Citation: Ibrahim BABA & Hafsat MUHAMMAD & Audu BABA (2020). Nazarin Kishi A Cikin Finafinan Hausa. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. .8 Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660
NAZARIN KISHI A CIKIN FINAFINAN HAUSA
Ibrahim BABA
Hafsat
MUHAMMAD
Audu
BABA
1.0 Gabatarwa
Ayyukan Adabi na
Hausa cike suke da bayyana halayya na jama’a iri-iri; sawa’un waɗannan halayyar
kyawawa ne ko kuwa akasinsu. A cikin ayyukan Adabin da suka fi mayar da kai a
yanzu wajen bayyana hoton rayuwar al’ummar Hausawa akwai finafinai na Hausa.
Masu rubutawa da tsarawa gami da shirya finafinan Hausa sun mayar da hankali
matuƙa kan abin da ya shafi zamantakewar al’umma, musamman
abin da ya shafi rayuwar soyayya tsakanin matasa da ‘yan mata, da kuma rayuwar
auratayya tsakanin ma’aurata, yadda zaman yake da kuma saɓanin da ka iya ɓullowa a sakamakon
wani abu. Har wa yau, finafinan sukan ƙunshi sauran sassan
rayuwar al’umma ta ɓangarori daban-daban.
A wannan takarda, an duba halayyar mutane, musamman mata ta fuskar nuna kishi a
cikin finafinan Hausa. Kishi wata halitta ce ta zahiri da ba ganinta ake a da
idanuwa ba wadda Allah ke halittar bayinSa damɓare a zukatansu, shin wannan kishin
mai kyau ne ko akasin haka. Maza da
mata suna tattare da wannan ɗabi’a ta kishi; gwargwadon yadda abin yake a zukatansu da
kuma yadda suke sarrafa shi. Wannan nazari ya gudana ta hanyar kallon finafinai
guda goma sha biyu cikin ɗimbin finafinan da
aka shirya waɗanda suka shafi
kishi, dubi da yanayin lokaci. An yi amfani da hakan ne domin su wakilci suran
finafinan. Tsakuro finafinai guda goma sha biyu kacal kuwa, ya faru ne
sakamakon taƙaita lokaci da bayani. An samo waɗannan finafinai ta
hanyar tattarowa da kuma ziyartar shagunan sayar da finafinan Hausa, da wuraren
masu turawa a wayoyi, da tuntuɓar wasu cikin masu shirya finafinan Hausa.
1.1 Ma'anar Fim
Fim shi ne bayyana
rayuwar al’umma cikin fasaha a aikace, ta hanyar ɗauka da na’urori masu naɗar sautuka da hotuna
masu motsi domin nuna wa al’umma don faɗakarwa. A wata ma’ana kuwa, za mu iya cewa,
Fim wata keɓantacciyar hanya ce
da wasu masu hikima suke amfani da ita a aikace domin nuna hoton rayuwar
al’umma mai kyau ko maras kyau, da nufin hannunka mai sanda ko gyara ga wanda
ya ji ko ya ga wannan fim ɗin. Shi kuwa ‘Yar’adua (2007 sh. 30) ya yi nasa ta'arifin
da cewa, "Fim wata hikima ce ta hoto mai motsi da take ɗauke da mutane, wato
hotunansu maza da mata, yara ko manya, ko kuma ma wanin mutane, wanda aka ɗauka ta hanyar yin
amfani da na'urar ɗaukar hoto ta
musamman, tare da bai wa mutane damar tafiyar da wasu ayyuka ta fuskar
kwaikwayo ko wanin sa, a wani ɗan lokaci da aka keɓe wanda shi yake ɗauke da wani saƙo na musamman kan
nishaɗi da gargaɗi da wa'azi da
soyayya da tarihi ko wanin haka, zuwa ga al'ummar duniya".
Idan muka yi la'akari
da waɗannan ma'anoni guda
uku, za mu iya kallon ma'anar fim a taƙaice da cewa, wata keɓantacciyar hanya ce
tsararriya ta sarrafa hikima da fasaha a aikace; wanda ake amfani da na'urar ɗaukar hoto mai motsi
da sautuka, domin isar da wani saƙo na musamman ga
al'umma, ta hanyar zayyano matsaloli da hanyoyin magance su ko uƙubar wanda ya munana.
1.2 Ra’in
Bincike
Hausawa kan cewa,
“Kowane allazi da nasa amanu”, kamar haka abin yake ga kowane bincike na ilimi
da nasa ra’in, wanda zai zama shi ne maɗosar wannan bincike, sannan ya zama abin karɓuwa ga masana manya
da ƙanana.
Bisa haka, wannan bincike an ɗora shi a kan Ra’in Nason Adabi a Al’adu (Folk-Cultural Theory) wanda William
Bascom ya zama ɗaya cikin manyan
mabiyanta, sannan ya yi rubuce-rubuce a ƙarƙashin wannan
mazahaba. Daga bayan sa, an samu masana irinsu Robert Gorges, M. O. Jones,
Daniel Crowley da sauransu.
Wannan mazahaba ta
mayar ta hankali wajen daidaita hikima ta isar da ma’ana ko ƙaramin saƙo ko harshen magana
da ayyuka na gyara rayuwar al’umma ta yau da kullum. Haka kuma mazahabar tana
biyar sawun yadda al’umma take ƙoƙarin bayyana abin da
ya shafe ta. Asalin wannan mazahaba ya faro ne ta kallon yadda hikima da sauran
dabaru na fasahar baka suka danganci abubuwan da al’umma take gudanarwa. A yau,
ayyukan mazahabar ba su tsaya a haka ba, an shigar da fasahar zamani ta amfani
da na’urorin kwamfuta wajen alaƙanta maganganun adabi da al’adu,
musamman a Amurka. A Amurka an fi amfani da wannan ra’i wajen nazarin al’adu na
Hip-Hop da rawar disco da rawa ta masu tsiraici da al’adun da ake shirya
finafinai a kansu (finafinan Hollywood, Bollywood, Nollywood da Kannywood) da
sauransu. (Gusau, 2015, sh. 49-50).
1.3 Dabarun
Gudanar Da Bincike
Wannan bincike, ya
gudana ta hanyar ginshiƙin hanya ta tattara bayanai, wato bayanan da suka wakana
a faya-fayen bidiyo, bayan an kalla aka kuma naƙalto ɓangarorin da ake buƙata domin gudanar da
aiki a kai.
2.0 Asalin Samuwar Finafinan Hausa
A wannan ɓangaren, takardar ta yi ƙoƙarin bibiyar a salin
samuwar finanan Hausa ne. an yi hakan ne da hanyar bitar wasu ayyukan magabata
da suka yi bayanin samuwar finafinan kamar yada yake a nan ƙasa.
'Yar'aduwa (2007, sh.
30) ya bayyana samuwar fina-finan Hausa, abu ne da ya faru a ƙarshen ƙarni na ashirin (Ƙ. 20). Amma farkon
abin da ya ɗora tubalin samuwar
sa shi ne wasan kwaikwayo. Kuma shi kan sa wasan kwaikwayo ya samu ne bayan
Turawa mulkin mallaka sun kafu, kuma har sun yi nisa wajen shimfiɗa tsare-tsare da suka
shafi ilimi da tsarin mulki da sarauta.
Binta (2008, sh.
11-16) ta bayyana tarihin samuwar fina-finan Hausa dubi da nazarce-nazarce daga
mawallafe-wallafen masana, misali Bargery (1934), Chamo (2005, sh. 36), Inuwa
(2009) da Garba (2009), inda yawancinsu bakunansu sun daidaita da na juna ta fuskar
asalin fina-finan Hausa. Misali, majigi hoton farko da Hausawa suka fara cin
karo da shi kafin sauran hotuna da ake nunawa. An fara nuna majigi ta hanyar
sanya allon kallo a saman mota.
Binta (2008, sh.
15-16), bayan tattara bayanan masanan da ta yi game da samuwar fina-finan
Hausa, sai ta nuna cewa, a cikin shekarar 1998 ne masu shirya finafinai suka
yunƙuro
suka kafa ƙungiya ta masu wannan harkar domin su yi magana da murya ɗaya. Tun daga wannan
lokaci sana'ar shirya fim ta bunƙasa, kuma ga shi ƙofar shiga wannan
sana'ar a buɗe take, sai aka dinga
tururuwa cikin ta maza da mata, saboda amfanin da ake ganin masu wannan sana'a
sun fara samu. Gaskiya ne, wannan sana'a ta samar wa matasa da dama aiki, maza
da mata sun zama 'yan wasa da masu shiryawa da masu ba da umarni da masu ɗaukan nauyi, masu waƙoƙi da masu kwalliya da
masu ɗaukan hoto da 'yan
kasuwa da sauransu. Wannan sana'a ta haɗa mutane iri-iri, kuma kowa yana da tasa
wadda ta shigo da shi wannan sana'a. Da wannan sana'a suka yi mata rajista suka
sa mata suna Kannywood Industry (wato masana’antar shirya finafinai ta Hausa).
A ƙarƙashin wannan
masana’anta akwai kamfanoni da suke shirya fina-finai kuma cibiyar wannan ƙungiya Kano.
Kamfanoni sun haɗa da na garuruwan
Kaduna, Abuja, Sakkwato, Maiduguri da sauran wurare.
2.1 Ma'anar Kishi
Masana da dama da
masu nazari sun bayyana ma'anar kishi a cikin kundayensu. Misali, Rabi (1998) a
cikin Binta (2009, sh. 92) ta bayyana cewa "Kishi wani hali ne da mutum
yake tsananin son abu ba tare da tarayya da wani ba".
Garba (1998, sh. 334) ya kawo ma'anar kishi da
cewa, "Kishi cikin jikin mutum yake, sai dai kuma mata sun fi nuna shi da
aiwatar da shi. Mata na da hanyoyin nuna kishi kanar ta magana, da habaici da
karin magana da lugude da waƙa,
ko ta shanti ko ta niƙa ko
zungurar wani abu inda kishiya take, yadda za ta farga da ita ake, ko wata
shewa, ko dai wani abu makamancin waɗannan".
2.2 Rabe-raben Kishi
Masana sun bayyana
kishi kan iya zama kyakkyawa ko mummuna, kuma dukkansu ana iya gane su ta irin
yanayin da aka bayyanar da su.
Binta (2009, sh. 94 –
118) ta yi bayani game da rabe-raben kishi, inda ta kasafta su zuwa gida uku,
kuma kowane ta yi bayani da buga misalai gwargwadon iko. A dunƙule, ga yadda ta
kasafta su:
2.2.1 Kishi Tsakanin Kishiyoyi
Wato irin kishin da ke
tsakanin matan mutum guda. Irin wannan kishin ya faru a fina-finai da dama
kamar Rikicin Cikin Gida (2018) na kamfanin Ɗan
Hajiya Film Production Kano.
2.2.2 Kishin Uwar Miji
Wannan shi ne irin
kishin da uwar miji ke yi ga matar ɗanta. Irin wannan kishi ya faru a fim ɗin Uwar Miji da
sauransu.
2.2.3 Kishin Faccala
Wato irin kishin dake
tsakanin matan wa da ƙani a junan su. Irin wannan kishin ya faru a fim ɗin Ƙawayen Amarya (2018)
na kamfanin 2 Effect Empires Kano.
3.0 Kishi A
Fina-finan Hausa
A rayuwar zahiri,
kishi kan sanya mata aikata abubuwa daban-daban na halaka wanda a ƙarshe yake zama
sababin jefa rayuwar kishiyoyi ko mazajensu ko kuma su ɗin a karan kansu
cikin mawuyacin hali. Idan aka leƙa ga fina-finan Hausa
ma za a iske cike suke da fina-finai masu ɗauke da irin waɗannan halaye na kishi tsakanin mata. A
nan, za a kawo wasu fina-finai da kishi ya bayyana ƙarara da kuma irin
abin da mace take aikatawa a sakamakon wannan kishi, sawa'un a kan kishiyarta
ce, ko 'ya'yan kishiya, ko maigida ko kuma wani cikin dangin miji, musamman
mahaifiyar miji.
3.1 Kishi Kan Sa Mace
Ta Kashe Kishiyarta
A cikin fim ɗin Akushi (2018) na
kamfanin Oscar International an ga yadda Lami ta hallaka kishiyarta ta hanyar
amfani da magani. Lami wadda suke auren Malam tare da kishiyarta, ta rasa
haihuwa wanda kishi ya hana ta nutsuwa, a ƙarshe kuma ta halaka
ta.
3.2 Kishi Kan Sa Mace
Ta Yi Wa Kishiyarya Asiri, Ta Shiga Duniya
A cikin fim ɗin Matar Uba (2018)
na kamfanin Halifa Abubakar Inɓestment Nigeria Limited, ya zo da irin wannan kishin, a
inda aka bayyana:
Malam: Ai ni ma ba cewa na
yi zai rabu da ita ba, ita za ta rabu da shi, za mu kore ta ta bar gidan ta
shiga duniya har abada ba wanda zai ƙara jin labarin inda
take, kuma har abada ba za ta dawo ba.
Asabe: To ai ni Malam a
daidai na, ai in wannan ita kenan sharaɗin, na amince. Mata ta shige min rayuwa, haka
kawai ta same ni da mijina ta raba ni da shi.
A nan, mun ji yadda
aka yi, kuma ƙarshe hakan ta faru, inda ta yi asirin da ya sanya Mariya
ta shiga duniya, ba a ƙara ganin ta ba sai labarin mutuwarta aka ji.
3.3 Kishi Kan Sa Mace
Ta Kashe Uwar Mijinta
Kamar yadda aka sani,
kishi kan sanya mace kisan uwar miji. Ya zo a cikin fim ɗin Dalal (2018) na
kamfanin A. Y. I Universal Motion Pictures Kano inda hakan ta faru. Hafsat
matar Jamil ta haɗa kai da mahaifiyarta
da ƙanin
mahaifiyar Jamil, wato Alhaji Bala domin ganin bayan mahaifiyar Jamil ɗin. Mahaifiyar Jamil
ta sanya ya ƙara aure sakamakon rashin mutunci da tsatsube-tsatsuben
da Hafsat da mahaifiyarta Hajiya Mama suke yi don ganin sun mallake shi. Haka
kuwa aka yi, amma bayan ya yi auren sai da suka rinƙa asirai, ƙarshe sai da kishi ya
sanya ta kashe uwar Jamil ɗin da goyon bayan Hajiya Mama da Alhaji Bala.
3.4 Kishi Kan Sa Mace
Ta Kira Danginta/Ƙawayenta Domin Dukan Kishiyarta
Hafsat ta aikata irin
wannan a cikin fim ɗin Dalal (2018),
bayan Mijinta Jamil ya ƙara aure. Ga yadda suka yi:
Ƙawa 1: Ai ni haushinki
nake ji, ya za a yi a ce kina zaune duk kishin kin nan wai har mijinki ya yi
aure ya shigar da amaryar gida kina zaune a falo ba ki ɗauki wani mataki ba,
kin ban kunya wallahi.
Hafsat: To ya zan yi? Ai ba
kwa nan ne, ko ba gaskiya ba?
Ƙawa 1: To ai
yanzu ga mu mun zo.
Ƙawa 2: Ai wannan cin
mutunci ne da cin amana.
Hafsat: Ai dama na sani,
daman jira nake ku zo mu afka musu.........
Ƙawa 3: Ai ga mu mun zo,
sai ki tashi yanzu mu afka musu.
Hafsat: Abin da nake ao,
kirawo min su Falmata, kafin su zo mu je mu afka musu, duk abin da ta tafasa ta
ƙone.
Haka kuwa aka yi,
domin daga nan sai suka nufi ɗakin Amaryar inda suka rufe ta da duka bayan ta fito daga
ɗakin.
3.5 Kishi Kan Sanya
Mace Ta Daina Yi Wa Mijinta Biyayya Da Kyautatawa
Fim ɗin Lubna (2018) na
kamfanin Ƙalarawi Enterprises ya nuna hakan, yayin da Ibrahim ke
zaune lafiya da matarsa, amma sakamakon ya nuna mata zai ƙara aure sai da
kishin ta ya bayyana, har ta canja masa a yanayin mu'amala da kyautatawa.
Ibrahim: Tun lokacin da na
ce zan ƙara aure shi kenan kika bi kika canja.
Mata: Me ka gani? Ni ba
komai.
Ibrahim: A'a da komai,
walwala ta canja, ‘clearing’ ya canja, akwai abubuwa da yawa da kike min a
gidan nan kin daina su. Kai amma kina da zafin kishi!
Mata: Ai kishi dole ne,
duk macen da ka ga ba ta da kishi to wallahi ba ta son mijinta. Amma kishi ya
zama dole, abin da kake so dole ka yi kishi.
A nan, mun ga yadda
kishi ya janyo ta daina kyautata wa mijinta, walwala ta sauya, ladabi ya sauyu.
A fim ɗin Matar Mijina
(2018) na kamfanin Al-Rahuz Film Production Kano, an ga yadda Jalila ta sauya
mu'amalarta da mijinta a sanadiyyar ya ce zai ƙara aure, inda suna
zaune cikin zaman lafiya da walwala, amma da ya zo da maganar aure sai matsala
ta nemi kunnowa.
Adam: Ya za ki ji idan
aka ce miki zan ƙara aure? (Bayan abin da ya bayyana a fuskarta na damuwa
da kiɗimewa). Ya ya na ga
duk jikinki ya yi sanyi?
Jalila: Ka ga duk zaman
lafiyar da muke, ka ga duk ƙaunar junan da ke tsakani na da kai,
da zarar ka ƙara aure za ka neme su ka rasa.
Adam: Ban gane me kike
nufi ba!
Jalila: Ina nufin zan buɗe wani sashi na daga
Jahannama! Wallahi da faɗuwar gaba za ka rinƙa shigowa gidanka.
Wannan ya nuna a baya
suna zaman lafiya, amma sakamakon maganar ƙarin aure da ya yi
mata, sai ta furta waɗannan kalamai.
3.6 Kan Sa Kishiyoyi
Rikici A Cikin Gidansu, Su Rinƙa Faɗa A Junansu
Fim ɗin Rikicin Cikin Gida (2018) na kamfanin Ɗan Hajiya Film
Production ya nuna irin wannan kishi, inda A'isha da Maryam waɗanda matan Sadiƙ ne suke faɗa a junansu a
koyaushe.
Bayan Maryam ta ɗebo ruwa ta watsa wa
A'isha wadda ke kwance a kan doguwar kujera a falo, sai A'ishan ta miƙe tsaye.
A'isha: Ni kika watsa wa
ruwa?
Maryam: An watsa miki.
A'isha: Lalle kin yi
kuskure, wallahi sai kin yi nadamar abin da kika aikata a jikinki.
Maryam: Ke da Allah dakata!
Wacce take faɗa a baki ba za ta iya
aikatawa ba, ke kin san tsohuwar kuka ta wuci runguma wallahi sai dai sara.
A'isha: Haka kika ce?
Maryam: Ƙwarai kuwa.
Sai A'isha ta ɗauki kwalba ta kwaɗa wa Maryam a ka, nan
take faɗa ya kaure a
tsakaninsu. A taƙaice dai, kishi kan sanya irin wannan faɗa a kowanne lokaci,
ta yadda ba wani sauran zaman lafiya a gidan.
3.7 Kishi Kan Sa Mace
Ta Rinƙa Yi Wa Mijinta Rashin Kunya, Ƙarshe Ma Ta Iya
Lalata Auren Ta
Irin wannan al'amari
ya faru a fim ɗin Mubeenah (2017) na
kamfanin Mai Shadda Inɓestment, inda
Mubeenah ta ɗauki aniyar cin
zarafin mijinta a yayin da ya zo mata da maganar ƙarin aure.
Adnan: Bai kamata
'ya'yanmu su gane cewa akwai wata matsala tsakaninmu ba, ko kaɗan ba ni da niyyar na
cutar da ke ko na wulaƙanta ki, ba wai na yi shi da niyya ba ne.
Mubeenah: Dan Allah ka dakata
min! Kana so ka ce min yarinyar ce ta janyo ka ta ce lalle sai ka aure ta? Kana
so ka ce min ba ka taɓa furta mata kana son
ta ba kenan?
Adnan: Ni fa ban ce haka
ba, amma ina so ki fahimce ni, kuma ina so ki yi min kyakkyawan zato.
Mubeenah: Ka ga dan Allah ka
yi haƙuri kar ka min wata lakca ba abin da za ka faɗa min na fahimta. Don
haka ka je ka yi duk abin da ka ga dama, amma ina so ka sani, ni ban isa na
hana ka abin da ka ga dama ba, amma idan ka yi kuskuren yin aure, wallahi
tallahi za ka yi nadama, za ka ga kuma abin da zai biyo baya.
Haka al'amarin ya
faru, domin bayan auren ta yi ta fitina har sai da ta kai ta lalata rayuwar
auren ta hanyar saki suka rabu.
3.8 Kishi Kan Sanya
Kishiya Ta Kira Kishiyarta Da Karuwa
Fim ɗin Rikicin Cikin Gida
(2018) na kamfanin Ɗan Hajiya Film Production ya zo da hakan, wato yayin da
Maryam ta gyara falo a ranar girkinta, sai A'isha ta zo ta kwanta.
Maryam: To tsohuwar kilaki!
Sai ki tashi ki fita daga falon nan saboda yau ba ke kika gyara falon ba,
ballantana ki zo ki wani kwanta ki baje, sai ki bari lokacin da kika yi sai ki
zo ki kwanta.
3.9 Kishi Kan Sanya
Mace Ta Rinƙa Zargin Mijinta
Ya zo a cikin fim ɗin Halin Kishi (2008)
na kamfanin Global Time Moɓies yayin da Abdallah ya yi yunƙurin ƙarin aure, sai kishi
ya sanya matarsa Zainab ta rinƙa zarginsa da fasiƙanci. A gefe guda
kuma ta rinƙa yin barazanar kisa ga Zara'u (Budurwar mijinta) matuƙar ba ta rabu da
mijin nata ba.
3.10 Kishi Kan Sanya
Mace Ta Rinƙa Yi Wa Kishiyarta Ƙage Da Sharri A Gaban
Mijinsu
Irin wannan, ya faru
fim ɗin Matar Uba (2018)
na kamfanin Halifa Abubakar Inɓestment Nigeria Limited, inda Malam Nasidi ya zauna yana
jimamain rashin sanin inda Mariya ta shiga, sai Asabe take mata ƙage.
Malam Nasidi: Yau fa kwana uku ba
mu ga Mariya ba, ba mu san halin da take ciki ba har yanzu.
Asabe: Kai kake ta da
hankalinka, ni fa ina ganin Mariya gajiya ta yi da zaman gidan nan, tana so ta
ga duniya, duniya ta gan ta, ta gogu, ta buɗe ido, idonta ya yi tar a duniya.
Malam Nasidi: Dakata, Mariya ba
za ta yi haka ba, na san ta sarai.
Asabe: Ba a shaidar mutum,
mutum ai shege ne, Malam mutum shege ne........
A nan, duk da Mariya
ba ta nan, ta ma ɓata, amma sai ga shi
kishi ya sanya Asabe aibantata; ta hanyar yi mata ƙage.
3.11 Kishi Kan Sanya
Kishiya Ta Rinƙa Azabtar Da 'Yar Kishiyarta
Sanin kowa ne, kishi
kan haddasa ƙiyayya da gaba da kuma tsana. Haka zalika, kishi kan
sanya mace ta rinƙa azabtar da ‘ya’yan kishiyarta. A cikin fim ɗin Matar Uba (2018)
na kamfanin Halifa Abubakar Inɓestment, an ga yadda Asabe ta rinƙa azabtar da Amira
'yar gidan Mariya; bayan ta yi wa Mariya ɗin asiri. Ta rinƙa ɗaura mata talla, kuma
idan ba ta sayar ba ta rinƙa jibgar ta, ba isasshen abinci, ba
barci wadatacce, wanda a ƙarshe sai da K.B saurayinta ya yi sanadiyyar tafiyar ta
bariki.
3.12 Kishi Kan Sanya
Kishiya Ta Kashe Mijinta
Fim ɗin Mariya (2018) na kamfanin Mai Shadda Inɓestment Limited an ga
yadda hakan ta faru. Mariya, wadda aka yi mata auren dole da Sarkin Fawa Malam
Sada ba tare da tana son sa ba. Shi kuma ya kasance mai auri saki ne, sannan
yana da 'ya'ya. A haka aka yi auren, wanda bayan yin sa Mariya ba ta ba da kai
ga Malam Sada ba.
Wata rana ta aika a
sayo mata maganin ɓera domin ta zuba
masa a abinci ya ci ya mutu, a dalilin ba ta son shi sai bayan ta zuba,
tausayi, da imani ya zo mata, sai ta ɗauka ta je za ta zubar. Ashe duk abin da yake
faruwa a idanun Talatu (uwargidan Malam Sada) ake yi, inda ita kuma tuni ta faɗa kogon kishi da
Mariya. Ganin Mariya za ta zubar da wannan abinci mai guba, sai ta zo ta karɓe abincin ta aika
masa; alhali ta san da guba a ciki. Malam Sada bayan ya ci abincin, cikinsa ya
murɗe har ya mutu, sai
Talatu ta koma tana cewa ai Mariya ce ta kashe shi. Bayan Shari’a ta yi zurfi,
gaskiya ta bayyana cewa Talatu ce ta kashe shi saboda kishi.
3.13 Kishi Kan Sanya
Mace Ta Rinƙa Haukar Ƙarya
Mace takan yi haukar ƙarya da da'awar
aljanu sun kama ta yayin da mijinta ya nemi ƙarin aure. Ya zo a
fim ɗin Hawainiya (2014)
inda Jamila ta rinƙa haukar ƙarya yayin da mijinta Shu'aibu ya zo
mata da batun ƙarin aure.
3.14 Kishi Kan Sanya
Mace Ta Rinƙa Tozarta Mijinta Da Yi Masa Gori
Ya zo a fim ɗin Mu Zuba Mu Gani
(2018) inda Sakina ta fara goranta wa mijinta Ahmad jarin da ta ba shi a
dalilin ya zo ƙara aure. Bayan ta same shi a falo yana shirye-shiryen
fita ɗaurin aurensa kamar
yadda aka gaya mata, sai ya yi ta ƙoƙarin nuna mata ba
wurin kowa zai je ba, ƙarshe ta nemi mintuna biyu a wurinsa. Bayan ta juya za ta
shiga ɗakin girki, sai ya
ce:
Ahmad: Wayyo
uwargidana.....
Sakina: (Ta juyo da mamaki a
fuskarta) Uwargida kuma?
Ahmad: Kuma Amaryata, ki
bari na ƙarasa zance, ke an fara magana ba a ƙarasa ba sai ki
shigo.
Bayan ta tafi zuwa
kicin, ta dawo hannunta a baya, ta nufo shi, sanna ta nemi ya rufe idanuwansa,
sannan ta watsa matsa manja a babbar rigarsa. Daga cikin maganganun da suka yi
akwai:
Ahmad: Ban gane ba, ya aka
yi na yaudare ki? Me kike nufi da haka?
Sakina: Kar ka yi tsammanin
Allah bai toni asirinka ba, duk abin da kake Allah ya tona asirinka na sani.
Wato an ɗaura auren ka yau
kana sauri za ka tafi wajen dinner. To bari na faɗa maka, wallahi tallahi ba za ka cuce
ni ka ce na ba ka kuɗi mu yi kasuwanci ka
je ka yi aure da shi ba.
Haka dai rikici ya ɓalle tsakaninsu, har
bayan an yi auren ta ci gaba da goranta masa wannan kuɗi, ta hana amaryar
zuwa wurinsa. Dukkanin tashe-tashen hankulan da suka faru, sun faru ne a
dalilin ƙarin auren da ya yi, wanda kishi ya jagoranci aikata
komai.
4,0 Abin Da Bincike Ya Gano
A cikin takardar, an
gano yadda masu shirya finafinan Hausa suka mayar da hankali wajen shirya
finafinai masu alaƙa da kishi, sannan kuma aka gano yadda kishin ke gudana.
Har wa yau, binciken ya gano zurfin kishi na ‘ya’ya mata da yadda suke ƙoƙarin bayyana shi a
aikace. Har wa yau, an nuna yadda mata ke ƙyamatar kishiya ta
hanyar nuna baƙin kishi. Takardar, ta hakaito yadda mace kan sauyawa ga
mijinita a dalilin ya yi niyyar ƙarin aure, da kuma
yadda suke nufatar mummunan ƙudiri a yayin da aka yi musu kishiya.
Takardar ta nuna yadda zahirin kishi yake a tsakanin al’ummar Hausawa wanda
finafinai mabambanta suka yi hasashe.
A cikin takardar, an
gano halin da mummunan kishi ke jefa kishiyoyi da mazajensu da kuma ‘ya’yan
kishiyoyin, sannan kuma ta bayyana sakamakon da ake samu a dalilin aiwatar da
mummunan kishi ga wadda ta kasance ta aikata.
5.0 Kammalawa
Bayan tattaro bayanai
da aka yi yayin buɗe wannan takarda, waɗanda suka haɗa da ma'anar fim da
samuwarsa, sannan aka yi bayani dangane da kishi da yadda yake aukuwa. A cikin
takardar, an bayyana sabubbban faruwar kishi a tsakanin al'umma, inda aka
karkatar da bayanin kishin da ke tsakanin kishiyoyi, wato matan da suke auren
mutum ɗaya. Har wa yau, a
cikin takardar, an ga yadda kishi yake a cikin fina-finan Hausa, ta yadda aka
ciro misalan a cikin fina-finai daban-daban wanda yawan su ya kai goma sha
biyu, sannan aka ga irin illar da ke bayuwa ga mazajen da matansu ke aiwatar da
mummunan kishi, da waɗanda ake aikawatar,
da kuma sakamakon da ke komawa kan masu aikatawar. Takardar ta ƙarƙare da bayanin abin
da bincike ya gano a tattare da kishi da kuma tabbacin samuwar finafinan Hausa
masu alaƙa da kishi.
Manazarta
Abubakar, H.
(Producer) & Muhammad, H.A (Director). (2018). Matar Uba. [Film].
Halifa Abubakar Investment
Bargery, G.P. (1934). A Hausa-English
dictionary and English-Hausa vocabulary. Oxford University
Press.
Binta, M. H. (2009). Taƙaicin mata A fina-finan Hausa. [Kundin digiri na biyu]. Jami'ar Ahmadu
Bello Zaria.
Bridge, B. (Producer) & Sa’eed, Y.
(Director). (2018). Rikicin Cikin Gida.
[Film]. Ɗan Hajiya Film Production
Chamo, I.Y (2005). Saƙo a fina-finan Hausa: Nazari a kan jigo da rabe-rabensa.
[Kundin digiri na biyu]. Jami'ar Bayero,
Kano.
Danja, S.M &
Muhammad, Y. (Producers) & Muhammad, Y. (Director). (2018). Ƙawayen
Amarya.
[Film] Two Effect Empires Kano.
Ɗanhajiya, N.
(Producer) & Oscar, S. (Director). (2018). Akushi. [Film]. Oscar International.
Garba, R. (1998). Nazarin
jinsi a adabi: Tsokaci kan matsayin mace a rubutattun
wasan kwaikwayo na
Hausa.
[Kundin digiri na biyu]. Jami'ar Ahmadu Bello Zaria.
Garba, R. (2009). Hoton mata a cikin
fina-finan Hausa: Gyara ko ɓarna. Muƙala
wadda aka gabatar a taron ƙara wa juna sani kan
fina-finan Hausa, a ɗakin taro na Kongo
Zaria. Kaduna.
Gusau, S. M. (2015). Mazhabobin ra’i da tarke a adabi da al’adu na Hausa. Century
Researh and Publishing.
Hotoro, A.R.
(Producer) & Oscar, S. (Director). (2008). Halin Kishi [Film]. Global Time
Mo ies.
Isma’il, A.Y
(Producer) & Gumzak, A.S (Director). (2018). Dalal. [Film].
A.Y.I. Universal Films.
Inuwa, B. A (2009). Kutsen baƙin al'adu cikin fina-finan Hausa. [Kundin digiri na Uku]. Jami'ar Bayero
Kano.
Laku-laku, J. (Producer) & Ayagi, H.Y. (2018). Lubna. [Film]. Ƙalarawi Enterprises Kano.
Lawal, Sh. (Producer)
& Saira, A. (Director). (2014). Hawainiya.
[Film]. Saira MoVietone.
Mai Kwashewa, A.A. (Producer) & Mafia,
S.N. (Director). (2018). Matar Mijina.
[Film]. Al-Rahuz Film Production Kano
Maishadda, A.B
(Producer) & Gumzak, A.S. (2017). Mubeenah.
[Film]. Maishadda Inɓestment.
Maishadda, A.B.
(Producer) & Nuhu, A. (Director). (2018). Mariya. [Film]. Mai Shadda InVestment Limited.
Mia, M., Maishadda, A.B (Producers) & Alƙali, K.S. (Director).
(2018). Mu Zuba Mu Gani. [Film]. MIA
Enterprises.
Mu’azu, U. (Producer) & Saira, A.
(Director). (2016). Ɗakin Amarya. [Film]. Asnanic MoVietone Kano.
Yar'aduwa, T. M (2007). Wasan kwaikwayo na
Hausa: Nau'o'insa da sigoginsa. Benchmark Publishers.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.