Wata rana Munazara (Muqabala) ta kasance tsakanin babban Malamin Fiqhun nan Imamu Abu Hanifa da wasu Mulhidai masu kore samuwar Allah.
Ana cikin tattaunawa sai
Imamu Abu Hanifa ya ce musu:
"Me za ku ce game da
mutumin da ya ce muku ya ga wani babban jirgin ruwa, yana mak'are da kaya, an
cika shi da kayayyaki daban - daban, yana tafiya a cikin Teku, ga igiyar ruwa
mai tsanani tana ta juyawa, ga iska mai karfi tana ta kadawa, amma duk da haka
jirgin nan yana ta tafiya a seti babu abin da yake kada shi, amma kuma jirgin
ruwan ba shi da matuki da yake tuka shi.
To shin kuna ganin haka zai
yiwu?!".
Sai suka zabura suka ce:
A'a, wannan kam ba zai yiwu ba!
Ai wannan hankali ba zai
kama ba!
Kai, ko da a mafarki hakan
ba zai faru ba!
Sai Imam Abu Hanifa ya ce:
"Subhanallah!
Idan a hankalce ba zai yiwu
a samu jirgin ruwa ya yi tafiya a seti ba tare da matuki ba, to ta yaya zai
yiwu a hankalce a ce: wannar Duniya da muke gani, mai cike da halittu daban -
daban, ma'abociyar halaye da yanayi mabanbanta, ga ta da fadin kasa iya ganinka,
amma a ce: -wai- ta faru ne ba tare da Mahalicci ba, kuma babu mai gudanar da
ita a yanzu haka?!".
Ai nan da nan Mulhidai sai
suka rude, suka ce: lallai ka fadi gaskiya.
To jama'a, ku duba ku gani
fa!
Ashe rashin hankali ne mutum
ya zo ya rena wa mutane hankula ya ce: babu Allah, babu Mahalicci, babu mai
gudanar da Duniya da dukkan abin da ke cikinta na manyan halitu da mutane.
Duk mai hankali in ya fadi
haka to shi ma ya sani a cikin zuciyarsa cewa; karya kawai yake yi.
Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.