𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Malam Wata mace ce take tambayar Malam Tana cewa Ku Maza kuna da matan aljanna "HURUL-IN" mu kuma me gare mu? Shin mu ma muna da maza a aljanna?
BABU BANBANCI TSAKANIN MAZA
DA MATA WAJEN AURE A ALJANNAH
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Babu banbanci tsakanin Maza
da Mata wajen Aure a Aljannah, Aure yana daga cikin abeben da rai take so,
Allah kuma ya yi ma yan Aljanna al'kawarin wannan.
وَفِيهَا مَا تَشْتَهِيهِ الْأَنفُسُ وَتَلَذُّ الْأَعْيُنُ ۖ وَأَنتُمْ فِيهَا خَالِدُونَ.
Acikin Aljanna akwai ababen
da rai take kwaɗayi, da ababen da idanuwa ke
jin dadinsu.
Don haka babu banbanci
tsakanin Namiji da Mace wajen jin daɗin
rayuwar Aure a Aljanna.
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Ta sake cewa: To amma fa AlƘur'ani ya siffanta "HURUL-IN"
da siffofi na Musanman, amma kuma bai siffanta Mijin da Mace za ta so ta Aure a
Aljanna ba??
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Maganarki gaskiya ce, sai
dai AlƘur'ani yana magana da Mutane ne da
gwargwadon abin da ransu take so kuma take kwaɗayi.
Kin ga Maza a Jumlace siffar Mace tana da muhimmanci a wurinsu, don haka sai
aka wasafta musu ta Aljannah, Ita kuwa Mace abin da ya fi muhimmanci a wurinta shi
ne halaye da dabi'un Namiji da kyakkyawar mu'amalarsa gare ta.
Maza koda sun girma a
Shekaru, to suna son Mace. Amma ita Mace idan girma ya zo Mata, Lamarin Maza
yana sauyawa a wurinta kwarai.
Don haka ma da Maza zasu
zauna hira, to zancen Mata da Aure yana daga cikin abin da yake sanya su nishaɗi,
wannan yasa AlƘur'ani ya yi musu
magana da abin da ransu tafi so da kwaɗayi.
A Lokacin da ita kuma Mace take da kunya da Ɓoye
soyayyarta/kaunarta a wurin jama'a, don haka itama sai AlƘur'ani ya girmama wannan dabi'a tata.
Da zamu lura da dillalan
Kawalai na zahiri dana kafofin sada zumunta masu yaɗa
badala zamu ga Mace ita suke nunawa Maza don neman kuɗi,
amma da wuya kaga ana tallata Namiji don Mata suzo su nemeshi!
To wannan shi ne tsarin
rayuwa a haka aka yi Mutane, cewa Namiji shi ne zai rika bin Mace ba Macece za
ta rika nemansa ba. Don haka AlƘur'ani
ya dace da Fitrar Mutane.
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Ta sake cewa: Ai kuwa ban taɓa
tunanin cewa AlƘur'ani
yana kula da dabi'u da halayen Mutane Mabanbanta ba.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Tare da haka dole ki bada
gaskiya cewa Allah maɗaukakin Sarki Adaline acikin
hukuncinsa, baya zalunci, Annabi Sallallahu alaihi Wasallam Ya ce:
...ما في الجنة أعزب
Babu Gwauro ko Gwauruwa a
Aljanna.
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Ta sake cewa: Haba dai, yau
na fara jin wannan Hadisin.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Kwantar da hankalinki, zaki
Auri wanda kike so a Aljanna kuma za a baki kyawun da ya fi na "HURUL
IYN" sannan za a baki Shekaru irin na Budurwa, saboda Aljanna gida ne da
Allah ya tanada don ya sakankama bayinsa na kwarai, daɗin
cikinta baya yankewa.
Mace tana da halaye
Mabanbanta a Aljanna kamar haka:
1. Ko dai ta kasance ta Mutu
gabanin ta yi Aure a duniya, ko ta mutu bayan ta rabu da Mijinta, ko kuma ta
samu Aljanna amma Mijinta yana Wuta (Wal Iyazu billah), to a nan Allah zai Aura
mata Miji daga Mazan duniya waɗanda suka shiga Aljanna.
2. Ko kuma Mijin Mace ya
mutu bata Auri wani ba bayansa, to a nan Allah zai daura mata Aure da shi Mijin
nata na duniya.
3. Ko kuma ya kasance bayan
Mijinta ya mutu ta sake wani Auren, to anan Allah zai bata zaɓi
acikin Mazajen, sai ta zaɓo wanda take so, ko kuma ya
zaɓo
wani na daban, ko kuma Allah ya zaɓa
mata mafi kyawun dabi'unsu. Abin nufi dai a kowane irin yana yin Mace ta Mutu,
tana da Miji a Aljanna.
Ni'imomin Aljanna basu
wasaftuwa, Annabi Sallallahu alaihi Wasallam Ya ce, Allah Ta'ala Ya ce:
َأَعْدَدْتُ لِعِبَادِي الصَّالِحِينَ مَا لَا عَيْنٌ رَأَتْ، وَلَا أُذُنٌ سَمِعَتْ وَلا خطرَ على قلبِ بشرٍ، اقرأوا إن شئتم فَلَا تَعْلَمُ نَفْسٌ مَا أُخْفِيَ لَهُمْ مِنْ قُرَّةِ أَعْيُنٍ جَزَاءً بِمَا كَانُوْا يَعْمَلُونَ.
Na tanadawa bayina na kwarai, abin da Idanuwa basu taɓa gani ba, kunne bai taɓa ji ba, bai kuma taɓa darsuwa a zuciyar wani Mutum ba, ku karanta idan kun so: Rai bata san abin da aka ɓoye mata na sanyin Idanuwa ba, sakamakone na abin da kuka kasance kuma aikatawa.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.