Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Saci Kudin Mijina Da Niyar Yin Sana'a Daga Baya In Mayar Masa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam. Na debi kuɗin mijina dubu saba'in (70,000) bai sani ba amma da niyar yin sana'a daga baya in mayar masa. To kuma kuɗin gaba ɗaya sun narke hankalina ya tashi dan Allah ya sani ban ɗauka da niyar sata ba, na ɗauka da niyar mayar masa duk lokacin dana samu jarina. Bayan kuɗin sun lalace na gaya masa cewar yana bina kuɗi dubu saba'in (70,000) amma bai yarda ba daga baya ya nemi sanin ya aka yi yake bina kuɗi haka in gaya mai, saboda na nemi ya yafe min shi kuma yaƙi yafewa, wai sai na faɗa masa yadda aka yi. Shi ne na rabu da maganar amma malam shin zan iya biyan sa a hankali ta hanyar sana'ar da nake yi in dinga bashi manja inna kin karbar kuɗin har na biya sa kuɗin sa ko kuwa?

NA SACI KUƊIN MIJINA DA NIYAR YIN SANA'A DAGA BAYA IN MAYAR MASA

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Gaskiya kin tafka babban kuskure tun farko, watakila ma shi ya sanya jarin naki ya rushe bai yi albarka ba. Domin hakika kin aikata cin amana adukiyar mijinki. Kuma tabbas idan har kika mutu baki tuba ba, Allah zai yi miki hisabi akansa.

Dukiyar mijinki amana ce wacce Allah ya danka ahannunki amatsayinki na matarsa. Kamar yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Ya ce: "MACE MAI KIWO CE ADAKIN MIJINTA KUMA za a TAMBAYETA GAME DA KIWON DA AKA BATA".

Kin ga bisa wannan dalilin, haramun ne ki ɗauki Kuɗinsa ba tare da saninsa ba, alhali yana kulawa da abincinki da abin shanki da suturarki bai tauye miki hakki ba. Idan kuma kika aikata haka, to kin fitar da kanki daga cikin sahun mafiya alkhairin mataye, kuma kin shigar da kanki cikin sahun maciya amana kamar yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Ya ce "Mafi alkhairi daga cikin mataye, ita ce matar da idan ka kalle ta za ta faranta maka zuciya, Kuma idan ka umurceta zatayi maka biyayya, kuma Idan baka nan za ta kiyaye maka amanar kanta da kuma dukiyarka". (Ibnu Jareer da Ibnu Abee Hatam ne suka ruwaitoshi).

Shawarar da zan baki anan ita ce: Kiji tsoron Allah ki fito ki gaya masa gaskiyar abin da kika aikata masa na laifi, sannan ki nemi yafewar laifin bisa alkawarin cewa zaki biyashi Kuɗinsa da kika ɗauka. Idan ya ce ya yafe miki to shikenan. Idan kuma bai yafe ba, to wajibi ne ki biyashi koda da kaɗan-kaɗan ne.

Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce. "NAGARTATTU DAGA CIKIN MATAYE, SUNE MASU YIN BIYAYYA GA MAZAJENSU, MASU KIYAYE AMANA BISA ABIN DA ALLAH ya yi UMURNIN KIYAYEWA (WATO MASU KIYAYE AMANAR JIKINSU DA KUMA DUKIYAR MAZAJENSU).

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Na Saci Kuɗin Mijina da Niyar In Mayar Masa – Mene Ne Hakkina?

‘Yar’uwa, dukiya ta mijinki amana ce gare ki. Daukar abin sa ba tare da izininsa ba, ko da niyyarki ta kasance “in yi sana’a in mayar masa daga baya,” haramun ne a shari’a. Manzon Allah ya ce:

«كُلُّكُمْ رَاعٍ وَكُلُّكُمْ مَسْؤُولٌ عَنْ رَعِيَّتِهِ، وَالإِمَاءُ رَاعِيَاتٌ وَكُلُّكُمْ مَسْؤُولٌ عَنْ أَمَانَةِ زَوْجِكُمْ»

Dukanku mai kiwo ne kuma dukanku za a tambaye ku game da abin da ke karkashin kulawarku. Mace mai aure ma za a tambaye ta game da amana da aka danka mata.”

(Riwaya: Ibn Jarir da Ibn Abi Hatim)

Abin da ya kamata ki yi:

1. Gaya gaskiya ga mijinki.

Bai kamata ki boye laifin ba. Bayyana abin da ya faru da niyyar neman gafara da biyayya.

2. Nemi yafiyar mijinki.

Idan ya yafe, alhamdulillah. Idan bai yafe ba, ki fahimci cewa shari’a ta wajabta ki mayar da kuɗinsa ko da a hankali ne.

3. Biya kuɗin a hankali idan bai yarda da ara ara ba.

Ko a hankali, matukar yana cikin ikon ki. Amma ki tabbata yana sane da tsarin.

4. Tuba da adalci a zuciya ga Allah.

Ka tuna ayar Allah:

«يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا أَوْفُوا بِالْعُقُودِ»

Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku cika alkawuran ku.”

(Surah Al-Ma’idah 5:1)

5. Gyara halaye da ladabi.

Nuna biyayya, gaskiya, da rikon amana a gaba domin Allah ya albarkaci zaman aure.

Taƙaitaccen Shawara:

Gaya gaskiya cikin ladabi.

Nemi yafiya.

Mayar da kuɗin mijin ko da a hankali.

Ki tuba ga Allah, kuma ki riƙa rikon amana gaba ɗaya. 

Post a Comment

0 Comments