Ticker

6/recent/ticker-posts

Ka'idojin Rubutun Hausa - Darasi Na Farko

👉 Ku danna SUBSCRIBE domin ƙarfafa mana guiwa.🙏

💡 A kullum muna maraba da shawarwarinku da gudummawarku.👍

https://www.youtube.com/@AmsoshiTV

Ba kara zube ake yin rubutu ba. Akwai dokoki da ƙa’idojin da harshe yake gindayawa waɗanda suka shafi rubutu a cikinsa. Rubutu zai yi tsafta ne kawai yayin da aka bi waɗannan ƙa’idojin rubutu. Idan aka saɓa musu kuwa, haƙiƙa rubutun zai kasance mai mishkila.

Wani ƙalubalen da ake samu shi ne, ba kowa ba ne ya damu da kiyaye ƙa’idojin rubutu. Da yawa daga cikin rubuce-rubucen Hausa da muke gani a kan allunan tallace-tallace da jikin motoci da kekenapep da sauransu, suna cike da kurakurai masu tarin yawa. Wani babban al’amari ma shi ne, har cikin ɗalibai da manazarta Hausa akan samu waɗanda suke rubutu bisa kuskure.

Tashar Amsoshi TV ta yi yunƙurin samar da laccoci game da ƙa’idojin rubutun Hausa. An tsara laccocin cikin salon ɗaukar ƙa’idojin ɗaya bayan ɗaya ana tattauna su. Wannan zai sa a samar da gajerun bidiyoyi ba masu gundura ba.

Da yardar Allah, duk wanda ya bi laccocin daga farko zuwa ƙarshe, zai ƙware a fannin rubutun Hausa.

Muna maraba da shawarwari ko gyara a kowane lokaci. Za ku iya turo mana tsokacinku ko tambayoyi ta sashen ‘comment’ a ƙasan kowane bidiyo.

 


Hausa Orthography: Writing with Rules, Not Guesswork

Writing in Hausa is not done randomly - it follows clear orthographic rules set by the language itself. A text is only clean and correct when these rules are respected. Once they are broken, the writing becomes messy and difficult to understand.

Unfortunately, many people do not pay attention to these rules. Countless Hausa writings on billboards, vehicles, tricycles, and even in academic work are riddled with errors. Shockingly, such mistakes are sometimes found even among students and researchers of Hausa.

To address this, Amsoshi TV has developed a series of short, engaging lectures on Hausa orthography. Each lecture focuses on one rule at a time, explaining it clearly and practically.

With consistency, anyone who follows the full series will develop real competence in Hausa writing.

We also welcome your feedback, corrections, and questions anytime - simply drop them in the comments section of any video.

Post a Comment

0 Comments