Abu ne sananne makiya Addinin Muslunci cikin Munafukai da Yahudawa da Nasara da Rafidha 'Yan Shi'a da Mulhidai sun yi gangami sun yi taron dangi sun hada karfi da karfe wajen cin mutuncin Annabi (saw) ta hanyar bata shimfidarsa da jifan matarsa A'isha (ra) da alfasha, don su aibanta Annabi (saw) su aibanta Addinin da ya zo da shi.
Wannan ya sa wani Pastor a fadar Paparoma ya samu daman kai
farmaki ga Addinin Muslunci a gaban Alkali Abubakar Al-Baqillaniy, sai ya jefo
tambaya a kan haka. To amma bari ka ji martanin da Alkali Abubakar
Al-Baqillaniy ya mayar masa:
Sai Alkali Abubakar Al-Baqillaniy ya ce: Mata ne biyu aka
danganta musu alfasha; Maryam da A'isha, amma sai Allah ya wanke su.
Ita dai A'isha (ra) tana da miji, kuma ba a ga ta zo da d'a ba.
Amma ita kuma Maryam (ra) ta zo da d'a, kuma kowa ya san ba ta da miji.
Saboda haka, in tuhuma ce, wa ya fi kusa da tuhuma tsakanin
mace mai miji da ba ta zo da d'a ba, da kuma mace maras miji, amma sai ga ta da
d'a a hanu?
Don haka A'isha (ra) ita ta fi nisa da wannar tuhuma, duk da
cewa; dukansu biyu sun kubuta daga wannar tuhuma ta karya. Amma idan hakan ya
fado a tunanin mai lalatacciyar kwakwalwa, to zai fi tuhumar Maryam (ra) Uwar
Isa Al-Masihu (as) fiye da A'isha (ra).
Amma mu a wajenmu, dukkansu biyu sun tsarkaka daga aikata
alfashar da aka tuhume su da ita. Allah ya wanke su daga saman bakwai.
Amma ku kun tuhumi wacce take da miji kuma ba ta zo da d'a ba,
amma mu kuma mun wanke wacce ba ta da miji amma ta zo da d'a.
Sai Paparoma ya ce: Kai Pastor, shin kana da jawabi a kan
wannar amsa?
Sai ya zazzare idanu, ya rasa abin fada 😅.
Ai daga nan sai majalisi ya watse!
Akwai wata tambaya da Wazirin Paparoma ya yi wa Alkali Abubakar
Al-Baqillaniy a gefe ya ce masa: Ku Musulmai kuna da kabilanci da ta'assubanci.
Me ya sa kuke halasta wa kawunanku auren mata Yahudawa da Kiristoci amma kuna
haramta a auri naku matan, miye dalili?
Sai Alkali Abubakar Al-Baqillaniy ya ce: Mu muna auren mata
Yahudawa ne saboda mun yi imani da Annabi Musa (as), muna auren mata Kiristoci
saboda mun yi imani da Annabi Isa (as). Ku ma duk lokacin da kuka yi imani da
Annabi Muhammad (saw) to ku zo mu aura muku 'ya'yanmu mata.
Da aka sake haduwa a zama na uku, sai Alkali Abubakar
Al-Baqillaniy ya kai mummunan farmaki ga Paparoma ya ce masa: Me ya sa Allah ya
hade da mutum (Christ's Humanity and Divinity, Hypostatic union), ta yaya za ka
mana bayani har mu fahimci hakan?
Sai Paparoma ya ce: Ai abu ne mai sauki, ma'ana Allah yana da
surori guda biyu; daya ta allantaka wato ta Uba, daya kuma ta mutuntaka, wato
ta 'Da. Kuma ya yi haka ne kawai don yana so ya tsiratar da mutane daga halaka.
Sai Alkali Abubakar Al-Baqillaniy ya ce: Shin ya san cewa; za a
kashe shi, a giciye shi (Cross of Jesus) a yi masa haka?
Idan ka ce bai san Yahudawa za su yi masa haka ba, to kenan shi
ba Allah ba ne kuma ba d'an Allah ba. Saboda ba zai yiwu a ce Allah bai san
gaibi ba.
In kuma ya san da hakan, amma ya yarda aka yi masa haka bisa
saninsa to ba shi da hikima, saboda hikima tana hana mutum ya afka cikin
bala'i. In kuwa ba shi da hikima to shi ba Allah ba ne ba kuma d'an Allah ba.
Nan da nan Paparoma ya rikice ya rasa abin fada.
Daga nan sai aka dage zaman.
Sai Paparoma ya yi alkawari ga Alkali Abubakar Al-Baqillaniy
cewa za su sake haduwa a taro na musamman cikin tarukan Addinin Kiristanci.
Da ranar ta zo, Alkali Abubakar Al-Baqillaniy ya halarci wajen
taron, taro ya yi taro, an kawata wajen yadda ya kamata. Sai Paparoma ya
girmama Alkali Abubakar Al-Baqillaniy ya ba shi kujera kusa da shi.
Suna zaune bisa wannan hali sai ga can babban Pastor
(Patriarch) ya iso. Kuma da ma Paparoma ya fadakar da shi a kan ya kiyayi
kaifin basirar Alkali Abubakar Al-Baqillaniy, ya ce masa: Ka kiyaye shi, kuma
ka zama a fadake, don kar ya disga ka a cikin jama'a.
Sai ga shi ya iso cikin tawagarsa, ana biye da shi, dogarawa
suna dauke da Bible, ana bin bayansa da turaren wuta, yana isowa wajen aka
tashi tsaye don girmama shi. Sai Paparoma ya ba shi wurin zama a kujerar gefe
da shi. Sai ya fiskanci Alkali Abubakar Al-Baqillaniy ya ce: wannan shi ne
shugaban fastoci (patriarch), jagoran Addini, waliyyin Kiristoci.
Sai Alkali Abubakar Al-Baqillaniy ya gaishe shi, ya ce: yaya
iyalai, yaya yara?
Nan da nan taro kaure da mamaki, kowa ya murtuke fiska, suna
mamakin wannar tambaya, suna inkari ga Alkali Abubakar Al-Baqillaniy.
Sai Alkali Abubakar Al-Baqillaniy ya ce: Menene abin inkari a
cikin maganata?
Za mu karasa insha Allahu.
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.