Ticker

6/recent/ticker-posts

Mai Sallar Farilla Zai Iya Bin Mai Sallar Nafila?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin ko ya halatta mai sallar farilla ya yi koyi da mai sallar nafila ko kuma akasin haka?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Alal-haƙiƙa wannan wata mas'alace da Malamai sukayi saɓani a kanta, magana ta farko daga cikin maganganun da Malamai sukayi ita ce:

Mazhabin SHAFI'IYYA da kuma HANABILA sun tafi ne a kan cewa ya halatta mai sallar farilla ya yi koyi da mai sallar nafila. Daga cikin dalilansu sun kafa hujja da wannan Hadisi na Mαnzon Allαh (Sallallahu Alaihi Wasallam) wanda bayan sun idar da sallar asubah sai Mαnzon Allαh (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ga waɗansu mutane guda biyu a gefe ba su yi sallah tare da su ba, sai ya tambaye su meye ya hana ku ku yi sallah tare da mu? Sai suka ce ai mun riga munyi sallarmu ne tun a gida, sai Mαnzon Allαh (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce da su:

"فلا تفعلا، إذا صليتما في رحالكما ثم أدركتما الإمام ولم يصل فصليا معه، فإنها لكما نافلة"

 (رواه أبو داود)

MA'ANA:

Kada ku sake yin irin haka, nan gaba idan kuka riga ku ka yi sallarku a gida kuma sai ku ka zo ku ka riski Liman a Masallaci ba su yi sallah ba, to ku yi sallah tare da shi, ita wacce kuka sallata tare da Liman ta zama nafila a gare ku.

Sannan su ka ce Ma'azu Ɗan-Jabal ya kasance yana zuwa Masallacin Mαnzon Allαh (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi sallar Isha'i da shi, daga nan kuma sai ya koma unguwarsu kuma dama shi ne Liman a can, mamu suna jiransa ya je ya yi musu sallar Isha'i, haka Ma'azu Ɗan-Jabal ya kasance ya na yi kullum kuma Mαnzon Allαh (Sallallahu alaihi Wasallam) bai hanashi ba, tare da cewa shi sallar da yake yi musu limancinta a matsayin nafila ta ke a wajensa tunda ya riga ya yi tasa tare da babban Liman wato Mαnzon Allαh (Sallallahu Alaihi Wasallam).

Magana ta biyu ita ce: Mazhabin MALIKIYYA da kuma HANAFIYYA suka ce ba ya halatta mai sallar farilla ya yi koyi da mai sallar nafila, su kuma daga cikin dalilansu sun kafa hujja da Hadisin Mαnzon Allαh (Sallallahu Alaihi Wasallam) da ya ke cewa:

"إنما جعل الإمام ليؤتم به، فلا تختلفوا عليه، فإذا ركع فاركعوا……………"

 (رواه البخاري ومسلم)

MA'ANA:

Haƙiƙa an sanya Liman ne dan (ku mamu) ku yi koyi da shi, kada ku saɓa masa, idan ya yi ruku'u kuma sai kuyi……

Suka ce idan mai sallar farilla ya bi mai sallar nafila to haƙiƙa ya saɓawa Liman a wajen niyya, danhaka ba zai yi koyi da shi ba, To amma sai dai Malaman da suka tafi akan cewa ya halatta ayi suka ce wannan Hadisi da Mαnzon Allαh (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce kada a saɓawa liman yana Magana ne a kan kada a saɓa masa ne a cikin ayyukan sallah, shi ya sa ma a cikin Hadisin ya ce kada ku yi ruku'i har sai Liman yayi, kada ku ɗago daga ruku'i har sai Liman ya ɗago.

Danhaka magana mafi Inganci ita ce ya halatta mai sallar farilla ya yi koyi da mai sallar nafila ko kuma akasin haka, sannan ya halatta mai sallar farilla ya yi koyi da mai sallar farilla ko da kuwa nau'in sallolin sun bambanta da juna kamar mai sallar azahar ya yi koyi da mai sallar la'asar, ko kuma mai sallar ramuwa ya yi koyi da mai sallar lokacinta ko kuma akasin haka, Malamai suka ce duk Ya halatta a yi hakan.

шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ

 Mυѕтαρнα Uѕмαи

 08032531505

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments