👉 Ku danna SUBSCRIBE domin ƙarfafa mana guiwa.🙏
💡 A kullum muna maraba da shawarwarinku da gudummawarku.👍
https://www.youtube.com/@AmsoshiTV
Kalmomin aikatau ba a haɗa su da kowace kalma a duk inda suka fito a cikin
rubutun Hausa. Yayin bayanin ƙa’idojin rubutu, akan tattauna kalmomin aikatau a
ƙarƙashin ƙa’idojin daban-daban. Wannan ya danganta da siffar aikatau ɗin da
kuma wurin da ta fito a cikin jumla. Bugu da ƙari, ya danganta da kalmomin da
suka zo gabaninta ko waɗanda suka zo bayanta.
A wannan bidiyo, an tattauna “aikatau
mai gaɓa ɗaya.” Lamarin aikatau mai gaɓa ɗaya ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda
suka fi ba wa marubuta matsala. Sau da dama akan haɗe ta da wasu kalmomi. Hakan
na faruwa ne saboda dalilai da za su iya haɗawa da:
1. Furucin aikatau mai gaɓa ɗaya
kaɗan ne. Sau da dama a baki akan ji an furta su tare da wata kalma da take
gabansa ko bayansa.
2. A rubutu gaɓa ɗaya kawai yake
da shi. Kasancewarsa mai ɗauke da baƙi da wasali kawai, hakan yakan ruɗa wasu
marubuta, wanda yakan kai ga sun haɗe shi da wata kalma ta daban.
Ko ma yaya abin yake, rubuta aikatai mai gaɓa ɗaya tare da wata kalma kuskure ne. A cikin wannan bidiyo, an kawo misalan aikatau mai gaɓa ɗaya tare da tattauna misalansu a cikin jumloli.
Verb Forms in Hausa Orthography
In Hausa orthography, verbs are not joined to just any word wherever they appear. When explaining the rules of writing, verbs are discussed under different principles, depending on their form and the position they occupy within a sentence. They are also influenced by the words that come before or after them.
In this video, we discuss the case of the “single-syllable verb.” This type of verb is one of the most challenging for writers, as it is often mistakenly joined with other words. This usually happens for reasons such as:
1. Pronunciation: Single-syllable verbs are rare, and in spoken language they are often pronounced together with the word before or after them.
2. Form: In writing, these verbs consist of only one syllable (a consonant and a vowel). Because of their simplicity, many writers mistakenly attach them to the next word.
Regardless of the reason, joining a single-syllable verb with another word is incorrect.
In this video, we provide
examples of single-syllable verbs and show how they function within sentences.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.