Citation: Isah Abubakar KAROFI & Lawal ALIYU (2020). Wasu Kayan Gargajiya Na ‘Ya’yan Duma Na Ayyukan Mata Hausawa. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. .8 Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660
WASU KAYAN GARGAJIYA NA ‘YA’YAN DUMA NA AYYUKAN MATA
HAUSAWA
Isah Abubakar KAROFI
Lawal ALIYU
Tsakure
Wannan takardar ta kawo jerin kayan gargajiya na ‘ya’yan duma waɗanda mata Hausawa suke ayyuka da su a gidajen
Hausawa. Sannan kuma, an bayyana ma’anar fere da ‘ya’yan duma da bayani a kan
aikace-aikace da ake yi da su a gidajen Hausawa. Haka kuma an ziyarci kasuwanni
da shaguna, an kuma yi ganawa da masana da masu sana’ar ƙorai da tsofaffi mata domin
tattaro bayanan da aka yi amfani da su aka gina takardar.
1.0 Gabatarwa
Kayan gargajiya na
ayyukan mata Hausawa wasu kayayyaki ne waɗanda yanayin zamantakewar iyali na Hausawa ta
dogara da su wajen yin mu’amala ko tassarufi na yau da gobe. Su kuma waɗannan kayan gargajiya
na ayyukan mata, kaya ne da ake samun su daga ainihin ‘ya’yan duma.
2.0 ‘Ya‘yan
Duma
Hausawa sukan shuka
‘ya’yan duma a gonakansu ko kuma su fito da kansu a cikin gonaki a sakamakon an
kai irin a cikin takin gargajiya. Bayan sun ƙosa ne masu sana’ar ƙwarya da dangoginta suke
fafa waɗannan nau’o’in
‘ya’yan duman da zarto zuwa biyu,
sannan su kankare tuwon cikin duman su samar da wasu kayayyakin ayyukan mata a
gidajensu (Karofi, 1986, sh. 8).
Masu fere[1]‘ya’yan
duma, suna fasawa ne tare da gyara ‘ya’yan duma da dangoginsu domin su samar da
wasu kayan ayyuka ga mata Hausawa kamar masaki
da ƙwarya da ɗashiya da ludayi
da goran duma da sauransu. Kayayyakin
da ake samarwa daga ‘ya’yan duma suna da yawa.
Akwai ƙwarya da masaki da ludayi da ɗashiya da sauransu.Haka kuma, Masu sayar da ƙorai[2] su ne
mutanen da suke tallata nau’in kayan gargajiya waɗanda ake samarwa daga ‘ya’yan duma a
kasuwanni da lunguna da saƙo-saƙon ƙasar Hausa.
C.N.H.N. (2006,
sh.139) ta ba da ma’anar fere ‘ya’yan duma da fasa ƙwarya ko dangoginta da wuƙa ko zarto, musamman ƙwarya.
Karofi (2020) ya
bayar da ma’anar fere da cewa:
sana’a ce ta gyara
tare da fitar da tukar ‘ya’yan duma da ke a ciki domin a samar da kayan ayyuka
ga mata Hausawa. Masu fere suna amfani da zarto
da makatsi a yayin fafa ‘ya’yan duma
zuwa gida biyu domin samar da kayan ayyuka na mata Hausawa a gidajensu. (sh.
74-75)
Har wa yau kuma, masu
fere ‘ya’yan duma suna fere da gyara ‘ya’yan duma ne da dangoginsu domin su
samar da wasu kayan ayyuka ga mata Hausawa kamar masuka da ƙorai da ɗashiya da ludaya
da kuma goran dumada sauransu, domin
yin ayyukan da zamantakewar Hausawa ta yau da kullum ta dogara a kansu.
3.0 Tarihin
Ginuwar Kayan Gargajiya na‘Ya’yan Duma
Zaman Hausawa kafin
cuɗanya da baƙi, Gusau, (2013, sh.
767) ya bayyana shi da cewa, lokaci ne na zaman Hausawa kafin su fara cuɗanya da wasu al’ummu,
lokaci ne wanda suka gudanar da rayuwarsu bisa tsarin kansu.
A wannan lokaci
Hausawa, musamman mata a ƙasar Hausa, suka dinga gudanar zamantakewar gida bisa
wani karɓaɓɓen tsari wanda al’ada
da kuma al’umma suka yarda da su (Bilkisu, 2015, sh. 78).
Hausawa al’umma ce
wadda ta mallaki hanyoyin gudanar da rayuwa ciki har da hanyoyin da suke bi
wajen samar da kayan aikin mata Hausawa na gargajiya waɗanda su matan suke
sarrafa su a cikin gida. Wannan hanyar rayuwa ce da ta amince su yi amfani da
kayan aiki na gargajiya tsantsa (Karofi, 2020, sh.115).
Ta haka ne mata
Hausawa suka sami wasu kayayyaki na gargajiya waɗanda suke amfani da su wajen tafiyar
da ayyukan zaman gidajen Hausawa a matsayinsu na ‘ya’ya ko matan Hausawa ko
yayye da ƙannen Hausawa wato ‘ya’uwan haihuwa. Daga cikin waɗannan kaya na
gargajiya kuwa da kayan da ake samu daga ‘ya’yan duma. Har kuwa a yau, ana
amfani da su a gidajen Hausawa, duk kuwa da tasirin da Hausawa suka samu na
wanzuwar wasu baƙin kaya.
4.0 Jerin
Wasu Kayan Gargajiya na ‘Ya’yan Duma
A wannan ɓangaren za a kawo
bayanai a kan wasu kayan gargajiya na ayyukan mata Hausawa waɗanda ake samarwa daga
‘ya’yan duma.
4.1 Ƙwarya
Hausawa sun samiƙwarya daga yaɗon duma babba ne. Ana
fafa ƙwarya ne a raba ta biyu, a kuma a kankare ta a fitar da
totuwar da ke ciki, sannan a wanke ta. Ƙwarya tana girma sosai da
zurfi da faɗi. Amfanin ƙwarya shi ne a zuba hatsi
ko garin da aka samar daga hatsi don abinci ko zuba kaya ko ajiye wasu abubuwa
da sauransu. Ana amfani da ƙwarya domin rigar hatsi ko shinkafa ko
gero ko waninsu (Karofi, 1986 sh. 8).
4.2 Masaki
Tushen masaki ɗaya ne da naƙwarya, shi ma ana samun sa
daga yaɗon duma. Sai daimasaki ya ɗara ƙwarya girma da faɗi. Hausawa mata suna
amfani da masaki ne a wajen wankan
jego ko yin fito ko yin kiɗa irin na goge da na amada da sauransu (Karofi, 1986 sh.
10).
Haka kuma, Hausawa
suna yi wa jariri wanka da masaki.
Wannan ne ya sa ake yi wa jariri tawai da cika
masakinka a yayin da za a yi masa wanka ko kuma bayan an gama masa wankan.
Bayan haka, mata kuma suna amfani da masaki
wajen shiƙar gyaɗa, musamman a lokacin kaka, shi mamasaki akan yi kiɗan amada da shi.
Duk da yake wasu
Hausawan na amfani da masaki, a yau
akwai wasu Hausawan da suka ɗauki baho da manyan bokitai da kuma babbar robar wankan
jego da ta wankan jarirai suna mu’amala da su.
4.3 Ɗashiya
Ɗashiya ƙwarya ce ƙarama sai dai ta fi ƙoƙo girma, kuma ita ma ɗashiya masu sana’ar fafar ƙorai ne suke fafa ta zuwa
gida biyu, sannan a cire tukar, a kuma katse ta sarai yadda za ta yi
sumul-sumul. An fi sanin ɗashiya da gidauniyar fura ta ango. Ƙwarya ce wadda ta sha zane
da ado iri-iri wanda ake yi wa suna da sha-bari-kallo.
Sha-bari-kallo wasu zane-zane ne ake
yi wa ƙwarya ɗashiya kwalliya iri daban-daban waɗanda ake shafa wa
farar ƙasa domin a daɗa ƙawata ƙwaryar furar da su.
Amfanin ɗashiya shi ne zuba fura
wadda aka dama, musamman furar ango (Gwarjo da wasu, 2005, sh. 119).
4.4 Gwagwa
Gwagwa ita ma ƙwarya ce ƙarama ake yi wa
hudoji ƙanana ta yadda ba za ta iya riƙe ruwa ba. Gwagwa abu ce wadda take kama da rariya.
Mata masu yin daddawa su ne suka fi yin amfani da ita domin wankin kalwa. Ta
haka ne mata suke rarrabe kalwa da dussa da kuma yashin da aka yi sassafar
kafin a ruɓa ta cikin maruɓɓai. Haka kuma, wasu mata kan yi amfani da ita domin tsane ƙuli-ƙuli idan an ɗebe shi daga cikin
man gyaɗa da sauran ayyuka
makamanta da haka (Karofi, 1986, sh. 8).
4.5 Goran Duma
Goran duma wani ɗan gora
ne wanda ake samarwa daga kayan duma. Goran
dumayana da ciki daga ƙasa, sannan daga sama kuwa yana da
tsukakken baki da ɗan kai. Wannan kan
shi ne ake yankewa sai a fitar da kututun da ke a cikinsa, sannan a wanke shi a
riƙa
zuba ruwa a cikinsa ta kan nasa da aka yanke. Kuma ana ɗaura masa igiya ko
zare a kansa domin riƙewaa yayin tafiya. Ana amfani da goran duma wajen zuba ruwa domin wasu buƙatu na yau da kullum
kamar kama ruwa ko tsarki ko alwala da sauransu.
4.6 Ludayi
Akan samiludayi a darni ko a danga ko kuma a
shuka iri na ‘ya’yan ludayi. Ludayi yana da yaɗo irin na ƙwarya ko kabewa. Idan ludayi ya ƙosa ne ake fafe shi
kamar yadda fafe ƙwarya a raba shi gida biyu. Sannan kowane ɓari ya zama ludayi na kansa, sai a fitar da tukar da
ke ciki a wanke su sosai[3]. Siffar ludayi kuwa, yana da zurfi ko ciki da
baki zagayayye, wato yana da zurfi, da dogon mariƙi, wato hannu. Ana
amfani da ludayi domin shan fura ko
koko ko kunu da sauransu.
4.7 Matsami
Matsami ludayi ne babba, amma yana da hudoji a ƙoƙonsa, hudojin yin su
ake yi bisa buƙata gwargwadon ƙarfen huji, musamman
bayan ya yi zafi. Matsami shi abu ne
mai yaɗo, yana kama da yaɗon ludayi, yakan hau darni ko danga,
musamman a ƙauyuka. Bayan matsami
ya ƙosa akan fafe shi a cire tukar da ke cikinsa a kai wa maƙera su yi masa hudoji
ƙanana
da ƙarfe
da aka zafafa da zafin wuta ta yadda matsamin
zai riƙa zubar da ruwa kamar gwagwa.
Mata Hausawa suna
amfani da matsami ne wajen tsame
abinci wanda ake tsamewa daga cikin ruwan zafi irin su ɗanwake da ɗangauda da ɓula da sauransu
(Karofi, 2020, sh. 78).
4.8 Mara
Mara[4] wata sakaina[5]ce wadda
aka yi mata gyara na musamman don amfani ga mata Hausawa a gida. Da mara ne mata Hausawa suke kwashe tuwo
daga cikin tukunya ko su zuba shi a
cikin ƙorai ko akusa ko
kwanoni. Sannan mata sukan yi suyar gyaɗa da mara da sauran duk wani abinci da yake
buƙatar
a kwashe shi.
4.9 Bango
Bango wani nau’in goran
duma ne babba wadda ake shukawa. Siffarsa iri ɗaya ce da ta goran duma irin wanda Hausawa suke
alwala da shi, sai dai shi babba ne. Amma sai dai har zuwa kammaluwar wannan
bincike, hannu bai kai kan samuwar Bango ba, wanda hakan ba ya rasa nasaba da
tasirin addinin musulunci a kan al’ummar Hausawa. Wannan dalilin shi ya kawo
rashin samuwar hotonsa (Bango) a nan sama.
Mata Maguzawa su ne
suka fi amfani da shi wajen zuba burkutu, wato giyar hatsi, bayan ta gama
dahuwarta. Sai kuma sauran mata Hausawa, musamman mazauna karkara, sukan yi
amfani da bango wajen ɗaukar ruwa daga rafi
(Karofi, 1986, sh. 7).
4.10 Moɗa
Kamar yadda al’ada ta
nuna, Hausawa sukan yi amfani da wani ɗan ƙoƙo domin ribar ruwa
daga tulu ko makamancin haka a madadin moɗa a yanzu. Ana yin moɗa ne daga gora ko
ludayin duma, amma mai tanƙwasa a kai, sai a
gyara su, su koma fasalin moɗa. Masu sana’ar fafeƙwarya su ne suke fafa moɗa[6] su fitar da tukar,
sannan a wanke.
Amfanin moɗa shi ne ɗibar ruwa daga cikin randa ko tulu ko wani mazubi
makamancin waɗannan. (Karofi, 1986,
sh. 11).
4.11 Maruɓɓai
Maruɓɓai wasu tsofaffin ƙorai ne da ake cunkushe su da guntayen kessa[7]
ake shimfiɗawa ƙasa da sama bayan an
zuba kalwa domin a ruɓa ta a matsayi na maruɓɓai.
Mata masu yin daddawa
suna amfani da maruɓɓai wajen ruɓa kalwa dafaffiya
domin ta nuka ko ta ruɓa a ji daɗin daka ta a yi
daddawar da ake sawa a miya (Karofi, 2020 sh. 82).
4.12 Zunguru
C.N.H.N (2006) ta ba
da ma’anar zunguru da “ɗan duma mai ɗan tsayi da mata kan
zuba kwaɓaɓɓen lalle a ciki su
cusa hannu wajen yin ƙunshi” (sh. 497).
Zunguru wani kwakwararren mazubi ne, dogo wanda ake
samun sa daga ‘ya’yan duma.
Amfanin zunguru shi ne yin ƙunshi na hannu ga
mata. Ana saka kwaɓaɓɓen lallen ƙunshi cikinsa daidai
buƙatar
mai ƙunshi. Daga nan, sai a cusa hannu zuwa guiwa domin yin ƙunshi. Ana barin
hannun a cikinsa har zuwa wani ɗan lokaci. Mata tsofaffi da amare su aka fi sani da
amfani da shi domin yin ƙunshi (Karofi, 2020, sh. 82-83).
5.0 Kammalawa
Wannan bincike ya yi
bayani ne a kan kayan gargajiya na ayyukan mata Hausawa waɗanda ake samarwa daga
‘ya’yan duma. Kamar yadda ya gabata, a wannan nazari kuma, an kawo jerin wasu
kayan gargajiya waɗanda ake samu daga
‘ya’yan duma mata Hausawa suke amfani da su a gidajen na aure.
Daga nan kuma, aka
bibiyi ma’anoni na kayan gargajiya na ‘ya’yan duma kamar yadda suka tusgo a ƙamus da kuma na
fannin ilimi kamar yadda manazarta da marubuta suka faɗe su a cikin
littattafansu. Sannan kuma, aka zo da tarihin ginuwar kayan gargajiya na
‘ya’yan duma kamar yadda Hausawa suka samar da su har kuma gami da bayani a kan
masu sana’ar fafe ƙwarya da sauran ‘ya’yan duma. Haka kuma, an yi taƙaitaccen sharhi da
bayanin yadda waɗannan kayan gargajiya
na ‘ya’yan duma suke yin tasiri a hidimomi da dangogin rayuwar Hausawa ta yau
da kullum.
Har wa yau kuma, an ƙawata wannan takarda
da kawo hotuna na waɗannan kayan gargajiya
na ‘ya’yan duma domin daɗa zuwa da nesa kusa
tare da kawar da tababa.
A wannan bincike har
ila yau, an fahimci kayan gargajiya na ‘ya’yan duma da mata Hausawa suke amfani
da su a gidajensu, suna da sauƙin mallaka, kuma masu inganci ne ga su
masu tallafa wa zamantakewar mata Hausawa., musamman na mabambantan ayyukansu.
Uwa-uba kuma, kayayyaki ne waɗanda suke ƙara tallafa wa
tattalin arziƙin Hausawa. Wani abin lura a kan irin wannan nazari na
kayan gargajiya waɗanda ake samarwa daga
‘ya’yan duma, haƙiƙa ya nuna Hausawa mutane ne masu doguwar tsinkaye da
tunani, musamman wajen lura da abubuwan da Allah ya hore masu waɗanda suke a zagaye da
su, har suka ɗauke su a matsayin
matallafa tafiyar da rayuwarsu.
Manazarta
C.N.H.N (2006). Ƙamusun
Hausa.
Ahmadu Bello University Press.
Gwarjo, Y.T. da wasu
(2005). Aure a jihar Katsina. Hukumar
binciken tarihi da kyautata al’adu.
Gusau, S.M. (2013). Dangantakar waƙoƙin baka
da al’adun Hausawa: Bunƙasa ko koma-baya. The Deterioration of Hausa Culture.
Katsina:
State History and Culture Bureau in Collaboration with Umaru Musa Yar’adu’a University.
Idris, B. (2015). Dattakko a tunanin Bahaushe: Tsokaci daga
adabin baka. [Kundin digiri na ɗaya]. Jami’ar Ahmadu Bello.
Karofi, A.M. (1986). Kayan cikin gidan Bahaushe jiya da yau:
Sigoginsu da amfaninsu. [Kundin digiri na ɗaya]. Jami’ar Bayero.
Karofi, I.A. (2020). Tasirin Zamani a kan kayan aikin mata Hausawa na gargajiya. [Kundin digiri na biyu. Jami’ar Bayero.
[1]. Masu fere ‘ya’yan duma, suna
fasawa ne tare da gyara ‘ya’yan duma da dangoginsu domin su samar da wasu kayan
ayyuka ga mata Hausawa kamar masaki
da ƙwarya da ɗashiya da ludayi da goran duma da
sauransu.
[2] .
Masu sayar da ƙorai su ne mutanen da suke yi waƙorai da dangoginsu ado iri-iri da wuta,
wani bi ma har sukan zane ko hotuna ko rubuta wasu ayoyi ko wani nassi ko wasu
sunayen mutane ko na garuruwa da sauransu a kansu.
[3].Idan ludayi bai wanku sosai ba, to, zai dinga yin wani ɗaci-ɗaci.
[4] .
Wata sakaina ce da aka gyara
musamman don kwasar tuwo daga tukunya.
[5] .
Wata tsagi-tsagi ne naƙwarya
wadda ta fashe ko wani ɓangare ne n fasasshiyar ƙwarya ko masaki.
[6] . Kuma waɗannan masu ayyukan
ƙwarya ne suke gyara gorako ludayisu zama moɗa wadda musamman ake ɗibar
ruwa da ita.
[7] .
Kessa guntayen tsofaffin tabarmi ne na kaba waɗanda ake yin ruɓin daddawa da su. Har zuwa yau,
kuma tsofaffi mata da sauran mata Hausawa masu yin daddawa suna aiki da su,
amma wasu matan sukan haɗa buhunnan leda da wasu robobi su
dinga yin ruɓin kalwa da su kamar maruɓɓai na kessa.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.