Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Kayan Tsintuwa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malam. Idan mutum ya samu wani abu a hanya, shin ya Halatta ya ɗauka ya yi amfani da ita?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumusalam warahmatallahi wabarakatuh.

Tsintuwa ya rabu kashi uku:

1. Na farko: Tsintuwan abin da bashi da ƙima mai yawa, kamar tsintuwar Sanda, ko wani abin sha kaman lemu misali, ko Biredi misali. Ko irin tsintuwar naira ashirin. Dai duk abin da a aladance an san mai ita bazai damu da ita ba idan ta ɓace. To idan mutum ya tsinci irin wannan abu to zai yi amfani dashi babu laifi. Saboda Hadisin da Abu dawud ya rawaito

Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) ya yi rangwame game da tsintuwar sanda, ko igiya ko makamancin su. Wanda ya samu ya yi amfani dasu Abu Dawud: 1717. (Sheikh Nasirud-din Albani ya raunata Hadisin.).

2. Na biyu: abin da idan aka barshi bazai salwanta ba har mai shi ya zo ya same shi. Kaman raƙumi, ko kujera, da makamantansu. Shi wannan baya halatta a ɗauka. Domin an tambayi Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi game da tsintuwar Raƙumi sai ya ce: Ina ruwanka da ita? Tana tare da ruwan shanta da abin da zai tsare mata ƙafafun ta, tana zuwa wurin ruwa tasha, sannan tana cin bishiya har ta kai ga mai ita. Sahihul Bukhari: 2372

Wannan Hadisi yana nuna cewa ba’a tsintuwar raƙumi ko wata dabba da za ta iya komawa zuwa ga mai ita. Ya shiga ƙarƙashin wannan hadisi duk wani abu da idan aka barshi mai shi zai iya zuwa ya ɗauki kayansa ba tare da wani matsala ba kamar yadda mukayi bayani a baya.

3. Na Uku: Dukiya da za ta iya salwanta idan aka barta, kaman Rago ko akuya da makamantansu. Ko kuma sauran dukiyoyi kaman kuɗi na takarda, ko zinari ko azurfa. Idan abin da aka tsinta dabba ne kaman rago ko akuya to wanda ya same ta zai yi ɗayan abubuwa uku:

1. Ko ya yanka yaci naman. Amma idan mai ita ya dawo zai biya shi kuɗin dabbar.

2. Ko ya siyar da dabbar ya ajiye kuɗin duk randa aka samu mai ita sai ya bashi.

3. Ko ya ajiye ya cigaba da kiwon dabbar har randa Allah zai kawo mai shi. Idan ya ɗauki lokaci mai yawa yaga bazai iya cigaba da ajiya ba to sai ya yi amfani da ɗayan hanyoyi biyun farko.

Idan kuma dukiyar da ya samu kuɗi ne to zai ajiye. Yasan yawan kuɗin da yana yin kuɗin sannan ya yi shela wa mutane. Zai yi ta sanar wa har na shekara guda. Idan aka yi shekara guda ba’a samu mai shi ba to sai ya yi amfani da shi ko ya ba da sadaƙar sa. Amma idan mai dukiyar ya dawo yana neman ta to zai biya shi.

An rawaito daga Annabi Sallallahu alaihi Wasallam an tambaye shi game da tsintuwa sai ya umarci wanda ya yi tsintuwa da ya san siffar abin da ya tsinta idan kuɗine misali to yasan yawan kuɗin sannan yasan yana yin kuɗin ta yadda idan mai shi ya zo ya yi bayani da ya gamsu cewa nashi ne sai ya bashi. Sannan sai ya nemi mai ita har tsawon shekara guda. Idan bai samu mai ita ba to sai ya yi amfani da dukiyar ko ya ba da sadaƙa. Wannan Hadisi Bukhari ya rawaito shi a hadisi na 2372.

Ya kamata mu lura da abubuwa kaman haka:

1. Kafin mutum ya ɗauki tsintuwa dole sai ya aminta da kansa cewa zai nemi mai dukiyar, sannan kuma zai kiyaye dukiyar har a samu mai ita. Idan yasan bazai iya haka ba to haramun ne ya ɗauki wannan tsintuwa.

2. Dole yasan adadin kuɗin ko nau’in Dukiyar kamar yadda hadisin da muka kawo a sama ya yi bayani.

3. Dole idan ya ɗauki dukiyar ya yi shela ya nemi mai ita. Zai yi shelan ne kuma da yana yi da ya dace da zamanin sa. Misali ko ta gidan rediyo ko ta waya da makamantansu.

4. Idan mai dukiyar ya zo kuma ya siffanta dukiyar daidai to dole a miƙa masa dukiyar sa.

Idan ba’a samu mai dukiyar ba to wanda ya samu ta zama tashi. Ko ya yi sadaƙa da ita ladan ya kai ga mai dukiyar ko kuma ya yi amfani da ita. Amma idan mai dukiyar ya dawo zai mayar masa da dukiyar sa. Wannan shi ne taƙaitaccen hukuncin Tsintuwa.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments