Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Kayan Tsintuwa Da Kayan Da Ba A San Mai Shi Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum warahmatullah, malam tambayata ita ce akwai wani bawan Allah da ya yi ajiyan kaya, ya tafi kimanin shekara huɗu kenan har waɗanda suka tafi tare sun dawo Amma shi bai dawo ba, kuma har na tambayi wanda suka kawo kayan tare sai ya nuna bai san shi ba, alhali shi ya yi masa jagora, to malam ya zan yi da wannan ajiya?

HUKUNCIN KAYAN TSINTUWA DA KAYAN DA BA A SAN MAI SHI BA:

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salamu, duk wani kaya da aka same shi ba a san mai mallakarsa ba ta hanyar tsintuwa ko ajiyewa, za a yi cigiyarsa ne na tsawon shekara ɗaya, a wararen taruwan jama'a, kamar a kasuwanni da ƙofofin masallatai, da makamantansu. Idan aka yi ta cigiya lokaci bayan lokaci har shekara ɗaya ta cika ba a sami mai kayan ba, to sai wanda ya tsinta ya yi sha'aninsa da wannan kaya, kamar yadda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya bayyana a lokacin da wani mutum ya tambaye shi game da kayan tsintuwa a hadisi mai lamba ta 1722 da Muslim ya ruwaito.

Amma duk lokacin da mai kayan ya dawo ya faɗi siffar kayansa, aka tabbatar nasa ne, to za a dawo masa da abinsa, domin kamar bashi ne, amma idan bai dawo ba kwata-kwata, to shi kenan ya zama kayan Allah, kamar yadda malamai suka yi bayani a littafan fiƙhu.

Sai dai su waɗannan kayan da kika ce sun yi shekara huɗu, to fa ba cigiyarsu kuka yi ba a tsawon wannan lokaci, to idan haka ne, daga yanzu za a fara cigiya a duk inda ake tunanin daga nan kayan suka zo na tsawon shekara ɗaya, idan mai shi ya zo ya ba da bayaninsu kamar yadda suke, sai aba shi kayansa, idan kuma ba a sami mai shi ba a tsawon shekara ɗayan nan da aka yi ta cigiya, to shi kenan sai ku yi amfani da kayan, kamar yadda hadisai a Sahihu Muslim suka tabbatar.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

HUKUNCIN TSINTUWA:

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Wani bawan Allah ne ya tsinci Naira 500 kuma bai ga wadanda zai yi wa cikiya ba Ya ya kamata ya yi da kuɗin tsintuwar?, suna ajiye yanzu haka kusan wata ɗaya.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To dan’uwa idan mutum ya yi tsintuwa ya wajaba a gare shi ya yi cigiya har tsawon shekara guda, idan bai samu mai ita ba, daga nan zai iya amfani da ita, amma in mai ita ya zo daga baya zai biya shi, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 5761.

Amma idan abin da ya tsinta dan kaɗan ne ba shi da yawa, to ya halatta ya yi amfani da shi ko da bai yi cigiya ba, saboda abin da aka rawaito cewa: Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya ga wani dabino akan hanya, sai ya ce: In ban da ına tsoron na sadaka ne da na ci. Muslim ya rawaito a lamba ta: 2527, sai hadişin ya nuna dan karamin abu ba ya buƙatar cigiya.

Malamai şun yi saɓani wajan iyakance tsintuwar da ba ta buƙatar cigiya, wasu sun ce za a koma al’adar mutane, duk abin da mutane şuke ganinsa ba a bakin komai ba, to in an tsince shi ba ya buƙatar cigiya, Ibnu Khudama ya hakaito daga Imamu Malik cewa: bai wajaba mutum ya yi cigiyar abin da bai Kai a yanke hannu saboda shi ba, wato ɗaya bisa huɗun dinari, haka nan sayyadina Aliyu ya tsinci dinare ɗaya ya yi amfani da ita ba tare da ya yi cigiya ba.

Abin da ya gabata yana nuna cewa: mutukar ba ka samu mai (500) ɗin da ka tsinta ba a kusa da Kai, ya halatta ka yi amfani da ita ba tare da cigiya ba, tun ba kuɗi ne mai yawa ba, kuma mai ita ba zai kwallafa rai Akanta ba.

Don neman karin bayani duba: Al-mugni 6/351.

Allah ne mafi Sani.

Jamilu Yusuf Zarewa

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

Post a Comment

0 Comments