Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Salafiya Kuniya Ce?

A- SHIN SALAFIYYA ƘUNGIYA CE?

A kullum in an yi magana a kan Kungiyoyi an ce: 'Yan Kungiyar Salafiyyun, sai wasu su zabura suna cewa: Salafiyya ba KUNGIYA ba ce.

To matsalar ita ce: a gaskiya ba za ka fahimci abin da ake fada ba, matukar ba ka san ma'anonin wadannan kalmomi masu zuwa a Yaren Larabci ba.

الأمة، الملة، الجماعة، الفرقة، الحزب، الطائفة، الفئة، التنظيم

In ka ce: Salafiyya ba Kungiya ba ce, to zan yarda da kai, in Salafiyya a matsayin Manhaji kake nufi, wato Tafarkin Sunna da Sahabbai da Tabi'ai da mabiyansu suke kai a Aqida da bin Sunna da nisantar Bidi'a da yakarta, ba a matsayin mutane mabiya ba.

Amma in Salafiyyun a matsayin mabiya kake nufi to sai in ce maka: idan mutane suka tattaru suka ware daga sauran Ahlus Sunna suka hadu a kan wata manufa, suka kira kansu da 'Yan Salafiyya to kai tsaye sun zama Kungiya. Sawa'un sun yi tsari, sun nada Shugaba da Sakatare da Ma'aji, sun bude office sun tsara aiyuka ko kuma suna zaune ne a barwatse kawai, suna aiyukansu ba tare da wani tartibin tsarin aiki na musamman ba.

Saboda ai da ma mutane ne Kungiyar ba Manhajin da suke kai ba. Saboda da za a rasa ko mutum daya a kan wani Manhaji to da babu kungiya, Amma da zarar an samu mutum 3 zuwa sama a kan wata tafiya, ko Manhaji to sun zama Kungiya kai tsaye (automatically).

Don haka KUNGIYA ba suna ne na Manhaji ba, a'a, suna ne na mutanen da suka tattaru a kan Manhajin. Don haka kamar yadda muke da 'Yan Kungiyar Izala haka muna da 'Yan Kungiyar Salafiyyun, wato mutane ko jama'a da suka tattaru suka fahimci juna, suka ware daga sauran Ahlus Sunna suka ce mu ne: Salafiyyun. Wanda ba ya cikinmu kuwa ya zama Dan Bidi'a, ko Hizbiy, Harkiy, ds.

Wannan ya sa za ka yi mamaki, matasa sun wayi gari suna kutsawa cikin magana a kan KUNGIYOYI da yi musu hukunci amma ko hakikanin ma'anar kalmar ta KUNGIYA ba su sani ba.

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

B - MAFARKIN AN BIYO MUTUM DA SANDUNA

Mutum zai yi mafarki, ya ga wasu mutane sun biyo shi da sanduna suna dukansa kamar za su kashe shi, yana gudu yana ihu, yana neman wajen tsira. A cikin mafarkin yana jin ciwon dukan da ake yi masa, yana jin zafi, yana ihu da kururuwa.

Wanda yake kusa da shi a zaune yana kallonsa zai ga yadda yake ta birgima a kan shimfidarsa, tare da alamar yana halin shan wahala, da jin jiki, ya yi shargab da gumi.

In ya samu ya farka zai tashi a firgice cikin razana da tsoro, saboda wahala da ya sha, da abin tsoro da ya gani.

To wannan yana daga cikin dalilai na hankali da wak'i'i da suke tabbatar da azabar Kabari da kuma azabar Lahira. Amma abin mamaki Mulhidi da ya shiga wannan hali a cikin mafarki, sai ya wayi gari yana inkarin azabar kabari da tashi bayan mutuwa!

To kamar yadda ka ga haza a cikin mafarki a cikin baccinka, wannan yana tabbatar da cewa; kamar haka za ka sha duka a cikin kabarinka da kuma ranar Lahira a cikin wutar Jahannama.

Wannan yake nuna mana cewa; Mulhidai ba su hankali ba su da lura.

Ya Allah ka ba mu hankali, ka yi mana tsari da tabewa.

Dr. Aliyu Muh'd Sani

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments