƙin fada ita ce a yaba
tara da kwarzanta basarake ko ubangida da iyalansa da kuma dukkan masoyansa
domin a ɗaga darajarsu, sannan
kuma idan hali ya yi a muzanta tare da ƙasƙantar da maƙiya da kuma abokan
hamayyarsa.
Tsoho (2004), ya nuna cewa makaɗa kan yi amfani da
yabau na kwalliya ne ta hanyar amfani da sunan dabbobi ƙarfafa, ko wasu
abubuwa masu ƙarfi, ko kuma ma wasu iskoki domin nuna iko da ɗaukaka da kuma nuna
cewa iyayen gidan nasu na iya ci gaba da zama kan mulki ko da magabtansu ba su
so. Ya ƙara da cewa dabbobi da ake amfani da sunayensu a yaba
sarki kan kasance dabbobi ne masu ƙarfin gaske waɗanda ke iya tsare
kansu. Tsoho ya nuna cewa makaɗa kan yi amfani ne da waɗannan abubuwa su yaba sarki kai tsaye
ba tare da wata sakaya ma’ana ba, kuma ana amfani da su ne don a nuna cewa
sarkin da ake yabawa ya buwaya wajen ƙarfi da iya mulki,
(Tsoho, 2001, sh. 4-5).
Makaɗi Narambaɗa ya sarrafa yabau na kwalliaya a cikin
Bakandamiyarsa ya ce:
Jagora: Ai ga Giwa tana abin da takai,
Yara: Ga ‘yan namu na kallonta babu mai damar
cewa komai.
A nan makaɗi Narambaɗa na ƙoƙarin fayyace girma ne
da isa ta sarki Amadu Bawa, don haka sai ya zaɓi ya yaba masa ta hanyar sarrafa yabau
na kwalliya, inda kai tsaye ya kira shi da ‘Giwa’ wadda dabba ce mai girma da
isa da kuma kamala a cikin dabbobin dawa. Haka kuma domin ya ƙasƙantar da sauran masu
adawa da gwarzon nasa, sai su kuma ya kira su da ‘yan namu, wato su ‘yan ƙananan namun dawa ne,
wanda ko a zahiri idan giwa na tsaye duk sauran ‘yan ƙananan dabbobi sukan
shiga taitayinsu ne su ɓuya domin gudun ta
tattake su.
A wani wurin kuwa da ya tashi bayyana ƙarfi da irin galabar
sarkin a kan masu jayayya da shi, sai ya sarrafa yabau na kwalliya ya ce:
Jagora: Ai Baban Shamaki karo sai Rago,
:Bunsuru kau da gabanka kar a jima bakin
banza.
A nan makaɗin na yaba jarumta ne da iya faɗa na gwarzon nasa,
don haka sai kai tsaye ya siffanta shi da rago wanda Allah ya yi wa ƙarfi da iya karo.
Sannan kuma sai ya hori masu jayayya da shi da su kauce kada ya raunata su,
bayan ya kira su da ‘Bunsuru’, wanda ba ya yiwuwa a haɗa shi da rago wajen ƙarfi da iya faɗa.
3.3 Yabau Aikatau
Nau’in yabau ne wanda yake tafiya da aikatau,
so tari yabau aikatau kan zo ne da harɗaɗɗen suna, inda akan haɗa aikatau da suna sai
a kira mutum da shi. Irin waɗannan sunaye sukan nuna irin ayyukan da wanda ake yabo ya
yi ne, ko kuma waɗanda zai yi. Sannan
kuma sunayen sukan samo asali ne daga aikatau, kuma suna zama suna ne a lokacin
da aka ɗafa musu wani abu,
wato a ƙara wa kalmar aiki wani ɗafi don ta sauya ma’ana ta koma suna.
Misali kalmar ‘tanƙwafa’ (aiki), sai a yi mata ƙari da ɗafin /u/ ta koma ‘tanƙwafau’ (suna).
Tsoho (2001), ya nuna cewa an yi amfani da
ire-iren waɗannan sunaye ne a
lokacin ana yaƙe-yaƙe a ƙasar Hausa, kafin
daga baya aka fara amfani da su wajen yabon sarakuna kasancewar sun gaji yaƙi. Haka kuma ya ƙara bayyana cewa
akwai ire-iren waɗannan sunaye da ake
yaba sarakuna da su waɗanda sun samu ne a
dalilin haɗa aikatau da suna ko
haɗa aikatau da aikatau,
misali ci-fansa, ƙi-sake, sa-gudu, toya-matsafa da ƙi-gudu da sauran su.
Su ma ire-iren waɗannan sunaye da ake
yi wa sarakuna kirari da su, Tsoho (2001), ya nuna cewa duk suna cikin nau’in
yabau aikatau. Misalin yabau aikatau a cikin bakandamiyar Narambaɗa:
Jagora: Toya-matsafa Sadauki na Abdu
:Baban Isa baban Buwai
:In don nan ka gama lafiya
Da zaran an ji wannan ɗan waƙar, za a fahimci cewa
ana wasa wani sarki ne tare da yaba masa domin a fito jaruntarsa fili. Don haka
sai makaɗin ya sarrafa yabau
aikatau, inda ya kirara gwarzon nasa da ‘Toya-matsafa’ kuma ‘Sadauki’, waɗanda duk sunaye ne da
ke fayyace jarunta da kuma gwarzantaka.
A wani wurin kuwa cewa ya yi:
Jagora: Ah! Jikan Shehu mai dubun doki ɗan na Ammani,
Yara: Gawurtacce na Magajin Rahin Hausa.
Narambaɗa ya yaba gwarzon nasa ne da kalmar
‘Gawuratacce’, wadda ke nufin wani shahararren jarumi kuma babban sarki, kuma a
iya cewa asalin kalmar daga ‘gawurta’ ta tsiru wadda ta zama suna, inda makaɗin ya sarrafa ta ya
yabi sarkin.
4.0 Kammalawa
Daga bayanai tare da misalan da suka gabata,
za a ƙara fahimtar cewa tabbas zuga da yabau muhimman tubala ne
da makaɗan fada ke sarrafawa
domin ganin sun waƙe basarake cikin harshe mai ƙayatarwa da burgewa.
Wannan maƙala ta yi ƙoƙarin nazartar waɗannan tubala ne guda
biyu na ‘zuga’ da ‘yabau’ da kuma yadda makaɗi Ibrahim Narambaɗa ya yi amfani da su
wajen gina bakandamiyarsa. A ƙarshe maƙalar ta tabbatar da
cewa makaɗin ya ci nasarar
sarrafa waɗannan tubala wajen
wasawa da koɗawa da kuma cicciɓa sarkin Gobir na Isa
Amadu Bawa. Sannan kuma sarrafa tubalan ya ba makaɗin dama ya fayyace
iya mulki da jarunta da muhibba da kuma asali na sarkin. Haka kuma maƙalar ta haƙƙaƙe cewa, makaɗin ya samu nasarar
taskace nau’o’in zuga da yabau daban-daban a cikin bakandamiyar tasa, wanda
hakan ya sa waƙar ta ginu ainun kuma ta kai bantenta na ‘Bakandamiya’.
Manazarta
Ayuba A. (2012). Zuga da yabau: Matakan yabo
a bakandamiyar Abubakar Akwara. Champion
of Hausa Cikin Hausa, A Festcrift in Honour of Ɗalhatu Muhammad.
Bello, G. (1976). Yabo zuga da zambo a waƙoƙin fada. Harsunan Nijeriya, ƁI.
Bunza, A. M. (2003). Kashin baƙi sai taro: Riwayar bakandamiyar Gambu
a zaren tunanin manazarta al’ada. A Seminar Paper,
Usman Ɗanfodio University.
Bunza, A. M. (2009). Narambaɗa. IbrashIslamic Publication Center.
Dunfawa, A. A. (2004). Zuga a cikin waƙoƙin fada. Algaita Journal of Current Hausa Reserch in
Hausa Studies, 3 (1).
Gusau, S. M. (1996). Makaɗa da mawaƙan Hausa. Fisabas Media Serɓice.
Gusau, S. M. (2002). Saluhu Jankiɗi sarkin taushi. Baraka Publishers.
Ibrahim, M. S. (1982). Kowa ya sha kiɗa. Longman Nigeria PLC.
Muhammad, D. (1981). Bakandamiya: Towards a
characterization poetic masterpies in Hausa. In Balogun, A.et al (ed). Nigerian
Magazine.
Tsoho, M. T. (2001). Tubalin ginin yabo: Tsokaci
kan yabau a waƙoƙin iko. Ahmadu Bello University.
Yakawada, M. T. (2002). Eulogues: The
building blocks of Hausa praise songs. [Unpublished doctoral dissertation].
Ahmadu Bello University.
Umar, M. B. (1985). Symbolism in oral poetry: A study of symbolical indices of social status in Hausa court songs. [Unpublished M. A. thesis, Ahmadu Bello University.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.