Ticker

6/recent/ticker-posts

Ta’aziyyarmu “ASUU” Ga Marigayi Janar Buhari

Daga

Aliyu Muhammad Bunza,
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Jihar Sakkwato
21/07/2025

Ta’aziyyarmu “ASUU” Ga Marigayi Janar Buhari

1. Bisimillahi Rabbana Mahaliccin gwaraje,

2. Na yi salati gun Muhammadu mayan mazaje

3. Da Sahabbai da mumin aje gemu da saje

4. Kai kak ƙaddaro hawanmu kujeru gadaje

5. Wada kay yo mu babbaƙu haka nan Kai jajaje

6. Wasu bukka suke shiga wasu manyan gidaje.

7. Ga wasu ba wurin zama dole jiki ƙuraje

8. Mai azumi talakka dole shi jure wa saje

9. Duk mai rai ya san akwai mutuwa ƙi garaje

10. In ta zo a dole miƙa wuya babu turje

11. Da talakkan gari da sarki duk ta yi murje

12. Bari murna karen ka ya yi wa zomo garaje

13. Wata rana da kai da shi sai dai iske gwarje

14. Komai ɗaukakar mutum za su yi gwarje gwarje

15. Kan mutuwar Tafawa mun shekara jaje-jaje

16. Kan Sardauna duk gari an ka rufe gidaje

17. Mutuwar Murtala ƙasa tas shiga jarje-jarje

18. Tas shiga ukku askrawa na darje-darje

19. Haka Shagari yaw wuce bayan juye-juye

20. Sani Abacha yaw wuce ba wani canje-canje

21. Yar’aduwanmu yaw wuce Gudulok shi ya gaje

22. Taw wurgo wurin Buhari Janar tay yi garje

23. Ba shakka ƙasarmu ta yi hasaran gwaraje

24. Ga kishin ƙasa da sa ƙarya murje-murje

25. Aka bar sace-sace goro ya koma a gwanje

26. Kun san shi Buhari sau biyu yah hau gadaje

27. Dole a aske yai kurakurai ga su darje.

28. San da yake da askarawa harsa ka hurje,

29. Ba su faɗi a ƙaryata, wa zai yin garaje?

30. In an ce Buhari, ka ce ƃera da maje.

31. Ya hana yaudarar ƙasa a yi manyan gidaje

32. Soja wuta da ba su Turanci sai na gwarje

33. Yaf faɗa cikin siyasa ta yi mai ƙuraje.

34. Aka kutsa Kurakurai anka yi gurje-gurje

35. Ai ƙwarar hatsi gidan kowa ta fi soje

36. Marigayi Buhari ya yi wa, ASUU garaje

37. An yi fito-fito da shi kan yaƙin mazaje

38. Haƙƙoƙinmu an ci su ana gwarjegwarje.

39. Ai mun ji shi ya tuba kan garje-garje

40. Mun yahe shi Rabbana kai shi saman gidaje

41. Can Firdausi mai hilon tubabbin mazaje

42. Gwannati ke ji namu haƙƙi duk mun ajijje.

43. Ɗan bashinmu kar a tura fayil a turje

44. Yada muka yafe yaudara sai a biya gudaje

45. Ni dai na wakilci ASU mayan mazaje

46. Sunana Aliyu Ɗanbunza garin gwaraje

47. Babban ɗalibin malaman farko masu saje

48. ASU ba ta yin kalami ya kasance lauje

49. Mun yahe Buhari ga mu zuwa ba garaje

50. Mu duka Rabbana ya kai mu ga manyan gadaje

51. Can Firdausi ba a tsufa ba a ƙuraje.

Aliyu Muhammad Bunza
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Jihar Sakkwato
21/07/2025
A Arkilla, Sakkwato
Ƙaramar Hukumar Wamakko.

Post a Comment

0 Comments