Ticker

6/recent/ticker-posts

Babu Wata Mas'ala Maras Amfani A Addini

Mas'alolin Addini mataki-mataki suke, akwai manyan Mas'aloli, wadanda ake kiransu da sunan "Usulu al-Deen", akwai kuma kananan Mas'aloli, wadanda ake kira da sunan "Furu'u al-Deen". Kuma mas'alolin kowane nau'i su ma mataki mataki suke, akwai wadanda barin aikata su yana fitar da mutum daga Muslunci, akwai kuma wadanda ba su haka ba.

Haka kuma Malamai suna kasa duka Mas'alolin Addini zuwa kashi biyu; Mas'alolin Ilimi da kuma Mas'alolin Aiki.

Na farko: su ne Mas'alolin da Allah da Manzonsa suka ba da labarinsu, wadanda suka zo a Nassoshi na labari ba na aiki ba. Su wadannan wajabi ne Mumini ya sansu, kuma ya yarda da su, ya gaskata Allah da Manzonsa a cikinsu.

Na biyu kuma: su ne Mas'alolin da Allah da Manzonsa suka yi umurni a yi aiki da su a aikace, na umurni da hani. Su wadannan wajibi ne a aikata wajibai daga cikinsu, kuma wajibi ne a nisanci haramun a cikinsu.

Mas'alolin farko suna alaka ne da ilimi da imani da gaskatawa, na biyu kuma suna alaka ne da aiki da biyayya da da'a.

Idan an lura za a ga duka wadannan nau'o'i biyu na mas'alolin Addini wajibi ne Mumini ya yi aiki da su, wadanda Allah ya ba da labari dole Mumini ya gaskata Allah da Manzonsa, na aiki kuma, dole Mumini ya aikata wajibai da farillai daga cikinsu.

Saboda haka babu wata mas'ala ta Addini da za a ce ba ta da amfani, matukar ta zo a Littafin Allah ko Sunnar Manzonsa (saw).

Idan muka dauki mas'alar makoman Iyayen Annabi (saw) za mu ga tana cikin nau'i na farko ne, wato Mas'alolin Ilimi, wadanda Allah ya sanar da Annabi (saw), shi kuma (saw) ya ba mu labari. Don haka wajibi ne mu gaskata Manzon Allah (saw).

Kai da kake cewa; Mas'alar ba ta da amfani, la'alla ka manta ne da cewa; hukunce-hukuncen Allah ba nau'i daya ne kadai ba, nau'o'i uku ne:

1- Hukuncin Allah na Qaddara.

2- Hukuncin Allah na Shari'a.

3- Hukuncin Allah na Sakamako.

Kamar yadda ya wajaba ka tabbatar da Hukuncin Allah na Shari'a, haka kuma ya wajaba ka tabbatar da Hukuncinsa na Qaddara da na Sakamako. Sheikh Ibnu Si'idiy ya ce:

(({والله يحكم لا معقب لحكمه} ويدخل في هذا حكمه الشرعي والقدري والجزائي)).

تفسير السعدي = تيسير الكريم الرحمن (ص: 420)

(({Allah yana hukunci babu mai cin gyaran hukuncinsa}, hukuncin Allah na Shari'a da na Qaddara da na Sakamako duka sun shiga cikin Ayar)).

Tabbatar da wadannan duka yana daga cikin tabbatar da cikan Mulkin Allah da kadaita shi a hukunci. Sheikh Ibnu Si'idiy ya tabbatar da cewa; yana daga cikin cikan Mulkin Allah kasancewarsa mai Hukunci, yana magana a kan haka sai ya ce:

((وكمال التصرف وكمال الرأفة والرحمة، والحكم العام للعالم العلوي والعالم السفلي، والحكم العام في الدنيا والآخرة، والحكم العام للأحكام الثلاثة التي لا تخرج عنها جميع الموجودات:

[1] ـ الأحكام القدرية حيث جرت الأقدار كلُّها والإيجاد والإعدام، والإحياء والإماتة، والإيجاد والإعداد والإمداد كلُّها على مقتضى قضائه وقدرهِ.

[2] ـ والأحكام الشرعية حيث أرسل رسله، وأنزل كتبه، وشرع شرائعه، وخلق الخلق لهذا الحكم، وأمرهم أن يمشوا على حكمه في عقائدهم وأخلاقهم، وأقوالهم وأفعالهم، وظاهرهم وباطنهم، ونهاهم عن مجاوزة هذا الحكم الشرعي، كما أخبرهم أنَّ كلَّ حكم يناقض حكمه فهو شرٌ جاهليٌ من أحكام الطاغوت.

[3] ـ والأحكام الجزائية، وهو الجزاء على الأعمال خيرها وشرها في الدنيا والآخرة، وإثابةُ الطائعين، وعقوبةُ العاصين، وتلك الأحكام كلُّها تابعةٌ لعدله وحكمته وحمده العام، فهذه النعوت كلُّها من معاني ملكه)).

فتح الرحيم الملك العلام (ص: 32 - 33)

Sai ya bayyana mana cewa; hukuncin Allah da suka shafi dukkan halittu guda uku ne, sai ya ambace su kamar yadda na gabatar a farko. Na ukun shi ne: Hukuncin Allah na sakamako, inda ya ce:

((Na uku su ne Hukunce-hukuncen Allah na sakamako, shi ne sakamako a kan aiyukan bayi, na alheri da na sharri a Duniya da Lahira, da sakayya wa masu da'a, da ukuba ga masu sabo. Wadannan hukunce-hukunce dukkansu suna biye ne da adalcinsa da hikimarsa da gamammen kamalarsa, wadannan siffofi duka suna cikin ma'anonin Mulkinsa)).

Ma'ana; duk hukuncin da Allah ya yi na shiga Aljanna, ko shiga wuta ga wani bawa, to mu sani; wannan bawan mallakan Allah ne, kuma Allah ya yi masa wannan hukunci ne saboda adalcinsa, don ba zai zalunci kowa ba, kuma saboda hikimarsa ne, saboda ya san makomar da ta dace da kowa.

Saboda haka bai kamata Mumini ya shigar da hankalinsa cikin Hukuncin Allah na sakamako ba, kamar yadda bai kamata ya shigar da shi cikin Hukuncinsa na Kaddara ba. Saboda wadannan hukunce-hukunce guda biyu Sirrin Allah ne. kamar yadda wasu hukunce-hukunce na Shari'a ba mu iya riskan hikimar shar'anta su, to rashin sanin hikimar Allah cikin hukunce-hukuncensa na Kaddara da na Sakamako ya fi wahalar riska. Don haka babu hanyar kubutar Imanin bawa da tsiransa a wadannan hukunce-hukunce guda biyu illa mika wuya da sallamawa, tare da Imani da cewa; Allah mai adalci ne, ba zai zalunci kowa ba, ba zai azabtar da wanda bai cancanci azaba ba. Kuma mai hikima ne, yana sakamako ma kowa ne bisa abin da ya cancanta ya dace da shi. Kamar yadda su kuma hukunce-hukuncen Shari'a tsira yake cikin aikata su.

Saboda haka kuskure ne ka kalli wata Mas'ala da Allah ya ba da labarinta, ko Manzonsa ya ba da labarinta ka ce: Ba ta da amfani, don kawai kai a zatonka mas'ala ta aiki ce kadai mai amfani.

Amma kasancewar kowace mas'ala tana da amfani komai karancinta ba ya hana kiyaye Qa'idar lura da Barna da Maslaha wajen bayyana wasu mas'alolin, ana lura da lokaci, da kuma wuri, da yanayin mutane. Duk mas'alar da za ta haifar da barna ko rarrabuwar kai, ko za ta fitini gama-gari a Imaninsu, matukar ba ta cikin Manyan Mas'alolin Addini lallai ya kamata a barta har zuwa lokacin da za a samu Maslahar bayyanata. Kamar a ware wasu mutane a karantar da su ba tare da sauran gama-gari ba, wadanda bayyana mas'alar za ta fitine su a Addininsu. Amma 'Yan Bidi'a kam, bai kamata a daga musu kafa ba, don idan an biye su, dukkan Hadisan da suka saba Bidi'o'insu za su karyata, ko su yi Tawilinsu, kamar yadda suke Tawilin Ayoyin Siffofin Allah.

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments