Bayan Paparoma ya sa an ajiye masa Kujera a bayan wata karamar kofa gajeruwa, don Alkali Abubakar Al-Baqillaniy ya shigo masa a sunkuye, sai ya ja ya dake a kan kujera, ya sa a shigo da Alkali Abubakar Al-Baqillaniy ta wannar gajeruwar kofa, don ya shigo a sunkuye kamar mai yi masa ruku'u.
Alkali Abubakar Al-Baqillaniy isowarsa ke da wuya, ya ga kofar
shiga gajeruwa ce, ga can Paparoma yana zaune a can ciki, kawai nan take ya yi
gajeren nazari, sai ya gano dabarar Paparoma. Shi kuwa kawai sai ya juya baya,
ya sunkuya ya shiga kofar ta baya - baya, duwawunsa na fiskantar Paparoma
(Akramakumullah 🙈),
har sai da ya isa gaban Paparoma, sai ya mike tsaye, ya juyo ya fiskanci
Paparoma.
Nan da nan mamaki ya kama Paparoma, sai ya razana da Alkali
Abubakar Al-Baqillaniy.
Sai ya fara masa magana a kan tufafinsa, don me ya sa bai
kiyaye musu tsarin da suke bi ba?
Sai Alkali Abubakar Al-Baqillaniy ya ce masa: Da irin wannan
shigar muke shiga wajen Babban Sarkinmu, wanda Allah da Manzonsa suka umurce mu
da yi masa da'a. Amma ba sa yi mana inkari. Saboda haka ni Malamin al'ummar
Musulmi ne, idan na yarda da abin da kuke so, na shigo ba bisa shigata na
tufafi ba, to na wulakanta ilimi, kuma na wulakanta kaina, kuma mutuncina zai
zube a idon al'ummar Musulmai.
Sai Paparoma ya ce: to mun karbi uzurinka. Kuma matsayinka a
wajena mai girma ne, matsayin manyan mutane ne. Ba kamar ta sauran jakadu ba
ne.
Sai Alkali Abubakar Al-Baqillaniy ya mika masa Wasikar Adhudud
Daula, sai ya bude ya karanta. A farkon Wasikar an rubuta cewa:
"Na aiko maka da Mai magana da yawun al'ummar Musulmi, don
na girmama ka, na karrama ka".
Sai ya tambaye shi: Me wannan yake nufi?
Sai Alkali Abubakar Al-Baqillaniy ya ce: Saboda ni Malami ne da
yake magana a kan Aqidun Muslunci, a kan tabbatar da samuwar Allah da faruwar
dukkan halittu, da tabbatar da Siffofin Allah, da magana a kan Tauhidi, da
raddi ga Barahima, Mananiyya, Majusawa da Yahudawa da Kiristoci. Kuma ina
tabbatar da hujjojina ne da dalilai na hankali da duk abin da yake da alaka da
haka na dalilai na Nassoshi, kuma ina yin raddi ga kungiyoyin Muslunci 72, ina
tabbatar da gaskiya.
Sai Paparoma ya ce: to ina so ka tabbatar da hakan.
Sai Alkali Abubakar Al-Baqillaniy ya ce ba damuwa idan Sarki ya
ba da izini.
Sai aka kai shi masauki.
To Alkali Abubakar Al-Baqillaniy yana can masaukinsa har ranar
Lahdi ta zo, sai Paparoma ya aika a zo da shi. Sai ya ce: shi fa Malamin
Musulmai ne ba kamar sauran jakadu ba, shi ba zai zauna a tebur da aka dora
naman alade da giya ba.
Sai Paparoma ya tabbatar masa ba za a kawo naman alade da giya
a zaman nasu ba.
Ya je ya zauna, bayan an gama cin abinci, sai Paparoma ya
tambaye shi ya ce: Kuna ikirarin cewa; daga cikin Mu'ujizar Annabinku wata ya
tsage a zamaninsa, ta yaya za ka mana bayani mu gamsu hakan ya faru?
Sai Alkali Abubakar Al-Baqillaniy ya ce: Eh, da gaske hakan ya
faru. Wata ya tsage gida biyu a zamanin Annabinmu Muhammad (saw), mutanen da
suke wajen duka sun gani, da duk wanda ya dace da kallon sama a lokacin.
Sai Paparoma ya ce: Me ya sa ba dukkan mutane ne kowa da kowa
ya gani ba?
Sai Alkali Abubakar Al-Baqillaniy ya ce: Saboda mutane ba su
san hakan zai faru ba.
Sai Paparoma ya ce: Shin akwai dangantaka ne tsakaninku da
watan, ya tsage amma sauran mutane ba su sani ba, sai dai kawai a ce ku
Musulmai ne kadai kuka gani, alhali sararin samaniyar ba ta ku kadai ba ne?
Sai Alkali Abubakar Al-Baqillaniy ya ce: To ku ma
"Ma'ida" da kuke da'awar an saukar wa Annabi Isa (as) daga sama, ku
kun ganta lokacin da aka saukar amma Yahudawa, Majusawa, Barahima da Mulhidai
duka ba su gani ba, shin dangantaka ne a tsakaninku da ita?
Ga nan Girkawa a kusa da ku amma duka su kasa gani sai ku kadai
kawai kuka gani?
Nan da nan sai Paparoma ya rude, ya ji amsa mai toshe baki. Sai
ya sa a kira wani Fada, ya ce: shi ba zai iya ja da Alkali Abubakar
Al-Baqillaniy ba, saboda da ma Sarkinsa da ya aiko shi ya ce: babu kamarsa
cikin Malaman Musulmai a zamaninsa.
Shi ma dai wancan Fadan ya ce ba shi da amsa a kan wannar
mas'alar.
Sai Alkali Abubakar Al-Baqillaniy ya ce: ba kun yarda cewa;
Duniya a dunkule take kamar kwallo ba?
Sai ya ce: Eh.
Sai Alkali Abubakar Al-Baqillaniy ya ce: Shin kana inkarin abu
ya faru a wani yanki na Duniya ba tare da ya faru a wani yankin ba?
Misali kisfewar rana, ana yi a wani waje, amma ba a yi a wani
wajen. Haka taurari, ana ganinsu a wani wajen, a wani wajen kuma ba a ganinsu a
lokacin. Ko kana nufin dole idan an yi kisfewar rana sai an gani a ko'ina a
fadin Duniya?
Sai Fada ya ce: Eh, babu mai iya gani sai wanda ranar take
setin yankinsa.
Sai Alkali Abubakar Al-Baqillaniy ya ce: to haka tsagewar wata
ma, wadanda watan yake setin yankinsu su za su iya gani, sauran mutanen Duniya
kuma ba za su gani ba.
Sai Fada ya ce: to ai matsalar na wadanda suka ruwaito ne.
Sai Paparoma ya tambayi Fada ya ce: ta yaya za iya sukar
maruwaitan?
Za mu cigaba insha Allahu.
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.