Ticker

6/recent/ticker-posts

Tattalin Arzikin Kasar Hausa da Al’adun Hausawa Kafin da Bayan Zuwan Turawa

Citation: Bugaje, H.M. (2025). Tattalin Arzikin Ƙasar Hausa da Aladun Hausawa Kafin da Bayan Zuwan Turawa. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 4(1), 35-40. www.doi.org/10.36349/tjllc.2025.v04i01.004.

TATTALIN ARZIKIN ƘASAR HAUSA DA ALADUN HAUSAWA KAFIN DA BAYAN ZUWAN TURAWA

Daga

Dr. Hauwa Muhammad Bugaje

Sashen Harsuna da Al’adun Afirka
Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya
hhmbugaje@gmail.com

Tsakure

Tattalin arziki shi ne ƙashin bayan ci gaban kowace alumma a duniya. Ana iya gane ci gaban tattalin arzikin alumma ko koma-bayansa ta hanyar nazarin aladun wannan alumma. Haka kuma, adabi a mafi yawan lokaci yakan zama jagora na fahimtar alumma, halin da ta kasance a jiya da yau da kuma hasashen inda za ta samu kanta a ciki a gobe. Wannan maƙala mai suna:  ‘Tattalin Arzikin Ƙasar Hausa da Aladun Hausawa Kafin da Bayan Zuwan Turawa’ ta ginu ne bisa manufar waiwayen hanyoyin bunƙasar tattalin arziki da ƙasar Hausa. An nazarci halin da tattalin arzikin ƙasar Hausa ya kasance, da tagomashin da baƙi suka yi wajen ci gaban tattalin arziki, da al’adu na neman arziki a ƙasar Hausa. An yi amfani da hanyoyin tattara bayanai daga litattafai da nazartar waƙoƙi da hira da masana tattalin arziki da al’ada. Har ila yau, an ɗora wannan aiki bisa ra’in sauyin al’adu wanda ya ginu a kan yadda al’adun al’ummomi suke sauyawa da abubuwan da suke haifar da sauyin. Sakamakon wannan bincike ya gano cewa Hausawa suna gina harsashin tattalin arzikinsu bisa kyawawan ɗabi’u na gaskiya da riƙon amana da taka-tsantsan. Haka kuma, an gano manyan sana’o’in gargajiya na Hausawa su ne farauta da noma da saƙa da rini da jima da sauransu, kuma dukkaninsu zamananci ya yi tasiri a kansu. A ƙarshe, an bayar da shawarar faɗakar da al’umma da a koma wa hanyoyin gargajiya da sana’o’in gargajiya da suka gina tattalin arzikinmu a baya domin samar wa al’umma mafita a kan halin da ake ciki na ƙuncin rayuwa da talauci da rashin aikin yi.

Titilun Kalmomi: Tattalin Arziki, Al’adun Hausawa, Ƙasar Hausa, Zuwan Turawa

 

1.1 Gabatarwa

Ƙasar Hausa ƙasa ce mai daɗaɗɗen tarihi da arziki da kuma sana’o’i daban daban da suka taimaka wajen bunƙasar tattalin arzikinta. Tun kafin kasantuwar ƙasar Hausa a ƙarƙashin dunƙulalliyar daula guda ɗaya,wato daular Usmaniyya, garuruwan da ake kira ƙasashen Hausa sun shahara ta fuskar tattalin arzikinsu, musamman ma irin sanaoinsu na gargajiya da aka sansu da su. Har ila yau, cuɗanyar Hausawa da baƙi ya taimaka wajen bunƙasar tattalin arziki tun kafin shigowar Turawa a yankin yammacin Afirka. Bayan zuwan Turawa, tattalin arzikinsu ya bunƙasa sakamakon shigowar zamananci. Masu iya magana dai suna cewa tun kafin a haifi uwar mai sabulu balbela take da farinta. Saboda haka, wannan muƙala ta yi duba a kan tattalin arzikin Hausawa da aladun gargajiya da suka taimaka wajen bunƙasar tattalin arzikin, da kuma halin da ƙasar Hausa ta samu kanta a ciki a yau ta fuskar tattalin arziki.

2.1 Ƙasar Hausa da Alummarta

Ƙasar Hausa tana a farfajiyar Afrika ta yamma, wadda ta haɗa da arewacin Nijeriya, da kudancin Nijar, da wasu sassa na yammacin Afirka. Su kuwa Hausawa mutane ne da ke zaune a ƙasar Hausa kuma suke magana da harshen Hausa. Ƙasar Hausa ƙasa ce niimtacciya, mai yalwar ƙasar noma da manyan koguna, da tsaunuka, da dazuzzuka (dajin sahel, mai ƙarancin itatuwa da kuma dajin Sabana, wato daji mai yawan itatuwa, masu duhuwar ganyaye). Wannan ƙasa ita ce mazaunin Bahaushe na asali, amma Hausawa sun watsu kuma sun yi kaka-gida a sassa daban daban na yammacin Afirka kamar Ghana da Chadi da Mali da Senegal da sauran ƙasashen Afirka. A yau, Hausawa sun watsu a sassa da dama na duniya. Haka kuma, Hausawa mutane ne da a yau suka zamo mafi yawa daga cikin alummomin Afirka ta yamma, domin bincike ya nuna cewa masu magana da wannan harshe sun kai kimanin mutane miliyan saba’in (Sani & Umar, 2018 sh. 24). Haka kuma harshensu ya zamo harshe goma sha ɗaya a jerin harsuna mafiya yawan jama’a a duniya.

Al’ummar Hausawa al’umma ce mai daɗaɗɗen tarihi da al’adu na ƙwarai. Haka kuma, ta ginu a kan zaman lafiya da kyakkyawan tsarin zamantakewa da taimakon juna da karrama baƙi. Tsarin zamantakewar Bahaushe tsari ne da ya tanadar wa kowa abin yi, babu mai zaman banza, kuma babu cima-zaune. Misali idan muka fara da cikin gidan Bahaushe, uba shi ne jagora kuma mai ɗaukar nauyin iyali baki ɗaya, amma da zarar ya sami haihuwa musamman ɗa namiji, zai kasance ya samu magaji, wato wanda zai girma ya taso ya gaji sana’arsa. Haka kuma, ta fuskar tattalin arziki, ɗaukacin iyalai suna taruwa su noma abincin da za a ci na shekara a gonar gandu. Haka kuma, kowane ɗa musamman magidanci a cikin iyalin gidan yana da ƙaramar gonarsa da zai noma abin da zai sayar domin biyan bukatun yau da kullum.

Har ila yau, tsarin zaman unguwa, zama ne na taimakekeniya da cin abinci tare musamman tsakanin magidanta da taimaka wa wanda ya yake bukatar taimako ta fuskar gini da noma da sauran ayyukan ƙarfi. Haka kuma, akwai tsari na shugabanci tun daga matakin mai unguwa, zuwa dagaci zuwa hakimi da kuma babban jagora wato sarki. Ta fannin tattalin arziki kuwa ƙkowace sana’a tana da shugabanta wanda akan yi wa sarauta da zai wakilci masu wannan sana’a da tabbatar da ɗorewa da bunƙasar sanaoin. Misalin waɗannan sarautu sun haɗa da sarkin noma da sarkin dawa da sarkin fawa da sarkin maƙera har ma da sarkin mayu. (Tahir, 2024)

2.2 Ma’anar Tattalin Arziki

Masana da manazarta al’adun Hausawa irin su Auta (2006:196) da Nuhu (2019:133) sun yi nazarin tattalin arzikin Bahaushe dangane da la’akari da wasu daga cikin sana’o’in da Hausawa suke yi. Auta (2006:196) ya bayyana tattalin arziki da cewa tsari ne na sarrafa albarkatun ƙasa da sauran niimomin da Allah ya yi wa ɗan Adam domin samar da muhimman abubuwa da ake gina rayuwa da su. Har ila yau, Nuhu, (2019:133) ya bayyana tattalin arziki da cewa tsari ne na inganta hanyoyin shigar kuɗi da sauran abubuwan bukatun ɗan Adam kamar abinci da muhalli da sutura.

Sani da wasu (2019 sh. 46) sun nazarci ma’anonin tattalin arziki da masana daban-daban suka kawo, inda daga ƙarshe suka tafi kan cewa tattalin arziki yana nufin renon dukiya ko wani abin mallaka mai amfani da tarisi ga cigaban rayuwa ta hanyar yin amfani da dabarun tattali da adana da killacewa. Bunƙasar tattalin arziƙi na faruwa ne yayin da abin mallaka ko dukiya ta haɓaka.” Domin haka, za a iya bayyana tattalin arziki a matsayin hanyar samar da dogaro da kai ga al’umma ta hanyar nema da tsimi da tanadi da sarrafa dukiya domin ci gaban ƙasa.

3.1 Tattalin Arzikin Ƙasar Hausa Kafin Zuwan Turawa

Babbar hanyar tattalin arzikin ƙasar Hausa a jiya, wato kafin zuwan Turawa shi ne manyan hanyoyin neman arziki da suka shahara a wancan lokaci, wato kasuwanci da sanaoi da ƙwadago. Haka kuma, babban abin da ya yi wa Bahaushe jagoranci a neman arziki shi ne ɗabi’a, wato kyakkyawar ɗabi’arsa ta juriya da haƙuri da taka-tsantsan da kawaici da riƙon amana da kunya da biyayya da sauransu. Waɗannan ɗabi’u su suka yi wa Bahaushe jagoranci, har ma yakan yi karin magana da cewa ‘mai arkizi ko a kwara ya sayar da ruwa. Mutum zai iya tashi zuwa neman arziki ba tare da jari ba, amma ya riƙe gaskiya da amana, domin ya yi imani su ne babban jarinsa. Har ila yau, Bahaushe yana da tsarin tsimi da tanadi da suka taimaka wajen kyautata al’adun neman arzikinsa a jiya. Bahaushe mutum ne jajirtacce mai haƙurin nema da aiki tuƙuru tun asalinsa. Domin haka tun asalinsa ya fara neman arziki ta hanyoyi kamar haka:

a.      Noma: masu iya magana kan ce “noma na duƙe tsohon ciniki, kowa ya zo duniya kai ya tarar. Sana’ar noma tana ɗaya daga cikin daɗaɗɗun sana’o’in Bahaushe da ba a samu tarihin wanda ya kawo wa Bahaushe ita ba. Wato tun da aka ga zabuwa da zanenta aka ganta. Bahaushe ya daɗe da gane muhimmancin noma da samar da abinci, kuma sai aka yi dace yana rayuwa a shimfiɗaɗɗiyar ƙasa mai dausayi da ta dace da aikin noma. Daga cikin abin da ƙasar Hausa ta shahara wajen nomawa akwai gero da dawa da wake da gyaɗa da auduga da sauransu.

b.      Farauta: sana’ar farauta sana’a ce da Hausawa suka yi riƙo da ita tun lokaci mai tsawo har zuwa yau. Sanaa ce da ake gudanar da ita bayan ɗaukewar ruwan sama, kuma bayan an adana amfanin gona. Wannan sana’a ta shafi shiga daji da nufin kama ƙananan dabbobi domin samar da nama da fatu da za a iya sarrafawa domin a samar da abin amfani kamar takalma, salkuna, jikkuna da sauransu. Bincike ya nuna cewa sana’ar farauta da ta noma su ne sana’o’i mafi daɗewa a duniya, musamman ma a ƙasar Hausa.

c.       Ƙwadago: ƙwadago wato aiki domin samun abin biyan bukata. Hausawa sun daɗe suna ayyuka da dama da za su taimaka masu wajen samun abin masarufi da zai tallafi rayuwarsu. Daɗaɗɗun ayyuka da suka daɗe a ƙasar Hausa sun haɗa da gini da aiki a gonaki da dakon kaya da sauransu.

d.     Fatauci: Hausawa sun daɗe da gudanar da fataucin shigowa da fitar da kaya tsakaninsu da maƙwabtansu. Hausawa suna fatauci da alummomi irin su Asbinawa da Buzaye da Nufawa, da Gwanjawa, Wangarawa da sauransu. A ƙarni na goma sha bakwai ƙasar Katsina ta kasance cibiyar kasuwanci ta yammacin Afirka, inda fatake daga wurare da dama na yammacin Afrika sukan zo domin cinikayya. A wannan lokaci ana saye da sayarwa ta hanyar musaya, wato bani gishiri in baka manda, abin da suke ce wa furfure, daga bisani kuma aka riƙa amfani da wuri a matsayin kuɗi na cinikayya.

4.1 Shigowar Baƙi da Bunƙasar Tattalin Arzikin Bahaushe

Masu iya magana kan ce “Baƙo raɓa ne…’ shigowa da kwararowar baƙi cikin ƙasar Hausa sun taimaka matuƙa wajen bunƙasar tattalin arzikin ƙasar Hausa. Wasu daga cikin baƙin da suka zauna sun daɗe da sajewa da narkewa da Hausawa wanda a yau ba su da wani harshe ko ƙasa ban da Hausa. Haka kuma, sun kawo sanaoi da dama da a yau ake masu kallon sanaoin Hausawa na gargajiya. Daga cikin waɗannan baƙi akwai Buzaye da iyayen gidansu Asbinawa waɗanda yunwa ta koro daga ƙasarsu wato Agadez. Haka kuma, akwai Wangarawa da Larabawa da suka shigo domin fatauci da yaɗa addini, da Fulani da suka fito daga Futa-toro da Mallawa daga ƙasar Mali da Bare-Bari daga ƙasar Barno da Ƙwarori daga Lebanon da har ma da Nupawa daga ƙasar Nupe da Yarbawa daga daular Oyo da Inyamurai da sauransu. Dukkanin waɗannan ɓaƙi sun taimaka wajen bunƙasar tattalin arzikin ƙasar Hausa da kuma inganta aladu na suturu da gine-gine da abinci da saye da sayarwa da sauransu.  Daga cikin sana’o’in gargajiya na Hausawa da suka samu tagomashin zuwan baƙi tun kafin zuwan Turawa akwai:

a.      Sana’ar ƙira: ƙira sanaa ce ta sarrafa ƙarfe da narkar da shi domin samar da kayayyakin amfani musamman kayan aikin gona da na farauta da kayan yaƙi da sauran kayan amfanin gida da na kwalliya dangin ƙarafa. Wannan daɗaɗɗiyar sana’a ce a ƙasar Hausa, sai dai zuwan baƙi musamman Buzaye ya haɓaka da bunƙasa ta, da kuma samun ƙari a kan nauoin kayayyakin da Hausawan suke samarwa.  Buzaye gwanaye ne fannin  sarrafa ƙarfe musamman takobi da wuƙaƙe.

b.      Sana’ar Rini: wannan sana’a ce ta rina kaya wadda take tafiya kafaɗa da kafaɗa da sana’ar bugu. Idan marina suka rina kaya, masu bugu su suke buga kayan su kwantar da duk wata tattara da kayan suka yi, su gyara su yadda za a ji daɗin sayarwa. Duk da cewa sana’a ce daɗaɗɗiya a ƙasar Hausa, amma zuwan baƙi musamman mutanen Mali ya ƙara haɓaka wannan sana’a ta hanyar sanin sababbin dabaru na rini. Zuwan baƙi a yau ya kawo sabbin dabaru na rini ta amfani da yaduka da aka sarrafa daga kamfanoni, maimakon kaya na saƙi da ake rinawa. Dangane da kayan da ake rinin, a da ana amfani da kayayyaki na gargajiya irin su baba, a yau, akwai sinadaran kemical da dama da ake amfani da su wurin rini da suke bayar da launuka daban daban, kuma cikin sauƙi.

c.       Sana’ar Jima: ita kuma wannan sana’a ce ta sarrafa fatu da goge su domin sayarwa ga dukawa da sauran masu sana’ar sarrafa fatu. Wannan sana’a ta taimaka matuƙa wajen haɓakar tattalin arzikin ƙasar Hausa. Ana fitar da fatu da ake sarrafawa zuwa ƙasashe daban daban na duniya. Duk da cewa fitacciyar sanaa ce da aka san Bahaushe da ita, amma zuwan baƙi musammman Ƙwarori ya taimaka wajen haɓakarta kasancewar an ƙara samun sababbin dabaru na inganta sanaar daga wurinsu.

d.     Sana’ar Sassaƙa: masu iya magana kan ce “sara da sassaƙa ba ya hana gamji toho. Sassaƙa daɗaɗɗiyar sana’a ce a ƙasar Hausa. Akan samar da kayayyakin amfanin gona irin su ƙota da kayan amfanin gida irin su akushi da turmi da kujeru da ludayi da ƙoshiya da sauransu. Zuwan baƙi musamman inyamurai ya taimaka wajen haɓaka sana’ar, domin ta hanyarsu ne aka koyi aikin kafinta, kamar yin gadaje da kujeru da sauran ayyuka na kafita.

Waɗannan kaɗan ne daga ɗumbin sana’o’in gargajiya da suka wanzu da ƙasar Hausa tun kafin zuwan Turawa. Haka kuma, waɗannan sana’o’i sun bayar da gagarumar gudummawa kuma suna ci gaba da bayarwa wajen bunƙasar tattalin arzikin alumma. Abin shaawa game da Bahaushe shi ne aladarsa ta hankaka mai da ɗan wani naka, a kullun Hausawa suna ƙoƙarin zamanantar da sana’o’insu da ƙara samun dabaru na bunƙasa tattalin arzikinsu ta hanyar koyon kowace irin sanaa suka ga za ta taimaka wa rayuwarsu tare da hausantar da ita yadda za ta dace da al’adunsu da addininsu. Wannan dalili ya sa Hausawa suka kasance masu karɓar baƙi a kodayaushe tare da nazarin abin da za su iya ƙaruwa daga waɗannan baƙin. Hakan kuma ta sa baƙi da yawa suka ƙi komawa ƙasashensu suka rikiɗe suka zama Hausawa ba tare da sun farga ba.

4.2  Tattalin Arzikin Ƙasar Hausa Bayan Zuwan Turawa

Tattalin arzki shi ne ƙashin bayan zuwan Turawa ƙasar Hausa da sauran sassa na yammacin Afirka. Sahun farko na Turawan da suka tako wannan yanki su ne waɗanda suka zo a 1879, da niyyar ciniki da kasuwanci a ƙarƙashin kamfanin  U.A.C na wani baturen Ingila Sir George Goldie, wato United Africa Company, wanda daga baya Gwamnatin Ingila ta yi amanna da ayyukansa, ta sauya masa suna zuwa Royal Niger Company, kuma ta ba kamfanin izinin yin ciniki da mulki a yankin kogin Neja wanda har da ƙasar Hausa a ciki. A taƙaice dai wannan kamfani ya yi shigar burtu ya mamaye yankin kogin Neja har ma sun sami nasarar jan ragamar mulkin Nijeriya a ranar 1 ga watan Janairu, 1900 ƙarƙashin jagorancin Gwamna Lugga (Lord Lugard). (Yahaya, 1988)

Ba haka kawai wannan kamfani ya kutso kai yammacin Afirka da ƙasar Hausa ba, sai da ƙungiyoyin Turawa suka aiko da masana domin su binciki yadda ƙasashen Afirka suke da yadda aladunsu suke gudana da  harshensu har ma da addininsu. Haka kuma, sun binciko hanyoyin sadarwarsu ta ruwa da ƙasa, da tsarin cinikinsu. Daya daga cikin waɗannan masana wato Henry Barth ya bayyana ƙasar Hausa da wuri mafi kyawu da niima da ya taɓa gani a rayuwarsa. Har ma ya ƙara da lissafa irin kayayyakin da ake nomawa a wannan ƙasa, kamar gyaɗa da auduga da riɗi da sauransu.

Shigowar Turawa ya taimaka wajen canza al’amura ta fuskar kasuwa da ciniki da tsarin tattalin arziki baki ɗaya. Haka kuma, ya sauya tsarin gudanar da mulki da hanyoyin shiga da ficen kuɗi da ɗaukacin tsarin tafiyar da al’amura. Kodayake a iya cewa sun kawo sabon tsarin sufuri da tsarin hada-hadar kuɗi na bankuna inda aka buɗe banki na farko a Kano a 1914, wato Colonial Bank. Daga baya aka sauya masa suna zuwa Bank of British West Afrika, ya kuma sake sabon sunan da aka sanshi da shi har zuwa yau wato First Bank. (Adamu, 1982)

Tabbas a iya cewa an samu ci gaba ta fuskar ciniki da kasuwanci a ƙasar Hausa bayan zuwan Turawa musamman saboda yawaitar kasuwanni da kuma yadda aka shimfiɗa hanyar jirgin ƙasa domin dakon kayan da ake nomawa a ƙasar Hausa zuwa ƙasashen Turai. Arziki ya fara yawaita sai dai kuma sannu a hankali sana’o’in gargajiya sun fara durƙushewa, dogaro da abin da Turawa suke samarwa daga arzikinmu ya fara jefa mu cikin ƙaƙa-nika-yi. Misali dogaro da kayayyakin masarufi da suturu da abinci da abubuwan hawa da Turawa suka zo da su, tare da watsi da waɗanada muka gada daga iyaye da kakanni. Wannan dalili ya sa shahararren mawaƙin nan wato Mamman sarkin Taushi ya bayyana muhimmancin riƙo da aladun gargajiya, har ma yana ganin babu wani abin a zo a gani da Turawa suka zo da shi, domin sun tarar muna da komai:

Gindin Waƙa: Nufinta ne wasan gargajiya,

      : Ta sa mu ƙara fahimtar juna.

 

Jagora: Mutane kowacce tsare kayan ubanka ko kayan kakanka,

Y/Amshi: Idan kana da tunani,

 Wannan mutum mutane ina laifi nai?

 

Jagora:  Ka ji zakkuwar Turawa sun tad da mu,

  Muna da sana’ar hannu,

 

Y/Amshi: Ai muna da al’adunmu,

  Na gargajiya da za mu gadara mu ma. 

(Waƙar Al’adun Gargajiya ta Alhaji Mamman Sarkin Taushin Katsina, ta FESTAC 1977)

Mawaƙin ya jero masu sanaoin gargajiya da dama a ƙasar Hausa kafin zuwan Turawa kamar maƙera da masaƙa da dukawa da majema da wanzamai da sauransu. Turawa sun samu galaba a kan Hausawa ta hanyar cusa wa matasa shaawar ayyukan Gwamnati da ƙyamar sanaoin gargajiya da kasuwanci da fatauci irin wanda suka gada daga iyayensu. Mafi yawa daga matasa da iyayensu suka shahara a fataucin goro ko fatu da suturu, a yau sun watsar da su sun rungumi ilimin boko da ayyuka na gwamnati. Sana’o’i irin su noma da saƙa da sassaƙa an bar su a hannun ɗaiɗaiku. Haka kuma, an samu yawaitar ayyukan ƙwadago saboda shigowar kamfanoni da masanaatu da ayyuka na haƙar maadanai da sauransu.

5.1  Kammalawa

Daga waɗannan bayanai da aka gabatar za a fahimci cewa Hausawa sun daɗe suna fafutukar neman arziki kuma sun kafa tsarin tattalin arziki mai inganci a ƙarnonin da suka gabata. Wannan ya sa Dr. Mamman Shata Katsina ya bayyana irin niimar da take danfare a Arewa, a waƙarsa ta “’Yan Arewa ku bar barci Nijeriyanmu akwai daɗi.” A wannan zamani akwai bukatar al’umma musamman matasa su dage wajen rayawa da inganta sana’o’insu na gargajiya waɗanda suka ɗaga martabarsu a baya. Akwai bukatar kyakkyawan shiri na wayar da kan matasa da mata domin su shirya tunkarar ƙarnonin da ke tafe ta hanyar zamanantar da sana’o’in gargajiya da farfaɗo da hanyoyin neman arziki, tare da sabunta hanyoyin tattali da amfani da fasahar zamani a ayyukan noma da kiwo da saƙa da kasuwanci da hada-hadar kuɗi da sauransu. Akwai jan aiki gaban matasa a yau na tashi tsaye da tuna irin gwagwarmaryar da kakaninsu suka yi a ƙarnonin da suka gabata, domin masu iya magana kan ce kowa ya ci zomo ya ci gudu, haka kuma, zomo ba ya kamuwa daga kwance kuma in ka ji wane ba banza ba. Muna fata wannan ƙarni ya zamo mana ƙarnin farkawa ta fuskar tattalin arziki da cigaban ƙasa.

Manazarta

 Adamu, M. (1980). The Hausa factor in West African history. Ahmadu Bello University Press in collaboration with Oxford University Press.

Alhassan da Wasu. (1982). Zaman Hausawa. Zaria Institute of Education.

Auta, A. L. (2006). Tattalin arzikin al’umma: Nazarin sana’o’i da kasuwancin Hausawa. Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies, 1(4), 194–204.

Bugaje, H. M. (2014). Karin magana mahanga tunani: Nazarin lokaci a Hausa. (Undergraduate thesis). Ahmadu Bello University, Zaria.

Bunza, A. M. (2006). Gadon feɗe al’ada. Tiwal Publishers.

Garba, C. Y. (1991). Sana’o’in gargajiya a ƙasar Hausa. Spectrum Books.

Ibrahim, U. (2018). Gudummawar baƙi yan kasuwa da fitattun sana’o’in Kanawa daga 1900–2015. (Undergraduate thesis). Department of African Languages and Culture, Ahmadu Bello University, Zaria.

Nuhu, A. (2019). Sana’o’in Maguzawan Katsina a rigar zamani. Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies, 12(2), 133–147.

Sani, A.-U., & Umar, M. M. (2018). Global growing impact of Hausa and the need for its documentation. Contemporary Journal of Language and Literature, 1(1), 16–34. http://sgpicanada.com/index.php/CJLL/issue/download/1/Abu-Ubaida%20Sani%20and%20Muhammad%20Mustapha%20Umar

Sani, A-U., Buba, U. & Mohammad, I. (2019). Wanda ya tuna bara...: Biɗa da tanadi a tsakanin Hausawa matasa a yau. Global Academic Journal of Humanities and Social Sciences, 1(2), 44-50. www.doi.org/10.36348/gajhss.2019.v01i02.001.

Tahir, R. M. (2024). Tsaro da sarauta a Bahaushiyar al’ada. Paper presented at the Hausa Week Conference 2024, Department of African Languages and Culture, Ahmadu Bello University, Zaria.

Yahaya, I. Y. (1988). Hausa a rubuce: Tarihin rubuce-rubuce cikin Hausa. Kamfanin Gaskiya.

Post a Comment

0 Comments