Ticker

6/recent/ticker-posts

Yarfe a Tarihin Siyasar Jam’iyyu a Kasar Hausa: Duba Cikin Rubutaccen Zube

Article Citation: Yusuf, J. & Sani, A-U. (2025). Yarfe a tarihin siyasar jam’iyyu a ƙasar Hausa: Duba cikin rubutaccen zube. Scholars International Journal of Linguistics and Literature, 8(10): 234-246. https://doi.org/10.36348/sijll.2025.v08i10.001.

YARFE A TARIHIN SIYASAR JAM’IYYU A ƘASAR HAUSA: DUBA CIKIN RUBUTACCEN ZUBE

Na

Jibril YUSUF, Ph.D.
Department of Nigerian Languages and Linguistics,
Kaduna State University, Nigeria
Email: yusuf.jibril@kasu.edu.ng
Phone: +2347030399995 

Da

Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and Cultures,
Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | abu-ubaidallah@fugusau.edu.ng
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736

Tsakure

Manufar wannan takarda ita ce nazartan yadda ‘yan siyasa suke amfani da abubuwa na ɓatanci ga abokan hamayyarsu na siyasa. Tunanin wannan takarda ya taso ne duba da yadda yan siyasa suka mayar da wannan abu tamkar in babu shi to siyasar ma ba za ta yiwu ba. Wannan ya sa aka ga dacewar a shiga cikin ayyukan adabi na rubutaccen zube a gani shin ‘yarfe’ yana da asali ne tun kafuwar siyasar jam’iyyu ko kuwa bai daɗe da samuwa ba? An yi nazarin yarfe a cikin tarihin siyasa da aka kundace a cikin ayyukan rubutaccen zube. An ɗora binciken kan ra’in ‘Tarihanci’ inda ya yi jagorancin zaƙulo tarihin yarfe a harkokin siyasar ƙasar Hausa. Takardar ta gano cewa, yarfe abu ne da ya ginu a cikin siyasar jam’iyyu tun daga farkon lamari. Bugu da ƙari, har yanzu ana amfani da shi domin neman ƙarin mabiya da kuma shafa wa abokan hamayyar siyasa kashin kaji, wanda hakan kan taimaka ga samun nasara ko faɗuwa a zaɓe.

Fitilun Kalmomi: Yarfe, Siyasa, Jam’iyyun Siyasa, Ƙasar Hausa

1.0 Shimfiɗa

Samuwa da bunasar siyasar jam’iyyu a asar Hausa ya zo da wasu abubuwa da suka zama tamkar gishiri a cikin miyar siyasar a ƙasar Hausa. Tun a farkon siyasar jam’iyyu, a ƙasar Hausa an riƙa samun musayar yawu daga magoya bayan jamiyyu masu hamayya da juna. An samu rubuce-rubuce cikin jaridu da wasiƙu da jawaban siyasa waɗanda suke ƙunshe da alamuran siyasa da suka faru a wancan lokacin. Yarfe yana daga cikin irin waɗannan abubuwa da suka zama tamkar ruwan dare a cikin siyasar jam’iyyu, kuma ya ci gaba da gudana har zuwa wannan jamhuriya da ake ciki, wato jamhuriya ta huɗu. Ayyukan adabi sun riƙa fito da hoton yadda al’amuran suka shafi yarfen suka riƙa gudana, inda aka riƙa amfani da su domin shaf wa jamiyyu da yan siyasa kashin kaji, ta hanyar manna masu wani aibu da ba su ji ba, ba su gani ba. Irin waɗannan al’amura na ɓatanci ga jam’iyya da magoya bayansu shi ne wannan takarda ta ƙuduri aniyar yin nazarinsu domin ganin yadda suka ginu a cikin tarihin siyasar jamiyyu a ƙasar Hausa.

1.1 Waiwaye

Nazari a kan ayyukan adabi da suka haɗa da rubutattun waƙoƙi da rubutattun wasannin kwaikwayo da kuma rubutattun zube ba sabon abu ne a fagen nazarin Hausa ba, musamman idan aka yi laakari da irin gudummawar da masana da manazarta suka bayar wajen fito da muhimman abubuwan da suka ƙunsa. Masana da manazarta irin su Mashi (1986) da Birniwa (1987) da Funtua (2003) da Ɗangulbi (2003) da Ɗanillela (2010) da Sani (2012) da Adamu (2019) da Adamu (2021) sun yi waɗannan nazarce-nazarce ne ta la’akari da yadda adibai suka baje kolin basirarsu kan al’amuran siyasa a cikin ayyukansu na adabi. Yawancin nazarce-nazarce da ayyukan da aka gudanar sun shafi nazarin zubi da tsari da salo da kuma jigo ne; sai aikin Idris (2016) ya yi nazarin bijirewa a waƙoƙin siyasa da Yusuf (2018) wanda ya yi nazarin tarihin Jamiyyar PDP a cikin rubutattun waƙoƙin siyasa.

Dangane da batun samuwa da bunƙasar siyasar jam’iyya kuwa, za a iya alaƙanta shi da cuɗanyar da aka samu tsakanin Turawa da al’ummar ƙasar Hausa. Birniwa, (1987 sh. 27-28) ya bayyana cewa tun a wuraren shekarun 1930-1940 ne aka fara jin ƙamshin samuwar ƙungiyoyin siyasa a Arewacin Nijeriya. An samu ɓullar ƙungiyoyi da dama duk da cewa ba su fito fili ƙarara a karon farko sun kira kansu da jam’iyyun siyasa ba, amma dai sun samar da cibiyoyin da sukan riƙa haɗuwa lokaci-lokaci domin tattauna al’amuran siyasa. Su kuwa Dudley (1968 sh. 78-79) da Idris (2016 sh. 51) suna da ra’ayin cewa, an fara samun ɓullar ƙungiyoyi ne a tsakanin shekarar 1943-1944. Ƙungiyoyin da aka samar wannan lokacin sun haɗa da; Ƙungiyar Inganta Rayuwar Mutanen Bauchi (BGIU) wadda Sa’adu Zungur ya kafa a 1943, da Ƙungiyar Tattaunawa ta Mutanen Bauchi (BDC) a 1944, da Ƙungiyar Zumunta ta Sakkwato (YSC) a 1945, da Ƙungiyar Matasa ta Kano (KYA) a 1948 da Ƙungiyar Matasan Zariya (ZYA) ita ma a 1948 da sauransu. Waɗannan ƙungiyoyi da ma wasu duk an kafa su ne a tsakanin 1943 zuwa 1948, waɗanda su ne suka narke suka zama jam’iyyar NPC a shekarar 1951, daga baya kuma wasu suka ɓalle suka kafa jam’iyyar NEPU. Waɗannan Jam’iyyun da aka samu wato NEPU da NPC su ne suka kasance manyan jam’iyyun siyasa guda biyu masu hamayya da juna a ƙasar Hausa.

Duk da cewa masana da manazarta sun bayar da gagarumar gudummawa kuma suka cancanci yabo, amma ba a samu wani aiki na nazarin ilimi da hannu ya kai kansa wanda aka yi nazarin yarfe daga cikin rubutaccen zube na Hausa ba. Wannan ne ya sa aka ga dacewar tattauna wannan batu a cikin wannan takarda domin ganin yadda yake da kuma yadda ake gudanar da shi a cikin siyasa.

2.0 Bitar Muhimman Kalmomi

A nan an kawo ma’anonin muhimman kalmomin taken maƙalar ne. Yin hakan zai ba da haske wajen fahimtar inda maƙalar ta dosa da kuma abubuwa da nazarin ya tattauna a kansu.

 

2.1 Ma’anar Yarfe[1]

Ƙage da Ƙazafi kalmomi ne da suke da makusantan ma’anoni da juna ko ma a ce ma’anarsu guda, sai dai kowacce da asalinta, kuma ana iya amfani da wata a maimakon wata. Kalmar Ƙage Bahaushiyar kalma ce, tana ajin suna ne mai ɗauke da jinsin namiji. Tana nufin a ce mutum ya yi abin da bai ji ba, bai gani ba ko kuma a ƙulla masa sharri (CNHN, 2006 sh. 273). Ƙazafi kuwa kalma ce da take da asali daga Larabci wato Ƙazaf, wadda Hausawa suka ara suka yi mata ƙarin -i a ƙarshenta ta koma ƙazafi. Maanar kalmar a Hausa da Larabci duk abu guda take nufi. Kalmar Ƙazafi suna ne mai ɗauke da jinsin namiji, kalmar tana nufin laƙa wa mutum laifi ko yi masa sharri (CNHN, 2006 sh. 279).

Kalmar Yarfe Bahaushiyar kalma ce, tushen kalmar shi ne [yarf-], da aka yi mata ɗafin [-a] a ƙarshenta sai ta koma [yárfà] wadda take kalmar aikatau ce mai ɗauke da karin sautin sama-ƙasa, daga gare ta ne aka samo kalmar [yarfe] bayan an shafe wasalin ƙarshe [-a] aka yi wa tushen kalmar ɗafin [-e] a ƙarshenta, sai ta koma [yárfé] wanda ya sa karin sautinta ya sauya zuwa sama-sama maimakon sama-ƙasa a kalmar yarfa, sai kuma sauyawar karin sautin ya haifar da sauyawar ajin nahawun kalmar daga aikatau zuwa suna[2].

Ƙamusun CNHN (2006 sh. 479-480) ya bai wa kalmar yarfe ma’anoni guda biyar kamar haka:

i- Maka ko daka

ii- watsa

iii- ƙaga

iv- aika da, musamman na zagi

v- amfani da hannu don share wani abu.

Daga cikin waɗannan maanonin, maana ta biyu da ta uku ne suke da alaƙa kai tsaye da wannan takardar, domin a ƙarƙashin maana ta biyu an ba da misali da ‘na watsa masa taɓo kuma duk abin da aka watsa masa taɓo to an ɓata wannan abin, domin zai nuna alamomi a wurare da dama a jikinsa. Ita ma maana ta uku daga cikin maanonin an ba da misali ƙarƙashinta kamar haka: ‘Sun ƙaga masa laifi. Ke nan kalmar yarfe tana nufin ƙaga wa wani mutum wani laifi kamar yadda aka bayyana ta a sama. Idan aka ƙaga wa wani mutum wani laifi wanda bai ji ba, bai gani ba yakan zubar masa da ƙima ko ya rage masa ƙima a idon mutane. Idan magoya bayansa ne sai a samu wasu su dawo daga rakiyarsa.

Don haka, kalmar tana nufin a sanya wani baƙon abu a jikin wani ta yadda zai iya yin ɗigo-ɗigo a jikinsa har ya fito a gani. Alal misali, kamar a samu farar tufa a yarfa mata manja ko wani baƙin mai wanɗa zai zama an ɓata wannan tufar. Manufar yarfe a siyasance ita ce ɓatawa, kamar yadda aka yarfa wa wannan farar tufar wasu launuka don a ɓata ta.

Kalmomi biyu na farko wato ‘ƙage da ƙazafi dukkansu kalmomi ne da ake amfani da maanarsu a cikin harkokin yau da kullum, kuma in aka yi amfani da su suna iya dacewa da ko wa aka jefa da su. Akan iya cewa an yi wa wane ƙage, ko an yi wa wane ƙazafi, amma kalmar yarfe ta kasance kalma ce da ta keɓanci siyasa. A siyasance ba a cewa an yi wa mutum ƙage ko ƙazafi, sai dai a ce an yi masa yarfe[3]. Ke nan, daga bayanan da suka gabata za a fahimci cewa, kowane yarfe, ƙage ko ƙazafi ne, amma ba kowane ƙazafi ko ƙage ne yarfe ba.

Yarfe wani yanayi ne da abokan hulɗar siyasa sukan ɗauko wani abu su ɗora wa wani wanda bai ji ba bai gani ba don kawai a ɓata shi a siyasance. Yarfe zai iya kasancewa a tsakanin ‘yan jam’iyya guda masu hamayya da juna, waɗanda sukan ƙirƙiri wani abu su jingina shi ga wani abokin hulɗar siyasarsu na jamiyya guda don su musguna masa. Akan kuma samu yanayin da jamiyya guda ake, amma ana ƙarƙashin wani uban gida na siyasa, sai a yi wa juna yarfe don neman samun gindin zama a wajen iyayen gidan nasu. A wani gefen kuma yakan iya zama ba jamiyya guda yan siyasar suke ba, sai a ƙirƙiri wani abu a jefa wa abokin hamayya don mutane su dawo daga rakiyarsa, don neman samun nasara a kan jamiyyar da ake hamayya da ita[4]. Alal misali an ga yadda aka riƙa yamaɗiɗi da wani batu da ake cewa wai ɗan takarar shugabancin Nijeriya a jamiyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya ce, Allah ba ya karɓar adduar talakawa. Kuma duk wanda aka tambaye shi yaushe ya faɗa? A ina ya faɗa? Babu wanda zai iya kawo hujjar muryarsa, ko hoto mai motsi, ko kuma a rubuce, sai dai a ce kawai haka aka ce. Wa ya ce? Shi ma a nan sai kuma a fara yan kame-kame. Maana dai yarfe ne aka yi masa wanda kuma ya yi tasiri ƙwarai a zukatan alummar ƙasa. Akwai ire-iren waɗannan misalai da dama da aka riƙa samu a cikin siyasar jamiyya, sai dai waɗanda wannan bincike ya taƙaita a kansu su ne waɗanda aka samu a cikin rubutaccen zube kaɗai ban da na baka.

A taƙaice, kalmar Yarfe bisa fahimtar wannan nazarin tana nufin faɗin wani abu da bai tabbata ba, tare da danganta shi da abokan hamayyar siyasa ko jam’iyyar siyasa ko ɗan siyasa, wanda zai sa jamaa su ga baƙinsu.

2.2 Tarihi

Kalmar tarihi Balarabiyar kalma ce wato (At-tarikh) kamar yadda ƙamusun harshen Larabci Lisan Al-Arab ya bayyana, wanda yake nufin abubuwan da suka shuɗe. CNHN (2006 sh. 428) ya bayyana kalmar tarihi da cewa labarin abubuwan da suka wuce.

Ta fuskar ma’ana ta ilimi kuwa, Carr (1961 sh. 8) ya nuna cewa, tarihi shi ne bin diddigin abubuwa da suka faru na gaskiya ta hanyar samun tabbas daga masanin tarihi. Ya nuna cewa, ana samun tabbas a kan labarin da ya shuɗe ne ta hanyar wanda ya ga abin da ya faru ko ya ji, ko samun kayayyakin tarihi ko rubutaccen bayani da masana tarihi kan rubuta tare da duba lokaci da bigire da jerantuwar tunani a kan labarin, da dai sauransu.

Lawal (2018 sh. 47) ya ce, kafin tarihi ya amsa sunansa na tarihi sai ya cika wasu sharuɗɗa, kamar bayani daga wanda ya ji ko ya gani (oral tradition) ko samun kayan tarihi (Archaeological source) ko rubutaccen bayani daga masana tarihi (written decument). Kuma ana la’akari da bigire da lokaci da jerantuwar tunani a labarin.

Ta la’akari da ma’anonin da ka kawo a sama, wannan binciken yana da fahimtar cewa, tarihi yana nufin tabbataccen bayani kan faruwar wani abu a wani ayyanannen lokaci da ya shuɗe. Yana iya kasancewa na baka ko rubutacce.

2.3 Ma’anar Siyasa

An bayyana kalmar siyasa da cewa, Balarabiyar kalma ce wadda asalinta daga kalmar “saasa” ne, amma saboda ƙaidar tasarifi na nahawun Larabci sai kalmar ta koma siyaasa, wadda take nufin juyawa a kan wani lamari ko kuma yarda da wani ko jiɓintar al’amarin al’umma tare da saninsu ko ba tare da saninsu ba (Idris, 2016 sh. 49).

A cikin Ƙamusun CNHN, (2006 sh. 397) an kawo ma’anoni huɗu da suke bayyana siyasa kamar haka:

a.       Tafiyar da al’amuran jama’a ta hanyar neman ra’ayinsu da shawarwari da su.

b.      Rangwame, musamman a ciniki.

c.       Dabara ko wayo.

d.      Iya hulɗa da jama’a.

A ma’ana ta ilimi kuwa, masana da dama sun bayyana fahimtarsu dangane da ma’anar siyasa, inda suka dubi kalmar ta fuskoki mabambanta. Daga cikinsu akwai:

A ra’ayin Mashi, (1986 sh. 16) ya bayyana siyasa ne ta fuskoki uku: Hanya ta farko ya bayyana ta da ma’anar salo. Sauran hanyoyin kuwa wato ta biyu da ta uku, ya bayyana siyasa da cewa sulhu ko sauƙi. Waɗannan ma’anoni da ya bai wa siyasa ba za su rasa nasaba da yadda siyasa ta kasance hanyar lallashi ko lallaɓa mutane domin neman goyon bayansu ba. Haka kuma ya kalli siyasa a matsayin yaudara ko ƙarya, saboda yadda yan siyasa kan tsara wani lamari na yaudara domin neman biyan buƙata.

A ra’ayin Funtua, (2003 sh. 19-20) ya nuna siyasa da cewa, ararriyar kalma ce ta Larabci wadda take nufin sauƙi ko rangwame ko jin ƙai. A da, da zarar an ce wa mutum ɗan siyasa to ana nufin mutum mai jin ƙai, kuma mai rangwame, wato dai mutum mai jin tausayin al’umma.

Shi kuwa Idris, (2016 sh. 49) ya bayyana siyasa da cewa hanya ce ta tafiyar da mulkin jama’a a zamanance ko a gargajiyance. Haka kuma dabara ce ta jawo hankalin mutane ta hanyar karkata ta inda suka sa gaba a kowane fage. Misali idan ɗan siyasa ya lura da abin da mutane suka fi so, to shi ma sai ya karkata ta can ko da kuwa da gaske har cikin zuciyarsa ba yana nufin hakan ne ba.

A taƙaice dai, idan aka dubi waɗannan ma’anoni da aka bai wa siyasa za a iya cewa, siyasa tana nufin neman ra’ayin jama’a ta hanyar amfani da lafuzza masu daɗi da suka ƙunshi tausasawa da nuna jin ƙai da rangwame da ƙarya, domin samun biyan wata buƙata wadda kan iya kasancewa ta neman shugabancin al’umma ko cimma wani buri na rayuwa.

3.0 Ra’in Bincike

An ɗora wannan bincike a kan Ra’in Tarihanci (Historicism Theory), wanda masanin falsafa Karl Wilhelm Fredrich Schlegel (1772-1829) ya samar. Masana da manazarta irin su, Blackburn (1994) da Barry (1995) da Habib (2008) da kuma Lawal (2018) sun ba da ma’anar tarihanci daidai fahimtarsu kamar haka:

A fahimtar Blackburn (1994 sh. 167) ya bayyana ma’anar tarihanci hanya ta fahimtar abubuwan zahiri na zamantakewa ta yadda za a iya bin diddigin faruwarsu da haɓakarsu, domin ba a iya gane abubuwan zahiri na rayuwa, kamar dimokuraɗiyya ko sassaucin ra’ayi ta la’akari da yadda suke a yanzu, ba tare da kallon tarihinsu ba. Masanin ya nuna cewa sanin tarihin abubuwan da suka faru a cikin al’umma musamman abin da ya shafi salon shugabanci kamar na dimokuraɗiyya ko wasu ra’ayoyi na rayuwa, ba a iya fahimtarsu ta hanyar duban halin da ake ciki a yanzu, dole sai an koma ga tarihi.

Shi kuwa Barry (1995 sh. 170) a tasa fahimtar ya bayyana tarihanci da cewa, wata hanya ce ta ƙulla alaƙa tsakanin matanin adabi da wanda ba na matani ba, sau da yawa masu ɗauke da lokacin tarihi iri ɗaya. Ya nuna cewa, a cikin nazarin adabi ta fuskar tarihanci akan ƙulla alaƙa ne tsakanin matanin adabi wato rubutaccen adabi da wanda ba rubutacce ba. A nan idan aka lura za a ga cewa ta hanyar tarihanci ne ake tabbatar da wani abu da ya faru a cikin tarihi da zamanin da ya faru ta hanyar amfani da matanin adabi.

Habib (2008 sh. 147) a tasa ma’anar ya bayar da wasu siffofi ne da za a iya tantance tarihanci da su, inda ya nuna cewa, dole ne a karanci adabi ta muhallin al’adarsa, da sauran muhallan tattaunawa waɗanda suka kama tun daga siyasa da addini da ƙawa ko kwalliya, da kuma tattalin arziƙi. A nan masanin yana nufin idan har za a yi nazarin adabi ta mahangar tarihanci to wajibi ne a dubi wasu mihimman abubuwa waɗanda akan tattauna a kansu kamar siyasa da addini da tattalin arziƙi da sauransu. A wata ma’ana da Lawal (2018 sh. 34) ya kawo, ya ce, tarihanci yana nufin duba yadda al’amuran tarihi suke a cikin matanin adabi ta hanyar la’akari da rubutaccen tarihi domin samun tabbas.

Ke nan, idan aka dubi waɗannan ma’anonin da aka kawo sama za a iya cewa tarihanci ba wani abu ba ne illa, nazarin wasu al’amuran da suka shafi rayuwa waɗanda suka danganci al’ada da addini da siyasa da tattalin arziƙi da sauran gwagwarmayar rayuwa a cikin matanin adabi ko ba na matani ba ta hanyar duba zuwa ga ingantaccen tarihi.

An fara amfani da ra’in tarihanci ne tun a ƙarni na 18. Rain yana bayani ne a kan yadda tarihi yake bayyana hanyoyi da tsarin rayuwar alumma. Haka kuma, yana bayyana yadda wasu alamurra suka faru a cikin wani zamani, da irin ci gaban da aka samu cikin aladu na can dauri da kuma bayanin wurin zaman wata alumma.

George Hegel (1770- 1831) yana ganin cewa tabbatuwar ‘yancin ɗan Adam shi ne maƙasudin adana tarihi, wanda kuma hakan kan samu ne kaɗai ta hanyar samar da tabbatacciyar ƙasa. A ganin wannan masani, sanin abin da ya faru a baya shi ne yake ba da damar rayuwa cikin yanci da fita daga ƙangin bauta, domin yakan ba da damar fahimtar inda aka fito don a ƙara ɗaura ɗamara zuwa inda aka dosa.

Ƙarƙashin wannan rain an sake samun wani sabon tunani a wuraren shekarun 1980 da aka kira shi da suna Sabon Tarihanci wanda wani Ba’amirke matarki mai suna Stephen Greenblatt ya samar a shekara ta (1980). Greenblatt ya samar da Sabon Ra’in Tarihanci ne a sakamakon wasu nazarce-nazarce da ya gudanar, sai aka buƙaci ya tattara ayyukan ya nazarce su ta fuskar wani rai na musamman, sai ya samar da wannan rai da ya kira Sabon Tarihanci New Historicism a shekarar 1980. (Lawal ,2018 sh. 35).

Nazari ta mahangar ra’in tarihanci, shi ne dubi zuwa ga al’amura na tarihi a cikin adabi ta hanyar danganta wannan adabin zuwa ga tarihi na haƙiƙa daga masana tarihi, kuma wannan tarihin ya kasance tabbatace ta sigar rubutu.

Greenblatt (1980 sh. 47) ya tabbatar cewa, tarihanci yana ɗauke da manyan ginshiƙai ko tubala guda biyu da ake dubawa a wajen tarken adabi. Ga su kamar haka:

a.       Matsayin Tarihi a Cikin Matani(Historisity of a Text)

b.      Sahihancin Tarihi a Rubutaccen Labari(Textuality of history)

Ke nan, a duk lokacin da ake tarken adabi ta mahangar tarihanci, sai an dubi yadda adabin yake ɗauke da zantuttuka na tarihi a cikinsa, wato yadda aka gina zantuttukan tarihi da nuna su a bisa tarihin na gaskiya. Na biyun kuwa, shi ne a nazarci yadda labarai ko bayanai da aka rubuta suke ɗauke da tarihin da su marubutan suka sarrafa da irin sahihancin wannan tarihin daga tunanin marubutan, wato ya kasance tabbatacce ne ta sigar bayar da labari. A ƙarƙashin waɗannan manyan tubala guda biyu ne ake tarken adabi ta mahangar ra’in tarihanci kamar yadda Greenblatt (1980 sh. 47) ya bayyana.

Idan aka dubi ra’in da kyau za a fahimci cewa, da farko an kira shi tarihanci ne kawai, sai bayan tatttara ayyukan da Greenblatt ya yi ne ya sake nazarinsu bisa ra’in na tarihanci sai ya kira su “Sabon Tarihanci”.

Dangane da bambanci tsakanin Tarihanci da Sabon Tarihanci kuwa, Habib (2008 sh. 147) ya ce, mafi yawan abubuwan da suka gabata a ƙarƙashin jagorancin Sabon Tarihanci ba wani sabon abu ba ne, sai dai za a iya cewa yana wakiltar salon nazari da bunƙasar tarihanci na gargajiya da ya gabata ne. Idan aka lura za a fahimci cewa, Sabon Tarihanci ba wani sabon abu ne na daban ba, sai dai za a iya cewa Sabon Tarihanci ci gaban Tsohon Tarihanci ne kawai, domin duk manufarsu ɗaya ce a fagen nazari.

Mabiya wannan mazahaba sun haɗa da: Louiz Montrose da Michael de Montaigne da G. B. Vico da George Hegel. Wasu daga cikin nazarce-nazarce na adabin Hausa da aka gudanar ta mahangar ra’in tarihanci sun haɗa da: Usman (2016) da Yusuf (2018) da Lawal (2018) da Bunza (2018) da Ali (2020)

Wannan ne ya sa aka ga dacewar zaɓen wannan ra’in domin ɗora shi a kan wannan takarda, kasancewar tana bayani ne kan abin da ya shafi yadda abokan hamayyar siyasa suka riƙa amfani da yarfe a cikin tarihin siyasar ƙasar Hausa, wanda ya fito a cikin rubutaccen zube na Hausa.

4.0 Nazarin Yarfe a Siyasar Ƙasar Hausa

Jam’iyyun siyasa sun shahara ƙwarai wajen yi wa juna yarfe, kasancewar kowacce tana so ta ɗaukaka a kan abokiyar hamayyarta, wannan ya sa abokan hamayyar siyasa sukan riƙa ƙaga aibu ga ‘yan’uwansu suna faɗa wa jama’a don su guje su, ko da kuwa daga baya za a fahimci cewa wannan abin da aka danganta jam’iyyar ko ɗan siyasar da shi ba gaskiya ba ne.

A lokacin da aka fara siyasar jam’iyyu a ƙasar Hausa, jamiyyu biyu ne aka kafa a ƙasar Hausa kuma suka yi tashe, sannan kuma dukkansu sun yi gwagwarmayar neman mulki, inda ɗaya ta yi nasara, ɗaya kuma ta zama jamiyyar hamayya. Al’adar siyasa ce dole in za a tallata jam’iyya ko ɗan takara, bayan an yi amfani da yabon abin da ake tallatawa, wajen faɗin ingancinsa, sai kuma a kushe abokin haɗinsa ko abokin hamayyarsa domin a sake fito da hasken abin da ake tallatawa ya fito fili, al’umma su karɓe shi, su kuma guji wanda ba shi ba. A wurin wannan kushen ne ake samun yarfe ga jam’iyyun siyasa.

Tun daga jamhuriya ta farko an riƙa samun irin waɗannan bayanai a cikin rubutaccen zuben Hausa, inda jam’iyyu biyu masu hamayya suka yi ta yi wa juna yarfe a tsakaninsu. A wasu lokutan ma ba tsakanin jam’iyyun kaɗai yake tsayawa ba, har ma da yan jamiyya, inda akan kama suna, wani lokaci kuma sai dai a yi ishara. Jam’iyyar NEPU da Jam’iyyar NPC sun yi suna wajen irin wannan siyasar, wadda za a iya cewa daga gare su ne tsarin siyasar jam’iyya ya ginu a ƙasar Hausa. Irin waɗannan misalai na yarfe sun fito a cikin rubutaccen zube na Hausa, waɗanda suka yi nuni da irin wainar da aka toya a fagen siyasar Jamiyyu a wancan lokacin. Daga bisani, an ci gaba da samun yarfe a cikin rubutattun ayyukan zuben Hausa waɗanda suka ci gaba da fito da hoton yadda siyasar jamiyyu ta gudana har zuwa yau.

Dangane da wannan nazarin an raba yarfen siyasa zuwa gida uku, sannan an ɗauki kowanne an yi bayaninsa tare da misalan da suka dace kamar haka:

1.      Yarfe na addini

2.      Yarfe na ƙima/halaye

3.      Yarfe na tafiyar da shugabanci

4.1 Yarfe Na Addini

Kalmar addini tana nufin hanyar bauta wa Ubangiji (CNHN, 2006 sh. 3). A mana ta ilimi kuwa, Farouk (2006 sh. 49) ya nuna cewa, kalmar addini ararriyar kalma ce daga Larabci, wadda take nufin hanyar da ɗan Adam yake dogara a gare ta domin bauta wa mahalicci da kuma bin hukunce-hukuncen sharia domin kwaɗayin kyakkyawar sakamako duniya da lahira.

Shi kuwa Muhammad (2006 sh. 6) ya ce, addini yana nufin yadda mutum ya fifita wani abu, ya kuma bauta masa, ko dai suna ganinsa ko kuma ba su ganin sa. Ɗan Alhaji (2006 sh. 17) ya nuna cewa, addini wata babbar hanya ce da ɗan Adam yakan bi domin ganawa da ubangijinsa, yarda da shi da muƙa wuya a gare shi da kuma kiyaye ƙaidoji da kuma dokokin wannan hanya kamar yadda Allah ya shimfiɗa. Idris (2010 sh. 7) ya bayyana addini da cewa, hanyar bauta ce da yarda da Allah a bauta masa ta yin abin da ya ce da barin abin da ya ce a bari. Haka kuma Hanya ce ta bauta wa wani abu saɓanin Allah don neman biyan buƙata.

A fahimtar wannan takarda, addini hanyar rayuwa ce ta ɗan Adam, wadda ake bi ta hanyar yarda da saudaukar da kai da kuma bauta domin samun biyan buƙata ko kariya ko kuma tsira a gaban Ubangiji. A siyasance addini yana taka muhimmiyar rawa wajen neman shugabanci da kuma tafiyar da shi, kasancewar shi ne hanyar rayuwar da ‘yan Adam suke bi kuma suka amince da shi. Ita kuwa siyasa ta kasance ginshiƙi a rayuwar ɗan adam wadda yake gudanar da ita da saninsa ko ba da saninsa ba. Wannan ya sa yan siyasa suka riƙa amfani da addini wajen cimma burikansu na siyasa ta fuskoki da dama.

Yarfen siyasa yana daga cikin abubuwan da aka riƙa amfani da addini wajen gudanar da shi, inda aka riƙa amfani da wasu abubuwa na addini domin daƙile tafiyar abokan hamayya. Kasancewar addini yana da tasiri ƙwarai a wajen masu shi ko mabiyansa akan samu wasu yan siyasa su yi amfani da shi wajen shafa wa abokan hamayya wani mummunan abu wanda zai sa a ga baƙinsu, a ƙyamace su.

Tarihi ya nuna cewa ‘yan siyasa sun riƙa yi wa abokan hamayyarsu yarfe ta hanyar amafani da addini kamar yadda Paden (1973 sh. 122) ya kawo bayanai a kan irin rikice-rikicen da aka riƙa samu a tsakanin mabiya aƙidun Tijjaniyya da Ƙadiriyya har suka riƙa yi wa juna yarfe kamar haka:

The Sultan of Sakkwato later denied that the riot was between Qadiriyya and Tijaniya, throughout the country and more especially in big towns, live amicably without interference in each other’s religious belief. He referred to the rioters as ‘Yan Wazifa’ who are going beyond their bounds... to them even prayer five time a day was forbidden.

Fassarar marubuci:

Sarkin Musulmi ya ƙaryata batun rikicin da ya faru tsakanin Tijjaniyya da Ƙadiriyya, waɗanda suke zaune lafiya a duk faɗin ƙasar musamman ma a manyan garuruwa, inda ya bayyana cewa waɗansu masu neman wuce gona da iri ne; masu cewa sallah biyar a wuni haramun ne, waɗanda ake kira yan wazifa suka tayar da rikicin.

A farkon kafuwar siyasar jam’iyyu aƙidun Addinin Musulunci sun taka muhimmayar rawa a a cikin siyasar ƙasar Hausa, duk kuwa da cewa shaihunnan waɗannan ɗariƙu ba yan siyasa ne ba, kuma ba su da alaƙa da ita, amma an yi amfani da darajarsu da na aƙidunsu a cikin siyasar wancan lokacin, inda suka kasance tamkar ma su ne jamiyyun a karon farko. Idan aka yi laakari da magoya bayan kowace jamiyya za a ga cewa akasarinsu mabiya aƙida guda ne, duk da cewa akan samu wasu yan kaɗan da suke da bambancin aƙidar. Alal misali, Jam’iyyar NPC ta su Ahmadu Bello Sardauna kaso mafi tsoka na mabiyanta ‘yan Ƙadiriyya ne, haka ma dukkan manyan masarautun ƙasar Hausa ɗariƙar Ƙadiriyya suke bi in ban da fadar Kano a wancan lokacin zamanin Sarki Abdullahi Bayero wanda shi mabiyin ɗariƙar Tijjaniyya ne[5]. Ita kuwa jam’iyyar NEPU ta su Malam Aminu Kano mafi yawa na mabiyanta a wancan lokacin ‘yan Tijjaniyya ne. Wannan dalilin ne ya sa ko da aka riƙa samun rikice-rikice tsakanin aƙidun biyu sai aka riƙa danganta shi da siyasa.[6] Dangantakar siyasar da take tsakanin aƙidun biyu ya sanya suka riƙa yi wa juna yarfen siyasa a tsakaninsu.

Idan aka dubi bayanin da yake sama za a fahimci cewa, kasancewar Sarkin Musulmi Baƙadire kuma a wancan lokacin dukkan sarakuna suna goyon bayan jamiyyar NPC ne, wannan ya sa ya yi wa yan NEPU waɗanda suke yan Tijjaniyya ne galibinsu yarfe da cewa sun ce sallah biyar a wuni haramun ne kamar yadda misalin ya nuna. Duk da cewa a cikin bayaninsa bai fito ƙarara ya ce yan Tijjaniyya ba, amma ya yi amfani da kalmar Yan Wazifa wadda kalma ce ta ƙasƙanci da ake faɗa wa yan Tijjaniyya a wajen Lardin Kano[7]. Idan aka duba za a ga cewa wannan yarfe ne na addini domin kuwa ‘yan Tijjaniyya ba su haramta sallah ba, sai dai kawai za a ga hakan a matsayin wanin salo ne na rage wa aƙidar da ma mabiyanta magoya baya waɗanda suka kasance yan NEPU a wancan lokacin domin raunana siyasarta.

Irin wannan ya ci gaba da bayyana a cikin ayyukan adabin Hausa na zube, inda ‘yan siyasa suka riƙa yi wa abokan hamayyarsu yarfe don mabiya su ji cewa jam’iyyar da suke bi ba ta cancanci su bi ta ba. Galibi a siyasa irin waɗannan abubuwa da akan yi yarfe da su ƙaga su ake yi ba tare an ji ko an gani ba, abin nufi babu tabbas a faruwarsu. Alal misali, jamiyyar NPC ta ce jamiyyar NEPU jamiyyar kafirai ce, don ɗabiunsu irin na Kirista ne. Dubi abin da suka ce:

... tsakanin ‘yan NPC da na NEPU waɗanne ne ɗabiarsu irin ta Kirista ce? Har wasu daga cikinsu sukan ce ba sa bin addinin Musulunci? (Nadabo, 1960).

Duk da cewa tambaya ce aka yi, amma dai ta sigar yarfe ce aka yi ta domin dai amsar a ƙarshe za ta faɗa kan NEPU ne, domin kuwa yan NPC ne suke tambayar, kuma a jaridar gwamnati wadda ba a sanya bayanan ‘yan hamayya a cikinta, balle kuma abin da ya shafi yarfe. Idan aka duba a cikin wannan misali za a ga cewa an yi wa ‘yan hamayya ne yarfe cewa ɗabiunsu irin na Kiristoci ne, wanda an san dai cewa kaso mafi tsoka na alummar ƙasar Hausa Musulmi ne, kuma addinin Kirista yana takin saƙa ne da na Musulunci. Wannan ya sa yan jam’iyyar NPC suke ganin idan suka jefi NEPU da mummunar kalma irin wannan zai haifar masu da koma-baya. Haka kuma ba wai ɗabiunsu ne kaɗai irin nan Kirista ba, domin ana iya samun wani Musulmi mai yin wasu ɗabiu irin na Kirista, sai suka ƙara masu da cewa ai wasu ma daga cikin yan hamayya sukan ce su ba Musulmi ba ne, wato dai sun ma yi ridda, sun bar addinin Musulunci ke nan. Idan aka duba za a ga cewa wannan ba ƙaramar magana ba ce, domin kuwa jifar yan jamiyya da kafirci ba ƙaramin illata jamiyyar zai yi ba don al’ummar ƙasar Hausa akasarinta Musulmi ne.

Kamar yadda ‘yan NPC suka riƙa nuna cewa, jamiyyar NEPU jamiyya ce ta kafirai maƙiya addini, su ma NEPU sun yi amfani da wannan yarfen ta hanyar nuna cewa shiga jamiyyar NPC ko AG tamkar shiga kafirci ne, kamar dai yadda wannan misalin ya nuna:

...domin ni har abada ba zani shiga AG ko NPC ko wata jam’iyya ba illa NEPU wadda na dade kuma nake ciki a yanzu. Domin shiga NPC ko AG shiga uku ne, saboda haka Allah ya tsari Musulmi da shiga waɗannan jamiyyu... (Alasan, 1961).

Wannan misalin ya nuna cewa duk jam’iyyar da ba NEPU ba to shigar ta tamkar shiga uku ne. Idan aka ce mutum ya shiga uku kuwa ana nufin ya shiga masifa da bala’i ke nan. Babu kuwa wata masifar da ta kai kafirci, wannan ya sa a cikin misalin da yake sama aka ƙarasa da adduar neman tsarin duk wani Musulmi da shiga Jamiyyar NPC da AG, wato duk Musulmi bai kamata ya shiga jamiyyun ba, to wanda ya shiga fa? Ke nan, ba Musulmi ne shi ba.

A siyasance, idan aka lura cewa mutum yana da muhimmanci a cikin tafiyar wata jam’iyya to za a yi duk yadda za a yi domin karkato hankalinsa don ya bi wata jam’iyyar da ba ita ba, kuma kowace jam’iyya za ta so ya kasance a cikinta domin irin amfanin da zai jawo mata. Idan aka bi duk hanyar da za a bi domin raba shi da jam’iyyar da yake ba a yi nasara ba, sai kuma a nemi hanyar da za a ɓata shi don dai a yi irin abin nan da ake cewa a fasa kowa ya rasa, wato a bi shi da yarfe don a karya lagon siyasarsa. Irin wannan ne ya faru da Hassan a cikin littafin Tura Ta Kai Bango, inda abokan hamayya na jam’iyyar hamayya suka yi masa yarfe cewa ya shiga jam’iyyar kafirai. Dubi misalin da yake a ƙasa:

Eh to lafiya, amma ba lau ba. Hassan ne na ga yana neman ya shiga hanya ta Allah wadai, wadda sharrinta ba shi kaɗai zai shafa ba, har da danginsa da mutanen gari. A taƙaice dai yana neman kawo jamiyyar siyasa ce ta kahurai a nan garin.

‘Kahurai ɗan nan?

‘Kahurai Inna! Mu kuma muna ganin yadda mai gidan nan ya nuna masa hanyar makaranta bai kamata ba a ce karatun da ya yi ya zo ya tafi a banza ke nan. (Katsina, 1983 sh. 43-44)

A wannan misalin idan aka duba za a ga cewa, magoya bayan jam’iyyar Riƙau ne suka tafi suka samu mahaifiyar Hassan suka ce ai jamiyyar da su Hassan ɗin suke son kawowa garinsu jamiyya ce ta kafirai, kuma yana neman shiga. Wannan ya sa hankalin mahaifiyarsa ya tashi don ta ji zancen cewa ɗanta zai shiga mummunar hanyar da ba shi kaɗai sharrinta zai shafa ba har da danginsa da sauran mutanen gari. Domin Hassan ɗan gidan malamai ne, kuma ya samu tarbiyya irin ta malanta bai kamata a ji shi ya shiga irin wannan hanya ba. Idan aka duba za a ga cewa yarfe ne aka yi wa Hassan na addini, inda aka danganta jamiyyarsa da ta kafirai don kawai a ɓata shi a wajen mahaifiyarsa don ta hana shi bin jamiyyarsa ta Sauyi.

Kasancewar al’ummar Hausawa suna girmama shugabanninsu matuƙa, wannan bai sa sun girmama wani shaani na siyasa fiye da addini ba. Hakan ya sa abokan hamayyar siyasa, musamman na jamiyyar hamayya ta NEPU suka riƙa amfani da wannan wajen yi wa magoya bayan NPC yarfe ta hanyar nuna cewa ai sun fi girmama Sardauna da shugabanninsu na siyasa fiye da Ubangiji. Sun nuna cewa yadda suke tsoron Sardauna ba su jin tsoron Allah haka. Dubi dai abin da suke cewa a cikin wannan misalin:

Kai wawa, jahili, daƙiƙi, sususu, bari in gaya maka duk cikin Shariar Islama ba inda aka ce a nuna bambanci, ba inda aka ce a bada kuɗi don neman galaba, ba inda aka ce a girmama Sardauna a wulaƙanta gyartai. In kuwa akwai, ka gaya mani ayar da ta ce a yi kukan masallaci na ƙarya don jin daɗin Sardauna da jam’iyyarsa... (“Addinin Musulunci a Mazahabar Maliki”, 1960).

Idan aka dubi wannan misalin da yake sama za a fahimci cewa, mayar da martani ne aka yi ga kalaman abokin hamayya. A cikin wannan martanin an yi wa shugabannin jam’iyyar NPC yarfe ta hanyar ƙaga masu wasu batutuwa munana da kuma danganta su da su ba tare da ƙwaƙƙwarar hujja ba. A cikin misalin an nuna cewa ‘yan NPC suna aikata wasu abubuwa na addini ne domin ganin idon Sardauna ko don su faranta masa. Misali, ɗaukaka Sardauna saboda samun duniya da wulaƙanta talaka. Haka kuma an nuna cewa suna yin kuka a masallaci ne ba don tsoron Allah da ya cika zuciyarsu ba, sai don Sardauna da jam’iyyarsa su ji daɗi.

Idan aka dubi waɗannan bayanan da misalan da aka kawo za a fahimci cewa, ‘yan siyasa suna amfani da addini wajen yi wa abokan hamayya yarfe domin nuna wa al’umma cewa ba su cancanci a bi su ba.

4.2 Yarfe Na Ƙima/Halaye

Ƙima yana nufin hali na ban girma (CNHN, 2006 sh. 244). A siyasa ana la’akari da halaye da ɗabiun yan siyasa wanda dole ne a zahiri su kasance na ƙwarai domin magoya bayansu samu dalili da ƙwarin guiwar goya masu baya da kuma tallata su domin zaɓensu. Samun yan siyasa da wasu munanan ɗabiu ko wasu miyagun halaye ko tarihin wani abin kunya yakan sa a yi wa jamiyyarsu suka da mummunar shaida ta hanyar danganta su da wannan halin wanda zai iya raunana farin jinin jamiyyar ga magoya bayanta.

A cikin tarihin ginuwar siyasa an riƙa samun inda yan siyasa suka riƙa yi wa abokan hamayyarsu yarfe don nuna cewa ba su da halin kirki, ko kuma ba za a samu wani abin kirki da alumma za ta amfana ba in aka zaɓe su. Alal misali, a cikin jaridar Sodangi an ga inda aka yi wa jam’iyyar NEPU yarfe da cewa cuta take yaɗa wa magoya bayanta kamar haka:

...amma NEPU ta zama tunku da ƙararrawa mai jawowa dangi cuta koyaushe, ita ko kujera ɗaya ba za ta samu ba, sai ta koma Kudu wajen Enugu ko ta lasa a can. (“A.G. Na Maganin Mutuwa a Arewa”, 1959).

A nan ɗaya daga cikin magoya bayan NPC ne yake nuna cewa Jamiyyar NEPU babu alheri tattare da ita, inda ya kwatanta jamiyya da wani dabba mai suna tunku, wanda ya ce ba ya kawo wa ‘yan’uwansa alheri, kullum sai sharri. Don haka magoya bayan jam’iyyar ba za su samu wani alfanu daga gare ta ba sai dai cutuwa da za su yi. Ya nuna cewa ba za ta samu ko kujera ɗaya ba a Arewa idan aka yi zaɓe, sai dai ta koma Kudu ko za ta samu a can. Idan aka dubi yadda ya nuna cewa Jam’iyyar NEPU tana yaɗa wa yayanta cuta za a fahimci cewa lallai yarfe ne ya yi wa jam’iyyar ta hanyar amfani da wani hali mummuna na yaɗa cuta, don dusashe haskenta ga mogoya bayanta. Duk da cewa babu wanda aka ji cewa jam’iyyar ta sa masa wata cuta ko kuma ta jawo masa wani sharri, illa dai ya ƙaga zancen ne don ya sanya wa jamaa shakku a kanta.

A wasu lokuta akan nemi abin da za a shafa wa ɗan siyasa domin ya zubar masa da mutunci a idon a jamaa. Irin wannan ya bayyana a cikin littafin Dambarwar Siyasa kamar haka:

Ganin cewa haƙarsu ba ta cim ma ruwa ba... sai suka ƙudurci ko ta wane fanni sai sun dakushe farin jinin Farfesa tare da zubar masa da mutunci a idon jamaa. Ranar wata Lahadi tarkonsu ya kama kurciya, domin a ranar ne suka samu nasarar shigar da wata yarinya ya shekara goma sha biyu cikin gidan gonar Farfesan, a daidai lokacin da ya je duba wani aiki da aka gudanar. Bayan yan iskan sun yi mata rubdugun fyaɗe, sai suka lallaɓa suka sulale ba tare da wani ya gan su ba, tare da yada ta a bakin hanyar shiga da fita ta gidan gonar. Tun daga nesa Farfesan ya hango ta a yashe, cikin hanzari ya yunƙura da niyyar kai mata agaji, tabbacin da ya samu tana da sauran numfashi a jikinta ya sa ya yunƙura tare da cicciɓar ta da niyyar sa ta a mota ya kai ta asibiti, a daidai wannan lokacin yan sanda suna zuwa. Abin ka da ture, take suka zargi Farfesa da aikata wannan aika-aika. (Aminiya-Trust, 2021 sh. 41).

A cikin wannan misalin za a fahimci cewa yarfe ne aka shirya wa Farfesa a matsayinsa na mutum mai gaskiya da riƙon amana da kuma mutunci a cikin alumma wanda gaskiya da mutunci suka sanya jamaa suke ƙaunarsa, kuma suka tsayar da shi takarar gwamna a wata jamiyya, inda yan hamayya suka lashi takobin ko ta halin ƙaƙa sai sun tabbatar bai kai labari ba. Bayan tsallake dukkan makirce-makircen da aka riƙa ƙulla masa ne aka yi tunanin a shirya masa yarfen da zai taɓa mutuncinsa ya sa alumma su dawo daga rakiyarsa. Idan aka duba za a ga cewa, fyaɗe mummunan abu ne a cikin alumma, wannan ya sa aka danganta ɗan takarar da shi ta hanyar jefar da yarinyar a bakin gidan gonarsa, kuma aka jira sai da ya zo inda take aka ce ana zargin shi ya yi mata. Irin wannan yakan faru a cikin siyasa, inda za ka ji an zargi wani ɗan takara da yi wa wata cikin shege, ko wani makamanci haka, a yaɗa don a sanya masa baƙin jini a cikin alumma. Irin wannan ya fito a cikin jaridar Gaskiya Ta fi Kwabo wadda ta ruwaito wani yarfe da aka yi wa mataimakin shugaban ƙasa a jamhuriya ta biyu cewa ya yi wa wata mata cikin shege kamar haka:

Wata mujallar kasar nan mai suna ‘The Week’ ta taɓa buga wani labari, inda ta nuna cewa, wata matar aure ta shaida wa kotu cewa Alex Ekwueme ne ya yi mata ciki har Allah ya sa ta sami ƙaruwa... Amma shi Ekwueme ya ce abin da Adeline ta fada karya ne kuma bata suna ne. (“Ekwueme zai ba mu kunya”, 1999).

Alex Ekwueme shi ne mataimakin shugaban ƙasa a jamhuriya ta biya, kuma shi ne aka yi wa wannan yarfen a lokacin ana shirye-shiryen sake zaɓen su a karo na biyu a shekarar 1983. Wata matar aure ce mai suna Adeline ta yi iƙirarin cewa shi ne ya yi mata cikin shege har ta haifi yaya biyu, inda shi kuma ya ƙaryata. Ya nuna cewa abin da ta faɗa ba shi da tushe, hasali ma yarfe ne kawai aka masa domin a ɓata masa suna.

Sau da dama an sha zargin ‘yan NEPU da tsaurin ido ga mahukunta, kasancewar sun yi imani cewa mahukunta suna danne masu haƙƙoƙinsu. Wannan ya sa duk yadda suka juya ko suka furta wani abu yan NPC sukan ɗauke shi a matsayin tsageranci ne maimakon neman haƙƙi. A wata wasiƙa da aka samu a jaridar Sodangi an nuna yadda ‘yan jam’iyyar NPC suke jingina wa ‘yan NEPU rashin tarbiyya, inda har a cikin wasiƙar ya kira yan NEPU da cewa sun raina iyayensu. Dubi wannan misalin:

Ina so Edita ka ban ɗan fili don in bayyana rashin tarbiyyar NEPU. Abin mamaki, don wanda ya ce mahaifinsa ma ba kowa ba ne, ina ga wani? Kwanan baya ne can, ranar da suka yi lacca a Tudun Wada, sun taso suna komowa gida... suna ta ƙetare babban titi babu tunanin komai, sai ga wata mota ta ɓillo daga Airport. A nan suka dinga yi wa mai motar tsawa tun yana nesa, wai ya tsaya sai Firimiya ya wuce wato Malam Aminu Kano... bayan wucewar wannan direba sai wasu jakan yan NEPU suka bi shi da zagi. Wannan kuwa rashin tarbiyya a fili ke nan. (Lallai Babu Tarbiyya”, 1957).

 A cikin wannan misalin, an nuna yarfe ne inda aka bayyana cewa ‘yan NEPU ba su da tarbiyya. An sani cewa tarbiyya muhimmin abu ne a rayuwar Hausawa, kuma duk wanda ya rasa ta ana yi masa masa kallon mutumin banza maras ƙima da daraja a idon mutane. Haka kuma duk wanda ya rasa tarbiyya ana kallon sa a matsayin wanda ba ya ganin mutuncin kowa. Wannan ya sa a cikin misalin bayan marasa tarbiyya da aka kira su, sai kuma aka ce sun raina iyayensu, in kuwa hakan ta kasance to ke nan babu wani mai sauran mutunci a idonsu. Da wannan ‘yan NPC suka riƙa nuna wa alumma cewa magoya bayan NEPU tsageru ne marasa kunya da mutunci, don haka kada a bi su ko kuma a goya masu baya.

Daga cikin yarfe na ƙima wani lokaci akan danganta shi da wani makusancin ɗan jamiyya, wanda ake ganin zai iya shafar su har ya yi tasiri a cikin siyasarsu. Alal misali, wani ɗan siyasa wanda yake tsohon shugaban ƙaramar hukuma ne, a lokacin da yake neman kujerar ƙaramar hukuma an yi masa yarfe da cewa mahifinsa ɓarawon keke ne lokacin yana matashi, don haka ba za a zaɓi wanda yake da gadon sata ba, bayan kuwa hakan bai taɓa faruwa ba.[8] Irin wannan yarfen ya yi kama da wanda aka nuna a cikin littafin Tura Ta kai Bango kamar haka:

Ni ai da ma na san wannan yaron bai gaji arziƙi ba. Ubansa fa Na-Torami har ya mutu itace yake sarowa yana sayarwa. Kwana bakwai ma kafin ya mutu, sai da na sa shi ya kawo min kai uku har gida... Wani ya ce, Yo shi kansa Garban fa? Ubansa ba mahauci ba ne, karen lahira? (Katsina, 1983 sh. 21-22)

A cikin wannan misalin ana an yi wa ‘yan jam’iyyar Sauyi ne yarfe cewa talakawa ne ‘ya’yan matsiyata ba su da komai, duk da cewa suna da jama’a kuma sun zamar wa jam’iyyar Riƙau ƙadangaren bakin tulu. An nuna cewa ai Hassan mahaifinsa sanaar saro itace yake zuwa ya yi, ya zo gari ya sayar. Shi kuwa Garba an ce wai mahaifinsa mahauci ne karen lahira. Irin waɗannan abubuwan akan samu duk yarfe ne don jama’a su ɗauka cewa ai ba wata ƙima suke da ita a cikin alumma ba. Bayan kuwa babu ruwan shugabancin siyasa da arziƙinsu matuƙar dai sun cancanta, amma sai a yi amfani da ƙimarsu a yi masu yarfe da shi.

Yana daga cikin yarfe a jingina wa mutum wani mummunan aiki wanda bai aikata ba, ko kuma ya aikata sai a yi ƙoƙarin danganta mummunar aikinsa ga wasu don a nuna cewa duk haka suke ko kuma halinsu guda. Wannan ya yi daidai da wani misali da aka samu a cikin jaridar Sodangi wanda aka yanke wa wani ɓarawon agwagi shekara ɗaya a gidan yari. Dubi misalin:

Mai shari’a ya sami Gambo da laifin satar agwagi bayan an tambaye shi (Gambo) ya tabbatarwa da shari’a...sai mai shari’a ya yanke masa hukunci da shekara ɗaya. Har wa yau dai ashe a jikin rigar mutumin nan a gaba da baya duk tauraro ne a jikinta... To wannan abin kunya ko lallai ya kai a ce da mai shari’a an ji kunya ko ba ita a ce dai mai riga da tauraro ya sato agwagi... (Mohamed, 1960).

An tuhumi wani mai suna Gambo da satar agwagi, kuma an same shi da laifi. A matsayinsa na wanda aka samu da laifin sata, sai kawai aka yanke masa hukunci daidai da laifin da ya aikata. Bayan haka sai aka lura cewa, a jikin rigar ɓarawon akwai hoton tauraro wanda yake alama ce ta jamiyyar NEPU, sai aka nuna cewa ai ɓarawon nan ɗan NEPU ne, don haka sai ‘yan NPC suka ce ‘yan NEPU su faɗa wa mai sharia sun ji kunya. In kuwa ba su da kunya to su faɗi cewa an kama mai riga da alamar tauraro ya saci agwagi. Wannan shi ma zai iya kasancewa yarfe ne kawai irin na siyasa, domin kuwa da ganin tauraro a jikin rigar ɓarawo ba zai tabbatar cewa shi ɗan NEPU ne ba, don yana iya kasancewa ma rigar sato ta ya yi a wani wuri ya sanya ta ba tare da laakari da alamar da take jikinta ko na wace jam’iyya ce ba. Don an kama wani ɗan jamiyya da laifi ba shi yake nuna cewa duk ‘yan jam’iyyar ne suka yi laifin ba, hasali ma su laifin bai shafe su ba.

Wani misalin yarfe na halaye shi ne, yadda za ka ga wata jam’iyya tana faɗin miyagun maganganu a kan wata, inda za ta riƙa danganta ta da munanan halaye kamar su hassada da ƙarya da cin amana da dai sauransu. A wannan misalin da yake ƙasa an samu irin wannan:

...Ofishin ba da labarai na jam’iyyar NEPU ya Zargi Jam’iyyar NPC a kan sunan nan da ta yi na irin halin nan nata na hassada a kan maganar da awolowo ya yi cewa babu irin mulkin da ya fi dacewa da Nigeria illa na jamhuriya. (Bai Kyautu NPC Ta Soki Maganar Da Awolowo Yayi Ba, 1961).

A cikin wannan Misalin NEPU ta siffanta jam’iyyar NPC da ɗabiar hassada, inda ta nuna cewa da ma halin jamiyyar ne, domin a ganin NEPU shawarar da Awolowo ya bayar kan tsarin mulkin da ya kamata a bi shi ne daidai, kawai dai hassada ce ta sanya NPC sukar wannan batu. Idan aka duba za a ga cewa, hassada mummunan abu ne, kuma babu wanda zai so a danganta shi da shi, su kuwa a wurin ‘yan siyasa abu ne da suke amfani da shi don hana abokin hamayya motsi. Ya zama wani hali na ‘yan siyasa wanda da zarar an ga kuskuren ɗan siyasa aka nemi yi masa gyara sai a ce hassada ake yi masa. Wannan ya sa abokan hamayya da zarar sun yi magana sai a ce hassada ce suke yi wa jam’iyya ko ɗan siyasa ba da zuciya ɗaya suke yi ba.

Samun tababa a cikin nasabar mutum babban abu ne da kan sa mutum ya rasa ƙimarsa a idon mutane, wannan ya sa yan siyasa kan riƙa yin yarfe a duk lokacin da aka samu wata ƙofa wadda ta ba su damar hakan. A baya an yi ta yaɗa maganganu na yarfe da suke nuna cewa wani mataimakin shugaban ƙasar Nijeriya tsintacce ko kuma ba a san iyayensa ba. Yan hamayya sun yi ta amfani da wannan domin dasusashe haskensa. Irin wannan ya fito a ciki littafin Kowa Ya Bi inda aka nuna cewa gwamnan jihar bai san iyayensa ba. Ga misalin:

... to amma yadda za ku san batun ƙaryar shekarun da takardun da ma uwa uba rashin tabbacin iyayen gwamna don kowa ya san a gidan marayu ya girma. Sannan har yanzu gwamna ya kasa fitowa ƙarara ya ƙaryata zarge-zargen a idanun duniya. Sai kame-kame yake yi idan an tambaye shi. An ma taɓa tambayar mai ba shi shawara a kan batun shari’a sai ya ce wai a je gidan marayu za a ga tarihinsa a rubuce. To ya ‘yan’uwa mu da Allah (SWT) ya ba mu wannan babban gari mai tarihi ga manyan bayin Allah da waliyyai wai mun ba wa jikan Musailamatul-Kazzabi yana mulkarmu ku san ba zai yiwu ba. (Gwammaja, 2007 sh. 30)

Kamar yadda aka riƙa yada cewa wancan mataimakin shugaban ƙasar ba shi da iyaye, haka wannan misalin ya nuna cewa gwamnan bai san iyayen sa ba a gidan marayu ya tashi, kuma yan hamayya ne suka sanya shi gaba suna yi masa yarfe da wannan. Ba sabon abu ba ne a siyasar Nijeriya a zargi mutum da rashin takardun karatu, wanda a lokuta mafi yawa akan samu yarfe ne kawai domin idan aka bincika akan tarar sun yi har ma da shaida. Akan yi wa mutum yarfe da cewa ba shi da iyaye ne don a rage ƙimarsa a idon duniya musamman idan an rasa da me za a ɓata sunansa da shi.

Jam’iyyar NEPU ta kamanta jamiyyar NPC da jam’iyyar gumaka, inda ta yi kira da kada a zaɓe ta. Kalmar gunki dai an san wani abu ne da aka sassaƙa ko a ƙera ko a gina wanda yake da sifar mutum ko wani abu mai rai, wanda ba ya iya amfanar da kansa komai, kuma ba ya iya kare kansa daga cutarwa ko ya kare wani. Gunki ba ya magana ba ya motsi balle ya iya aiwatar da wani abu. Ga misalin kamar haka:

...ina jan hankalin mutane masu zaben NPC da su manta da ita domin jam’iyyar gumaka ce... (Gasakas,1961).

 A nan ‘yan jam’iyyar hamayya ne suke yi wa masu mulki yarfe da cewa jam’iyyarsu ta gumaka ce. A nan ɗayan uku ne, ko dai jam’iyyar ba ta iya tsinana wa al’umma komai kamar yadda gunki ba ya iya amfanar kansa balle waninsa, ko kuma manyan jam’iyyar NPC ne aka danganta su da gumaka domin ana yi masu biyayya tamkar yadda ake bauta wa gumaka, ko kuma su ‘yan jam’iyyar baki ɗaya daga shugabannin har mabiyan bautar gunki suke yi ba Allah suke bauta wa ba. Tun daga taken wasiƙar da jaridar ta buga za a fahimci cewa, mai wasiƙar yana nufin duk wanda ya bi jamiyyar NPC ya ɓata kamar dai yadda mai bautar gumaka yake ɓatacce kamar yadda Musulunci ya nuna.

Bayan faɗuwar jamiyyar PDP a babban zaɓen ƙasa a shekarar 2015, shugaba Muhammadu Buhari ne ya zama shugaban ƙasar Nijeriya a jamiyyar APC. Bayan rantsar da shi ya yi fama da rashin lafiya, inda ya tafi jinya ƙasar Birtaniya. Bayan dawowarsa don ci gaba da gudanar da harkar mulki, sai aka yi ta raɗe-raɗin cewa ai ainihin Buhari ya mutu, an sauya shi ne da wani mai kama da shi mai suna Jibril daga Sudan. Wannan zance ya yi tashe a cikin alumma kasancewar tun da ya dawo sai karsashinsa ya sauya ya ragu tamkar ba Buharin da aka zaɓa ba. Wannan ya sa wasu alummomi daga wasu ɓangarorin ƙasar suka riƙa kiransa da Jibril na Sudan. Shugaba Buharin ya nuna cewa shi ne da kansa ba a sauya shi da na bogi ba. Dubi wannan misalin:

A jiya Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa shi ba na bogi ba ne, ya bayyana hakan ne a ganawar da ya yi da al’ummar Najeriya mazauna kasar Poland a birnin Krakow a ziyarar da ya kai kasar domin halartar taron sauyin yanayi na Majalisar dinkin duniya. A yayin ganawar, wani dan Najeriya ne ya yi masa tambaya a kan cewa shin da gaske ne cewa shi ne Buhari da aka sani ko kuma wani ne ke kwaikwayon sa da ake kira Jibril daga Sudan. Shugaban ya yi Allah wadai masu yada wannan jita-jitar tare da cewa, ba su san ya kamata ba... (Adamu, 2018).

Shugaba Buhari ya fito ne ya tabbatar wa duniya cewa yarfen da ake yi masa cewa shi ba na bogi ne ba, shi ne dai gangariyarsa, ba wani ne yake kwaikwayonsa ba, kuma ya nuna rashin jin daɗinsa da wannan labarin da ake ta yaɗawa. Irin wannan yarfe ne na ƙima domin ana nuna cewa ba shi da nagarta kamar yadda aka san shi a farko kama mulkinsa a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa.

A jamhuriya ta huɗu an samu wata hanya ta yarfe wadda za a samu wani ɗan bangar siyasa a biya shi, sai a kitsa masa abin da ake so ya fito ya faɗa a wata kafar watsa labarai, kuma in ma wani abu ya biyo baya iyayen gidansa na siyasa su ne za su tsaya masa don fitar da shi. Irin waɗannan mutane da akan ɗauka haya a siyasance ana kiran su da sojojin baka. Aikin irin waɗannan sojojin bakan shi ne su fito su ƙalubalanci yan hamayya ta hanyar yarfe ko kuma su kare iyayen gidansu ta hanyar yi wa abokan hamayya yarfe. Irin wannan misalin na sojan baka ya bayyana a cikin littafin Da Bazarku inda aka bai wa wani sojan baka mai suna Auwalu wasu bayanai na yarfe a rubuce wanda aka yi wa Farfesa Auta. Ga misalin:

Wai yaro ƙarami kamar Auwalu wanda mahaifinsa ma almajirinka ne wai shi ne yau zai shiga gidan rediyo yana faɗar wai Farfesa ma da ake kiranka na je-ka-na-yi-ka ne… kuma wai kai ɗin nan Bafillatani ne, don haka idan aka yi kyakkyawan bincike wai kai ba ma mutumin ƙasar nan ba ne... Farfesa Auta ya yi murmushi ya ce, na saurari duk abin da yaron nan ya faɗa, amma kai da ji ka san rubuta masa aka yi ya haddace domin haka ka rabu da su ko ba-daɗe ko ba-jima gaskiya dai ɗaya ce tal kuma siyasa ba da gaba muke yin ta ba. (Surajo, 2006 sh. 95).

A cikin misalin an nuna cewa Auwalu ya shiga gidan rediyo ya yi wa Farfesa Auta yarfe ta hanyar taɓa ƙimarsa da cewa wai shi ɗin Farfesan bogi ne, kuma wai in ma aka tsananta bincike a tarar cewa shi ba ɗan ƙasa ba ne don kawai shi Bafulatani ne. Don a nuna cewa sojan baka ne shi ɗaukar hayansa aka yi, sai Farfesa Auta ya ce, ai ko da jin yadda yake magana za a fahimci duk bayanan da yake faɗa rubuta masa aka yi ya haddace su, kuma in aka yi haƙuri gaskiya za ta bayyana.

Idan aka dubi dukkan bayanan da aka kawo a wannan ɓangaren za a fahimci cewa, wani nauin yarfe ne da ake amfani da ƙima ko halaye wajen yin sa. Akan yi amfani da irin wannan yarfen ne don taɓa ƙimar wani ɗan siyasa ko jamiyyarsa ko kuma nuna wani mummunan hali tare da danganta shi da shi.

4.3 Yarfe Na Tafiyar Da Shugabanci

Tafiyar da shugabanci wani nauyi ne na al’umma wanda akan ɗora wa shugabanni domin gudanar da alamuran alumma yadda ya dace bisa tsarin doka. Tsarin shugabanci na siyasa ya tanadi wasu tsare-tsare na dokoki waɗanda ake amfani da su wajen warwarewa da kuma daidaita abubuwan da suka shafi gudanar da alamuran jamaa, ba tare da sanya son zuciya ko kuma bai wa wani ɓangare fifiko a kan wani ba. Bin ire-iren waɗannan dokoki sau da ƙafa galibi shi ne yake haifar da daidaito da adalci da kuma zaman lafiya. Sau da dama duk wanda ya bijirewa irin wannan tsarin doka akan kalle shi a matsayin mara gaskiya.

Duk da cewa bin waɗannan dokokin tsarin mulki shi ne daidai kuma abin da ya dace, amma wasu kan yi amfani da wannan don ganin wallen masu so su ɗabbaƙa su, har ma a wasu lokuta a zarge su da rashin yin abin da ya dace tun da ba su bar kowa ya yi yadda ya ga dama ba. A cikin siyasa akan yi wa ɗan siyasar da ya nuna cewa in ya hau mulki zai riƙe gaskiya da adalci ba tare da nuna sani ko sabo ba yarfe da cewa zai wulaƙanta manya ko zai ci mutuncin wasu. Alal misali, a lokacin da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yake gudanar da yaƙin neman zaɓe ya yi ta bayyana cewa zai hana cin hanci da rashawa da almundahana da dukiyar ƙasa, kuma duk wanda ya saci dukiyar ƙasa za a ƙwato, sai aka riƙa yi masa yarfe cewa yana da niyyar cin mutuncin manya ne. Wannan ya sa abokan hamayya suka dage don ganin bai kai labari ba. Irin wannan misali ne na yarfe na tafiyar da shugabanci, domin ana nuna cewa ga hanyar da zai bi ne wajen tafiyar da jama’a idan ya samu ya ɗare karagar mulki. Irin wannan misalin ya bayyana a cikin littafin Da Bazarku... Ga misali:

...a cikin wannan jaridar tabbas na karanta wata hira da aka yi da Farfesa Auta a kan gyaran kundin tsarin mulkin ƙasar nan …Ya dai so ya yi taɓargaza ne, tun da cewa ya yi shi fa har yanzu bai iya faiyace takamaiman aikin da sarakuna suke yi ma talakawansu. Saboda haka wai shi yana ganin ya kamata a faiyace wannan lamari a cikin sabon kundin da ake shirin tsarawa... Lauya ya ce, to a nemo mana ita daga nan zuwa jibi ko gata, mu kuwa za mu yi farfaganda mu birkita abin da ya faɗa a ciki, shafa masa kashin kaji a idanun talakawa da sarakuna. Kai kuwa tauraruwarka ta haskaka hasken da ba wanda ya isa ya dusashe ta. (Surajo, 2006 sh. 50-51).

A cikin wannan misalin an nuna yadda ɗan takarar shugabancin ƙasa Farfesa Auta ya yi hira da yan Jarida ne kan batun yi wa kundin tsarin mulki gyaran fuska, inda ya nuna cewa ya kamata a fayyace aikin sarakuna a cikin kundin tsarin mulki. Wannan ya sa aka shirya nemo jaridar a birkita zancen a shigar da abin da za a yi masa yarfe da shi don a shafa masa kashin kaji. Idan aka duba wannan yarfe ne na tafiyar da shugabanci, domin ya nuna idan ya samu dama zai yi gyara ga kundin tsarin mulki ta hanyar bayyana irin aikin da ya kamata sarakuna su riƙa yi wa talakawa, amma sai aka nuna za a shafa masa kashin kaji da wannan don alumma su dawo daga rakiyarsa, kuma tauraron abokin takararsa ya haskaka.

Wani lokaci idan ana so a yi wa ɗan siyasa yarfe sai a yi masa riga-malam-masallaci ta hanyar aikata wani abu don nuna cewa shi ya kasa, ko kuma a yi kira gare shi ko jamiyyarsa kan aikata wani abin da ya dace ba don ana son a aikata ɗin ba, sai don alumma su yarda cewa jamiyyar hamayya ba ta kan tsarin da ya dace ko ba ta bin doka da oda. Alal misali, jaridar Leadership Hausa ta buga wani labari wanda ta ce jam’iyyar hamayya ta PDP ta yi kira ga gwamnan jihar Kebbi da ya miƙa ragamar mulki a hannun mataimakinsa bayan bayyana cewa gwamnan yana shirin tafiya aikin Hajji. Ga misalin:

Mataimakin gwamnan jihar Kebbi, Sanata Umar Abubakar Tafida, ya nesanta kansa da sanarwar da jam’iyyar hamayya ta PDP ta fitar na neman a miƙa ragamar mulkin jihar biyo bayan gwamnan jihar na shirin tafiya aikin Hajji 2024.

Tun da farko dai jam’iyyar PDP ce ta fitar da sanarwa a ranar Laraba 5 ga watan Yuni a Birnin Kebbi inda ta buƙaci Gwamnan Jihar da ya miƙa ragamar mulki ga mataimakinsa tun da yana shirin tafiya Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin bana. (Birnin-Kebbi, 2023).

Idan aka duba za a ga cewa a doka idan gwamna zai yi tafiya irin wannan zai bar ragamar tafiyar da al’umma a hannun mataimakinsa ne, amma sai aka jiyo jam’iyyar hamayya tana yin kira ga gwamnan jihar da ya yi hakan. Wannan idan aka kula za a ga cewa yarfe ne na tafiyar da shugabanci, domin yana nuna cewa kamar gwamnan ba ya bin tsarin doka na tafiyar da mulkin jihar ne, kuma wannan zai iya yin tasiri ga al’umma wajen ganin wallen gwamnan. Hakan ne ya sa mataimakin gwamnan jihar ya fito ya mayar masu da martani cewa, ko da yaushe gwamnan jihar yana miƙa mulki ga mataimakin nasa ko da tafiyar yini ɗaya ya yi na barin ya jihar. Dubi abin da ya ce:

A cewar Sanata Umar, “Mun yi mamakin da’awar da ƴan hamayya ke yi na cewa a miƙa min ragamar mulki, domin ko da rana ɗaya Gwamna Nasir bai taɓa hanani yin aiki ba. (Birnin-Kebbi, 2023).

Idan aka duba za a fahimci cewa wannan yarfe ne aka yi wa jam’iyya mai mulki ta hanyar nuna cewa ba su iya tafiyar da shugabanci ba, ko kuma ba su bin doka a tsarin shugabancinsu.

A lokacin mulkin shugaba Buhari musamman daga 2015 zuwa 2019, an ɗauka cewa duk wanda ba ya tare da shi to kamar mutum ne da bai yi imani ba, domin ana ganin kauce wa tsarin tafiyar Buhariyya kamar kafirci ne a siyasance. Wannan yana daga cikin dalilan da suka sanya da yawan yan siyasa suka bi ɗariƙar Buhariyya ba don suna so ba, sai don su tsira da imaninsu a siyasance a fuskar mabiyansu. In ba haka ba za a bi su da yarfe cewa suna hamayya da Buhari ko tafarkinsa. Dubi wani misali mai kama da wannan a ƙasa:

Saboda mutane sun dauki Shugaba Muhammadu Buhari tamkar mahadi da saba masa tamkar saba wa Allah ne, sai wasu ’yan siyasa suke amfani da wannan dama wajen bata abokan siyasarsu don su lalata su. Duk wanda yake son lalata maka siyasa sai ya ce kana fada da Buhari. (Mustapha, 2015).

Akwai waɗanda aka gurgunta tafiyar siyasarsu sanadin yarfen da aka yi masu da cewa suna faɗa da Buhari, domin a lokacin mutane suna yi wa Shugaba Buharin kallon wani waliyyi a siyasance wanda saɓa masa tamkar saɓa wa Allah ne, shi ya sa idan ana so a ɓata siyasar wani sai a yi masa yarfe da cewa yana yi wa Buhari zagon ƙasa ko yana faɗa da shi. Irin wannan ya karya alkadarin yan siyasa da dama a zamaninsa.

Idan aka dubi waɗannan bayanai da suka shafi yarfen siyasa, za a fahimci inda aka fito a tarihin ginuwar siyasar jamiyyu a ƙasar Hausa, wanda wannan shi ne ya share hanya zuwa sauran jamhuriyoyin da aka samu bayan ta farko. Irin waɗannan sun ci gaba da faruwa a cikin siyasar ƙasar Hausa, kuma an ci gaba da amfani da su a matsayin hanyoyin samun magoya baya da kore wa abokan hamayyar siyasa mabiya.

5.0 Sakamakon Bincike

Daga bayanan da aka kawo a sama an fahimci cewa tarihin ginuwar siyasar jam’iyyu a ƙasar Hausa yana cike da wasu alamura waɗanda suka zama tamkar gishiri a cikin miyar siyasar jamiyyu. Daga cikin waɗannan abubuwa kuwa akwai yarfe, wanda za a iya cewa yin amfani da shi a zahiri da kuma tsarin zamantakewa ba za a ce daidai ba ne, domin a wasu lokuta yakan taɓa mutuncin wani kai tsaye cikin abin da babu tabbas ko ma ba gaskiya ba ne, sai dai a siyasance ya zama hanyar jawo raayin alumma ne domin samun goyon bayansu.

Binciken ya gano cewa, yarfe ba sabon abu ba ne a cikin siyasar jam’iyyu a Arewacin Nijeriya, wato suna da asali tun daga farkon kafuwar jam’iyyun siyasa, kuma har yau ana amfani da shi domin cimma manufofin siyasa.

Wani abu kuma da binciken ya gano shi ne, yarfe yana taimakawa wajen samun nasara ko akasin haka a cikin siyasa, domin yakan kore wa wanda aka yi wa yarfen mabiya wanda kan sa ya rasa mabiya kuma ya yi rashin nasara a zaɓe.

5.1 Naɗewa

Wannan takarda ta tattauna a kan yadda aka riƙa amfani da yarfe ne a cikin tarihin ginuwar siyasar ƙasar Hausa. Tun da farko a cikin gabatarwa an kawo taƙaitaccen tarihin faruwar siyasar jamiyyu a ƙasar Hausa. Daga nan sai aka kawo maanar yarfe da siyasa domin haska inda sunan takardar ya dosa. Daaga bisani sai aka tsunduma cikin nazarin yarfe a cikin tarihin ginuwar siyasar ƙasar Hausa, wanda aka riƙa kawo misalai daga rubutaccen zube na Hausa. A ƙarshe, binciken ya gano cewa siyasar jamiyyu a ƙasar Hausa cike take da yarfe wanda ya samo asali tun daga farkonta, kuma ba abin mamaki ba ne idan aka ga an ci gaba da amfani da shi a fagen siyasar jamiyyu a yau matsayin wata hanya ta samun magoya baya da kuma kore wa abokan hamayya mabiya wanda hakan yakan taimaka wajen samun nasara a zaɓe ko akasinsa.

Manazarta

Adamu, A. I. (2021). Dabarun Jawo Hankali A Wasu Waƙoƙin Siyasa A Jihohin Kano Da Katsina da Zamfara Daga 2007 Zuwa 2018. Kundin Digiri na Uku, Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.

Adamu, J. (2018, Disamba 3). Wasu Sun Jahilce Ni, Ni Ba Na Bogi Ba Ne- Buhari. An samo daga https://aminiya.ng/wasu-sun-jahilce-ni-ni-ba-na-bogi-ba-ne-buhari/

Adamu, M. (2019). Kawatanci Tsakanin Rubutattun Waƙoƙin Siyasar Jumhuriya Ta Uku Da Na Jumhuriya Ta Huɗu A Nijeriya. Kundin Digiri na Uku. Katsina: Jami’ar Umaru Musa Yar’adua.

Addinin Musulunci Mazahabar Maliki. (1960, Yuni 4). A cikin Jaridar Daily Comet, B. Sh.

 

Alasan, M. (1961, February 11). Alla Ya Tsari Musulmin Gaskiya Shiga NPC Da AG. A cikin Jaridar Daily Comet, B. Sh.

A.G. Na Maganin Mutuwa A Arewa. (1959, Disamba, 9). A cikin jaridar Sodangi, shafi na 5.

Aminiya-Trust (2020) Dambarwar Siyasa. Kaduna: Tast and Print Ventures.

Bai Kyautu NPC Ta Soki Maganar Da Awolowo Yayi Ba Ta Neman Nigeria Ta Zama Jamhuriya Dr Azikiwe Ya Zama Shugaban Farko. (1961, Fabrairu 13). A cikin Jaridar DailyComet, B. Sh.

Barry, P. (1995). Beginning Theory: An Introduction to Literary and CulturalTheory. London: Manchester University Press.

Birnin-Kebbi, U. F. (2023, Yuni 6). Mataimakin Gwamnan Kebbi Ya Nisanta Kansa Da Kalaman PDP. An samo daga https://hausa.leadership.ng/mataimakin-gwamnan-kebbi-ya-nisanta-kansa-da-kiran-pdp-na-a-mi%c6%99a-masa-ragamar-mulkin-jihar/

Birniwa, H. A. (1987). Conservatism and Dissent: A Comparative Study of NPC/NPN and NEPU/PRP Hausa Political Verse from Circa 1946 To 1983. Kundin digiri na Uku, Sashen Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Blackburn, S. (1994). Oxford Dictionary of Philosophy. New York: Oxford University Press.

CNHN (2006). Ƙamusun Hausa na Jamiar Bayero. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

Dudley, B. J. (1968). Parties and Politics in Northern Nigeria. London: Frank Cass and Co, Ltd.

Ɗan Alhaji, D. (2006). Jigo, Salo da Tsari a Fina-Finan Sarauniya da FKD. Kundin Digiri na Ɗaya. Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya da Afirka. Zariya: Jami’ar Ahmadu Bello.

Ɗan’illela, A. (2010). Rubutattun Waƙoƙin Siyasa: Nazari A Kan Jihohin Sakkwato Da Kebbi Da Kuma Zamfara. Kundin Digiri na Biyu. Sashen Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Ɗangulbi, A. R. (2003). Siyasa A Nijeriya: Gudunmawar Marubuta Waƙoƙin Siyasa Na Hausa ga Kafa Dimokuraɗiyya a Jumhuriya ta Huɗu Zango na Farko. Kundin Digiri na Biyu. Sashen Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Ekwueme Zai Ba Mu Kunya. (1999, Fabrairu 8). A cikin Jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo, Shafi na 9.

Farouk, U. B. (2006). Dangantakar Harshe da Addini: Nazari a kan Ilimin Walwalar Harshe. Kundin Digiri na Ɗaya. Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

Funtua A.I. (2003). Waƙoƙin Siyasa na Hausa a Jumhuriya ta Uku: Yanaye-Yanayensu da Sigoginsu. Kundin Digiri na Biyu, Sashen Harsunan Nijeriya. Kano: Jamiar Bayero.

Gasakas. U. (1961, February 13). Na Fita Daga NPC, Ina Fata Allah Ya Nunawa Saura Batattu Hanyar Fita. A cikin jaridar Daily Comet B.Sh.

Greenblatt, S.(1980) Renaisance Self-Fashioning: From More to Shakespeare: Chicago: University of Chicago Press.

Gwammaja, A. S. I. (2007) Kowa Ya Bi. Kano: ASIN Publishers.

Habib, M.A.R. (2008). Modern Literary Criticism and Theory: A History. UK: Blackwell Publishing.

Idris, Y. (2010). Waƙoƙin Addini na Siyasa: Nazarin Waƙoƙin Emmanuel Wise Mai Molo. Kundin Digiri na Biyu. Sashen Harsunan Nijeriya da Afirka. Zariya: Jami’ar Ahmadu Bello.

Idris, Y. (2016). Bijirewa A Waƙoƙin Siyasa: Bincike Kan Waƙoƙin 1903-2015. Kundin Digiri na Uku. Sashen Harsuna da Aladun Afirka. Zariya: Jami’ar Ahmadu Bello.

Katsina, S. I. (1983) Tura Ta Kai Bango. Zaria: Northern Nigerian Publishing Company LTD.

Lallai Babu Tarbiyya. (1957, Disamba 8). A cikin jaridar Sodangi, shafi na 8.

Lawal, N. (2018). Adabi da Tarihanci: Nazarin Wasu Wasanni na Rudolf Prietze. Kundin Digiri na Biyu. Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.

Malumfashi, I. A. (2013). Taƙaddama Da Gwagwarmayar Siyasar Arewacin Nijeriya Daga Mawaƙan Siyasa A Bisa Faifan Nazari. Maƙalar Da Aka Gabatar A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Cibiyar Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero Kano, daga 14-16 Ga Watan Janairu 2013.

Mashi, M. B. (1986). Waƙoƙin Baka na Siyasa, Dalilansu da Sababinsu ga Rayuwar Hausawa. Kundin Digiri na Biyu. Kano: Jami’ar Bayero.

Mohamed. Z. (1960, Janairu 20). Dan Tauraro Da Sata. A cikin jaridar Sodangi. Shafi na 8.

Muhammad, H. (2006). Tasirin Al’ada da Addini da Boko ga Suturar Matan Hausawan Zamani. Kundin Digiri na Ɗaya. Sashen Harsunan Nijeriya da Afirka. Zariya: Jami’ar Ahmadu Bello.

Mustapha, O. (2015, Satumba 4). Yarfen Siyasa Ce A Ce Muna Gaba Da Buhari – Ali Wakil. An samo daga https://aminiya.ng/yarfen-siyasa-ce-a-ce-muna-gaba-da-buhari-ali-wakili/

Nadabo, Y. (1960, Janairu 13). Fam Biyar Ta Yi Mana Kadan. A cikin jaridar Sodangi Shafi na 5.

Paden, J. N (1973). Religion and Political Culture in Kano. London: University of California press.

Sani, M. M. (2012). Tunanin Siyasa a Waƙoƙin Malam Hassan Nakutama. Kundin digiri na Biyu. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Surajo, B. I. (2006). Da Bazarku. Kano: Gidan Dabino Publishers.

Yahaya, I. Y. (1988). Hausa A Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa. Zaria: NNPC

Yusuf, J. (2018). Tarihin Jam’iyyar PDP A Bakin Marubuta Waƙa. Kundin Digiri na Biyu. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Hira

1.      Hira da Farfesa Atiku Ahmad Dunfawa, malami a sashen Koyar da Harsunan Nijeriya Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato a ofishinsa, ranar 10 ga watan Yuni, 2024, da misalin ƙarfe 2:15 na rana.

2.      Hira da Dr. Isa Abdullahi Muhammad, malami a sashen Koyar da Harsunan Nijeriya Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato a ofishinsa, ranar 15 ga watan Yuli, 2024, da misalin ƙarfe 4:33 na rana.

3.      Hira da Dr. Rabiu Bashir, ɗan siyasa, kuma malami a sashen Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe, Jamiar jihar Kaduna a ofishinsa, ranar Alhamis 16 ga watan Mayu, 2024, da misalin ƙarfe 2:10 na rana.

4.      Hira da Dr. Dano Balarabe Bunza, tsohon ɗan siyasa kuma malami a sashen Koyar da Harsunan Nijeriya Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato a ofishinsa, ranar 10 ga watan Yuni, 2024, da misalin ƙarfe 2:37 na rana.

5.      Hira da Uwargidan Alhaji Ibrahim Lazuru, tsohon shugaban ƙaramar hukumar Lere, jihar Kaduna, a gidansa da ke Sabon Kawo Kaduna. Ranar 22 ga Maris, 2021, da misalin ƙarfe 5:40 na yamma.



[1] A mu’amala ko zance na yau da kullum ana iya kiran kalmar da “ƙage” ko kuma “ƙaƙe”, ta fuskar siyasa kuma akan ce “ƙaƙen siyasa” a karin harshen ƙasar Sakkwato, kamar yadda aka samu daga tattaunawar da aka yi da Dr. Dano Balarabe Bunza na sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato. Ranar 10/6/2024 a ofishinsa.

[2] Hira da Dr. Isah Abdullahi Muhammad malami a sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato. Ranar 15/7/2024 a ofishinsa.

[3] Hira da Dr. Rabiu Bashir, ɗan siyasa kuma malami a ofishinsa da ke sashen Koyar da Harsunan Nijejiya da Kimiyyar Harshe, jami’ar Jihar Kaduna, ranar 16 ga watan Mayu, 2024.

[4] Dubi ɗure na 3.

[5] Hira da Farfesa Atiku Ahmad Dunfawa a ofishinsa da ke sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato. Ranar 15/7/24 da misalin ƙarfe 2:15.

[6] Dubi Paden, J. (1973:122) Religion And Political Culture in Kano.

Dubi Scott, P. H. G. (1952:2) A survey of Islam in Northern Nigeria.

[7] Dubi Paden, J. (1973:199) Religion And Political Culture in Kano.

[8] Hira da Uwargidan Alhaji Ibrahim Lazuru, tsohon shugaban ƙaramar hukumar Lere, jihar Kaduna a gidansa da ke Sabon Kawo Kaduna. Ranar 22 ga Maris, 2021.

Yarfe a Siyasa

Post a Comment

0 Comments