Citation: Isah Abubakar KAROFI & Maryam Mansur YOLA Ph.D (2020). Wasu Kayan Gargajiya Na Masaƙa Da Na Maƙera Da Na Magina Da Na Masassaƙa Na Ayyukan Mata Hausawa Da Karin Maganganunsu. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. .8 Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660
WASU KAYAN GARGAJIYA NA MASAƘA DA NA
MAƘERA DA NA MAGINA DA NA MASASSAƘA NA
AYYUKAN MATA HAUSAWA DA KARIN MAGANGANUNSU
Isah Abubakar KAROFI
Maryam Mansur YOLA, Ph.D
Tsakure
Wannan maƙala, ta yi tattaki zuwa farfajiyar karin magana domin ta zaƙulo wasu karin maganganu masu
alaƙa da kayan
gargajiya waɗanda mata Hausawa suke yin
ayyuka da su. Hausawa suna samar da waɗannan kayan gargajiya na ayyukan mata daga albarkatun ƙasar Hausa kamar itace da
‘ya’yan duma da yumɓu da ƙarafa da sauransu. A wannan
takarda, an yi amfani da hanyoyi guda biyu wajen tsara ta waɗanda suka haɗa da hira da wasu masu aiwatar da sana’o’in amfanin mata da kayan
gargajiya, sannan da yin sharhi game da karin maganganun da aka zo da
misalansu. A zubin takardar an kawo misalai na karin maganganu a kan kowane
misali na kayan gargajiya na ayyukan mata, sannan kuma, aka yi sharhinsu.
1.0 Gabatarwa
Adabi wata hanya ce
wadda ake amfani da ita wajen bayyana rayuwar Hausawa baki ɗaya. Adabi ya ragaɗe dukkan ɓangarori na
zamantakewar Hausawa hatta kayan gargajiya na ayyukan mata Hausawa ba a bar su
a baya ba. Waɗannan kayan gargajiya
na ayyukan mata Hausawa suna da wasu karin maganganu waɗanda ake jinginasu a
gare su. A takardar nan, an kawo ma’anar karin magana ta ƙamusa da ta masana
adabin Hausa daban-daban da bayanin wasu kayan gargajiya na ayyukan mata
Hausawa. Haka kuma, an kawo kayan gargajiya na ayyukan mata Hausawa tare da
kawo wasu karin maganganu daga kowane daga cikin kayan gargajiya yake bayyana
aikinsa ko yanayinsa. Sannan kuma, an yi sharhi akan waɗannan karin maganganu
da kowane kayan gargajiyar aka ba da misalai da su.
2.0 Mana’ar Kayan Ayyukan Gargajiya na Mata Hausawa
Karofi ya bayyana
kayan ayyukan gargajiya na mata Hausawa da ‘Kayayyaki ne da yanayin
zamantakewar Hausawa ya samar da su tun daga zamani mai tsawo, har zuwa kuma
yau, Hausawa suna amfani da su a mu’amalolinsu na rayuwa ta yau da gobe’
(Karofi, 2020, sh. 66).
A tawa fahimtar kuwa, kayan gargajiya na
ayyukan mata Hausawa, kayayyaki ne da mata suke amfani da su a ayyukansu na
cikin gida, kuma waɗanda suke ɗaya daga kayan
gargajiya na Hausawa masu bunƙasa tattalin arziƙin ƙasar Hausa.
3.0 Karin Magana
Wasu masana na adabin
Hausa da dama sun ba da ma’anar karin magana kamar haka:
Umar (1987, sh. 21)
ya nuna karin magana, ‘wani shiryayyen zance ne da Hausawa kan yi cikin magana
a dunƙule domin bayyana wani darasi na musamman’.
Kamar yadda Junaidu
da ‘Yar’aduwa (2007, sh. 79) suka bayyana karin magana ‘wata ‘yar jimla ce
gajeriya da mai magana zai faɗa ta hikima, kuma ta ƙunshi saƙonni masu yawa idan
an tashi yin sharhinta’.
A ra’ayin Ɗangambo (2008, sh.
38) yana ganin karinmagana ‘dabara ce ta dunƙule magana mai yawa a
cikin zance ko a ‘yan kalmomi kaɗan cikin hikima’.
Shi kuwa Birniwa
(2005, sh. 57) ya ce,‘karin magana gajeruwar jumla ce da ake sakaya ma’ana da
ita, wadda idan aka warware ta sai ta bayar da ma’ana mai tsawo’.
Wannan ya tabbatar da
karin magana hanya ce ta isar da saƙo cikin hikima da
azanci.
4.0 Wasu
Kayan Gargajiya na Ayyukan Mata Hausawa da Wasu Karin Maganganunsu
A wannan ɓangaren za a kawo
wasu kayan gargajiya na ayyukan mata Hausawa, sannan kuma aka ba da misalan
wasu karin maganganu masu alaƙa da waɗannan kayan gargajiya na ayyukan mata
a fito da ma’anoni da tasirai na waɗannan kayan gargajiya na ayyukan mata
Hausawa.
Ga wasu misalan kayan
gargajiya na ayyukan mata Hausawa kamar haka:
4.1 Akushi
Akushi, masassaƙa suke sassaƙa shi daga itacen
marke ko gamji ko ƙirya ko waninsu masu ƙwari. Siffarsa da
girmansa kamar na ƙaramar ƙwaryar shan fura ne, amma shi na icce
ne, ba a yi masa murfi sai dai a rufe da ƙaramin faifai. Idan an zuba abinci a cikinsa
yakan daɗe bai huce ba kuma ba
ya saurin lalacewa. Amfaninsa shi ne cin abinci (Karofi, 2020, sh. 87).
Ga misalan wasu daga
cikin karin maganganun Hausawa da suka shafi akushi:
Ƙwarya ta bi ƙwarya, in ta bi akushi ta fashe
Ƙwarya ta bi ƙwarya, in ta hau akushi ba ta moriya
Abin mamaki furar
sayarwa a akushi
Babban yatsa ko bai
ci ba, yana riƙe akushi
Akushi game duniya
An ci tuwo an manta
da akushi.
(Hadiza, 2011, sh.
10-12).
Waɗannan jerin karin
maganganun da aka tsaro a sama, suna ɗauke da hoton akushi da tasirinsa a rayuwar Hausawa. Akushi ɗaya ne daga cikin
kayan gargajiya na cin abincin Hausawa game-gari. Karin maganar na daɗa fito da nagartar da
yake da shi idan aka kwatanta shi da kayan ayyuka waɗanda aka samar da su
daga duma irin su ƙwarya ko ƙoƙo da dangoginsu. Duka kayan duma suna da saurin fashewa a
yayin aikace-aikace na cikin gida.
4.2 Dutsen Niƙa
Dutsen niƙa, dutse ne mai sulɓi da ɗan tsawo kamar ƙafa ɗaya da rabi. Ana
girka shi bisa wasu ƙananan duwatsu waɗanda ake yi wa laƙabi da magirkai a kuma saka faifai daga gaba domin tara niƙaƙƙen gari. Daga durƙushe mata ke amfani
da dutsen niƙa tare da wani wanda
ake gurzawa a samansa wato ɗan dutsen niƙa mareɗi ko magurji. Amfanin
dutsen niƙa shi ne mayar da
hatsi su zama gari ko a markaɗa wake don a yi ƙosai ko kuma a markaɗa kayan miya don a yi
miyar abinci (Karofi, 2020, sh. 100).
Misalin karin maganar
da ta shafi dutsen niƙa:
Dutsen niƙa wahal da ubangiji.
(Gwammaja, 2018, sh.
15)
Wannan karin magana
yana nuna tasirin dutsen niƙa wanda yin aiki da shi wata wahala ce
ga mace wadda kuma ita ce ta mallake shi. Haƙiƙa yin niƙa da dutsen niƙa mace za ta wahalar
da jikinta sosai. Ke nan dutsen niƙa abin aiki ne da ke
gajiyar da jiki.
4.3 Gora
Fafaffen duma ne mai
tsukakken baki da ɗan kai a sama, kan
shi ne ake fafewa sai a fitar da kututun da ke a cikinsa, sannan a wanke shi a
riƙa
zuba ruwa a cikinsa ta nan domin zuwa ban ɗaki ko alwala ko don shan ruwa ga tsofaffi,
musamman matafiya (Salima, 2013, sh. 308).
Baya ga ƙaramin gora, akwai ƙaton duma da ake
amfani da shi wajen fito a kogi ko zuba nono ko kifi da sauransu (C.N.H.N,
2006, sh. 170).
Ga misalan wasu daga
cikin karin maganganu masu nuni da gora:
Ba a fafa gora ranar tafiya
Gora in ya cika, ba ya ƙara
Duniya kamun kifi ce,
kowa ya kama ya sa a goransa
Shegen gora, mai zubar da ruwan alwala
Ruwan gora akan sha su komai ɗacinsu. (Yunusa,
1985, sh. 83).
Waɗannan karin
maganganun suna daɗa fito da
tasire-tasiren gora daban-daban a rayuwar al’ummar Hausawa.
4.4 Kaskon Wuta
Kaskon wuta masu ginin tukwane suke yin sa, ana yi masa
faɗin baki, sai dai
matsakaici ne bai kai girman kaskon suya
ba. Ana amfani da shi domin ɗumama ɗaki wato a sanya garwashi a ciki a lokacin hunturu ko
sanyi (Karofi, 1986, sh. 4). Haka nan kuma, ana zuba garwashin wuta cikinsa
domin mai jego ta ji ɗumi. Ga misalan wasu
daga cikin karin maganganu waɗanda suke yin nuni a game da kaskon wuta:
Ko ya kula, kunama ta
harbi kasko
Ɗanyen kasko ba ya kai ruwa ban ɗaki
Kasko ba ya fashewa, a sa zare a ɗinke
Arziƙin kaza ƙadangare kan sha
ruwan kasko.
(Gwammaja, 2018, sh.
18).
Waɗannan karin maganganu
suna bayyana tasirin kasko da wani
abin aiki ne wanda ake yi da ƙasa wato yumɓu. Hausawa kan yi
amfani da kasko don zuba ruwa ga
tsuntsayen gida kamar kaji ko zabbi ko agwagi da sauransu. Sannan kuma, Hausawa
sukan yi wanka da shi, idan kuma ya fashe ya fi ƙarfin a ɗinke shi da zare ko
allura, sai dai a sake yin sabo. Haka kuma, a wasu karin maganganun kamar Arziƙin kaza ƙadangare kan ruwan kasko suna fito da abu mai yiwuwa da
maras yiwuwa a cikin zance.
4.5 Kuyafa/Cokali
Salima (2013, sh.
310) ta nuna cewa, ‘kuyafa masu
sana’ar sassaƙa suke sassaƙa shi daga itacen ƙirya ko gamji ko
aduwa ko marke ko kanya da wasunsu masu ƙwari’. Siffarsu iri ɗaya ce da ta ƙoshiya, amma bai kai tsawon
ƙoshiya ba domin ba shi da zurfi da faɗi sosai kamar ƙoshiya. Mata Hausawa suna
amfani da shi wajen motsa abinci da zuba miya ko man shanu da kuma cin abincin
kansa. Misalin karin maganar cokali
ko kuyafa:
Cokali a caka ka ga daɗi.
(Hadiza, 2011, sh.
81).
Wannan karin maganar
tana fito da amfanin cokali/kuyafa a matsayinsa na abin cin abinci
da sauran ire-iren waɗannan ayyuka na
gidajen Hausawa. Kuma wannan karin maganar yana nuna Hausawa mutane ne bisa
galibi masu cin daɗi ne a gidansa tun
kuwa kafin zuwan baƙi a ƙasar Hausa.
4.6 Ƙoƙo
Ƙoƙo shi ne mafi ƙanƙanta a cikin ƙorai, ke nan ƙwarya ce ‘yar ƙarama. Ana amfani da
shi don shan koko ko ɗibar ruwa daga tukunya ko randa ko tulu.Yawanci ƙoƙo shi ne moɗar Bahaushe ta asali. Ana kuma amfani da ƙoƙo domin yin malmalar
tuwo (Salima, 2013, sh. 310).
Ga misalan wasu daga
cikin karin maganganu na ƙoƙo kamar haka:
Allah ya mayar da ƙoƙo masaki
Zai gani a ƙoƙon shansa
(Hadiza, 2011, sh.
82)
Waɗannan karin
maganganun suna bayyana amfanin ƙoƙo na abin shan ruwa ko ɗibar ruwa ga al’ummar Hausawa. Hausawa suna
tasire-tasire da suke dangantawa da ƙoƙo kamar yadda wasu karin maganganu suke nunawa.
4.7 Ƙwarya
Daga yaɗon duma ne ake samar
da ƙwarya. Ana fafa ƙwarya a raba ta biyu, a kuma a kankare a fitar da totuwar da
ke ciki a wanke ta. Haka kuma, akan zuba ko ajiye wasu abubuwa makamantan waɗannan a ƙwarya. Har wa yau kuma,
ana amfani da ƙwarya domin rigar hatsi da ta shinkafa da sauransu (Karofi,
2020 sh. 75).
Ga misalan wasu daga
cikin karin maganganu na ƙwarya:
Ƙwarya ta bi ƙwarya ‘yar uwarta
Kowace ƙwarya da abokiyar burminta
Ƙwaryar da ta je ta zo, har
wadda ta shekare
Ƙwaryar arziƙi, ta fi kaɓakin tsiya
Ƙwaryar ƙwarai tana ragaya
Juye ban ƙwaryata
Ba kowace ƙwarya takan zama masaki ba
Mai cinikin shan
zuma, in reshe bai karye da shi ba, wata ran ƙwarya ta fashe masa
(Yunusa, 1985, sh. 85).
Waɗannan karin
maganganun suna fito da sigar ƙwarya a yanayinta na duma. Haka kuma, ana nuna tasirin ƙwaryaabin zuba gara a
lokacin bukin aure ko suna na gargajiya. Har wa yau kuma, waɗannan karin
maganganun suna daɗa nuna ire-iren
ayyukan ƙwarya a wasu al’adun Hausawa. Sannan kuma, wasu karin
maganganun suna nuna fifikon abubuwa masu amfani a kan marasa amfani.
4.8 Ludayi
A bisa gidajen
Hausawa ko gonaki ko a saman darni ko danga akan reni ludayi.Ludayi ana shuka
‘ya’yan ne masu yanayi na irin yaɗo na ƙwarya. Idan ludayi ya ƙosa ne ake fafa shi
kamar yadda ake fafa ƙwarya a raba shi gida biyu. Sannan kowane ɓari ya zama ludayi, sai a fitar da tukar da ake a
ciki a wanke sosai[1].
Siffar ludayi kuwa, yana da baki
zagayayye kamar ƙoƙo mai ɗan zurfi da kuma dogon mariƙi ko hannu. Ana
amfani da ludayi domin shan fura ko
koko ko kunu (Karofi, 2020, sh. 78).
Ga misalan wasu karin
maganganu na ludayi:
Moɗa ba iri ba ce, ludayi
ne, ya karkace
Allah ya sa ƙoƙon duma ya zama ludayi
Ruwa a ludayi ya ci mutum, bare na rijiya
Hantsi ya dubi ludayi
Ƙaryar ana yi, sadaka
da guntun ludayi.
(Gwammaja, 2018, sh.
17).
Waɗannan karin maganganu
da aka ambata a sama, suna nuna hoton ludayi
a matsayinsa wani abin aiki. Haka kuma, karin maganganun suna fito da alaƙar ludayi da wani abu na ɗibar ruwa.
4.9 Mara
Karofi (1986, sh. 41)
ya kira mara da marar kwashe tuwo. Mara wata
sakaina[2] ce da
aka gyara ta, musamman a dinga kwashe tuwo daga tukunya. Da mara mata
Hausawa suke kwashe tuwo daga cikin tukunya
a zuba a cikin akussa ko kwanoni da
kuma amfani da ita a wajen motsa gyaɗa idan ana suyarta.
Ga misalan wasu karin
maganganun da suke bayani kan mara:
Allah ya sa a kwashe
da mara
Idan da daɗi, ba a kwashewa da mara
Tuwon buski ba ai
maka mara.
(Yunusa, 1985 sh. 89)
Waɗannan karin maganganu
suna bayyana amfanin mara a cikin
gidajen Hausawa. Haka kuma, wasu daga cikin waɗannan karin maganganu suna ishara kan
abubuwan da mara take da dangantaka
da su.
4.10 Moɗa
Bisa al’ada, an san
Hausawa da yin amfani da ɗan ƙoƙo a madadin moɗa a yanzu. Hausawa
suna yin moɗa da gora ko ludayin duma, amma mai tanƙwasa a kai. Masu
sana’ar fafar ƙwarya su ne suke fafa moɗa su fitar da tukar cikinta,
sannan a wanke a yi amfani da ita. Amfanin moɗa shi ne ɗibar ruwa daga cikin randa ko tulu ko wasu abubuwa wuri makamantan waɗannan (Karofi, 2020,
sh. 81).
Ga misalan karin
maganganu na moɗa:
Moɗa ba iri ba ce, ludayi
ne, ya karkace
Tsabtar biri, kashi a
moɗa.
(Hadiza, 2011, sh.
84).
Waɗannan karin
maganganun suna fito da yanayin moɗa ta fuskar shukawa.
Waɗannan karin maganganu
suna nuna ayyukan moɗa a wajen Hausawa,
kuma moɗa aba ce wadda take buƙatar a tsabtace ta a
ko da yaushe.
4.11 Randa
Masu ginin tukwane su ke yin randa. Ana gina randa da
yumɓu da irin siffar tukunya sai dai ta ɗara tukunya girma. Ana yi mata ƙaramin baki ko wuya,
sannan ana yin wata kwalliya a wajen bakinta. Ana shafa mata jar ƙasa ko farar ƙasa domin ƙawata ta ga masu buƙata. Sannan ana yi wa
bakin randa murfi domin rufe ta. A
al’adance Hausawa na ajiye randa a
cikin ɗaki (Soba, 2015, sh.
54).
Ga wasu misalan karin
maganganun da aka gina a kan randa kamar
haka:
Randa uwar ruwa,
Kowa ya wuce randa ba ruwa yake nema ba,
Kogi na hangen ruwan randa ɗigen gyaran,
Da an ƙi da an so, sai uwar
ruwa randa,
Kada kogi ya hangi randa,
Randa ba ki cika, sai ranar salla,
Tulu shi ke yawo, randa,
na ɗaki zaune.
(Hadiza, 2011, sh.
87).
Waɗannan karin maganganu
suna bayyana alaƙar randa da
ruwa, sannan kuma, randa zaune ko
girke take wuri ɗaya ba ta yawo sai
dai a tarar da ita a ɗaki.Haka kuma, karin
maganganun suna nuna duk girman randa
ba ta kai girman kogi ba da sauran ayyuka da amfanin randa a wajen Hausawa.
4.12 Tabarma (Karamnu)
Masaƙan kaba su suke saƙa tabarmi. Tabarmin kaba bisa asalinsu farare ne a wajen Hausawa kuma su ne
ake kira da karamnu. Ana amfani da karamnu domin kwanciya da shanyar tuwo
da sauran nau’in abinci mai buƙatar shanya a rana kafin a yi amfani
da shi. Haka kuma, akan shanya wasa-wasa da daddawa da sauransu. kuma shanyar
tuwo gaya domin yin dabuwa (Gwarjo da wasu, 2005, sh. 119).
Ga wasu misalan karin
maganganu na tabarma/karamnu:
Tabarmar kunya, da hauka akan naɗe ta
Kowa ya raina mafari,
ba zai iya tabarma ba
Shimfiɗar fuska, ta fi
shimfiɗar tabarma
Mai wuri ya zo, mai tabarma ya naɗe
To, ku yi, in naɗe, in ji ɓarawon tabarma
Kowa ga gani da tabarmarsa sai dai ya rasa wurin shimfiɗawa.
(Gwammaja, 2018, sh.
40).
Waɗannan karin maganganu
suna fito da hoton tabarma a
matsayinta abin shimfiɗawa. Duka waɗannan karin maganganu
da wasunsu suna daɗa fito da tasirin tabarma a wajen zamantakewar Hausawa,
musamman a hulɗoɗinsu na tarbar baƙi.
4.13 Taɓarya
A hoton da ke a sama,
taɓarya ce a cikin turmi. Masu sana’ar sassaƙa suke yin taɓarya. Sannan kuma, ba da kowane itace ake yin taɓarya ba, sai an zaɓi ice mai juriya. Don haka, akwai buƙatar a yi zaɓen itace mai kyau,
mai ƙwari kamar itacen kaɗanya ko marke ko kanya ko aduwa da wasunsu da
suka dace, kafin a sassaƙa ta. Ana sassaƙa taɓarya kamar doguwar sanda, amma mai matsakaicin kauri da
babban kai a sama da ƙasa. Da taɓarya ake daka, akwai kuma
taɓarya ta sussukar hatsi da ta ƙulƙule ko jajjagen kayan
miya (Karofi, 1986, sh. 12).
Ga misalan wasu karin
maganganuna taɓarya:
Iya yi, iya reto,
sakatar haƙori da taɓarya
Ba ya zaune, ba ya
tsaye, kamar ya haɗi taɓarya
Ginar gyare da taɓarya
Dake bakin tsanya da taɓarya.
(Yunusa, 1985, sh.
92).
Waɗannan karin maganganu
suna fito da hoton taɓarya da yanayin tsarinta.
Haka kuma, waɗannan karin maganganu
suna nuna tasirin taɓarya a aikace-aikacen
Hausawa.
4.14 Tukunya
Hausawa sukan yi tukunya da yumɓu ne. Girman tukunya ya bambanta don haka ne ma ya sa
ake yi wa kowace tukunya suna daidai
da aikinta a cikin gida. Misali akwai, tukunyar
tuwo wadda ta kasu zuwa kashi biyu; akwai ta tuwon gida da kuma ta tuwon
buki. Sai kuma tukunyar miya.
Amfaninta tukunya shi ne yin tuwo ko
miya da kuma dafa abincin buki da sauran dafe-dafe na yau da kullum (Karofi,
1986, sh. 11).
Ga misalan wasu karin
maganganu a kan tukunya:
Muguwar miya ba ta ƙarewa a tukunya
Haƙuri hatsin tukunya ne, ba ya da wuyar ƙarewa
Ina tukunyar damo, ina ta guza
Tafasar tukunya ba ta rage gefe
Don gobe ake wanke tukunya
(Yunusa, 1985, sh.
91).
Waɗannan karin maganganu
da aka kawo a sama, suna nuna alaƙar tukunya da kayan ayyuka na gidajen
Hausawa waɗanda ake amfani da
ita domin girka abinci kamar tuwo da dafa shinkafa da kuma yin miya. Waɗannan karin maganganu
suna nuna tasiri na ayyukan mata a gidajen Hausawa.
4.15 Tulu
Tulu
kuma, masu ginin tukwane suke yin sa
da yumɓu. Tulu kuma ya bambanta da tukunya da kwatarniya. Akan yi wa tulu wani ƙaramin
baki mai kama da na goran duma. Kamar
yadda ake gasa sauran abubuwan da ake samar wa daga yumɓu
haka shi ma tulu ake gasa shi a wutar
ƙaiƙai
bayan an gina shi. Amfanin tulu shi
ne ɗaukar
ruwan sha da na yin abinci da sauran buƙatu
na gida da kuma sanyaya ruwan sha a lokacin bazara (Karofi, 2020, sh. 107).
Ga misalan wasu karin
maganganu na tulu kamar haka:
Ma sha ruwa magirmi,
amma ban da tulu
A juri zuwa rafi,
wata rana za a kashe tulu
Tsiya ta yi wa kanta,
tuwon tulu
Ban ga abin kai gida
ba, an ba makaɗi tulu
Ƙadangaren bakin tulu, a bar ka, ka ɓata ruwa, a kashe ka
a kas tulu.
(Gwammaja, 2018, sh.
36).
Karin maganganun da
aka jero a sama, suna fito da tasirin tulu
a matsayinsa na kayan ayyuka a gidajen Hausawa. Da tulu ake ɗaukar ruwa da kuma
ajiyarsa. Waɗannan karin
maganganun suna daɗa fito da tasirin
kayan ayyukan mata Hausawa a gida, kuma suna fayyace dangantaka wadda take
akwai tsakanin shi da Hausawa.
4.16 Wuƙa
Wuƙa wani mayanki ne wanda ake yi daga ƙarfe. Maƙera kan narka baƙin ƙarfe ko sanholama a
yi wuƙa da shi. Bayan an
gama wuƙa, akan yi mata ƙota ko ɓota wadda aka yi da
icce, sai a manne ƙarfen wuƙar a ƙotar, sai ya zama
mariƙi na wuƙar. Maƙera kan yi wuƙaƙe manya da ƙanana don
aikace-aikacen mata a gida. Don haka, a kowane aiki na cikin gida yana da irin
tasa wuƙa. Amfanin wuƙa shi ne yanka kayan
miya da nama da makamantan waɗannan ayyuka (Karofi, 2020, sh. 69-70).
Ga misalan wasu karin
maganganun masu magana a kan wuƙa:
Taɗin wuƙa ba ya kada gaban
doki
Gaskiya wuƙa, in ji zakara
Ba a rena maje wuya
sai ‘yar wuƙa
Wuƙar fiɗar giwa ba girma gare ta ba sai dai kaifi
An cewa akuya Sarkin
fawa ya mutu, ta ce oho! Ya mutu da wuƙar yanka ne?
(Gwammaja, 2018, sh.
34).
Waɗannan karin
maganganun sun fito da tasire-tasiren wuƙa ne a matsayin wani
abin yanka a gidan Hausawa.
5.0 Kammalawa
Wannan takarda an yi
nazarin wasu karin maganganu ne kamar yadda suka zama misalai na wasu kayan
gargajiya na wasu ayyukan mata Hausawa a gidajensu na aure. Da farko an kawo
bayanan wasu kayan gargajiya guda goma sha shidda (16), sannan aka zo da jerin
gwanon wasu karin maganganun waɗanda suka danganci kowane abin gargajiya na Hausawa da
mata Hausawa suke amfani da su kuma waɗanda aka jero su har goma sha shidda (16)
bisa gwargwadon yawan adadinsu. Daga nan kuma, sai aka yi sharhi na kowane
rukunin karin maganganun da aka kawo misalansu a kowane kayan gargajiya na
ayyuka na mata Hausawa.
Manazarta
Birniwa, H.A. (2005).
Tsintar dame a kala: Matsayin karin magana a cikin waƙoƙin siyasa. Ɗunɗaye Journal of Hausa
Studies, 57.
C.N.H.N. (2006). Ƙamusun
Hausa.
Ahmadu Bello University Printing Press.
Ɗangambo, A. (2008). Rabe-raben adabin Hausa sabon tsari.
Amana Publishers Limited.
Gwammaja, K.D.
(2018). Jagoran Nazarin Karin Magana.
K.D.G. Publishers.
Gwarjo, Y.T. da wasu
(2005). Aure a jihar Katsina. Hukumar
binciken tarihi da kyautata
al’adu.
Hadiza, S.K. (2011). Hausa Cikin Hausa. Sashen Hausa,
Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari.
Isah S. S. (2013). Buƙatar ƙamusun gargajiya na
Hausa: Misalai daga kayayyakin gidan Bahaushe. Himma Journal of Contemporary Hausa Studies, 4, (1).
Junaidu, I. da
Yar’aduwa, T.M. (2007). Harshe da adabin
Hausa a kammale. Spectrum Books Limited.
Karofi, A.M. (1986). Kayan cikin gidan Bahaushe jiya da yau:
Sigoginsu da amfaninsu [Kundin digiri na ɗaya]. Jami’ar Bayero.
Karofi, I.A. (2020). Tasirin zamani a kan kayan aikin mata
Hausawa na gargajiya [Kundin digiri na biyu]. Jami’ar Bayero.
Soba, S.A. (2015). Muhalli a idon Hausawa don makarantun gaba
da sakandare. Sawaba Press and Publishing Company.
Umar, M.B. (1987). Dangantakar adabin baka da al’adun
gargajiya. Triumph Publishers.
Yunusa, Y. (1985). Hausa a dunƙule. Northern Nigerian
Publishing Company Limited.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.