Ticker

6/recent/ticker-posts

Rabe-Raben Tagwaitakar Yankin Suna a Hausa

Citation: Yahaya ABBAS & Jamila Rabiu GOGA (2020). Rabe-Raben Tagwaitakar Yankin Suna A Hausa. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. .8 Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660

RABE-RABEN TAGWAITAKAR YANKIN SUNA A HAUSA

Yahaya ABBAS dJamila Rabiu GOGA

Abstract

This article is aimed at analysing different types of appositional nominal phrase syntactically. The objective of the research is to critically study the nature of the examples of nominal appositive construction in Hausa and classify them according to their type. The Examples were drawn from both oral and written literature for the purpose of the studyHowever, the written data used include three Hausa News Papers (Aminiya) that of Friday 11th March, 2016 and Friday 8th Afril, 2016 and Friday 15th July, 2016. Similarly, a Hausa Novel titled `Yartsana by Ibrahim Sheme and of course, some examples from Hausa grammar books were also used. Similarly, the Oral source came from fifteen (15) interviews with some prominent Hausa personalities in a Radio programme called “Da NGaba....” being organized by Vision, a Private Radio Station in Katsina. The research finds out that nominal appositive construction can be Loose and close, simple and complex, Full and partial, near and distance, restrictive and non restrictive.

Taƙaitattun Kalmomi da Ma`anoninsu a Ingilishi:

Tagwaitaka =Apposition

Turke = Anchor

Musaya =Appositive

Manunin Musaya =Appositive marker

Harɗantawa =coordination

Mai ƙaidi = Restricteve

Marar ƙaidi = Non-restrictive

Cikakkiya = Full

Ragaggiya = Partial

Tsayayya = Strict

Raunanniya = Weak

YSn =Yankin suna = Noun Phrase

YSn1 = Yankin suna na ɗaya = First Nominal Phrase

YSn2 = Yankin suna na biyu = Second Nominal Phrase

YSn3 = Yankin Suna na uku = Third Nominal Phrase

Sft1 =Siffatan Goshi = Pre-head Qualifier

K2 =Kai = Head

Sft2 =Siffatan Ƙeya = Post-Head Qualifier

Sn = Suna = Noun

Dss = da sauransu =Et cetera

1.0 Gabatarwa

Nazarin Tagwaitakar Yankin Suna (Appositional Nominal Phrase) (TYSn daga yanzu) ba sabon abu ne a harshen Hausa ba. Manazarta irin su Galadanci (1969) da Furniss (1991) da Newman, (2000) da Jaggar (2001), duk sun tofa albarkacin bakinsu a kansa. Sai dai babu ɗaya da ya yi nazari a akan rabe-rabensa. Manufar wannan takarda ita ce ta yi nazarin TYSn ta hanyar tantance rabe-rabensa ta fuskar ginin jumla a Hausa ta yin amfani da misalai da bayanai gamsassu.

Misalan TYSn da aka yi amfani da su a cikin wannan takarda an zaƙulo su ne daga hanyoyi guda biyu, wato rubutattun abubuwa waɗanda suka haɗa da littattafan Nahawun Hausa da littafin `Yartsana na Ibrahim Sheme (2003) da Jaridun Aminiya guda biyu na ranakun 11/3/2016 da 8/4/2016 da 15/7/2016. Sai kuma hira da aka saurara daga wani shiri mai suna “Da na gaba” wanda ake shiryawa a gidan Rediyon Vission da ke Katsina a Jihar Katsina, waɗanda suka haɗa da: “Hira da Abashe Mai Hoto da Hira da Abdullahi Muhammad Kaita”.

1.1 Mene ne Tagwaitakar Yankin Suna?

TYSn nau`in YSn ne da yake zuwa da yankunan sunaye guda biyu ko ma sama da biyu, ba tare da wani mahaɗi ba. Kowane yankin suna na ɗauke da kai guda. Yankunan sunayen duk abu guda suke nufi. Yankin suna na biyu, yana yin ƙarin bayani ne a kan na farkon. Bayan haka, za a iya sauya gurabun yankunan sunayen guda biyu ba tare da sauyin ya haifar da wata matsala a ginin jumla ko a ma`anar jumlar ba, a wasu lokuta. Ana iya share ɗaya daga cikin yankunan sunayen, ba tare da yin hakan ya haifar da wata matsala a ma`anar jumla ba.

A TYSn, YSn na farko ana kiran sa da turke. YSn na biyu ko sama da biyu ana kiran sa ko kiran su da musaya. A kodayaushe ana ja wa turke layi a ƙasansa a kuma kaurara rubutunsa a misalan wannan bincike. Shi kuma musaya ana yin rubutunsa a jirge.

A taƙaice TYSn na da tsari kamar haka: TYSn YSn+ YSn2 + (YSn3) + ..... Wannan yana nufin cewa dole ne TYSn ta ƙunshi YSnda YSn2. Ke nan zuwan YSn3 da abin da ya yi sama ba wajibi ne ba. Ga Misalai:

(1) a. ....inàa cìke dà àlhiinin rashìn mahàifiyaataa ÀAishatu...... (Yahuza, 2016, sh. 36)

b. ......mijìntà Màanu ya matsàa matà cêewàa tà baa shì Nairà dubuu

 8000..... (Aminu da Yahuza, 2016, sh. 7)

c. Sheehùn maalàmii Maalàm Raabi`ù àlƙaalin gàrinmù.

 (Furniss 1991, sh. 34)

2.0 Bitar Ayyuka da Suka Gabata

Aikin Galadanci (1969, sh. 16) ya gudanar da shi ne kacokan a kan Sassauƙan Yankin Suna. A cikin aikin ya taɓo batu a kan TYSn, inda ya taƙaita zancensa a kan ma`ana da misalai da ya kawo a kan TYSn. Ya nuna cewa, “Tagwaitakar Yankin Suna ta ƙunshi kawuna guda biyu ba tare da wani mahaɗi a tsakaninsu ba”. Ya kawo misalai kamar haka:

(2) a. [Àlƙaali] [maalàm Bàlaa]

b. [Uwar-gidaa] [Laadì]

c. [Àli] [sarkin-kàasuwaa]

Shi ma aikin Furniss (1991, sh. 34) ya taɓo batu a kan TYSn. Batun nasa ya taƙaita ne a kan ma`ana da misalai da ya kawo a kan TYSn. Ya nuna cewa, “Tagwaitakar Yankin Suna ta ƙunshi yankunan sunaye guda biyu ko sama da biyu. Kowane yanki yana jere da ɗan`uwansa.” Ya kawo misalin TYSn kamar haka:

(3) a. [Ministàn ìlmin Nàajeeriyàa] [Àlhajì Jibril Àmiinù].

b. [Ƙungiyooyin Mùsùlmii] [’yan yaaƙin sùnƙuurùu]

c. [Mutàaneàshirin] [faraaren huulàa] suka halaka.

d. [Mâi martàbaa Sir Àhmadu Bellòo][ Sardàunan Sakkwato].

e. [Su Audù] [sàmàarii] [màtàasaa].

Newman (2000, sh. 61) da Jaggar (2001, sh. 396) duk bayanan da suka kawo a kan TYSn sun taƙaita su a kan ma`ana ta TYSn da misalai da kuma bayani a kan tubalan da suke fitowa a cikin TYSn.

Curme (1931, sh. 89-921) ya raba TYSn a Ingilishi zuwa gida biyu:

A. Buɗaɗɗiyar tagwaitaka (Loose Appositive) misali:

 (4) a. Mary, the belle of the village. (Mary, Kyàkkyaawar ƙauyèn)

b. The Smith, the friend of my youth. (Smith, àbookin nan na ƙùrùuciyaatàa)

B. Rufaffiyar tagwaitaka (Close Appositive) misali:

(5) a. My friend Jones (Àbookiinàa Jones)

b. Uncle Tom (Kaawù Tom)

Mafi yawan malaman da suka yi aiki a kan TYSn da suka zo bayan Curme, irin su Gomez (1994) da Acuna-Farina (1996) da Heringa (2012) da Kim (2014) da sauransu, sun tafi ne a kan wannan kashe-kashe da ya kawo na “Buɗaɗɗiya da Rufaffiyar tagwaitaka”.

Quirk da wasu (1985, sh. 1302) sun kawo rabe-raben TYSn zuwa “Mai ƙaidi da Marar ƙaidi” (Restricteve and non restrictive) da “Cikakkiya da Ragaggiya” (Full and Partial) da “Tsayayya da Raunanniya” (Strict and Weak). Yana da kyau a fahimci cewa Quirk da wasu (1985) maimaikon su yi amfani da sunan “buɗaɗɗiyar tagwaitaka” ko “rufaffiyar tagwaitaka” sai suka kira su da “Nonrestrictive” wato (Marar ƙaidi) wadda take daidai da “buɗaɗɗiyar tagwaitaka” da kuma “Restrictive” wato (Mai ƙaidi) wanda yake daidai da “rufaffiyar tagwaitaka”.

Su kuwa Masana nahawun Hausa da suka yi magana a kan TYSn irin su Galadanci (1969) da Furniss (1991) da Newman (2000) sun fi mayar da hankali a kan ma`ana da nau`in tubalan da suke fitowa a cikin TYSn. Babu ɗaya daga cikinsu da ya kawo rabe-raben TYSn a Hausa. Sai dai Newman (2000) ya bayyana mana a cikin littafinsa cewa “sakamakon tattaunawa da suka yi tare da Jaggar ya fahimci cewa TYSn za ta iya rabuwa zuwa gida biyu: tagwaitaka mai ƙaidi da marar ƙaidi. Ya kawo misalai guda biyu kamar haka:

(6) a. Maalàm Muusaa maalàminmù yaa yi ràasuwaa[sic] (mai ƙaidi)

 (Malam Musa our teacher died)

 (Newaman, 2000, sh. 61)

b. Maalàm Muusaa maalàminmù yaa yi ràasuwaa[sic] (marar ƙaidi)

(Malam Musa, our teacher died)

 (Newaman, 2000, sh. 61).

Waɗannan misalan an kawo su ne kamar yadda Newaman (2000, sh. 61) ya kawo a littafinsa. Sai dai abin lura a nan shi ne, waɗannan jumloli duk ɗaya ne babu wani abu da ya bambanta su, saboda haka mai karatu zai yi wuya ya iya fahimtar bambancinsu. Inda bambanci yake wuri ɗaya ne, idan aka lura da fassarar da aka kawo ta Ingilishi, za a fahimci cewa akwai waƙafi da ya raba tsakanin “Malam Musa” da “our teacher” a misali na (6b) saɓanin misali na (6a) wanda babu alamar waƙafi a cikin fassarar Ingilishin.

Newman ya nuna cewa a misali na (6a) tagwaitaka ce mai ƙaidi domin kuwa yankin suna na “malaminmu” yana ƙarin bayani ne domin a tantance malamin da ake magana a kansa. Shi kuwa misali na (6b) tagwaitaka ce marar ƙaidi saboda yankin suna na “malaminmu” a misalin ya zo ne domin ya ƙara samar da wani bayani a kan “Malam Musa” wanda ba lallai sai an kawo ƙarin bayanin ba.

Shi ma Jaggar (2001, sh. 396) ya raba TYSn zuwa gida biyu, wato mai ƙaidi (restrictive) da kuma marar ƙaidi (nonrestrictive). Ya kawo misalai kamar haka:

(7) a. Muusaa direebà zâi kai kà (mai ƙaidi)

b. Muusaadireebà zâi kai kà (marar ƙaidi)

Abin da ya bambanta misalan nan da suka gabata na (7a-b) shi ne amfani da waƙafi a misali na (7b) wanda ke nuna cewa sunan “Muusaa” da aka ambata ya wadatar da wanda ake magana da shi ya gane wanda ake magana a kansa, saboda haka zuwan kalmar “direba”, ba wajibi ne ba kwalliya ce kurum, domin ƙarin bayani a kan “Muusaa”. Saɓanin misali na (7a) inda zuwan kalmar “direebà” take da matuƙar muhimmanci, domin tantance wanda ake magana a kansa.

3.0 Rabe-Raben Tagwaitakar Yankin Suna

A Hausa za a iya karkasa TYSn zuwa gida biyu manya. Ta yin la`akari da ginin jumla, da kuma ta yin la`akari da ma`ana. Ta yin la`akari da dangantaka ta ma`ana da ke tsakanin tubalan TYSn za a iya karkasa shi zuwa gidaje uku. Akwai TYSn mai tantancewa, da mai sunƙaƙewa. Akwai kuma ta kuskure da mantuwa. Sai dai saboda kar takardar ta yi yawa sosai an taƙaita binciken a kan rabe-raben tagwaitakar ta fuskar ginin jumla kurum.

3.1 Tagwaitakar Yankin Suna tFuskar Ginin Jumla

Ta fuskar ginin jumla, za a iya raba TYSn zuwa kashi huɗu. Kashi na farko: ta fuskar fayyacewa ko rashin fayyacewar tubalan guda biyu, za a iya raba ta zuwa cikakkiya da ragaggiya. Kashi na biyu: ta fuskar kusanci ko rashin kusancin tubalan guda biyu, ana iya raba ta zuwa ta nesa da ta kusa. Kashi na uku: ta fuskar yawan tubalan musaya a TYSn, za a iya raba ta zuwa sassauƙa da sarƙaƙƙiya. Kashi na huɗu: ta fuskar dangantakar YSn na ɗaya da na biyu za a iya raba ta zuwa rufaffiya (mai ƙaidi) da buɗaɗɗiya (marar ƙaidi).

3.1.1 Cikakkiyar Tagwaitakar Yankin Suna

Ita cikakkiyar TYSn, ita ce wadda tubalan gininta guda biyu suka cika wasu sharuɗɗa guda huɗu, kamar haka:

A. Ya kasance za a iya share ɗayan tubalan guda biyu, ba tare da yin hakan ya haifar da wata matsala a ginin jumla ba; kuma ya kasance jumlolin da aka samar, bayan share tubali na ɗaya ko na biyu saƙo iri ɗaya suke ɗauke da shi. Misali:

(8) a. ....sai ya kìraa màatarsà Faatimà a wayàa.

(Babanƙarfi, 2016, sh. 76)

Idan aka dubi wannan misalin da ya gabata, za a ga cewa za a iya share ɗaya daga cikin tubalan ba tare da yin hakan ya haifar da wata matsala ga ginin jumlar ba. Misali:

b. ....sai ya kìraa màatarsà a wayàa. .

Ko a ce

c. ....sai ya kìraa Faatimà a wayàa. .

Idan aka lura, duk da share tubali na biyu a misali na (8b) da kuma share tubali na ɗaya a misali na (8c), jumlar da aka samar bayan share tubalin karɓaɓɓiya ce a ginin jumlar Hausa. Haka kuma saƙon da jumlar take ɗauke da shi duk ɗaya ne da jumlar asali mai ɗauke da tubala guda biyu.

B. Ya kasance za a iya yin musayar gurbi tsakanin tubalan guda biyu ba tare da yin hakan ya kawo wata matsala ga ma`anar ginin tagwaitakar ba, ko ya haifar da wasu sauye-sauye ga TYSn ta asali ba. Misali:

(9) a. ......mijìntà Màanu yà màtsa matà cèewaa tà baa shi Naira

 dubuu 800..... (Babanƙarfi, 2016, sh. 7)

A sharaɗi na biyu na (B) za a ga cewa za a iya yin musayar gurbi tsakanin waɗannan tubala guda biyu, wato za a iya cewa:

b. .…..mijìntà Màanu yà màtsa matà cèewaa tà baa shi Naira

dubuu 800..... 1 2 (Babanƙarfi, 2016, sh. 7)

Ko kuma a ce:

c. .….. Màanu mijìntà yà màtsa matà cèewaa tà baa shi Naira dubuu

 800..... 2 1

Idan aka yi la`akari da misali na (9b) za a fahimci cewa an samu musayar gurbi a misali na (9c) tsakanin tubali na ɗaya da tubali na biyu, inda tubali na ɗaya ya koma a gurbin tubali na biyu shi kuma tubali biyu ya dawo a gurbin tubali na ɗaya.

C. Ya kansance duk tubalan guda biyu abu ɗaya suke nufi. Misali

(10) a. ...naa rasà màataatà Faatìima.....

 (Babanƙarfi, 2016, sh. 7)

A sharaɗi na uku na (C) za a ga cewa tubalan guda biyu duk abu ɗaya suke nufi, wato matata ita ce Fatima, kuma Fatima ita ce matata.

D. Ya kasance tubalan matsayinsu ɗaya a cikin jumlar. Misali:

(11) a. Shin ba ta yàudarìi Ɗaahirù direebà à kan haka bàa?

 (Sheme, 2013, sh. 21)

A sharaɗi na huɗu na (D), za a ga cewa duk tubalan guda biyu matsayinsu guda wato duk sun zo ne a matsayin karɓau kai tsaye[1]. Dubi wasu ƙarin misalai na cikakkiyar TYSn:

(12) a. Bàaƙôn naamù Àlhajì Bishir Ɓaatagaraawàa

(Shirin da na gaba: hira da “Hira da Saulawa Ishaƙ Batgatawa”)

b. ...daga jikinsà kuma akà halìtta màatarsààbookìyar zamansà,

 Hàwwaa. (Yahuza, 2016, sh. 36)

c. ....indà akà ɗauràa auren àbookiinàa kuma ɗan`uwaanàaNaasìr Ìbraahìm...... (Yahuza, 2016, sh. 36)

3.1.2 Ragaggiyar Tagwaitakar Yankin Suna

A gefe guda kuma, duk TYSn da ya saɓa wa ɗaya daga cikin waɗancan sharuɗɗa guda huɗu da aka ambata a baya (3.1.1), ita ake kira da ragaggiyar TYSn. Misali:

(13) a. Wani ma` àikacìn bankìi dà ya riƙà zuwàa wajentà wai shii

 Bàraa`ù Eemìyaa. (Sheme: 2003, Sh. 72)

Idan aka lura da wannan misalin da ya gabata na (13a) za a ga cewa ya cika wasu daga cikin sharuɗɗan can guda huɗu, alal misali tubalan guda biyu duk abu ɗaya suke nufi. Ke nan ya cika sharaɗi na “C”, domin kuwa Bara`u Emiya shi ne dai ma`aikacin banki, haka kuma ma`aikacin banki shi ne dai Bara`u Emiya. Haka kuma idan aka lura sosai za a ga cewa duk sunayen guda biyu matsayinsu guda a cikin jumlar duk sun zo ne a matsayin aikau[2] a cikin jumlar, kenan misalin ya cika sharaɗi na “D”. Sai dai kuma, wannan misali (13a) da wuya ya iya cika sharaɗi na “A”. Misali:

b.* Wani ma` àikacìn bankìi dà ya riƙà zuwàa wajentà wai shii.

c. Wani dà ya riƙà zuwàa wajentà wai shii Bàraa`ù Eemìyaa..

Idan aka share tubali na biyu aka bar na farko kamar a misali na (13b) za a ga cewa jumlar na buƙatar sauyi kafin ta zama cikakkiya. Idan kuma aka share tubali na farko aka bar na biyu kamar a misali na (13c) za a ga cewa jumla ta zama karɓaɓɓiya.

Haka kuma da wuya misalin na (13a) ya iya cika sharaɗi na “B” da ke magana a kan musayar gurbi. Misali:

d.* Wani Bàraa`ù Eemìyaa dà ya riƙà zuwàa wajentà wai shii ma` àikacìn bankìi.

Ta fuskar ma`ana, wannan misali da ya gabata na (13d) yana da matsala, domin kuwa tubali na farko da ya zo suna ne keɓantacce, bai kamata a ce an biyo shi da suna wanda yake ba keɓantacce ba. Sunan ma`aikacin banki bai keɓanta da wani ba, saboda haka ma`anar jumlar sai ta fito wani bambaraƙwai.

Ga wasu ƙarin misalai na ragaggiyar TYSn:

(14) a. ....zaa mù ɗaurà auren Tàwurnòo dà Wani àlmaajìrii mài suunaa

 Tukur. (Sheme: 2013, Sh. 40)

b. Wani ɗan kàasuwaa dà kèe sayar dà mânjaa da mân gyàɗaa a bàbbar kàasuwar dà kèe tsakiyàr birnin Bauchi, Àlhajì Àmìinu Mài mânjaa....... (Aliyu, 2016, sh. 12)

c. ......ɗaya daga cikìn sauran mazan jiyàaÀlhajì Shàtiimà Àli

 Monùnòo...... (Muhammad, 2016, sh. 5)

3.1.3 Tagwaitakar Yankin Suna ta Kusa

TYSn ta kusa ita ce wadda tubalan da suka gina ta suke dab-da-dab da juna. Babu wata kalma da ke ratsawa tsakaninsu. Ba a samun manunin musaya a irin wannan nau`in na TYSn. Manunin musaya tubala ne da suke zuwa dab da yankin suna musaya irin su “wato”, “wai”, “wai shi”, “mai suna” dss. A magana ta fatar baki ma ba a samun wata tazara tsakanin tubalan guda biyu. Haka nan a wajen rubutu ba za ka ga alamar waƙafi ta raba tsakanin tubalan ba. Yawanci a irin wannan nau`in TYSn ɗaya daga cikin tubalan kan zo ne a matsayin suna gama-gari sai ɗayan kuma ya zo a matsayin sunan yanka, ko akasin haka. Wani lokaci kuma ɗaya daga cikin tubalan zai zo da ma`ana ta gaba ɗaya sai ɗayan ya zo da ma`ana fitacciya. Misali:

 

(15) a. ....na rasà màataataa Faatimà.....

(Babanƙarfi, 2016, sh. 7)

b. Haalàyyar Mutàanee mazaa da maataa

(Sheme: 2013: Sh. 176)

c. ……..tà hanyàr nuunaa masù mìsàalai na `yan`uwansu ɗaalìbai dà suka faaɗàa cikìn tarkòn cîn hànci dà rashawaa…... (Haruna, 2016, sh. 3)

3.1.4 Tagwaitakar Yankin Suna ta Nesa

Ita kuwa TYSn ta nesa ita ce wadda ake samun tazara tsakanin tubali na ɗaya da na biyu a TYSn. Ga misali:

 

(16) a. Ɗìyaataa tà farkoo Safìyaa taa auri Inuwà Jibrin

(shirin da “Na gaba” Hira da “Àbdullàahi Kan-batuta”)

b. Mahàifìn naatà aikìi yà kai shi Màlumfashi Àlƙalì Jibrin

 (shirin da “Na gaba” Hira da “Kabir Mamman

 Barda”)

c. Wani Sanataa wandà kèe wakiltàr kudancin jihàr Taraaba a Màjàlisàr Dàttìjai mài suna Sanataa Emmanuel Bwacha yaa cee......

(Isa, 2016, sh. 4)

Idan aka lura da misalan da suka gabata na (16a-c) za a ga cewa akwai tazara tsakanin tubalan guda biyu.

3.1.5 Sassauƙar Tagwaitakar Yankin Suna

Wani lokaci tubalin da ake kira musaya, wato tubali na biyu a TYSn kan zo falan ɗaya wani lokaci kuma sama da ɗaya. Idan TYSn ta zo da musaya nau`i ɗaya a cikinta, sai a kira ta da sassauƙar TYSn. Misali:

 (17) a. ...tanàa gòoye dà `yarta mài suunaa Hadìiza...

(Babanƙarfi, 2016, sh. 7)

b. ....na rasà màataataa Faatimà.....

(Babanƙarfi, 2016, sh. 7)

c. Haalàyyar Mutàanee mazaa da maataa

(Sheme: 2013: Sh176)

Misalan da suka gabata na (17a-c) suna ɗauke ne da musaya falan ɗaya, kamar yadda ya zo a misali na (17a): “Hadiza” da misali na (17b) : “Faatima”. Haka nan idan aka dubi misali na (17c) shi ma za a tarar cewa falan ɗaya ne duk da cewa ya zo da harɗantawa[3]: “maza da mata”

3.1.6 Sarƙaƙƙiyar Tagwaitakar Yankin Suna

Idan kuma TYSn ya zo da musaya sama da ɗaya a cikin gini guda, to ana kiran sa da sarƙaƙƙiyar TYSn. Ga misali:

(18) a. [Su Audù] [sàmàarii] [màtàasaa].

 (Furniss, 1991, sh. 35)

b. [Mahàifinsa],[Marìgàayii][Àlhaji Muusaa `Yar`aduwàa], [Màtawàllen Kàtsinà]...... (Gwarzo, 2016, sh. 15)

Misalan nan da suka gabata na (18a da b) suna ɗauke ne da turke ɗaya wato “Su Audu” da kuma “mahaifinsa”. Shi kuwa musaya ya zo ne guda bibbiyu: “samari” da “matasa” a misali na (18a), sai kuma “marigayi Alhaji Musa `Yar`adua” da “matawallen Katsina” a misali na (18b), wanda hakan na nuna kowane yana ɗauke da musaya sama da ɗaya.

3.1.7 Buɗaɗɗiyar Tagwaitaka da Rufaffiyar Tagwaitaka

Ana samun buɗaɗɗiyar tagwaitaka a lokacin da waƙafi ya raba tsakanin tubali na farko da tubali na biyu, ko wata kalma ɗaya ko biyu ta shiga tsakaninsu. Idan kuma babu waƙafi a tsaakanin tubalan, kuma babu wata kalma da ta shiga tsakanin tubalan, to ke nan an sami rufaffiyar tagwaitaka. Dubi waɗannan misalai:

(19) a. Maalàm Muusaa maalàminmù yaa yi ràasuwaa[sic]

 (Newman 2000, sh. 61)

b. Maalàm Muusaa, maalàminmù yaa yi ràasuwaa [sic]

 (Newman 2000, sh. 61)

Idan aka yi nazarin waɗannan misalai guda biyu da suka gabata na (19a da b), za a fahimci misali na (19b) an raba tubalansa guda biyu ta yin amfani da waƙafi. Abin da ke nuna kowane ɓangare zaman kansa yake yi. Saɓanin misali na (19a) wanda babu waƙafi da ya shiga tsakanin tubalansa haka kuma babu wata kalma ko kalmomi da suka shiga tsakaninsu.

Abin da ya bambanta rufaffiya da buɗaɗɗiya abubuwa biyu ne. Abu na farko shi ne buɗaɗɗiyar tagwaitaka tana zuwa da waƙafi ko wata kalma ko kalmomi da ka iya shiga tsakanin tubalan guda biyu. Ita kuma rufaffiyar ba ta da wannan tsarin.

 

Abu na biyu shi ne ma`ana. Tubali na biyu da yake zuwa a rufaffiyar tagwaitaka yana zuwa ne domin ya tantance tubali na farko. Ita kuwa buɗaɗɗiya, saboda waƙafi ko kalma da ta shiga tsakanin tubalan ya sanya an sami wasu tubala guda biyu masu zaman kansu, masu ɗauke da bayanai biyu mabambanta. Tubali na biyu a buɗaɗɗiyar tagwaitaka yana ɗauke ne da wani sabon bayani a kan tubali na farko.

(20) a....daga jikinsà kuma akà halìtta màatarsààbookìyar zamansàHàwwaa.

 (Buɗaɗɗiya) (Yahuza, 2016, sh. 36)

b. .... auren àbookiinàa kuma ɗan`uwaanàaNaasìr Ìbraahìm...... (Buɗaɗɗiya) (Yahuza, 2016, sh. 36)

c. Haalayyar Mutàane mazaa da maataa. (Rufaffiya)

(Sheme: 2013: Sh176)

d.…….. mìsàalai na `yan`uwansu ɗaalìbai. (Rufaffiya) (Haruna, 2016, sh. 3)

4.0 Kammalawa

An yi nazarin misalai na TYSn da dama a ƙarƙashin nazarin ginin jumla, sai aka rarraba su ta fuskoki guda huɗu. Kashi na farko: ta fuskar fayyacewa ko rashin fayyacewar tubalan guda biyu na TYSn sai aka raba ta zuwa cikakkiya da ragaggiya. Kashi na biyu: ta fuskar kusanci ko rashin kusancin tubalan, sai aka raba ta zuwa ta nesa da ta kusa. Kashi na uku: ta fuskar yawan tubalan musaya a TYSn sai aka raba ta zuwa sassauƙa da sarƙaƙƙiya. Kashi na huɗu: ta fuskar dangantakar YSn na ɗaya da na biyu sai aka raba ta zuwa rufaffiya (mai ƙaidi) da buɗaɗɗiya (marar ƙaidi). Waɗannan su ne nau`o`in ko rabe-raben TYSn a Hausa kamar yadda wannan binciken ya gano.

Manazarta

Acuña-Fariña, J.C. (1996). The puzzle of apposition. On so-called appositive structures in English. Santiago de Compostela: UniversidAade, Servicio de.

Aliyu, H. (2016, July 15) Na Samu Rufin Asiri a Kasuwancin Manja. Jaridar Aminiya P 12.

Aminu, H. U. da Yahuza, B. (2016, April 8). Ya Kashe Matarsa a kan kuɗin GadoJaridar Aminiya, P 7.

Babanƙarfi, A. (2016, July 15). Ruwa Ya Ci Mai Goyo da `Ya`yanta Uku. Jaridar Aminiya P 7.

Curme, G. O. (1931). Syntax. Boston: D. C. Heath and Company.

Furniss, G. (1991). Second level Hausa: Grammar in action.SOAS, University of London.

Galadanci, M. K. M. (1969). The Simple Nominal Phrase In Hausa. [Unpublished PhD Thesis]. SOAS, University of London

Gómez, P. (1994). Apposition in English: A Linguistic Study Based on a Literary Corpus. Revista Alicantina de Estudios Ingleses 7: 83-95.

Haruna, A. (2016, March 11). Yadda Ɗalibai ke Damfara ta Yanar Gizo - Hukumar EFCC. Jaridar Aminiya P 3.

Heringa, H. (2012). Appositional Constructions. PhD Thesis, University of Groningen. LOT. http://www.rug.nl/research/portal.

Isa, M. (2016, March 11). Ci-rani ya Zama Matsala a Taraba. Jaridar Aminiya P 4.

Jaggar, P. J. (2001). Hausa. John Benjamin B.V.

Kim, J. (2014). Similarities and Differences Between the Close and Loose Apposition. In English. English Language and Linguistics 20.3, 79-98.

Newman, P. (2000). The Hausa language: An encyclopedic reference grammar. Yale University Press.

Quirk, R., S. Greenbaum, G. Leech & J. Svartvik (1985). A comprehensive grammar of the English language. Longman.

Sheme, I. (2003) `Yartsana. Kaduna: Informart Publishers.

Shirin da na gaba: hira da “Hira da Saulawa Ishaƙ Batgatawa”

Shirin da “Na gaba” Hira da “Àbdullàahi Kaita”

Shirin da “Na gaba” Hira da “Kabir Mamman Barda

Yahuza, B. (2016, April 8). Ashe Soyayya gamon Jini ce? Jaridar Aminiya, P 36.



[1] Karɓau kai-tsaye shi ne sunan da aiki ya faɗa a kansa wato “direct object” da Ingilishi.

[2] Aikau shi ne wanda ya yi aiki a jumla wato “subject” a Ingilishi.

[3] . Harɗantawa na nufin “coordination” a Ingilishi.

 Yobe Journal Vol. 8

Post a Comment

0 Comments