Ticker

6/recent/ticker-posts

Suturun Matan Hausawa Da Sauyesauyen Zamani a Yau

Cite this article as: Garba R. M. (2025). Suturun Matan Hausawa Da Sauyesauyen Zamani A Yau. Zamfara International Journal of Humanities, 3(2), 73-79. www.doi.org/10.36349/zamijoh.2025.v03i02.008

Suturun Matan Hausawa Da Sauyesauyen Zamani a Yau

SUTURUN MATAN HAUSAWA DA SAUYESAUYEN ZAMANI A YAU

Rukayya Muhammad Garba

Department of Hausa, Federal University of Education, Kano

Tsakure: A wannan bincike mai suna “Suturun Matan Hausawa da Sauye-Sauyen Zamani”, an aiwatar da shi ne a kan sauye-sauyen da baƙin al’adu suka yi tasiri a kan suturun matan Hausawa. Muhimman batutuwa da aka gina wannan bincike da su, sun haɗa da yin waiwaye a kan ireiren suturun matan Hausawa na gargajiya, inda aka yi bayaninsu daki-daki kuma filla-filla. A wannan aikin an kalli waɗansu abubuwan da suke haddasar da zamani aa cikin suturun matan Hausawa. Har ila yau a wannan bincike an fahimci matan Hausawa sun sami wasu nau’o’in suturun daban-daban sakamakon sauye-sauyen zamani ta fuskar suturun baƙin. Sannan sakamakon bincike ya sa aka lura da waɗansu hanyoyin da ake tunanin zamani ya yi tasiri a kan suturun da matan Hausawa suka rabauta da su masu tsari da kuma akasin haka. An zaɓi a ɗora wannan bincike bisa ra’i na mazhaban sauyin al’adu. Daga ƙarshe sannan an lura a yau mata musamman ‘yan mata suna sha’awart suturun zamani fiye da ta gargajiya, saboda jan hankalinsu sosai. Kai taye wannan bincike ya kuma lura sosai wasu daga cikin nau’o’in suturun gargajiya sun tasamma ɓata ko salwanta a wannan zamani ko lokaci mai ci.

1.0 Gabatarwa

Akan gudanar da bincike musamman a fage irin wannan na ilimi don ƙara fito da abu ƙarara domin al’umma ta ni’imantu da ƙara samun fa’idantuwa da abin da aka gano. Ashe kenan a iya cewa a duk lokacin da aka tashi gudanar da wani bincike na ilimi akan sami wata dama ta daɗa zazzaƙulo abubuwa masu ɗimbin amfani.

Wannan takarda ta yi ƙoƙarin fito da matsayin baƙin al’adun al’ummu waɗanda Hausawa suka haɗu da su, kuma suka yi dumu-dumu a cikin suturun matan Hausawa. Har ila yautakardar ta yi ƙoƙarin tantance al’adu da jirwayensu a cikin waɗannan sutura ta matan Hausawa da yadda ya haifar da sauye-sauyen zamuna mabambanta.

1.1  Ra’in Bincike

Mazhabar sauyin al’adu tana kokawa ne akan yadda tasirin baƙin al’adu na zamananci ko binanci yake mamaye al’adun gida na gargajiya, masu asali. Ta wani gefen kuwa an lura da yadda mutanen ƙauyuka suke tururuwa zuwa birane, su saje da al’adun wayewa da suka tarar, amma duk da haka, suna masu kiyaye al’adunsu na asali.

Ashe Kenan za a ga kamar mutanen karkara na shiga birane su bar al’adunsu, amma duk da haka al’adun nasu na asali na yin tasiri gare su. Dubi ma yadda yawancin shiryeshiryen talabijin da radiyo a birane suke wakiltar manufofin karkara.

Ita dai wannan hanya tana ƙoƙarin fayyace abubuwan da suke na rayuwar birni ne da kuma na rayuwar ƙauye, sannan suna ƙarfafa ba sai adabin karkara ba ne kawai yake zama adabin gargajiya (Gusau, 2016:51-52).

Ra’in sauyin al’adu, ra’i ne wanda wani masanin falsafar rayuwar al’umma, Georg Wilhelma Friendrich Hegel (1770-1831) ya assasa kuma almajiransa da wasu marubuta suka dinga ɗora shi a kan ayyukansu a bisa tunani na hangen nesa tare da hango wasu abubuwa waɗanda ka iya sanya al’umma ta dinga sassauyawa ko jujjuyawa a cikin gudanar da abubuwanta na rayuwa. Mukhtar, (2013-56) ya ɗauki ra’in Weinberg da Shabat (1956:58) inda yake da’awar cewa:

 “Sauye-sauye suna wakana ne cikin al’umma ba tare da an sani ba wato. Abubuwan da suke ɗauke da waɗannan sauye-sauyen su ma ba shela suke yi cewa suna ɗauke da wani sauyi da zai kawo wani sabon al’amari a cikin al’adun al’umma ba”. (Mukhtar 2013). Kamar yadda aka bayyana a baya, an ɗora wannan bincike ne a kan al’adun Hausawa da wasu sauye-sauye da suka bijiro a cikin yin su har suka sanya wasu suke ta jujjuyawa. Wannan ne ya haskaka aka janyo ko aka zaɓi ra’in sauyin al’ada aka kuma ɗora binciken a kansa. Wannan ra’in dangantakarsa da wannan bincike da aka ɗora aikin a kai shi ne kasancewar aikin za a gudanar da shi ne akan tasirin baƙin al’adun a kan suturun matan Hausawa jiya da yau. To wannan ra’in yana bigiran sauyin al’adu duba da tasirin baƙin al’adu na zamananci ko birananci. To duba da yadda suturun matan Hausawa na gargajiya tasirin baƙin al’adun ya tasar masju ta fuskokin nason kusa da nesa na suturun baƙin al’ummu.

2.0 Ma’anar Kalmar Al’ada

Ta samu fassara iri daban-daban a kuma fuskoki mabambanta. An kuma sami masana da manazarta al’adun Hausawa da dama sun tofa albarkacin bakinsu wajen bayar da ma’anar al’ada gwargwadon fahimtarsu misali. “Al’ada hanyar rayuwar al’umma” Ƙamusun Hausa, 2006:9). Haka shi ma Bichi, (2014) cewa ya yi: “Al’ada ta ƙunshi dukkan sassan rayuwa ta yau da kullum ta ɗan Adam, kamar su tsarin zamantakewa, da abinci da tufafinsa da waƙoƙinsa da sana’o’insa, da dai suturunsu”. Al’ada, na nufin dukkan rayuwar ɗan’adam tun daga haihuwar har zuwa ƙabarinsu. A ko’ina mutum ya samu kan sa, duk wata ɗabi’a da ya tashi da ita tun farkon rayuwa ya tarar a wurin da ya rayu ko yake rayuwa, to ita ce al’adarsa da za a iya yi masa hukunci a kai”. (Bunza, 2006).

2.1 Ma’anar Sutura

Sutura wato tufa ko arziƙi ko rufin asiri (Ƙamusun Hausa, 2006:404). Yayin da shi ma Almajir (2010:406) ya bayyana suturun Hausawa ta gargajiya da cewar: “Suturun Hausawa na gargajiya shi ne shaida ko alama wadda ake iya rarrabawa tsakanin wannan ƙabila da waccan. Saboda haka, shi tufafi kamar ma’auni ne da za a iya amfani da shin a duniya. Al’ummar Hausawa suna da suturunsu waɗanda suke riƙo da su ,masu tarin yawa, kuma sun sha bamban da waɗanda sauran ƙabilu suke sawa”.

3.0 Tasirin Baƙi na nesa a kan suturun matan Hausawa na Gargajiya

Akwai bayani da dama dangane da ma’anar tasiri daga bakunan masana da manazarta. “Tasiri na nufin muhimmanci ko dangantaka ko ƙarfi” . (Ƙamusun Hausa,. 2006). Zariya, (2000) ya ƙara bayyana ma’anar tasiri da cewa: “Tasiri yana nufin yadda al’adun wasu al’ummu suka samu karɓuwa a wurin wasu al’ummu na daban, wato shigar wata al’ada cikin al’adun wasu mutane ya kuma kasance wannan al’ada ta samu karɓuwa a wajen wannan al’umma”. Idan aka ce baƙin al’adu na nesa ana nufin al’adun al’ummomi waɗanda suka zo suka risƙi Hausawa daga uwa duniya mai nisa suka zo ƙasar Hausa da manufofi mabambanta. Waɗannan manufofi kuwa sun haɗa da yaɗa addinin musulunci ko na kirista da sha’ani na Fatauci ko kasuwanci ko saye da sayar da bayi da sauran mu’amalolin yau da kullum da ziyarce –ziyarcen buɗe ido da sada zumunci, sannan kuma uwa uba da mulkin mallaka. Waɗannan al’ummomi kuwa da za a bejiro da su a wannan aiki a yi musu kallo na ƙwaƙwaf tare da yin nazari ko kallon suturun da al’ummar Hausawa suka rabauta da su, su ne:

a. Larabawa

b. Turawa

c. Indiyawa

d. Sinawa

e. Azbinawa

Bayan cuɗanyar Hausawa da waɗannan baƙi ne, sai aka sami shigar wasu al’adu a rayuwar matan Hausawa musamman ta ɓangaren yanayin suturunsu. Ashe kenan wannan bincike zai mayar da hankali ne wajen zazzaƙulo wasu baƙin suturun matan Hausawa da suka cusa a cikin suturunsu na yau da kullum.

a)      Larabawa:

 “Wato mutumin da harshensa na haihuwa Larabci ne mutumin da mahaifinsa ɗaya daga cikin ƙasashen gabas ta tsakiya”. (Ƙamusun Hausa 2006:32). Ana hasashen addinin musulunci ya fara sako kai ne a ƙasar Hausa a wajen ƙarni na shida (6) zuwa na bakwai (7) bisa dalilan shigowar Larabawa da zimmar yaɗa addinin musulunci da kasuwanci, musamman cinikin bayi da fatu da makamai. Musulunci ya fara samun gindin zama a ƙasashen ne bayan Hausa da sarakuna suka fara shiga addinin. A lokacin sarkin Kano Nagufe Ɗariku (1194-124) wanda a wannan lokaci ne wasu Larabawa suka shigo da niyyar ciniki. Musulunci ya ƙara samun ɗaukaka a ƙarni na goma sha biyu (12). A Katsina kuwa a lokacin sarkin Katsina Muhammadu Korau (1320-1350). A Kano sarkin Kano Aliyu Yaji Ɗan Tsamiya (1349- 1385) wanda a lokacin sa ne malamai suka fara shigowa ƙasar Hausa gungu-gungu kamar irin su Abdurrahman Zaiti da Mandawari da Almaghili (Dokaji, 1978:19). Ana zaton ɗabi’un Larabawa masu kyau kamar kyautatawa wajen kasuwanci da kuma wadatattun tufafi (sutura), suka fara jan hankalin Hausawa. Sannu a hankali sai ya kasance Hausawa sun karɓe kusan duk halayya da ɗabi’un Larabawa waɗanda suka haɗa da harshensu da al’adunsu. Matan Hausawa sun sami sutura daga baƙi na nesa wato Larabawa waɗanda suka mayar da su suturunsu na yau da kullum. Daga cikin suturun daga baƙin sune sune kamar haka:

i. Doguwar riga

ii Hijabi

iii. Niƙafi

iɓ. Hular a-cuce

i. Doguwar Riga:

Wannan ma tana daga cikin sutura da matan Hausawa suka samu daga wajen larabawa, waɗanda idan mace ta sanya ta, za ta kama tun daga wuyanta har zuwa idon sawunta, taguwa ce wadda take rufe dukkan jikin mace. Musulunci musamman cewa ya yi duk mace al’aurace idan ban da fuskarta da tafukanta, wasu kuma sukan kira ta da jallabiyya.

Haka kuma akan sami wata doguwar rigar har ƙasa, amma tana da gajerun hannuwa da kuma kwalliya a jikinta sosai, tun daga wuyan rigar har wirjin rigar kwalliya tsalli-tsalli har a hannun rigar. A kan sami wata doguwar rigar mai kama da malin-malin (Babbar riga) ta maza.

ii. Hijabi:

Wannan ma yana ɗaya daga cikin sutura ko tufafin da al’ummar Hausawa suka ribatu da su, daga wajen Larabwa, kamar dai yadda suka ribatu da su Jallabiyyar ko doguwar rigar. Hijabi fallen ƙyalle ne wanda matan Hausa suke sanyawa tun daga kansu har zuwa sawayensu ko iyaka gwiwarsu yayin da akan bar sashin fuska a buɗe, musamman saboda umarni da addinin musulunci ya yi na mace ta rufe jikinta. Haka kuma yayin gudanar da sallah matan Hausawa sukan yi amfani da shi wajen wani sha’anin taro. Yanzu hijabi ya zama ruwan dare ya kuma kasu kasha-kashi, akwai na tsofaffi ko dattijai, akwai na manyan mata da na ‘yan mata har da yara na goye, su ma da irin nasu kuma hijabin yakan zo ne kala-kala ko iri-iri daidai kuɗinka daidai sha’aninka. Kasancewar kuɗi-kuɗi ne, akwai mai tsada da matsakaici da ɗan daidai. Hijabi ga matan Hausawa sutura ce mai kyau ga lulluɓe jiki dukkaninsa. Matan Hausawa sun rabauta da shi wanda ya taimaka wajen ture mayafi, saboda kashi saba’in da biyar (75%) na matan ƙasar Hausa sun rungume shi fiye da mayafi kasancewar yalwatar da matan suka samu a yayin gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum (Zahra’u, 2016).

iii. Niƙafi

Wato mayafi ne shi, wanda ake tsaga samansa kaɗan wanda ido yake fitowa daga sama, ana kuma yi masa jela guda biyu na ɗaurawa ko kuma ɗan maɓalli domin haɗa su wuri guda ya ɗaure goshin. (Zahra’u 2016 da Fatima, 2016). Wannan ma sutura ce mai kyau wadda matan Hausawa suka tasirantu da ita. A yau ko a wannan zamani sun aro suturar ne daga baƙin na nesa wato Larabawa..

b) Turawa

Bibiyar tarihin haɗuwar Hausawa da Turawa abu ne mai tsawo, wanda ya fara tun kafin shekara 1903, kamar yadda bincike ya nuna akwai ƙungiyoyin Turawa iri daban-daban da suka shigo Nijeriya lungun ƙasar Hausa wurin da aka fi sani da Nijeriya ta Arewa. Hausawa sun haɗu da Turawa sun zauna da Hausawa sun kuma bar musu wasu al’adunsu waɗanda suka shaƙu da su ta hanyar zama da maɗaukin kanwa. Dangane da ire-iren suturun Turawa da Hausawa suka ɗauka, wannan abu ne masu yawa a musamman idan muka yi la’akari da halin da suturun matan Hausawa suke ciki a yau. Matan Hausawa sun ɗauki tsarin suturun Turawa domin kuwa a yanzu suturun sun yi yawa a wajen matan Hausawa musamman ‘yan mata, inda suturun matan Hausawa na asali suke tasamma ɓacewa ko salwanta baki ɗaya. Suturun a yanzu idan aka lura sosai cikin suturun duk inda suke, sai a tarar ko dai tsarin suturunsu tsarin ɗinkin Turawa ne ko kuma yadin ainihin saƙar Turawa ne, ɗinkin Hausawa kuma matsattsu ɗamammu ne irin na turawa a yanzu. Don haka, duk irin ɗinke-ɗinke Turawa sun mamaye na Hausawa na gargajiya. Hausawa sun kuma samu canjin rayuwa ko canjin suturunsu ne kamar haka:

i. T. shat (Bulawus) mai dogon hannu

ii. T. shat (Bulawus) mai gajeren hannu

iii. T. shart (Amulas)

iɓ. Super getti (Shim ice mai ɗamara da siririn hannu)

ɓ. Pencil jeans na mata

ɓi. Torazo wandon dogo

ɓii. Siket

ɓiii. To my siket

iɗ. Kwat

ɗ. Jaket

ɗi. Ƙanana kaya/matsattsun kaya.

ɗii. Best (Shimi ‘yar ciki) da sauransu.

Bara’atu (2016).

i. T. Shat mai dogon hannu da gajeren hannu (Bulawus). Riga ce wadda matan Hausawa suke ta’amali da ita, yara da manyansu wadda suka sameta da cuɗanyar su da Turawa suna haɗa ta da siket ko dogon wando ko zani yayin zamansu na cikin gida ko unguwa ko makaranta, kasancewar T. Shirt ɗin daraja-daraja ce. (Fauziyya, 2016).

ii. T. shat Amulus Ita ma rigace ta zamani mai gajeren hannu galibinta damtsen wanda ya sanya ta a buɗe yake, rigace tamkar ta shan iska wadda aka tasirantu da ita daga wajen baƙi (Turawa).

iii. Supergetti (shimice ko misisi) Wato rig ace mai ɗamewa a jikin matan da suke sanya ta, tana da hannun shimi karamun hannu wanda turawa da ‘yan matansu har manyansu, suke sanyawa da yanayin zafi. Kamar yadda matan Hausawa suka ɗauka ana haɗata da siket ko dogon wando ko zani in za su fita makaranta ko unguwa sai su sanya ƙaton hijabi har idon sawu ko gwuiwarsu.

iɓ. Best (shimi) Riga ce wadda aka samu daga wajen Turawa wadda ake sanya ta kafin a saka kaya sai a ɗora mata kaya ko tufa ko sutura a kai domin kada a ga jikin wanda ya sanya ta, musamman idan shara-shara ne kayan. Shimi iri-iri ce akwai mai siririn hannu kuma iya ƙugune da doguwa har gwiwa. Amma ita ma hannun ta siriri ne ko mai ɗan faɗi kaɗan.

ɓ. Ƙananan kaya/matsattsun kaya

Haɗuwar Hausawa da Turawa ta ƙara haifar wa Hausawa musamman ‘yan matan zamani nan inda suke kwaikwayon wannan al’ada ta sanya ɗamammu ko ƙananan ko matsattsun suturun wanda za su kama su sosai da sosai ko ina a jikinsu inda suke haɗawa da dogon wando pencil ko siket ɗamamme wanda zai matse jikinsu ya fito da ilahirin surar jiki. Wanda wannan sutura ta zama ruwan dare daga cikin masu amfani da ita musamman ‘yan matan Hausawa. (Salaha, 2016).

4.0 Tasirin Baƙin Al’adu Akan Sutura Ta Yanayi

4.1 Suturar Amare

“Amare wato budurwa ko bazawara da ta yi sabon aure” (Ƙamusun Hausa 2006:15).

4.2 Sutura ta Amare

Wato waɗansu sutura ne waɗanda suka keɓanta da yanayi ko lokaci da ake buƙatarsu ko amfani da su, wanda za a gudanar da wani sha’ani ko shagali ko shagulgula. Amarya ko Amare su, suka keɓanta da waɗannan sutura waɗanda ake kiransu da (Special Wears). A cikin waɗannan suture na musamman na amare waɗanda suke amfani da su lokacin bikin aurensu. Sukan saka suturun baƙi na kusa da nesa kamar suturun Larabawa da Turawa da Indiyawa da Sinawa da Azbinawa. Haka kuma suna aro suturun kusa waɗanda suke makwabtaka dasu kamar Fulani da Bare-bari da Yarabawa da Nufawa da Inyamurai domin gudanar da waɗannan bukukuwa na aure. Daga cikin nason baƙin al’adu a cikin suturun matan Hausawa su ne kamar;

a. Rigar amarya shigar suturar Larabawa

b. Rigar amarya shigar suturar Turawa

c. Rigar amarya shigar suturar Indiyawa

d. Rigar amarya shigar suturar Sinawa

e. Rigar amarya shigar suturar Fulani (Fulfulde day)

f. Rigar amarya shigar suturar Bare-bari (Kanuri Day)

g. Rigar amarya shigar suturar Yarabawa (Yoruba day)

h. Rigar amarya shigar suturar Inyamurai (Igbo day).

4.2.1 Rigar Amarya ko Amare shigar Suturar Larabawa

Rigar amarya ko amare a ranar da suke yin shigar suturun Larabawa wanda ake kwaikwayon al’adun larabawa ta fuskar suturunsu. A ɓangaren suturun kuwa ita ta manya za ta sanya riga mai ɗan kauri daga ciki takan kasance mai ɗan tsawo tamkar shime iya gwuiwa mai siririn hannu kamar misisi sai kuma a sanya shigar hsara-shara daga sama “net” ko gown or (Special wears) wata amaryar tana sanya hula acuce ta gashi ta kuma ɗora net wani shara-sharan mayafi ne ɗan ƙanƙani idan tana so, wata kuma za ta gyara gashinta, ta yanko shi gaba, a ɗaure baya kamar a ƙasar Larabawa kuma rigar mai ƙyalliƙyalli ce da ɗaukan ido tana kuma da dogon hannu tsukakki daga kasa tsahonta yana da matuƙar yawa ga faɗi sosai tana jan ƙasa sosai. Yayin da ƙawayen amaryar su ma duk macen da ta halarci taron duk sukan sanya doguwar riga baƙa ta abaya ko jallabiya da ɗankwalinta a kansu. Haka kuma wani lokacin amarya kan sanya suturunta shigar Larabawa, doguwar rigace mai shara-shara galibi, ta kan saka wata a ciki mai ɗan duhu, sai kuma ta ɗaura wannan mai shara-sharan doguwa har ƙasa tana jan ƙasa mai kwaliya da ƙyal-ƙyali da daukan ido. Sai kuma ta ɗan yafa mayani shara-shara dogo, bayan ta sha hula larabawan asali ko wata takan ɗaura ɗan net, mai duwatsu ya yi bazar ga ɗaukan ido tamkar a cen ƙasar larabawa.

4.2.2 Rigar Amarya ko Amare Shigar Suturun Turawa

Wannan rigace wadda amarenmu suke sanyawa a jikinsu ranar bikinsu, inda suka tasirintu da suturun Turawa. Amare suke sanya riga shara-shara har tana jan ƙasa daga samanta kuma matsattsiya sosai daidai jikinta daidai girmanta. Haka kuma amarya tana iya sanya material mai kyau da ƙyalƙyali, amma ɗinkin Turai, a yi mata doguwar riga (Gown) ko a yi ƙananan kaya ƙaramar riga da siket ɗamammiye dogo a haɗa da goggoro kalal kayan. Wani nau’i na wannan riga kan faɗi a wuya ta yadda wani sashe na ƙirjin amarya, kamar wushiryar ƙirji kan bayyana a fili.

4.2.3 Rigar Amarya ko Amare Shigar Suturar Yarabawa (Yoruba day)

Yarabawa: su ne waɗanda harshen suna asali shi ne Yarbanci kuma suke da al’adu da ɗabi’u waɗanda su ne kawai aka fi sani da yin su. (Tukur, 1999:148). Cuɗanyansu da matan Hausawa wannan ya taimaka wajen saka matan Hausawa kwaikwayon suturun Yarabawa. Nau’in shigar suturun Amaren Hausawa da aka kwaikwaya daga wannan ƙabila a yau su ne kamar haka:

a. Leshi

b. Joje

c. Ashoke

d. Fele

e. Goggoro

4.2.4 Leshi

Leshi: yadudduka ne da yawanci matan Yarabawa ne suke saya su ɗinka a matsayin suturunsu na kwalliya. Yana kuma daga cikin jiga-jigan suturun su. Leshi yana da kaushi-kaushi da ‘yan huje-huje mai kama da saƙi ko kajanyi, wanda yarabawa suke amfani da shi don ɗaurawa musamman a lokacin gudanar da biki ko wani sha’ani. (Mu’azu 2013: 96-97). Leshi inda matan Hausawa da amare suke sakashi kamar riga mai dogon hannu ko gajeren hannu da zani ko siket don gudanar da shagulgulan bikin su na yau da gobe.

4.2.5 Joji

Joji wani irin zani ne na mata mai ratsin siliki a gefe da kuma tsakiya (Ƙamusun Hausa 2006:219). Shi Joji wani irin zani ne da aka saƙa shi da zare mai haske, sannan a yi masa ado da wani zare mai haske, sannan ana yi masa ado da wani zaren mai ruwan gwal ko silba mai kyalli ko tsarkiya launi-launi kamar rawaya ko kore-kore da sajuransu. Haka dai shi joji ana yi masa gamammiyar saƙa mai kauri kamar dai sauran saƙesaƙe na kayan adon Yarabawa. Joji shima ya shiga suturun matan Hausawa da Amare inda suke ɗinka rigar leshi buba mai dogon hannu su kuma ɗaura zanin su haɗa shi da goggoro a matsayin sutura. Haka kuma waɗansu suna yin sutura ne ta sanya rigar material ko leshi mai dogon ko gajeren hannu sai kuma su ɗaura zani akan rigar har ƙasa a kuma ɗaura wani zani iya guiwarta sai kuma a ɗaura goggoro mai launi daidai da kayan.

4.2.6 Ashoke

Ashoke: yadi ne da yake fitowa falle-falle ajikinsa. Mata sukan ɗinka shi a matsayin zane. Yawanci tsawon zannuwa mata a al’adar Yarabawa yakan fara ne daga iyakar cibiya zuwa ƙwaurin mata (Dayo 2002-92). Ashoke matan

Hausawa da Amare suke ta’amali da shi a matsayin suturun su musamman lokacin gudanar da wani sha’anin biki. Haka amare suna saka shi a matsayin sutura a yayin gudanar da shagulgulan bukukuwansu.

4.2.7 Goggoro

Goggoro: Yadi ne mai kyalli da kaushi falle ɗaya da yarabawa suke ɗaurawa alokacin wani sha’ani na biki ko taro na musamman. Akan kira wannan yadi da suna “Damask”. To wannan abun ɗaurawa (goggoro) shi ne ya yi tasiri a kan matan Hausawa har ya zame masu wani ɓangare na tufafinsu ko suturun su a yayin gudanar da bukukuwansu. Amare da iyayen Amare da iyayen Ango da ƙawayen Amarya da ‘yan’uwa da abokan arziƙi duk sukan saka. Goggoro ba sutura ba ce ta Bahaushe, amma ya aro ta ne daga yanayin tufafin Yarabawa saboda tsananin son abin da zai yi ya burge. Saboda shi goggoro yana ƙara fito da tsarin kwalliya.

5.0 Wasu dalilai da suka haifar da Tasirin zamani akan Suturun Matan Hausawa

Hanyoyin da suka taimaka wajen Sanya zamani ya yi tasiri a kan suturun matan Hausawa a yau sune. a. Wanzuwar ilimin boko/samuwar ilimin boko

b. Auratayya

c. Tafiye-tafiyen yawon buɗe ido

d. Kasuwanci/cinikayya

e. Bukukuwa

f. Yawan shaƙatawa

g. Shafin sada zumunci (Facebook, Twitter, Whatsapp da sauransu).

h. Jaridu da Mujallu da sauransu.

5.1 Wanzuwar Ilimin Boko/Samuwar Ilimin Boko

Zuwan ilimin boko ƙasar Hausa ya yi tasiri akan rayuwar Bahaushe ta yau da kullum. Ilimin boko ya zo da wasu sababbin al’amura game da rayuwafr matan Hausawa da ma duniya, inda suturun matan Hausawa suka tasamma ɓata ko salwanta ko gurɓata, (Mu’azu, 2013:297). Kasancewar canji sauyin lamarin rayuwa daya shafi matan duniya kazalika matan Hausawa abin suma ya shafe su. Sun gano abubuwa waɗanda ada can sun shige duhu a ɓangaren suturun matan Hausawa, saboda haka fasaharsu da wayon su da gogewar su sai ya ƙara ƙaruwa a fannin suturun su na yau da kullum. Kasancewar zuwan ilimin boko ya ƙara buɗewar ido, kai na ƙara wayewa inda ya jawo musu barin suturun matan Hausawa na asin da asin a ka kuma maye gurbinsu da sababbi ko baƙin suturun na nesa da kusa. Matan Hausawa sun rungume su hannu bibbiyu. Turawan sun kawo suturun irin nasu, sun kuma sauƙaƙe hanyoyin sayen kayan, ta hanyar rayuwarsu a kasuwa sun ƙawata shi da ado mai ɗaukan hankali a ido, sai dai kash inda gizo yake saƙa shine cewa kayan ƙyalƙyal banza domin kuwa ɗagale suke don haka suna bayyana wasu sass ana tsiraici ‘ya mace. Duba ga suturun matan Hausawa a yau, musamman ‘yan matan wannan zamani da wasu matan Hausawa zai tabbatar da hakan.

5.2 Auratayya

A gargajiyance, aure yana nufin wata yarjejeniya ce ta zaman tare tsakanin miji da mace bisa wani tsari na addini ko al’ada. (Zahra’u, 2013:271).

Auratayya da akan samu ya taimaka wajen kawo canjin suture a rayuwar matan Hausawa, kasancewar cuɗanya da ake samu ta fuskar auratayya an cuɗu an kuma cuɗe ya taimaka wajen samun suturun ƙetare wanda zai iya zaman a kusa ko na nesa. 5.3 Kasuwanci ko Cinikayya Kasuwanci yana nufin “Sana’ar saye da sayarwa a kasuwa” (Ƙamusun Hausa, 2006:238).

Sakamakon shiga da fice yanzu ga wasu matan Hausawa suke tafiya ƙasahsen ƙetare na kusa da na nesa sun taimaka wajen kawo sababbin suturun ga matan Hausawa. Cuɗanyarsu da mu’amalarsu ta yau da gobe ya haddasa sha’awar aron baƙin suturun, duba ga yadda matafiya suke safarar kayan suke kuma rububin sayansu. (Halima da Fatima 2016).

Kammalawa

Wannan takarda an yi ƙoƙarin gano baƙin al’adu cikin suturun matan Hausawa da suka samu sauyi ta dalilin zaman tare da cuɗanyar Hausawa da wasu fitattun ƙabilu na kusa da nesa da su, wanda suturun sun sami gindin zama inda aka zazzaƙu ko ire-iren bajewarsu a cikin suturun matan Hausawa a yau. An kuma kalli sutura ta yanayin binciken ya bibiyi wasu hanyoyin da ake ganin zamani ya yi tasiri a kan suturun mata. A dunƙule wannan bincike ana son ya zama zaburarwa ga masu nazarin al’ada da sauran mutane musamman matan Hausawa yana da kyau a yau


gare mu, mu ɗauki suturun baƙin masu kyau waɗanda bas u saɓawa addinin musulunci ba da al’adarmu ta asali ba, kasancewar suturun akwai na ƙwarai da kuma akasin haka.

Manazarta

1.      Almajir, T.S (2010) “Hikimomin Hausa”. Littafin Adon Ƙananan Makarantun Sakandare na ɗaya Kano. Fidan Publishers.

2.      Bichi, A.Y (2015) “Main Component of Hausa Culture” M.A Lecture (NLH8326) Katsina: Umaru Musa ‘Yar’adua Uniɓersity.

3.      Bunza, A.M (2006) “Gadon Feɗe Al’ada”. Lagos: Jiwal Nigeria Ltd. Cibiyar nazarin Harsunan Nijeriya (2006) Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero Kano. Zari’a: Ahmadu Bello Uniɓersity Press.

4.      Dayo, I.O. (2002) “Kamanci da Bambance-Bambancen da ke Tsakanin Tufafin Gargajiya na Hausawa da na Yarabawa” Kundin Digiri na Ɗaya. Sashen koyar da Harsunan Nijeriya. Kano: Jamiar Bayero.

5.      Dokaji A.A (2002) Kano ta Dabo Cigari: Zaria: NNPC.

6.      Gusau, S.M (2015) Mazhabobin Ra’i da Tarke a Adabi da Al’adu na Hausa. Kano: century Research and Publishing Company Limited Nigeria.

7.      Maryam, M. (2015) “Nazarin baƙin Al’adun Aure a Kano” Kundin Babbar Diploma Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya Kano: Jami’ar Bayero.

8.      Mu’azu da Satatima (2013) “Kwaɗon Al’adun Hausawa da na wasu ƙabilu”. Eɗcert of International Seminer the Detarioration of Hausa Culture Katsina State: History and Culture Bureau Umaru Musa ‘Yar’adua Uniɓersity.

9.      Mukhtar, I. (2013) Duba ga Al’adun Hausawa da cikin tafiya mai nisa: daga ina zuwa ina? In the deterioration of Hausa Culture Katsina Zaria, Ahmadu Bello Uniɓersity Press Limited.

10.  Tukur, A. (1999). “Kowacce Ƙwarya da Abokiyar Buminta”. Kano: Gidan Dabino.

11.  Zahra’u, W.I (2013) “Shin Baiko Aure ne”. Eɗcert of International Seminer the Detarioration of Hausa Culture Katsina State: History and Culture Bureau Umaru Musa ‘Yar’adua Uniɓersity.

12.  Zariya, Y. (2000). “Ado da kwalliyar Hausawa”. Kundin Digiri na ɗaya sashen koyar da Harsunan Nijeriya da na Afirka Zari’a.

Post a Comment

0 Comments