Ticker

6/recent/ticker-posts

Fadakarwa Game Da Rayuwarmu Mata Kan Zamantakewa Da Kishiya

Assalamu Alaikum

FADAKARWA GAME DA RAYUWARMU MATA, KAN ZAMANTAKEWA DA KISHIYA!

Daga

A’ishatu Muhammad Bazango

A yau dai na so in yi maganar da na daɗe ina son yi ban samu na yi ba sai yau, dangane da mata masu kishiya da suke zalunci da munafurci...

Dan Allah 'yan uwa mata zan yi magana game da yanda muke daukar rayuwar duniya da muhimmanci, da yanda muke daukar kishiya, mun manta da lahirarmu, ba ma tinanin mutuwarmu, ba ma tinanin hisabinmu.

Na sani cewa kishi halal ne, sannan akwai zafi sosai, amma dan Allah kar mu bari kishi ya raba mu da imaninmu, kar mu bari sheɗan ya yi tasiri a kanmu, a kan ɗan ƙaramin abu na rayuwar duniya, shin ba ma lissafi ne? ba ma tinani ne?

Na taso na ga gidan su Mahaifina mata biyu ne, kuma a iya zaman da na ga suna yi zama ne na fahimta Alhamdulillah, a kwana a tashi har Allah ya yi ma Uwar gidan rasuwa, bayan rayuwarta da wasu shekaru shi ma mijin ya rasu, ya rasu ba a dade sosai ba, ita ma ɗayar ta rasu. (Allah Ubangiji ya gafarta musu baki dayansu ya sa sun huta.)

Abin da ya sa na kawo wannan maganar, ya kamata mu yi nazari a kai sosai mu yi tinani, yanzu fa su shikenan sun yi rayuwarsu har sun wuce, to kamar haka ne misalin rayuwar duniya, da mai kishiya da wacce ba ta da ita, duk rayuwar da za a yi ba za a kai shekaru ɗari a duniya ba,  yanzu dan Allah wannan bai kai ya zama tashin hankali ba? bai kai mu shiga hankalinmu ba? rayuwar lahira ita ce din-din-din, abun da ka aikata a rayuwar duniya shi ne zai ba ka sakamakon lahira, mai kyau ne ko marar kyau.

Mu dinga tinawa, babu wanda yake tsara ma kansa rayuwa, da Amarya da Uwar gida tin kafin a haife su, kowa Allah ya rubuta cewa ga mijin da zai aure ta, babu wanda ya isa ya guje ma hukuncin Ubangiji. Ko da ke ba ki da kishiya, shin ba kya tinanin rayuwarki? ko kin san yanda rayuwa za ta kasance miki zuwa gaba? kin san miji zai iya mutuwa ya barki da yara? kin san za ki iya mutuwa ki bad yaranki? kin san miji zai iya mutuwa ki zo wani mai mata ya aure ki? ya kike gani idan a rayuwarki na baya kina da kishiya kin musguna mata? ba kya ganin ke ma hakan zai same ki?

To ke nan idan har mun san wannan mi zai saka mu biye ma sheɗan? Muna gaɓa da juna, muna zaluntar juna? Muna saka gaɓa a tsakanin yaranmu? Shin ba ma tinanin wannan da ba ma so, ita ma Allah ne ya halicce ta? baiwar Allah ne? idan muka zalunceta Allah ba ya barin wanda aka zalunta face Allah ya saka masa? ashe ba za mu ji tsoron Allah ba?

Ashe mutuwa bai ishe mu wa'azi ba? wata rana kamar yanzu ko wanne a cikinmu baya nan, duk mun mutu, sannan a lahira duk abin da muka aikata dole ne sai an mana hisabi a kai.

Ko da ace babu tashi bayan mutuwa, yanzu mutuwa ba za ta zama mana wa'azi ba? ga rayuwar kabari ba mu san mi za mu tarar ba? ga mutuwa koyaushe zuwa take babu sallama, shin mun shirya ma duka wadannan? ita mutuwa babu ruwanta da shekarunmu nawa ne, yaron da aka haifa yau ma ya tafi, wasu daga ciki ma suke mutuwa, manya sun mutu, ƙanana sun mutu, Malama sun mutu, 'yan siyasa sun mutu, shuwagabanni sun mutu, ke nan babu mai tsira a cikinmu? Dan Allah mu dena la'akari da shekarunmu, mu saka a ranmu ko yaushe za mu iya mutuwa, ko yau ko gobe ki anjima, ko mun shirya ko ba mu shirya ba. idan muka gina mai kyau kanmu za mu amfana, idan muka yi mummuna a kanmu ne.

Ba ma tinanin mu ma muna da yara ko ƙanne ko 'yan uwa? ba ma tinanin abin da muka yi ma wasu na zalunci mu ma za a iya yi ma namu?.

Allah ya kyauta ya sa mu dace baki dayanmu ameen ya rabbi.

Fadakarwa Game Da Rayuwarmu Mata Kan Zamantakewa Da Kishiya

Daga:

A’ishatu Muhammad Bazango
Ummu Amatulqahhar Kitchen
#Amsoshi Kitchen

Post a Comment

0 Comments