Ticker

6/recent/ticker-posts

Cigaba: Ma'anar Wasu Kalmomi II

A wannan cigaban na kalmomin da ake amfani da su wajen musanyar yawu tsakanin mabiya don mayar da martani ta hanyar cin zarafi, kunyatawa, baƙantawa, yarfe, ƙage, tozarci da kuma sharri; na tsinto kalmomi irin su: Matsolo, Tsinanne, Alade, Munafiki, Kare, Zararre, Motsattse, Matsiyaci, Fursuna, Murabus, Matsoraci, Mushiriki, Jahilai, Jaki, Dabba, Makaryaci, Ɗan Akuya, Ritaya Dole, Mai Shan Lemo, Tataccen Maƙaryaci da kuma 'Yan Tashin-tashina. Ganin yadda mabiyan suka zaƙe wajen yin amfani da kalmomin ya sa na tattaro su domin nazartarsu ta hanyar kawo ma'anarsu ɗaya-bayan-ɗaya. Ga su kamar haka:

MATSOLO - Mutum mai tsananin rowa.

TSINANNE - Wanda aka tsine wa, ko kuma mugu ko mummuna.

ALADE - Wata irin dabba ce gajeriya, ƙazama mai dogon baki da gajeriyar jela; an hana Musulmai cin namanta. Idan aka kira mutum da Alade ana nufin ƙazami mai dogon baki.

MUNAFIKI - Mutum mai ƙulle-ƙulle tsakanin mutane don ta da husuma.

KARE - Wani dabba ne mai ɗamammen ciki wanda girmansa ya yi na Akuya, yana da yawan faɗa da haushi, akan yi farauta ko zuwa kiwo ko tsaron gida da shi; haka kuma Musulmai ba sa cin namansa; yana da sunaye daban-daban dangane da launi kamar su: dirwa ko bule ko jatau ko bare ko duna. Idan aka siffanta wani da Kare, to ana nufin mai yawan faɗa ko haushi (mai ɗabi'a irin ta Kare).

ZARARRE - Mutumin da yake da taɓin hankali ko matsalar ƙwaƙwalwa.

MOTSATTSE - Taɓaɓɓe ko mahaukacin mutum.

MATSIYACI - Matalauci ko maras galihu. Ko mafaɗaci ko mai yawan rigima.

FURSUNA - Ɗan kurkuku ko ɗaurarre.

MURABUS - Sauka daga wani muƙami, musamman na saurata.

MATSORACI - Mai tsoro ko rago.

MUSHIRIKI - Mutum mai tsafi, bauta wa gumaka.

JAHILAI - Waɗanda ba su da ilimi. Ba su iya karatu da rubutu ba.

JAKI - Jaki wani dabba ne na gida mai dogayen kunnuwa da ƙaton kai mai kama da doki sai dai bai kai doki girma ba; babban aikinsa shi ne ɗaukar kaya. Idan aka kwatanta mutum da Jaki, to ana nufin daƙiƙi ko maras kan-gado.

DABBA - Dukkan haliitan mai ƙafa huɗu. Idan kuma aka ambaci mutum da Dabba, to ana nufin maras hankali.

MAƘARYACI - Mutum da ya saba da rashin faɗar gaskiya.

ƊAN AKUYA -  Mutum mai mummunan ɗabi'a ta bin mata (neman matan banza).

ƊAN - Makusanciyar dangantaka tsakanin wani abu da wani.

AKUYA - Ɗaya daga cikin dabbobin gida mai ƙaho da gajeriyar jela, ɗage a tanƙware, ana kuma cin namanta, ana shan nononta.

RITAYA DOLE - Tilastawa mutum barin aiki kafin cikar wa'adinsa.

RITAYA - Barin aiki bayan cikar wa'adi.

DOLE - Kalma mai bayyana tilasta yin abu ko barinsa.

MAI SHAN LEMO - Mutum mai shan kayan maye barkatai ba tare da izinin likita ba.

MAI - Kalmar tana da ma'anoni da dama. Amma a nan, tana nuna mallakar abu, misali: gari, doki da sauransu.

SHA - Sha ita ma kalmar ce mai harshen Damo. Amma a nan, tana nuni ne da haɗiyi ruwa ko wani abu mai ruwa-ruwa. Ko kuma zuƙar hayaƙin taba ta baki.

LEMO - Wata irin itaciya ce mai ƙaya wadda wani nau'inta yana da 'ya'ya masu tsami wani kuma masu zaƙi.

TATACCEN MAƘARYACI: Mutumin da ya ƙware wajen rashin faɗar gaskiya.

TATACCE - Ƙulli ko wani abu mai ruwa-ruwa wanda aka tace aka raba shi da dusa.

MAKARYACI - Mutum da ya saba da rashin faɗar gaskiya.

'YAN TASHIN-TASHINA - Masu dawo da maganar da ta wuce don wani ɓoyayyen manufa.

'YAN - 'Ya'yan wani/wasu (maza da mata).

TASHIN-TASHINA - Ambaton maganar da ta wuce.

Mohammed Bala Garba
22 October, 2025.

Cigaba: Ma'anar Wasu Kalmomi II

Post a Comment

0 Comments