Ticker

6/recent/ticker-posts

Nayi Mafarki Na Auri Wanda Ban Sanshi Ba

TAMBAYA (36)

Assalamu alaikum malam an tashi lafia Allah ya Kara lafia. Dan Allah mafarki ne nakeso in zaa iya fassaramu

Nice nayi mafarkin wani da abin dai ba yake sona da aure sai na amince mai a mafarki, sai naga kaman bikin auren nawa akeyi nasa kaya sabbi

Sai kwanakin baya kawaye na biyu suka kirani. Daya ta ce nayi aure. Dayan ta ce zatazo garin da nake saboda auren nawa a mafarki

AMSA

Aure a mafarki na nufin kulawar da Ubangiji SWT yake ga bayinSa. Haka kuma yana iya zama musiba ga rayuwar mutum. Idan mutum ya yi mafarkin ya auri mazinaciya to hakan na nufin shi mazinaci ne. Idan mutum ya aurar da mahaifiyarsa ga abokinsa a mafarki hakan na nufin zai siyar da gidansa. Idan mace mai ciki ta yi mafarkin ta yi aure hakan na nufin mace za ta haifa. Idan kuma ta yi mafarkin darenta na farko na lokacinda ta yi aure hakan na nufin namiji za ta haifa. Idan mace tanada da saitayi mafarki ta yi aure hakan na nufin za ta aurar da dan nata

A takaicedai mafarkin wadda takeda aure ko kuma mara aure na nufin alkhairi. Idan mara lafiya ta yi mafarkin auren mai ilimi hakan na nufin warakarta. Aure a mafarki yanada alaqa da kasuwanci. Idan mutum ya yi mafarkin ya auri mace kuma ba su dade ba ta mutu hakan na nufin zai samu wani aiki wanda zai sha tsananin wahala

Hakanan kuma idan mutum ya yi mafarkin ya yi aure, gashinan ana cashewa da kide-kide da masu rawa, hakan na nufin zai mutu a wannan wajen da ake sabon Allah din. Idan mutum ya yi mafarkin yana saduwa da matar da zai aura amman kuma bai ganeta ba kuma ba a sanardashi sunanta ba hakan na nufin mutuwarsa. To amman idan yaga matar da zai aura kuma ya ganeta ko kuma aka sanardashi sunanta a mafarkin hakan na nufin zai samu yalwar arziqi

SHARHI:

Aure shi ne darajar ko wacce ya mace baliga. Sannan kuma kamar yanda fassarar wannan mafarki ta nuna cewar idan mace ta yi mafarkin ta yi aure hakan na nufin kulawa da Ubangiji SWT yake ga bayinSa domin karesu daga fadawa zinace-zinace

Rahamar Allah SWT ce tasa ba iya qawarki guda daya ba har su biyu sukai miki mafarkin gashinan kinyi aure wanda shi ne burin kowacce kamilar mace mai lafiya

A shawarce sai ki dage da addu'a sannan ki sa iyayenki suma su tayaki da addu'ar Allah ya baki Miji Nagari mai addini (Sunnah Guy), wanda zai rabaki da rayuwar kadaici/zawarci

Muna roqo a wajen Allah, duk wadanda ba su da aure kuma suna da niyyar yi, ya Allah ka ba su abokan zama Nagari

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments