𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Wai shin idan mutum ya mutu an binneshi bayan kwana uku jikinsa zai ruɓe ya farfashe, shin koda mutum ya mutu da imani hakan ya shafe shi ko ya shafi mai imani da marar imani?
RUƁEWAR JIKIN MAMACI A CIKIN
KABARI
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
jinkirtawa mamaci kwana uku
sannan ayi masa addu'a ko kwana goma ko talatin ko arba'in da ƙudurce cewa jikinsa yana wuce wasu
matakai nabala'ai atsakanin waɗannan kwanaki na zuwansa
Kabari aikine daya saɓawa sunnah, kuma abune
dabashi dawani dalili, kuma bidi'ane wacce mutane suka farar da ita bayan shuɗewar
Annabi Sallallahu alaihi Wasallam da sahabbai.
Abunda ya zo asunnah shi ne
yiwa mamaci addu'a dazarar anbinneshi akabarinsa, sannan yiwa sauran matattun
musulmai gaba ɗayansu acikin jimillah da kuma keɓancewa
batare da kayyaɗe wani lokaci ba ko zamani
ba, mamaci yana buƙatar
addu'ar 'yan'uwansa musulmi koda wanne lokaci, komai tsawon zamani.
Amma cewa jikin mutum zai ruɓe ya
farfashe bayan kwana uku wannan ya Saɓawa
sunnah bashi dawani dalili daya tabbatar dashi, kuma ba asamu wani daka cikin
malamai magabata daya faɗi hakanba, ko kuma wani daka
cikin jagoririn musulunci, haka babu wani malami daka cikin malamai likitoci ko
masu sharhi daya faɗi hakan azamanin sahabbai
ba.
Maganar wai cewa mutum yana fashewa
ko kansa yana fashewa akwana ukunsa nafarko a kabari, sannan tunbinsa yana
fashewa a kwanaki gomansa na kabari, sannan sauran jikinsa zaifashe gaba ɗaya
a kwana arba'in, magane ɓatacciya, zancene nakarya,
babu wani dalili akansa, watakila wannan zancen shi ne asalin aikata bidi'ar
arba'in bayan mamaci ya mutu, tayanda ake wasu ababe mutane sutaru dan
ta'aziyyah, alaramomi sukaranta alƙur'ani,
hakika malamai sun ce wannan aiki bidi'ane.
Antambayi shaik usaimin
rahimahullah makamanciyar irin wannan tambayar sai ya ce: Wannan yana daka
cikin bidi'ar da mutane suke aikatawa idan mamaci yacika kwana arba'in, sai ahaɗa
masa wani dantaro wanda mutane zasu haɗu
agidan mamacin, sukaranta alƙur'ani
su kawata waje, wanda ahakikaninsa yana cikin babin tunawa mutum bakin cikinsa,
wanda haramunne. Fatawa Nurun Alardarbi (9/2).
Haka zama har tsawon kwanaki
uku bayan mutuwar mamaci ana addu'a da karanta alƙur'ani
da karɓar
masu ta'aziyyah shi ma yana cikin Abunda mutane suka kirkira bidi'ane baida
asali acikin addini.
Babu wani daka cikin malaman
musulunci wanda ya yi fatawa da halascinsa, Balle yazamto sunnah ko aikin
sahabbai.
Amma matakan da jikin ɗan
Adam yake bi bayan ya mutu harya koma kasusuwa Al'amarine wanda Allah kaɗai
yasanshi, kowanne jiki yakan saɓa dana wani wajan matakan
dazaibi kafin yazama kashi, ba dukkan jikin mutane ne sukebin mataki iri ɗaya
ba, ko zamani ɗaya ba, babu buƙatar musan waɗannan
matakan, ko bincike akansu, jikin yana wuce waɗannan
matakaine da gaggawa koda jinkiri, uwar hanjinsa tana fashewa akwana goma ko
samada haka, ko kasa dahaka, shagaltuwa da wannan irin bincike da tunani da
makamantansa zaikai mutum zuwa ga abunda ya fi wannan ɗin
girma, abunda ya fi dacewa mutum yashagaltar dakansa akai shi ne ruhi
"rai" shi ne halin da ran mutum zai tsinci kansa na Ni'ima ko azaba.
Sauda dama akan samu jikin
matacce yakwashe shekaru masu yawa babu abunda yafita daka gareshi, amma kuma
yana cikin azaba makaskanciya. Ga fir'auna Allah ya ce:
فَالْيَوْمَ نُنَجِّيكَ بِبَدَنِكَ لِتَكُونَ لِمَنْ خَلْفَكَ آيَةً ۚ وَإِنَّ كَثِيرًا مِنَ النَّاسِ عَنْ آيَاتِنَا لَغَافِلُونَ
Ayau zamu tseratar da gangar
jikinka danya zamto izina ga wanda zasuzo bayanka. Kuma lalle ne mãsu yawa daga
mutãne, haƙĩƙa,
gafalallu ne ga ãyõyinMu. (Suratul Yunus Aya ta
92).
Haka sau dayawa akan samu
gawar mutum ta rututtuke ta farfashe amma kuma mai gawar yana cikin Waɗanda
Allah yakewa ni'ima akabarinsu, kuma saika samuma yana daka cikin shahidai.
Yazo acikin littafin Akbaaru
makkah (2/351) da Muhallah ta ibnu hazam (1/42)
Daka mansuur bin
Abdurrahman, daka mahaifiyarsa ta ce: lokacinda aka kashe ibnu zubair yardar
Allah takara tabbata agaresu, Ibnu Umar yardar Allah takara tabbata agaresu
yashiga masallaci, sai akace dashi, Asma'u bintu Abubakar yardar Allah takara
tabbata agaresu tana wani ɓangare na masallaci, saiyaje
wajenta ya yi mata ta'aziyyah, ya ce: wannan lalacewar jikin bakomai bane,
"rai" yana wajan Allah maɗaukakin
sarki kiji tsoran Allah ki yi haƙuri,
saita ce: mai zaihanani na yi haƙuri,
alhali anbaiwa wata karuwa daka cikin karuwan banu isra'ila kyautar kan yahya
bin zakariyyah, isnadin hadisin ingantaccene.
Sannan saiya sauka zuwa
gefen kaburburan da alamunsu sun goge, saiyai duba zuwa wani kabari daka
cikinsu, saiyaga kashin kansa yahaɗe da
juna, saiyayi umarci wani mutum yarufeshi, saiya ce: Lallai irin wannan
lalacewar jikin gawa ba abunda yake cutar da ita, kawai rayuka akewa uƙuba ko ni'ima har zuwa ranar alkiyama,
Tafsiru ibnu rajab (2/102)
Asali shi ne azaba ko ni'ima
akabari ana yiwa ran mutum ne, hakika ruhinsa yana kai ni'imar ko azabar zuwa
jikinsa.
Dan haka cewa mutum yakan ruɓe ko
uwar hanjinsa yana fashewa dayayi kwana uku akabari wannan bashi da asali, kuma
babu bambancin kafiri da mumini, domin kamar yanda muka baiyana azaba ko ni'ima
ana yiwa rai ne ba gangar jiki ba, sai rai ya isar zuwa ga jiki.
Allah yakan tseratar dajikin
kafiri baiyi komai ba tsawon lokaci akabari amma kuma yana cikin azaba mai
girma, haka yakan cakuɗa jikin mumini a kabari amma
kuma yana cikin Ni'ima harzuwa ranar alkiyama.
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa
Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.