Ticker

6/recent/ticker-posts

Rubutun Hausa A Wajen Kasar Hausa

Wannan panel zai tattauna rawar rubutun Hausa a ƙasashen waje da tasirinsa a kafafen yada labarai da cibiyoyin al’adu, da gudummawar Hausawa mazauna kasashen Afirka wajen raya harshe da adabi.

RUBUTUN HAUSA A WAJEN ƘASAR HAUSA

1. Muhammad Rabiu (Abu Hidaya) ɗan jarida ne kuma gogaggen masani a kafafen yaɗa labarai, wanda ya shahara wajen rubutun Hausa na zamani, wallafe-wallafen yanar gizo, da tattauna al’amuran da suka shafi rayuwar yau da kullum ta al’umma. Shi ne Shugaban Kamfanin Muryar Afrika Media Link LTD, kamfani da ke aiki a fagen yada labarai da taskance tarihi da tallata rubuce-rubucen Hausa ta kafafen sadarwa na zamani. Kasancewarsa a cikin ƙasar Hausa, tare da gogewarsa a aikin jarida da kafofin sada zumunta, ya ba shi damar fahimtar halin da rubutun Hausa ke ciki a yau daga marubuta, masu karatu, zuwa hanyoyin yaɗa labari. A takaice, Abu Hidaya na daga cikin masu tasiri a rubutun Hausa na zamani, kuma ana yawan dogaro da shi wajen jagorantar tattaunawa (panel moderation) da sharhi kan makomar adabin Hausa a cikin gida da waje.

2. ENGR. Alhaji Abdourahaman Mahaman General Manager, RAKAMS – Jamhuriyar Nijar.  Injiniya Abdourahaman Mahaman gogaggen shugaba ne a harkokin kasuwanci da gudanarwa a Nijar. Kwarewarsa a mu’amala tsakanin al’ummomi da inganta harshen Hausa zai taimaka wajen karin haske kan yadda rubutun Hausa ke tsallaka iyaka, da rawar da ’yan kasuwa da kafafe ke takawa wajen yaɗa adabin Hausa a ƙasashen waje.

3. Alh. Sule Muhammed Adamu Sarkin Hausawa  Kasar Guinea Bissau. Shugaban 'yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje. A matsayinsa na Sarkin Hausawa kuma shugaba Alh. Sule Muhammed Adamu na da gogewa a jagoranci da  al’adu da haɗin kan al’umma. Zai ba da gudummawa mai muhimmanci wajen rawar sarauta da ƙungiyoyi a kare harshen Hausa, da tallafa wa marubuta da rubuce-rubucen Hausa a kasashen waje.

4. Alh. Muhammad Bilal CEO/MD, BILAL SEED. Alh. Muhammad Bilal kwararre ne a harkar kasuwanci, musamman noma. Kwarewarsa za ta taimaka wajen danganta rubutun Hausa da tattalin arziki, wato yadda adabi da  wallafe-wallafe da labarai ke tallafa wa ilimi da  kasuwanci da wayar da kai ga al’ummar Hausa a ƙasashen waje.

5. Alhadji Soulemana Yahaya PDG, Centre Culturel Haoussa Du Togo. Shugaban Cibiyar Al’adun Hausawa na  Kasar Togo. Alhadji Soulemana Yahaya jagora ne a fagen al’adu da harshe. Zai yi bayani kan rawar cibiyoyin al’adu wajen tallafa wa rubutun Hausa da adana al’ada, da ƙarfafa karatu da rubutu ta hanyar taruka, baje-kolin al’adu, da ayyukan ilmantarwa a Togo da kewaye.

Ko shakka babu wannan tattaunawa za ta samar wa marubuta da manazarta haske da mafita na yadda za su baje hajarsu a ƙasashen waje.

Rubutun Hausa A Wajen Kasar Hausa

Post a Comment

0 Comments