Wannan wani dandali ne da za a rabe aya tsakuwa kan abin da ya shafi rubutu a online daga inda ya fito da kuma inda ya dosa. Sahabbai da tabi'an adabi za su ɓarje guminsu a kai.
1. Dr. Aishatu Shehu Maimota fitacciyar masaniyar Adabin Hausa ce, musamman a fannin nazarin ƙagaggun labaran Hausa (Hausa prose fiction). Ta yi karatu a matakin digiri kamar haka; B.A (Hausa/Mass Communication), PGDE, MPPA, PGDHS, HPDCS, M.A (Hausa Literature), da Ph.D (Hausa Literature) a Bayero University, Kano, abin da ke nuna zurfin kwarewa da jajircewarta a harkar ilimi. Dr. Aishatu Shehu Maimota malamar jami’a ce a Sashen Harsunan Nijeriya na Northwest University Kano, inda take koyarwa da bincike a fannin Adabin Hausa. Ta shahara a matsayin mai nazari da tantance adabi (Literary Critic), musamman rubutattun labaran Hausa na zamani. Muhimmin abin yabo a aikinta shi ne kasancewarta sahabiya ta farko da ta mayar da Adabin Hausa na yanar gizo (online Hausa literature) a matsayin jigon binciken digirin Ph.D, inda ta binciki tasirin kafafen zamani ga rubuce-rubucen Hausa. Wannan bincike nata ya bude sabuwar kafa a nazarin adabin Hausa, tare da hada gargajiya da fasahar zamani. Ta hanyar koyarwa, bincike, da wallafe-wallafe, Dr. Aishatu Shehu Maimota ta bayar da gagarumar gudummawa wajen faɗaɗa tunani da sabunta hanyoyin nazarin Adabin Hausa, musamman a duniyar zamani ta yanar gizo.
***
2. An haifi Dr. Abu-Ubaida Sani a garin Misau da ke jahar Bauchi,
Nijeriya. Ya kammala makarantar firamare ta Sabon Gari Primary School, Misau,
Bauchi a shekarar 2006. A shekarar 2012 ya samu takardar shaidar kammala
makarantar sakandare daga Governmnet College Azare, Bauchi. Daga nan ya karanci
B.A. Ed. Hausa a Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato inda ya kammala a shekarar
2017 da digiri mai darajar farko (First Class). Shi ne ya riƙe
matsayin shugaban ɗalibai
na jami’ar a zangon karatu na 2016/2017. Ya yi bautar ƙasa a jahar Zamfara a
shekarar 2018/2019. Ya kammala digiri na
biyu a shekarar 2022, digiri na uku kuwa a shekarar 2025 (M.A. Hausa Studies da
Ph.D. Hausa Studies), duk a wannan jami’a wato UDUSOK. Ya rubuta littattafai da maƙalu sama da tamanin (80)
da aka wallafa a cikin gida Nijeriya da ƙasashen waje. Ya gabatar da maƙalu
sama da ashirin (20) a tarukan ƙara wa juna sani. Sun haɗa da waɗanda ya gabatar a Nijeriya da Amurka.
Edita ne na mujallu daban-daban a ƙasashen da suka haɗa da Nijeriya da Amurka da Indiya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa. Ya fara koyarwa a sashen
Harsuna da Al’adu na Jami’ar Tarayya Gusau a shekarar 2019. A shekarar 2021, ya
koyar da Hausa a African Studies Institute, University of Georgia, USA a
matsayin Foreign Language Teaching Assistant (FLTA). Shi ne ya assasa babbar
kafar nan ta intenet wato Amsoshi (www.amsoshi.com).
Game Da Shi:
https://www.amsoshi.com/2024/04/abu-ubaida-sani-hausa-contemporary.html
Kafar Intanet: www.abu-ubaida.com
English Blog: www.english-amsoshi.com
Proz: https://www.proz.com/translator/2563055
Google Scholar:
https://scholar.google.com/citations?user=GGf1TtoAAAAJ&hl=en
ORCID: orcid.org/0000-0001-6447-4334
***
3. Amrah Auwal Mashi an haife ta a ranar 8 ga Oktoba, 1998, a Ƙaramar
Hukumar Mashi ta Jihar Katsina. Ta yi karatun addini da na boko a garin
Katsina, inda ta kai matakin digiri na farko (Degree) a karatunta na boko.
Amrah Auwal Mashi marubuciya ce wadda ta shafe shekaru goma sha ɗaya (11) tana rubutu, abin da ke nuna
jajircewa, ƙwarewa, da ci gaba a harkar adabi. Ta yi aure, tana da yara biyu, kuma a
halin yanzu tana zaune a Abuja. Ta hanyar rubuce-rubucenta, a online Amrah
Auwal Mashi na taka rawa wajen bunƙasa adabi, tare da haɗa ilimin addini da na zamani, wanda ke ba
ayyukanta armashi da ma’ana a idon masu karatu.
***
4. Bamai Dabuwa fitaccen marubucin Adabin Hausa ne, musamman a
fannin ƙagaggun labarai (Hausa prose fiction). Ya shahara ne wajen rubuce-rubuce
masu ɗauke
da darussa na rayuwa, tarbiyya, soyayya, zamantakewa da gyaran halayen al’umma.
Rubutunsa na da sauƙin fahimta, amma suna ɗauke da zurfin ma’ana da salo mai jan
hankali, wanda ya sa ayyukansa suka samu karɓuwa a tsakanin masu karatu, musamman
matasa. Yakan yi amfani da labari a matsayin madubi don nuna matsaloli da
halayen da ke cikin al’umma, tare da jaddada muhimmancin tarbiyya da gaskiya.
Bamai Dabuwa yana daga cikin marubutan Hausa na zamani da suka taka rawa wajen
bunƙasa adabin Hausa ta hanyar rubuce-rubuce da ke da alaƙa da rayuwar yau da
kullum.
***
5. Hassana Labaran Ɗanlarabawa marubuciya ce ta Adabin Hausa,
haifaffiyar Jihar Kano, a Ƙaramar Hukumar Dala, unguwar Mai’aduwa, kusa da Masallacin Lawan. Ta fara
karatu tun daga matakin nazire har zuwa N.C.E, tare da zurfafa a karatun
addinin Musulunci, makarantar dare da Dalā’ilu, inda ta sauke Alƙur’ani da wasu muhimman littattafan addini. Ta yi aure, tana da yara biyu,
kuma ta haɗa
ilimin addini da na zamani wajen gina rubuce-rubucenta. Fara rubutu ya samo
asali tun tana ƙanana, sai dai rubutun online na haƙiƙa ya
fara ne a ƙarshen shekarar 2019, inda ta wallafa labarinta na farko mai taken Sanadin
Hoto. Daga bisani ta rubuta labarai da dama, ciki har da Hassana da Hussaina,
Cin Amanar Ruhi, Bahagon Layi, Garkuwa Biyu, Bahagon Layi Sabon Salo, Hayatul Ƙadri,
Mayafin Sharri, Dabba da Rigar Mutum, da Ɗaya a Cikin Dubu (haɗaka), tare da gajerun labarai masu yawa.
Daga cikin ayyukanta da aka buga akwai Cin Amanar Ruhi, Mayafin Sharri, da Ɗaya a
Cikin Dubu, yayin da sauran suka kasance na yanar gizo.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.