Citation: Muhammad ABDUL-ƘADEER (2020). Amfani Da Fasahar Sadarwa Ta Zamani Wajen Koyo Da Koyar Da Hausa. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. .8 Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660
AMFANI DA FASAHAR SADARWA TA ZAMANI WAJEN KOYO DA KOYAR DA HAUSA
Muhammad ABDUL-ƘADEER
Abstract
The Information and Communication Technology (ICT) today becomes part and parcel of human life. It penetrates every corner and angle of human activities such as business, media services, banking, health care, and educational sector among others. The aim of this paper is to examine the use of Information and Communication Technology in learning and teaching Hausa Books, interview, listening to radio, attending programmes and lectures are methods used in gathering data for this study. The paper discovers that, radio, computer, handset and projector which are part of ICT are used in teaching and learning Hausa.
Tsakure
A yau fasahar sadarwa ta zamani ta zama wani ɓangare da ɗan’adam yake tafiyar da al’amuran rayuwarsa ta yau da kullum. Wato ta shiga lungu da saƙo na harkokin rayuwar ɗan’adam da suka haɗa da: harkokin kasuwanci da na kafafan sadarwa da na bankuna da na kiwon lafiya da na ilimi da saraunsu. Manufar wannan takarda ita ce, duba yadda ake amfani da fasahar sadarwa ta zamani wajen koyo da koyar da Hausa. Bugaggun littattafai da hira da sauraron kafafan watsa labarai da halartar tarurruka da laccoci su ne hanyoyin da aka yi amfani da su wajen tattara bayanan da aka gudanar da binciken. Bincike ya gano cewa rediyo da tashoshin tauraron ɗan’adan da kwamfuta da wayar-tafi-da- gidanka da kuma na’urar majigi da ke wasu ɓangarori na fasahar sadarwa ta zamani duk ana amfani da su wajen koyo da koyar da Hausa.
1.0 Gabatarwa
Fasahar sadarwa ta zamani suna ta tara domin ta ƙunshi abubuwa da dama da suka haɗa da: rediyo da talabijin da wayar tafi-da-gidanka da kwamfuta da intanet da na’urar majigi da tashoshin tauraron ɗan’adam da sauransu. A yau wannan fasaha ta zama ruwan dare game duniya, domin ta yi ruwa da tsaki a duk harkokin rayuwar ɗan’adam ta yau da kullum. Ta shiga cikin harkokin kasuwanci ta yi dumu-dumu. Haka kuma ta yi ruwa da tsaki a cikin harkokin kiwon lafiya. Sannan ta faɗa cikin harkokin aikin bankuna da na gwamnati ta mamaye. har wa yau, fasahar ba ta tsaya a nan ba, domin ta shiga harkokin ilimi ta yi kane-kane.
Wannan maƙala ta duba yadda ake amfani da wannan fasahar sadarwa ta zamani wajen koyo da koyar da Hausa. Don haka, maƙalar ta ƙunshi: ma’anar sadarwa da hanyoyin sadarwa da ma’anar fasahar sadarwa ta zamani da kuma yadda ake amfani da fasahar sadarwa ta zamani wajen koyo da koyar da Hausa.
2.0 Ma’anar Sadarwa
Masana daban-daban sun bayyana ma’anar sadarwa kwatankwacin yadda suka fahimce ta. Daga cikin ire-iren waɗannan masana akwai: Zarruƙ, da wasu, (1986 sh. 21). Sun bayyana sadarwa da cewa: “Miƙa saƙo irin na hattara ko gargaɗi ko dai wata sanarwa ta musamman da kuma aikata wani abu sakamakon wannan saƙon. Irin wannan hulɗa da ke faruwa tsakanin al’umma ita ake nufi da sadarwa”. Shi kuwa Rambo, (2015 sh. 643) cewa ya yi: “sadarwa na nufin wata dabara da mai saƙo zai bi domin ya sami isar da saƙonsa kuma a fahimce shi, wani lokaci har a mayar masa da amsar saƙonsa. Don haka, hanya ce ta fahimtar juna da mu’amula ta yau da kullum a cikin al’umma”.
Bisa la’akari da waɗannan ma’anoni da suka gabata, a taƙaice za a iya cewa, sadarwa na nufin isar da wani saƙo ko saƙonni ga jama’a ta hanyar yin amfani da wasu ɓangarori na jiki ko wani abu domin busawa ko bugawa ko rubutawa ko kuma furta wata magana a baki.
2.1 Hanyoyin Sadarwa
A yau za a iya kallon hanyoyin sadarwa ta fuskoki guda biyu: wato hanyoyin sadarwa na gargajiya da kuma hanyoyin sadarwa na zamani (Zarruƙ, 2000 sh. 26-28).
2.1.1 Hanyoyin Sadarwa na Gargajiya
Hanyoyin sadarwa na gargajiya su ne hanyoyin da al’ummar Hausawa suka gada tun tale-tale daga iyaye da kakanni suke amfani da su wajen isar da saƙonninsu. Ire-iren waɗannan hanyoyi sun haɗa da: shela ko yekuwa da busa ƙaho da buga ganga ko kuge da kuma isharori daban-daban. Kamar: gwalo da gatsine da harara da guɗa da kururuwa da sauransu.
2.1.2 Hanyoyin Sadarwa na Zamani
Su kuma waɗannan hanyoyi na zamani baƙi ne a wajen al’ummar Hausawa domin sun samu ne a dalilin cuɗanya da wasu al’ummu na duniya. Ire-iren waɗannan hanyoyi na zamani sun haɗa da: rediyo da talabijin da jaridu da tarho da mujallu da wayar-tafi-da-gidanka da intanet da sauransu. Duk da cewa baƙin abubuwa ne al’ummar Hausawa ta tasirantu da su.
3.0 Fasahar Sadarwa ta Zamani
Fasahar sadarwa ta zamani tsari ne na aiwatar da sadarwa mai inganci da fa’ida, ta amfani da kayayyakin sadarwar zamani irinsu: kwamfuta da wayoyin salula da tauraron ɗan’adam da na’urorin sadarwar zamani da hanyoyin sadarwar zamani kamar: fasahar intanet da imel da saƙonnin tes da shirye-shiryen talabijin masu inganci da sauransu.
3.1 Amfani da Fasahar Sadarwa ta Zamani Wajen Koyo da Koyar da Hausa
Daga cikin kayayyakin fasahar sadarwa ta zamani da ake amfani da su wajen koyo da koyar da Hausa da wannan maƙala ta zo da su, sun haɗa da: rediyo da tashoshin tauraron ɗan’adam da kwamfuta da wayar-tafi-da gidanka da kuma na’ura majigi. Yanzu za a duba su ɗaya bayan ɗaya a ga yadda ake amfani da su wajen koyo da koyar da Hausa.
3.1.1 Rediyo (Radio)
Wannan wata hanya ce da ake amfani da ita domin watsa labarai da kuma isar da wasu saƙonni ga jama’a. A yau wannan hanya tana ɗaya daga cikin hanyoyin da ake amfani da su wajen koyo da koyar da Hausa. Misali: gidan rediyon Freedom na Kano suna yin wani shiri mai suna Adabi Madubin Rayuwa. Wato shiri ne da ya ƙunshi nazarin littattafan adabi. A shirin ana karanta littafi adabi ne na zube malami yana fashin baƙi dangane kayan cikin littafin. Wanda yake gabatar da shirin shi ne Garba Ibrahim Tsanyawa. Jagoran shirin kuma shi ne Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo. Ana gabatar da shirin ne ranar Lahadi da misalin ƙarfe takwas zuwa tara na dare. Masu sauraro sukan ribatu da abubuwa da dama daga shirin kamar ta fuskar: kalmomi masu zurfin ma’ana da maganganun azanci da mawallafi ya yi amfani da su da kuma kalmomin nazari. Shirin yakan taimaka wa ɗalibai masu nazarin Hausa a kwalejoji da Jami’o’i wajen laƙantar hanyoyi nazarin adabin Hausa. Saboda sukan kira jagororin shirin kai tsaye ta hanyar amfani da wayar-tafi-da-gidanka domin neman ƙarin bayani a game da wasu abubuwan da ba su fahimta ba. Wannan wata sabuwar hanya ce aka ƙirƙiro da mutum zai iya amfanuwa da ita wajen koyo ko koyar da Hausa ba tare da an yi haɗuwa irin wadda aka saba yi a cikin a aji ba.
Haka kuma akwai wani shiri da bankin Keystone ya ɗauki nauyi da shi ma wannan gidan rediyo na Freedom yake gabatarwa mai suna Aiki da Hankali, wanda marigayi Malam Habibu Sani Ɓaɓura da ke jami’ar Bayero, Kano yake jan ragamar shirin. Daga bisani Dakka Abdullahi Garba Imam ya karɓi ragamar akalar shirin. Mai gabatar da shirin shi ne Musa Best Tela Dirimin-Iya. Alƙalin shirin kuma shi ne Mohammed Umar Sharaɗa. Ana gabatar da shirin ne ranar Juma’a da misalin ƙarfe biyar zuwa ƙarfe shida na yamma. Wannan shiri ya ƙunshi wasa ƙwaƙwalwa ne. Wato a shirin akan karanto tambayoyi domin sauraron amsoshinsu daga masu takara da ba su wuce mutum uku ba da masu sauraro. Za a ba wa kowane ɗan takara dama ya zaɓi lamba ɗaya daga cikin lambobin tambayoyin da aka karanto. Idan ɗan takara ya zaɓi lamba sai a buɗe a karanto masa tambayar. Idan ya amsa a ba shi maki biyu, idan kuma ya kasa sai a miƙa tambayar ga sauran ‘yan takara. Idan su ma suka kasa amsawa, sai a miƙa ta ga masu sauraro, idan su ma ba su iya bayar da amsa ba, sai mai jan akalar shirin ya faɗi amsa. Sannan a ƙarshen shirin akan buƙaci alƙalin shirin ya karanto sakamako. Akan bayar da kyauta ga wanda ya zama zakara. A wannan shiri akan shiga fagen harshe da adabi da al’adun Hausa, a ciro wasu kalmomi ko jumloli ko baitoci a waɗannan fannoni a nemi ɗan takara ya bayar da ma’anarsu. Ta wannan fuska masu sauraro sukan ƙara rumbun kalmominsu da fahimtar wasu abubuwa da suka danganci Harshe da Adabi da Al’adun Hausa. A halin yanzu wannan shiri an dakatar da shi sakamon hutu na korona da ake ciki.
Sannan akwai wani shiri da gidan rediyon Arewa da ke Kano yake gabatarwa mai suna Hausa ba dabo ba. Mai gabatar da shirin shi ne Abubakar Ƙoƙi. Jagoran shirin kuma ita ce Dakka Hasiya M. Nafi’u. A shirin ana nazarin littattafan adabi ne da suka shafi wasan kwaikwayo da rubutun zube da kuma waƙoƙi. Wannan shiri yana taimaka wa ɗalibai masu nazarin adabin Hausa, wajen sanin makamar nazarin adabin Hausa. Ita ma wannan wata baƙuwar hanya ce da yanzu ake amfani da ita wajen koyo da koyar da Hausa ga mazauna gida.
3.1.2 Tashoshin Tauraron Ɗan’adam (Satellite)
Wannan ma wata kafa ta sadarwa ce da ake amfani da tauraron ɗan’adam wajen isar da saƙonni waɗanda za a iya gani da sauraro ta akwatin talabijin. Daga cikin tasoshi na tauraron ɗan’adam da ake gudanar da shirye-shiryen Hausa akwai: Arewa 24 da Zango da Wisal Hausa da Sunna TƁ da sauransu. Misali a tashar Arewa 24 akwai shirin da take gabatarwa wanda ake koyo da koyar da Hausa cikinsa. Ana yi wa shirin laƙabi da Harshe Tubalin Ginin Al’umma. A wannan shiri ana tattaunawa ne da wasu masana Harshen Hausa, a kan abin da ya shafi harshe da adabin Hausa. Ana gabatar da shirin ranar Lahadi tara zuwa goma na safe. Daga cikin malaman akwai: Dakka Abdullahi Garba Imam wanda ake tattaunawa da shi a kan karin maganganun Hausa. Malamin yakan baje kolin karin maganganun Hausa kana ya bi su ya yi musu fashin baƙi. Sai kuma Dakta Tijjani Shehu Almajir wanda ake tattaunawa da shi a kan Harshen Hausa. Shi kuma harshe yake baje koli ya bi ya yi fashin baƙi a game da abubuwan da ya ƙunsa. Ɗaya daga cikin masu gudanar da shirin shi ne Mukhtar Haruna. Wannan shiri shi ma masu sauraro sukan ƙaru da shi. Har ma suna yabawa da shi. Domin wani daga cikinsu ya taɓa faɗa mini cewa, idan yana sauraron shirin, sai ji kamar ba Bahaushe ba ne shi. Saboda abubuwan da ake bayani da yawa bai san su ba. Wannan hanya ita ma sabuwa ce a ɓangaren koyo da koyar da Hausa. Domin ita ma ba a buƙatar mutum sai ya je makaranta. Yana daga gida za a ba shi ilimi ya amfanu da shi ya kuma amfanar da wani.
3.1.3 Kwamfuta
Kwamfuta na nufin wata na’ura mai aiki da wutar lantarki ko batir, sannan take da ikon karɓar bayanai, ta sarrafa ta adana, sannan tana iya dawo da bayanan a duk lokacin da aka buƙaci hakan (Dawakin Tofa, 2012 sh. 3). Ita ma wannan fasaha ana amfani da ita wajen koyo da koyar da Hausa. Malamai sukan yi amfani da ita wajen kalato ɗanyun bayanai daga intanet tare taimakon maƙalutun sadarwa (modem) waɗanda za su yi amfani da su wajen shirya laccarsu kuma su adana su a cikinta. Yayin da suka zo lacca sai su buɗe suna karantawa suna yi wa ɗalibai bayani. Haka su ma ɗalibai kan yi amfani da ita wajen lalubo ɗanyun bayanai da za su amfana da su wajen gudanar da ayyukan da malamansu suka ba su. A yau wannan na’urar kwamfuta ta kasance mafi akasarin Malamai suna amafani da ita wajen gudanar da darussansu musamman a manyan makarantu. Wannan fasaha ita ma baƙuwa ce a fagen koyo da koyar da Hausa.
3.1.4 Na’urar Majigi (Projector)
Wannan kuma na’ura ce da ake amfani da ita domin nuna hoto mai motsi da wanda ba ya motsi ta hanyar amfani da hasken lantarki. Ita ma wannan fasaha ana amfani da ita wajen koyo da koyar da Hausa. Ta amfani da wannan fasaha Malami kan gudanar da laccarsa ba tare da ya yi rubutu bisa allo ba, sai dai kawai a yi amfani da wannan fasaha ta haskawa ɗalibai su dinga ganin abin da malaminsu yake karantawa a jikin wannan allo. Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau, da wannan fasaha ya yi amfani yayin ƙaddamar da laccarsa ta Waƙar Baka Bahaushiya (The Hausa Oral Songs) a rana 26 ga watan Mayu 2014. A lokacin da yake gabatar da laccar, nan take ana haska wa masu sauraro hoton rubutun da yake karantawa suna gani bisa allo. Haka kuma, Zahra’u Ibrahim Waya tta ma ta yi amfani da wannan hanya wajen gabatar da maƙalarta a taron ƙara wa juna sani da Cibiyar Nazarin Harsunan Nigeria, Fassara da Fasahar Ɗan’adam tare da haɗin gwiwar Sashen Harsunan Nijeriya da na Kimiyar Harshe da Harsunan Ƙetatare, Jami’ar Bayero, Kano ranar 2 zuwa 4 ga watan Satumba. Ita wannan hanya ba a daɗe da fara amfan da ita ba wajen koyo da koyar da Hausa. A taƙaice dai, ita ma baƙuwa ce a fagen koyo da koyar da Hausa.
3.1.5 Wayar-ta-fi-da-gidanka (Wayar Salula)
Wannan wata ƙaramar na’ura ce da ke ɗauke da madannai da akan yi amfani da ita wajen buga waya ko tura saƙo ko neman ɗanyun bayanai da ita ta hanyar intanet. Umar, (2014 sh. 521) ya bayyana wayar salula da cewa: “Hanyar sadarwa ce ta zamani wadda al’ummar Hausawa ke amfani da ita wajen biyan buƙatunsu na yau da kullum kama daga abin da ya shafi sada zuminci tsakanin ‘yan uwa da abokan arziki, ta hanyar kira ko magana ko ta amfani da wani sashe na wayar mai ba mutum damar shirya rubutaccen saƙo ko bayani domin isar wa ga wani ko wasu cikin ƙanƙanin lokaci, ba tare da ɓata kuɗi masu yawa ba”. Sai dai kuma ba al’ummar Hausawa ba ce kaɗai ke amfani da ita. Sauran al’ummu ma suna amfani da ita. Kamar yadda ake amfani da kwamfuta wajen lalubo ɗanyun bayanai (data) da akan yi amfani da su wajen gudanar da bincike ko koyo da koyar da Hausa, ita ma wannan fasahar sadarwa ta zamani akan yi amfani da ita, ta wannan fuska. Haka kuma, akan yi amfani da ita wajen ɗaukar laccar da malami ke gabatarwa a aji ko wajen wani taro na daban. Sannan akan yi amfani da ita a buga wa malamai ko masana domin yi musu tambaya yayin da aka buƙaci neman ƙarin haske daga gare su a game da wani abu da ya shige wa mutum duhu. Sannan ɗaliban sukan yi amfani da kafar sada zumunta ta “WhatsApp” su buɗe wani gruf domin ƙara wa junansu sani. Misali: akwai gruf mai suna “Aruli Ra’i Khalilil da wasu ɗaliban jami’ar Bayero Kano, masu neman digiri na biyu suka buɗe. A wannan gruf, ɗaliban suna ƙara wa junansu ilimi ne dangane da abin da ya shafi ilimin arulin Hausa. Har wa yau wani gruf ɗin da suka kira shi da suna “Asabe”. Shi kuma suna nazarin waƙoƙin Hausa ne a wannan gruf. Haka kuma, ma’aikatan gidan rediyo kan yi amfani da ita wannan fasaha ta sadarwa ta zamani wajen yin hira da malamai ko masana Hausa a game da harshen Hausa ba tare da sun ga juna ba duka da nufin ilimantarwa. Kamar yadda sauran hanyoyin sadarwa na zamani da aka ambata a sama, ita ma wannan fasahar sadarwa ta zamani baƙuwa ce ta fuskar koyo da koyar da Hausa.
Duk waɗannan hanyoyi da aka kawo a sama, na fasahar sadarwa ta zamani, hanyoyi ne da idan mutum yana da kusanci da su, zai kwashi ilimi cikin ruwan sanyi.
4.0 Kammalawa
A wannan maƙala an ga cewa ana amfani da fasahar sadarwa ta zamani wajen koyo da koyar da Hausa. A binciken an gano hanyoyin sadarwa na zamani daban-daban waɗanda ake amfani ake amfani da su wajen koyo da koyar da Hausa. Daga cikin hanyoyin da aka gano akwai: fasahar sadarwa ta rediyo da ta tauraron ɗan’adam da ta kwamfuta da ta na’uarar majigi da kuma ta wayar-tafi-da-gidanka. Sannan a gano cewa ta wannan fasaha ɗalibai sukan kwashi ilimi a zaune a ɗaki daga wajen malamansu ba tare da sun je aji sun zauna ba. Haka kuma, malaman haɗa da ɗaliban duk sukan yi tarayya ta yin amfani da fasahar domin neman bayanai a fannonin ilimi daban-daban da kuma adana su ba tare da sun ɓace ba. Har wa yau, amfahimci cewa mazauna gida sukan amfana da ita wannan fasahar sadarwa ta zamani wajen sauraron darussan Hausa daga malamai da masana fannoni Hausa daban-daban. A ƙarshe, ina fata wannan bincike zai zaburar da manazarta harshen Hausa ya kuma sa musu ƙaimi wajen faɗaɗa bincike a wannan fage. A wajena maƙalar sharar fage ce kawai ga manazarta Hausa, domin za su iya ɗaukar ɓangare ɗaya da aka kawo a maƙalar su zurfafa bincike a kansa ko kuma su ƙwaƙulo wasu fannoni na Hausa da ake koyo da koyarwa ta hanyar amfani da fasahar sadarwa ta zamani.
Manazarta
Dawakin Tofa, M. A. Y. I. (2012). Mukoyi kwamfuta a aikace. Salihu Memorial Enterprises.
Rambo, R. A. (2015). Fasahar sadarwa ta zamani ga al’adun al’ummar Hausawa. cikin Algaita Journal of Current Reseach in Hausa Studies, Special Edition Ɓol. 1. No, 1, 205-212. Department of Nigerian Languages, Bayero Uniɓersity.
Umar, M. M. (2014). Zumuntar Bahaushe a zamanin GSM. Garkuwan Adabin Hausa, A Festschrift in Tribute to Abdulƙadir Dangambo. Departmenta of Nigerin Languages, Kano: Bayero Uniɓersity.
Zarruƙ, M. R. da Kafin Hausa, A. A, da Al-Hassan, B. S. Y. (1986). Sabuwar hanyar nazarin Hausa: Don ƙananan makarantun sakandare littafi na biyu. Uniɓersity Press
Zarruƙ, M. R. da Kafin Hausa, A. A, da Al-Hassan, B. S. Y. (2000). Sabuwar hanyar nazarin Hausa: Don ƙananan makarantun sakandare littafi na ɗaya. Uniɓersity Press

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.