Ticker

6/recent/ticker-posts

Me Ya Sa Ba A Samun 'Yan Ta'adda A Cikin 'Yan Darikun Sufaye?

Tambaya da Amsa daga Dr. Aliyu Muhd Sani

Ana samun ta'addanci ne daga masu Guluwwi da wuce iyaka wajen girmama Shari'a, a sakamakon wauta da jahilci.

To su kuma 'Yan Darikun Sufaye, girmama Shari'a yana da rauni matuka a wajensu, ko a ce: kwata - kwata babu shi a wajen galibinsu, tare da yawan jahilcin da yake cikinsu. Wannan ya sa ba za a samu Guluwwi a cikinsu ba, saboda Guluwwi ana samunsa ne a wajen mai girmama Shari'a.

Abin da ake samu a cikin Sufaye shi ne sakaci da jafa'i ga Shari'a, da kuma son rayuwar Duniya da jefar da Shari'a. Shi ya sa aiyukan alfasha ba wani abin tsoro ba ne a wajensu. Wannan ya sa a cikinsu aka fi samun Zindikai 'Yan Boko Aqida, masu fada da Shari'a, har ake samun Mulhidai 'Yan Ittihadi, wadanda aka fi sani da 'Yan Hakika ko 'Yan Faira masu zagin Allah, su allantar da kowa da komai.

Sa'annan kuma mai girmama Shari'a ne yake aikin hani ga mummunan aiki, amma su kuma Sufaye, a wajensu da zarar mutum ya ce: "La ilaha illal Lah", wato ya fadi Kalmar Shahada to shi kenan ya tsallake, ba za a yi masa inkari ba komai girman munin kalmomin da yake furtawa, ko munanan aiyukan da yake aikatawa, ko da kalmomi da aiyuka ne na kafurci. Saboda haka a wannan babi su "Murji'a" ne, wadanda suke ganin da zarar mutum ya fadi Kalmar Shahada to babu abin da zai cutar da imaninsa.

Saboda haka, wanda komai da yake ko'ina shi ne Allansa har da kare da alade, yaushe zai girmama Shari'ar Allah Mahalicci da ya daukaka a saman dukkan halittunsa?!

Kuma ta yaya wanda bai girmama Allah Maudakaki ba, zai girmama Shari'arsa, har ya yi guluwwi a cikin Shari'ar ya zama Dan Ta'adda?!

Saboda haka, 'Yan Ta'adda su ne jahilan masu girmama Shari'a, masu guluwwi da wuce gona da iri saboda jahilci, su kuma 'Yan Darikun Sufaye ba a sa su cikin masu girmama Shari'a, shi ya sa ba za a samu Guluwwi a kan Shari'a a wajensu ba, balle a samu 'Yan Ta'adda a cikinsu.

Don haka masu dangantuwa ga Musulunci sun kasu kashi uku game da Shari'a:

1- Masu guluwwi wajen girmama Shari'ar saboda jahilci, su ne 'Yan Ta'adda.

2- Masu Jafa'i ga Shari'ar, su ne Sufaye da Zindikai da Mulhidai.

3- Matsakaita, wadanda ba sa jafa'i ma Shari'ar, suna girmamata bisa ilimi da basira da hikima, ba tare da guluwwi ba.

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments