Ticker

6/recent/ticker-posts

JAGORAN HAUSA Littafin koyar da hasken Hausa

JAGORAN HAUSA Littafin koyar da hasken Hausa

Cibiyar Al’adun Hausa

🆕 SANARWA

AN BUƊE YIN RAJISTAR SAYEN LITTAFI

«Jagoran Hausa»

Littafin koyon harshen Hausa

Bugawar Édition Ilimi

Domin bai wa ‘ya’yanku damar sanin asalinsu da nakaltar harshen iyayensu

Wannan littafi na zamani da sauƙin fahimta zai koyar da  Hausa ta yau da kullum, tare da:

Zantukan rayuwar yau da kullum

Ƙamusmai ɗauke da kalmomi da jimloli sama da 200

Ka’idojin nahawu, lafuzzi da al’adun Hausawa

📖 Shafi 218 – cike da launuka

💰 Farashi: 5000 FCFA kacal

Yi rajistar don mallakar naka tun yanzu!

Ka aiko mana da adadin kwafin da kake so da sunanka. Za a turo maka da takardar ajiyar littafi.

📲 Tuntuɓe mu:

WhatsApp : 672388803

Kira / saƙo : 692846494 | 674993082

Hanya ce mai sauƙida amfani don ‘ya’yanku su koya  su kuma ƙaunaci harshensu!

*** ***

Gabatarwa

JAGORAN HAUSA Littafin koyar da hasken Hausa. Littafin 1

Littafi ne da aka tsara shi domin masu farawa da koyon harshen Hausa, ya kuma dace da kowane mataki na karatu – daga yara, matasa, har zuwa manya. Littafin ya samo asali ne daga bukatar samar da kayan karatu na zamani da ke haɗa harshe da al’adu, tare da bai wa mai karatu damar koyon Hausa cikin sauƙi, jin daɗi da fahimta mai zurfi.

Tsarin littafin:

Littafin ya kasu kashi-kashi, inda kowanne sashe ya ƙumshi:

Gabatarwa da tambayoyi don yin taɓa ka lashe da tunani da jan hankali.

Hira da karantu domin ƙarfafa sauraro da magana.

Nahawu da ka’idoji tare da misalai masu sauƙi da aiki.

Furucin sauti (phonétique) don koyon sautukan Hausa yadda ya dace.

Aikace-aikace da rubutu domin sabawa da amfani da harshen.

Bayani kan al’adu don fahimtar rayuwar Hausawa da dabi’unsu.

Manufar littafin:

Sauƙaƙa koyon Hausa ga duk wanda ke so ya iya magana da rubutu cikin Hausa.

Taimaka wa ɗalibai da masu sha’awar Hausa su koyi kalmomi, jumloli, da tsarin magana cikin sauƙi.

Haɗa koyon harshen da fahimtar al’adun Hausawa don gina cikakkiyar ilimi.

Babban abin da littafin ke kunsa:

Littafin ya ƙumshi fannoni daban-daban na rayuwa kamar:

Zamantakewa da iyali: yadda ake gaisawa, gabatar da kai da iyali, hira da abokai.

Harkokin tattalin arziki: sayayya a kasuwa, sayar da kaya, yin ciniki da tattaunawa kan farashi.

Harkokin lafiya da walwala: yadda ake magana da likita, bayyana rashin lafiya, da shawarar kiwon lafiya.

Zama ɗan kasa: fahimtar dokoki, tambayoyi kan al’umma da tsari.

Kafofin watsa labarai: hira a gidan rediyo, labaran yau da kullum.

Al’adu da tarbiyya: karɓar baƙi, muhimmancin lafiya, da matsayin ilimi a al’ummar Hausa.

Ta haka, littafin yana ba mai karatu damar fahimtar Hausa ba kawai a matsayin harshe ba, har ma a matsayin hanya ta naƙaltar harshe da al’adun Hausawa.

*** ***

Ƙumshiya

Jagoran Hausa – littafi 'a 1, littafi ne da aka tsara domin koyar da harshen Hausa cikin hanya mai sauƙi, mai jan hankali kuma mai haɗa harshe da al’adu. Bugu da ƙari, littafin yana dauke da darussa daban-daban da suka shafi zamantakewa, kiwon lafiya, tattalin arziki, kafofin watsa labarai, da kuma ilimin zamantakewa da dokoki.

Littafin yana:

Koyar da yadda ake gaisawa da gabatar da kai cikin Hausa.

Bayar da hanyoyin hira kan iyali, abokai, makaranta, kasuwanci da sauran su.

Kara fahimtar yadda ake magana da likita, tambaya kan lafiya da bayar da shawara.

Bayar da dabarun magana da rubutu a kasuwa, tattaunawa da ciniki.

Taimaka wajen fahimtar dokoki da zamantakewar al’umma.

Gabatar da kafofin watsa labarai, hira a rediyo da labaran yau da kullum.

Bayar da haske kan muhimmancin al’adu irin su karɓar baƙi, zamantakewa da tarbiyya.

Ta hanyar:

Tambayoyi da misalai na rayuwar yau da kullum.

Hira da rubutu don ƙarfafa magana da sauraro.

Nahawu cikin sauƙi, tare da misalai da aiki.

Bayani akan sautunan Hausa domin inganta furuci.

A ƙarshe, wannan littafi yana bawa kowane mai karatu damar:

Magana cikin Hausa cikin sauƙi.

Rubuta kalmomi da jumloli cikin Hausa.

Koyar da al’adun da tsarin rayuwar Hausawa.

Girmama harshe da al’ada a matsayin hanya ta haɗa kai da juna.

Jagoran Hausa – littafi na 1 ba kawai littafin koyon harshe ba ne, amma hanya ce ta fahimtar zuciyar Hausawa, al’adunsu da dabi’unsu.

Post a Comment

0 Comments