'Yar Boko 1
Aminu Sani Uba (Abu Isah Asshankidey)
Bismillahir-rahmanir-rahim
1. Yau nai shirina farmaki zan kai mata,
Domin halinta ciki akwai lalata.
2. Da rashin tunani positive da akwai ɓata,
In nai bayani za ku yo fuskanta.
3. Waƙar a yau ta zo wajen 'yar boko,
Daure karanta kin ji ko ƙanwata.
4. Wata naggani lamarinta ya rikitar dani,
Ta sa ni ƙaulani akan lamurranta
5. Ku tsaya ku saurara ku fuskanta da kyau,
Yayye abokai yan uwana mata,
6. Lamarinta ya sa na bace a cikin duhu,
Na kasa gane gaskiyar fuskarta.
7. In tai gabas tai yamma sai kuma tai Kudu,
Ba istiƙama ɗai cikin sha’aninta.
8. Wataran ta sanyo lulluɓi harma niƙab,
Wataran kamar akuya idan ka ganta,
9. Wataran ka ganta tsa-tsaf kamar wata kamila,
Wataran kamar dabba ɗabi'u nata.
10. In har kana magana ta yo fakare ta ji,
Kafin ka ƙare nan ta tashi ta barta.
11. Ta ce a bar mata su yo ilimi a yau,
An ba ta dama ga shi ta jefarta.
12. Daga yin karatu sai ta ɗau girma na kai,
Ita bata auren wanda ba shi da mota.
13. Kowa ya zo ita bata so nai tallaka,
Ko ko ta ce ita ba ta son mai mata.
14. Haka bata son ustazu me cewa bari,
Wai tafi son mai kau da kai sha'anita.
15. Nazarinta ai ita yanzu ta zama mai aji,
Ta yo karatu bata son a Kwaɓeta.
16. 'Ya 'ya biyu ko ko uku ni sun isan,
Ban son jidali bani so na wahalta.
17. In har kana so to mu yo aure haka,
Kuma za na je office ka yo fuskanta.
18. In kaƙi kowa sai ya kama gaba nasa_
Ni ban zama a gidanka domin bauta.
19. Haka bani girki ban zama a gida kawai,
Kuma babu zancen zaka ƙaro mata.
20. Haka za ta na ta fadi da zayyana sharruɗa,
Ita hakima ta manta tarbiyyarta.
21. Ai duk mazaje ba su sonki da gaskiya,
In har ki so shi a gobe zaki wahalta.
22. Sam ba su sauke na su nauyi kin ji ko,
Kar ma ki yarda da zantukansa ƙawata.
23. Daɗi na baki za suke maki zahiri,
Amma a ransu dako su ke na mugunta.
24. Kai sai ka ce ta san abinda yake duhu,
Wannan da ba masaninsa sai Allanta.
25. Wannan ta farko ce akwai wata na gaba
Zan bayyana maku dukka siffofinta.
26. Ni ne Abu Isah Aminu da baituka,
Ni nar rubuta gata nan ku karanta.
Daga alƙalamin
Aminu Sani Uba
(Abu Isah Asshankidey)
08162293321
aminusaniuba229@gmail.com
Daren Asabar
07/06/1447
28/11/2025

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.