Ticker

6/recent/ticker-posts

Ina Mafita Ga Faduwar Darajar Marubuta Da Mutuwar Al'adar Karance-Karancen Littattafan Hausa?

👉 Ku danna SUBSCRIBE domin ƙarfafa mana guiwa.🙏

💡 A kullum muna maraba da shawarwarinku da gudummawarku.👍

https://www.youtube.com/@AmsoshiTV

A shekarun baya, marubuta mutane ne masu matuƙar daraja da ƙima a cikin al’ummar Hausawa. Sun kasance abin sha’awa da ake muradin ganin an zama kamarsu. A yanzu kuwa, al’amarin yana neman sauya zani. Al’umma ta daina kallon marubuta da wannan daraja da ƙima. Me ya haifar da hakan?

A ɓangare ɗaya kuwa, a da Hausawa sun kasance zaƙaƙure wajen karance-karance. Za a daɗe ana tuna tashen da littattafan Adabin Kasuwar Kano suka yi. Har sai da ta kai an samu shaguna da ɗaiɗaikun mutane da suke bayar da haya na littattafai. Mutanen da ba za su iya sayen littafi ba, za su je su karɓi haya domin su karanta su mayar wa mai haya abinsa. Haka kuma, an samar da manya da ƙananan ƙungiyoyin karance-karance. Duk wanda ya sayi littafi ya karanta, zai ba wa abokansa domin su ma su karanta, yayin da shi kuma zai karɓi waɗanda abokan nasa suka saya domin shi ma ya karanta.

A yau kuwa, wannan al’ada ta son karatu tana ƙoƙarin ɓacewa kwata-kwata. Hatta da dama daga cikin ɗaliban ilimi ba sa sayen littafi sai idan ya zama musu dole. Kallace-kallacen finafinai da hawa kafafen sada zumunta da sauran hanyoyin shagala da zamani ya zo da su sun maye gurbin karatu.

Wannan shagala tana ci gaba da haifar da illa ta fuskoki daban-daban. Darajar marubuta tana raguwa. Ƙwarin guiwarsu tana raguwa saboda babu wanda zai sayi rubutunsu. A ɓangaren ɗailbai kuwa, suna rasa kaifin tunani da hangen nesa da hikimomin da ake tatsa daga karance-karance da nazarce-nazarcen littattafai.

Ta wace hanya za a iya shawo kan wannan ƙalubale?

 


The Decline of Writers’ Prestige: The Death of the Hausa Reading Culture - What Is the Way Forward?

In the past, writers held great honor and respect among the Hausa people. They were admired, celebrated, and many aspired to be like them. Today, however, the situation is changing. Society no longer accords writers the same value and prestige. What caused this shift?

On the other hand, Hausas were once passionate readers. Many still recall the golden age of the Kano Market Literature boom. At that time, bookshops and even individuals offered books for rent. Those who could not afford to buy books would rent them, read, and return them. Reading clubs, both large and small, also flourished. Whenever someone bought a book, they would share it with friends to read, while in turn borrowing from others.

But today, this reading culture is nearly extinct. Even many students only buy books when it is absolutely compulsory. Movies, social media, and other forms of modern entertainment have largely replaced reading.

This shift has brought many consequences. Writers are losing their social value and confidence because fewer people buy their works. Students, meanwhile, are missing out on the sharpness of thought, vision, and wisdom that come from consistent reading and deep engagement with books.

So, the question remains: How can we revive this fading culture of reading?

Post a Comment

0 Comments