Paparoma ya ji Fada ya nuna akwai matsala a hanyar da aka ruwaito Mu'ujizar tsagewar wata ga Annabi Muhammad (saw), har ya ji dadi, ya samu kofar sukar Mu'ujizar ta Annabi (saw), shi ya sa ya tambayi Fadan, ta yaya za a soki maruwaita Mu'ujizar ta tsagewar wata?
Sai Fada ya ce: Irin wadannan Mu'ujizozi in da a ce sun
inganta, to dole a ce mutane masu yawa ne suka ruwaito daga wasu mutanen masu
yawa, haka har ya iso gare mu. Da a ce an samu haka da dole mu san hakan ya
faru. Amma tun da hakan bai faru ba, to wannan yana nuna cewa; kawai karya ce
aka kirkira.
Sai Paparoma ya juya ya fiskanci Alkali Abubakar Al-Baqillaniy,
ya ce: To kawo amsa.
Sai Alkali Abubakar Al-Baqillaniy ya ce: To ai abin da kuka
fada a kan tsagewar watan irinsa zan fada a kan "Ma'ida" (teburin cin
abinci) da aka saukar wa Annabi Isa (as) daga sama. Sai a ce muku: Da a ce da
gaske an saukar wa Annabi Isa (as) "Ma'ida" (teburin cin abinci) daga
sama to dole a ce mutane masu yawa ne suka ruwaito daga wasu mutanen su ma masu
yawa. Ta yadda ba zai yiwu a samu wani Bayahude ko Kirista ko Bathanawe face ya
tabbatar lallai hakan ya faru. Amma tun da ba su tabbatar da hakan ba, hakan ya
nuna labarin karya ne.
Nan da nan Paparoma da Fada da sauran fadawa a fadar suka rasa
ta cewa.
Ai daga nan sai taro ya watse.
Sai kuma aka sake wata haduwar a zama na biyu. Sai Paparoma ya
tambayi Alkali Abubakar Al-Baqillaniy ya ce: Mecece Aqidarku game da Al-Masihu
Dan Maryam (as)?
Sai Alkali Abubakar Al-Baqillaniy ya ce: Shi ruhin Allah ne,
kuma kalmarsa ce, bawansa, Annabinsa kuma Manzonsa. Kamar Annabi Adam (as)
yake, daga kasa Allah ya halicce shi sai ya ce masa kasance, sai ya kasance.
Sai ya karanto Ayar Suratu Ali-Imran [Aya ta 59].
Sai Paparoma ya ce: Ya kai Musulmi, Isa Al-Masihun ne kake ce
masa bawa?!
Sai Alkali Abubakar Al-Baqillaniy ya ce: Eh, haka muke fada,
haka yake a Addininmu.
Paparoma ya ce: Ba ku cewa; shi Dan Allah ne?
Sai Alkali Abubakar Al-Baqillaniy ya ce: Allah ya tsare mu.
{Allah bai riki wani d'a ba, kuma babu wani abin bauta a tare da shi...}
[Al-Muminun: 91]. Lallai kuna fadin magana mai girman muni.
Idan kun ce: Isa Al-Masihu (as) dan Allah ne, to waye Ubansa,
waye dan uwansa, waye kakansa, waye baffansa da kawunsa...?
Ya kirgo adadi na dangi. Sai Paparoma ya rude.
Sai Paparoma ya ce: Ya kai Musulmi, shin bawa yana halitta,
yana rayarwa, yana kashewa, yana warkas da makafi da kutare?
Sai Alkali Abubakar Al-Baqillaniy ya ce: Bawa ba ya iya yin
haka, duka wannan aiyukan Allah ne.
Sai Paparoma ya ce: To in ka san duka wadannan aiyukan Allah ne
ba na bawa ba, ta yaya Al-Masihu zai zama bawan Allah, daya daga cikin halittun
Allah, alhali ya zo da wadannan Mu'ujizozi, ya aikata duka wadannan abubuwan
mamaki?
Sai Alkali Abubakar Al-Baqillaniy ya ce: Allah ya tsare. Isa
Al-Masihu (as) bai rayar da matattu ba, kuma bai warkas da makafi da kutare ba.
Sai Paparoma ya tunzura ya ce: Ya kai Musulmi, shin inkarin
wadannan abubuwa kake yi, alhali sun shahara kowa ya san hakan?!
Sai Alkali Abubakar Al-Baqillaniy ya ce: Babu wani cikin
ma'abota ilimi da sani da fahimta da ya taba cewa; Annabawa su suke halittar
Mu'ujizozi da kansu, kawai Allah ne yake halittarsu, kuma yake aikata su, yake
gudanar da su a hanayen Annabawan don ya gaskata su a kan abin da suke kira
gare shi. Mu'ujizozin kamar shaida ce gare su.
Sai Paparoma ya ce: To ai kuma an samu mutane da yawa sun
tabbatar da cewa; duka wadannan suna cikin littafinku.
Sai Alkali Abubakar Al-Baqillaniy ya ce: Ya kai Paparoma, a
cikin littafin namu cewa aka yi duka abin da Annabi Isa (as) ya zo da shi na
Mu'ujiza sun faru ne da iznin Allah. Sai ya karanto masa Ayoyin daga
Al-kur'ani, Ayar Suratul Ma'ida [110], da Ayar Suratu Ali-Imrana [49].
Sai ya ce: Duka Annabi Isa Al-Masihu ya aikata su ne da iznin
Allah shi kadai ba shi da abokin tarayya, ba -wai- Isa (as) din ne ya yi su da
kansa kai tsaye ba.
Idan za a ce Al-Masihu Isa (as) da kansa ya rayar da matattu,
ya warkas da makafi da kutare, to kenan sai a ce: Annabi Musa (as) ma da kansa
ya tsaga kogi gida biyu, ya mayar da hanunsa ya yi fari idan ya fitar daga
hamatansa, kuma yake juya sandarsa ta zama macijiya. Saboda haka Mu'ujizozin
Annabawa ba aiyukansu ba ne kai tsaye, Allah ne yake yinsu sai ya gudanar da su
a hanunsu.
Saboda haka idan ba zai yiwu a ce: Annabi Musa (as) shi yake
yin Mu'ujizozinsa da kansa kai tsaye ba, to haka na Annabi Isa (as) ma, ba zai
yiwu a ce shi yake yi kai tsaye ba.
Sai Paparoma ya ce: To ai dukkan sauran Annabawa tun daga kan
Annabi Adam (as) har na bayansa suna kaskantar da kai ga Al-Masihu suna neman
biyan bukata a wajensa.
Sai Alkali Abubakar Al-Baqillaniy ya ce: To su Yahudawa kashi
ne a bakinsu da ba za su iya cewa; Al-Masihu (as) yana kaskantar da kai ga Musa
(as) yana neman biyan bukata a wajensa ba?
Ai kowane mabiyin wani Annabi zai iya cewa; Al-Masihu (as) yana
kaskantar da kai ga Annabinsa yana neman biyan bukata a wajensa. Don haka ba
banbanci a wannan ikirarin.
Can sai wani Pastor ya daga hanu, sai ya jefo tambaya ga Alkali
Abubakar Al-Baqillaniy ya ce: Me za ka ce a kan abin kunyar da matar Annabinku
ta yi, har ake tuhumarta da aikata alfasha?
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.