Citation: Bunza, A.M. (2025). Alƙur’ani Malamin Mallammai Shaihin Da Shaihuna Ka Roƙo Fatawa. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 4(1), 41-47. www.doi.org/10.36349/tjllc.2025.v04i01.005.
ALƘUR’ANI
MALAMIN MALLAMMAI SHAIHIN DA SHAIHUNA KA ROƘO
FATAWA
Daga
Aliyu Muhammadu Bunza
Department of Nigerian Languages
Usmanu Danfodiyo University, Sokoto,
Nigeria
Tsakure
Saukar Alƙur’ani na farko ya zo shekarar (610 CE), ya ƙare shekarar (622CE). Alƙur’ani an saukar da shi ga Annabi Muhammadu (SAW) ta
hanyar Mala’ika Jibril. Da kalmar “Iqra” aka fara magana. Littafi ne da ke da Surori
(114) da aka kasa zuwa hizifi (60). Ayoyi 6,666, kalmomi 157,935 da harufan da
suka gina su 668,684; Allah Ka buwaya. Asalin harufan harshen Larabci (28) ne.
Daga cikinsu akwai harufu 15 marasa masu ɗigogi, guda 13
kuma masu ɗigogi. Harufa 7 ke da ɗigo ɗaya, 3 ɗigo biyu, 2 ɗigo uku.
Manyan wasula su ne “Alu Baƙi" da “Alu
Ja” sai “wasulan sama da ƙasa” da “damma
da shadda”. Waɗannan suke ba da damar karanta alƙur’ani ga kowa. A fassara Alƙur’ani cikin harsuna 114. A harsuna 47 kawai aka samu
wallafa shi cikakke. A fagen masana, an yi tafsiran Alƙur’ani 2,700, amma 300 kawai aka samu wallafawa. A cikin
harsunan Nijeriya kimanin 500, an fassara Alƙur’ani cikin fitattun harsuna cikin rubutun bokon
harshe, da ajamin harshe. Daga cikinsu akwai: Hausa, Yoruba, Kanuri, Fulfulde,
Nupe, Kyanganci da Igbo. A tarihance, Indiya ta fara taron gasar karatun
addinai fiye da shekara 100 da suka gabata, shekarar da aka gayyato Musulmi shi
ne ya zama zakara. Ta karatun Alƙur’ani an fara
ta a Indonesia a shekarar 1940, sai Malaysia (1961), Saudiya ta fara a 1980. A
zamanin da muke ciki (2024), Nijeriya ce gaba da yawan mahardata Alƙur’ani wanda Daular Borno ke jagoranta. Harshen da ya fi
harsunan Nijeriya ga fassara Alƙur’ani shi ne
Hausa. A Najeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo ta
fara tsara shi a Kabi a matsayin karo na 39. Akwai buƙatar saka Alƙur’ani cikin
tsarin koyarwa daga Firamare zuwa Jami’a, a ƙara fassara Alƙur’ani cikin
Harsunan Nijeriya domin tsaro da kyautata shugabanci.
Fitilun Kalmomi: Alƙur’ani, Musulunci, Ƙasar Hausa,
Hausawa
Gabatarwa
Masanan duniya ba su
yi saɓani ba na kasancewar duniya mazaunin
halittu ne da mutane ke shugabanta. Babu wai, mahaliccin mutane, mutane ya ba
ragamar jagorar su kan kafa ta har ya zuwa yau. Mutanen da Allah Ya ba jagorar
mutane, su ne Annabawa da manzanni. Abin ban sha’awa, kowanensu Allah na ba shi
saƙo na
baka ko littafen da za a aje. Al’ummar farko annabi Adamu (AS) aka turo musu da
cikakken saƙon
baka; al’umma ta ƙarshe
kuwa (tamu) aka turo Annabi Muhammadu (SAW) da Alƙur’ani da zai
shugabance mu har ranar tashin duniya. Alƙur’ani ya zo
da shi, duk wani abu da ya saɓa masa kuskure ne babba, gyaran shi dole ne. tabbas Alƙur’ani ya zo da Musulunci, kuma Musulunci ya zo da Alƙur’ani ga yadda abin ya kasance.
Bayyanar Musulunci a Duniya
Dukkanin addinan da Allah Ya saukar ba su saɓa wa
kyakkyawar aƙida ba.
Addinin Musulunci an aiko manzonmu Muhammadu ɗan Abdullah
(SAW) da shi tare da babban littafenmu Alƙur’ani. Masana
tarihi sun yi kirdadon haihuwar Annabi Muhammad (SAW) cewa, ita ce ranar 12 ga
Watan Rabi’ul Awwal, wato rana ta uku a watan wadda za a ce Ogusta 29, 570CE,
wasu su ce, 20th April 571CE, wasu su ce, an haife shi ranar
Litinin. A ganin wasu, Musulunci a yau ya kai shekaru 1,400 domin wahayin Alƙur’ani na farko ya zo a shekarar 610, sai ya yi zuwa
Madina shekarar 622.
Har yanzu wasu masana tarihi suna zaton Annabi (SAW) ya
karɓo Musulunci shekarar 622CE, kimanin shekaru 1,382 a yau
2024. Daga Makka Musulunci a Afirka ya fara zuwa gabanin ko’ina a duniya.
Musulunci ya je a Habasha (Ethiopia) sau biyu, gabanin saukarsa a Madina. A taƙaice, ya nuna littafinmu mai tsarki Alƙur’ani da Makka da Habasha (Afirka) ya fara barbazuwa.
Manzo da kansa ya kai shi Jordan, Syria, Ta’if, Madina, Jerusalem, Masjid
Al-Qasra da sama ta bakwai. Musulunci ta hannun Sahabbai ya shiga Misra a zamanin
sarki Muqawatis, daga nan ya zarce Afirka ta Arewa. Daga nan, ya shiga kudu da
gabas na Asiya, daga nan sai India, sai Malysia, da Indonesiya, da China. ‘Yan
kasuwar Afirka ta Arewa, da Senegal, su suka yaɗa Musulunci a ƙasashen Afirka. A duniyarmu ta yau, ƙasashe 49 ke da babban tasirin Musulunci a ciki; ƙasar Mauriteniya ita kaɗai ke da kashi
100 na Musulmi a duniya, kuma dukkaninsu ahalil sunnah. A ƙasarmu (Nijeriya) a ƙarni na 9th wani ɗan kasuwa Ali
Ibn Ghanim shi ya kawo Musulunci a daular Kanen-Borno. A ƙasar Hausa kuwa, Sarkin Kano Muhammadu Rumfa (1463-1499)
ya fara karɓa Musulunci na daula. Ko’ina Musulunci ya bayyana Alƙur’ani ne limaminsa, shi ne mamu, shi ne ladan. Cikin
addinan duiya 10,000 da muke da su fitattunsu su ne: Christianity, Islam,
Hinduism da Buddhism, suke da 77% na addinan duniya. Alƙur’ani ya fi su littafi raba-gardama.
Mene ne Ƙur’ani?
Kalmar “Ƙur’aani” a
nahawun Larabci suna ne da aka ciro daga kalmar “aikatau” mai suna “ƙara’aa” mai nufin “a karanta” ko “a rera”. Tabbas Alƙur’ani da kansa ya ambace kalmar cikin suraa ta 9, aya
ta 111, da sura ta 75, aya ta 17-18. Wasu masana sun ce, kalmar tushenta daga
harshen Syriac ne wanda ya mamaye Middle East (Gabas da Tsakiya) da Estern
Arabia (Gabacin Arebiya), a taƙaice shi ne
harshen asali na ƙasar “Syria”
wanda asalinsa daga Edissa da tarihin ya fara tun ƙarni na ɗaya. Harshen Syriac wani karin harshe ne na Aramaic da
ake magana da shi har yanzu a tsakanin ƙasar Syria da
Iraqi, kuma ya samu karɓuwa sosai a Middle East (Gabas ta Tsakiya). A taƙaice, kalmar “Qur’an” mai nufin (karatu da rerawa) tana
da tushe daga kalmar harshen Aramaic da ake ce wa karatu: “qeryan-a”. Daga
sunayen da Alƙur’ani ya
ambata na kansa akwai: Al-ƙur’an,
Al-Kitabu, Al-Furƙan, Tanzeel,
da Al-Zikir, sun bayyana a cikin ayoyi daban-daban. A nan, za mu ga, dukkanin
littafan da Allah Ya saukar karatunsu ake yi da rera su da murya mai armashi
tun ƙarni na ɗaya zuwa yau
(2024).
Zubi da Tsarin Alƙur’ani
Alƙur’ani malamin
maluma ne mai tsarin da ya kyautu a tabbatar daga Allah yake; Mala’ika Jibrin
ya sadar da shi ga Manzon Allah (SAW). Ga fitattun zubi da tsarin da ya kamata
a ce zuciya ta kiyaye shi:
a.
An saukar da Alƙur’ani cikin
shekara (22) daga (610CE) zuwa (632CE).
b.
An fara saukar da shi ga Manzo (SAW) yana da shekara (40) aka ƙare shekarar (632CE) shekarar da Manzo (SAW) ya rasu (ƙaura). Allahu akbar!
c.
An wakilta Mala’ika Jibrilun zuwa ga Manzo (SAW); shi kuwa Manzo (SAW) ya
isar da shi ga duniya, da baki, ba a rubuce ba.
d.
Alƙur’ani na da
surori (114) da Musulmi suka kasa zuwa hijihi/hizufi (60).
e.
Surorin (114) suna da ayoyi (6236) in ba a lisafa da basmala ba, in an sa
ta za su kai (6348), akwai masu cewa, ayoyin (6666) saɓanin daga
karatu ne, ba ƙari ko ragewa
ba.
f.
Kalmomin da suka gina ayoyin (157,935) waɗanda ba a
maimaita ba su ne (5277), harafohin da suka gina kalmomin (668,684).
g.
Nassoshin gaba ɗaya an kasa su gida biyu: saukan Makka da na Madina.
Ƙunshiyar
Alƙur’ani
Alƙur’ani babbar
makaranta ce da duk wani abu da ya shafi ilmi in ya saɓa masa dabirta
ce; in ya yi daidai da shi gare shi ya samo. Daga cikin ƙunshiyar Alƙur’ani ne ilmukan
namu na duniya suka samu taƙama da
cigabansu. Lafiyar ƙwaƙwalwa da zuciya daga cikin Alƙur’ani masana suka gano yadda ake inganta shi. Daga
cikin ƙunshiyar Alƙur’ani za mu yi duba cikin tsarinsa, da zubin
nassoshinsa. Manyan abubuwa da ya kamata a kula daga ciki su ne:
a.
Cikin surorinsa (114) surar da ta fi tsawo da faɗi, ita ce
“Suratul Baƙra” mai ayoyi
(286).
b.
Daga cikin ayoyin surorin Alƙur’ani (114)
surar da ke da ayar da ta fi kowace aya tsawo ita ce “suratul Baƙraa” ayarta ta bashi, aya ta (282).
c.
Surar da ta fi gajere ga tsawo cikin surori (114) na Alƙur’ani ita ce “Suratul Kawsar” ayoyi (3) kaɗai take da.
d.
Surar da ke da basmala biyu daga cikin surori (114) ita ce “Suratul Namal”
sura ta (87) ayoyi na (30) da (90).
e.
Daga cikin surorin Alƙur’ani (114)
akwai ayoyi (15) da ake sujada ga karatunsu guda (4) wajibi ne saura (11)
mustahabbi.
f.
Daga cikin surorin Alƙur’ani (114)
surar da ke da sunan Allah cikin kowace ayarta ita ce, “Almjujadal”.
g.
Sunayen Allah da suka fi mamaye nassoshin ayoyin Alƙur’ani su biyu ne, Al-Ghafur sau (91) da Al-Rahim sau
(72).
h.
Sunan Anabin da ya yawaita cikin Alƙur’ani shi ne
Musa (AS) sau (136) da Annabi Isa (AS) sau (25); shi ya sa Annabi Musa kawai ne
suka yi magana fuska-da-fuska da Allah (SW).
i.
Cikin yardar Allah da ƙaddarowarsa a
cikin “Suratul Tauba” babu sunan “allah” a cikin ayoyinta. Allahu akbar!
Harufan Larabci Cikin Rubutun Alƙur’ani
Alƙur’ani da baki
Allah Ya ba Jibirilu (AS) domin ya sadar da shi ga Annabi (SAW) ga kunnensa
bisa karanta masa shi; shi kuwa shi karantar da duniya shi. Cikin Larabci Jibirilu
(AS) yake karanta wa manzo (SAW), shi kuwa Manzo (SAW) cikin Larabci yake koya
wa duniya. Sanin ba kowane Balarabe ba, kuma ba kowa ke jin Larabci ba, dole a
samu matsaloli cikin karantawa, da rerawa, da yau ake kira (tilawa). Abin lura
a nan shi ne:
a.
Harshen Larabci yana da harufa (28) duka waɗanda ke shiga
cikin kalmomin Alƙur’ani a
karanta su a ji sautinsu.
b.
Larabci a lokacin ba a rubuce yake ba, ko da akwai rubutunsa kaɗan ne ƙwarai.
c.
A rubuce cikin harufan Larabci (28) fiye da rabinsu a fagen furucinsu da
rubutu sun yi kusa da juna sai a samu matsalar fitar ma’ana kamar:
Ø Harafin “ra” iri biyu ne
Ø Harafin “sa” iri uku ne
Ø Harafin “wa” a rubuce iri uku ne
Ø Karafin “ha” iri uku ne
d.
Domin tabbacin ingancin karatu dole sai an yi alamomin da za a gano su,
tare da sanin lokacin Manzo (SA) da Jibirilu (AS) ba a yi su ba.
Wasulan Alƙur’ani
Tabbas! Sayyidina Ali (RA) ya gayyato Abu al-Aswad
al-Du’ali domin sa wa Alƙur’ani wasula.
An yi matakan a matakai daban-daban. Nasarar da aka ci ita ce:
1)
Fara ƙirƙiro ɗigagga ga baƙaƙe na sama da ƙasa:
a)
akwai masu ɗigo ɗaya;
b)
akwai masu ɗigo biyu
c)
akwai masu ɗigo uku
2)
Za mu ga akwai ɗigagga (19) da za mu ce:
a)
Ɗigo ɗaya ga harufa (7)
b)
Ɗigo biyu ga harufa (3)
c)
Ɗigo uku ga harufa (2)
3)
Abin da ya biyo ɗigagga wasula na sama da ƙasa
a)
Wasalin sama
b)
Wasalin ƙasa
c)
Wasulan ƙasa
d)
Wasulan sama
4)
Rufu’a ta biyo daga cikin da nata salo
a)
Na sama ɗaya
b)
Na sama biyu
c)
Rufu’a ba ta zuwa ƙasa sai sama ɗayarta da
biyunta
5)
Zancen Shadda
Shadda shi ne ɗaure harafi
biyu a furce su a baki su zama ɗaya, domin su kasance aya a furuci, amma biyu a rubutu:
6)
Zancen Ɗauri:
A kowane harshe na duniya akwai ɗauri a furuci
da rubutu. A Larabci ɗauri zai kasance da da’ira a sama:
7)
Babbar doka ita ce ta “alif” da aka fara yi a rubuce a littafin Allah, ita
ce:
a)
Alu baƙi
b)
Alu ja (Kowanensu launi ke fayyace shi, jan tawada da baƙa)
A karatu “Alu Baƙi" shi ne
sama, “Alu Ja” ƙasa. Waɗannan dokoki
da alamomi (7) su suka taimaka wajen karatun Alƙur’ani ga dukkanin Musulmin duniya.
Malamin Malaman Duniya
Mutanen da suka biyo bayan saukar Alƙur’ani a duniya, shi ya karantar da su ko da ba su yi
na’am da karatunsa ba. Duk wani abu da za a yi amfani ko aiki da shi, ko wani
abu da yake a bangon duniya an ambace shi cikin Alƙur’ani. Ga wasu ‘yan misalai a ɗan nazarce su
a hankali:
a.
Alƙur’ani ya
ambaci wasu mala’iku da sunayensu, wasu kuma da ayyukansu
b.
Cikin Alƙur’ani Aljanu
29 ya ambata
c.
Sunaye ƙabilu 12 aka
ambata cikin Alƙur’ani
d.
Sunayen tsirrai 22 aka ambata cikin Alƙur’ani
e.
Sunayen gulabe 4 ya ambata cikin Alƙur’ani
f.
Ya ambaci duwatsu sau 67 cikin Alƙur’ani
g.
Ya ambaci itaccen magani 10 cikin Alƙur’ani
h.
Ya ambaci abinci iri 20 cikin Alƙur’ani
i.
Alƙur’ani ya
ambaci yaƙe-yaƙe 7 da ake yi
j.
Ya ambaci laifukan haddi 7 cikin Alƙur’ani
k.
Fiye da ayoyi 200 suka ambaci dabbobi
Wanda Allah Ya hore wa fahimtar Alƙur’ani zai tabbata cewa, littafin Allah bai raga komai
da ke cikin duniya ba, sama da ƙasansa. Wannan
shi ne dalilin yi masa take da MALAMIN MALUNMA.
Gudumawar Nijeriya ga Haɓaka
Tafsirin Alƙur’ani
Aikin farko da Manzo (SAW) ya yi wa Sahabbansa shi ne
fashin baƙin Alƙur’ani da Alƙur’ani da
Hadisansa. Bayanin Sahabban Annabi (SAW) a kan Alƙur’ani shi ne ingantaccen tafsiri. A Afirka ba a rasa
tafsirai a Habasha da Masar da Sudan da Libya da Mauritania da Morocco da
sauransu. A ƙasarmu
Nijeriya da wuya a ce ba a yi shi Gobir da Kabi ba gabanin jihadin ƙarni na 19th. Waɗanda ake da
tabbaci su ne Tafsiran Malam Abdullahi Gwandu guda biyu, Diyaa ul Tawiili da
Kifaayatul Du’afahu. Sheikh Abubakar Gumi ya yi Raddul Azhan, Malam
Ahmed Helele ya yi Fatahul Basir, da sauransu. Fitattun Shehunai da suka
yi tafsiri na baka sun haɗa da Shaikh Nasiru Kabara, Sheikh Dahiru Bauchi, Sheikh
Ibrahim Sharif Saleh, Sheikh Sidi Attahiru Sokoto, Sheikh Malam Umar Bawa
Jangwarzo Gobir da sauransu. Akwai tabbacin cewa, a wannan ƙarni na duniya babu ƙasar da ta fi Nijeriya ta Arewa mahardata Alƙur’ani musamman in an duba a Daular Borno, da Daular
Kano, da Daular Zazzau, da Daular Gwandu. Waɗannan wurare
sun fi ƙasar Saudiyya
da Asiya da Falasɗinu da Indonesia da Aljeriya da Morocco da sauransu.
Mahardata akwai tabban a da a Daular Borno da Zazzau da Kano da Kabi a shekaru
(100) da suka gabata babu gidan da babu mahardaci (Alaramma) kuma babu garin da
babu Gwani kuma babu zamanin da babu Gangaran har yau 2024.
Rubutun Alƙur’ani da Fassara Shi Cikin Wasu Harsuna
Duniyar mutane tana da kimanin harsuna 7500 a yau (2024).
A lokacin Manzo (SAW) yawan harsunan ba su kai haka ba. Abin da magabata da
masana cikin Sahabban Annabi (SAW), da Tabi’ai suke fara shi ne fassara Alƙur’ani zuwa wasu harsuna da ba Larabci ba. An fassara Alƙur’ani cikin harsunan duniya (114). Cikakken fassarar Alƙur’ani an yi shi cikin harsuna (47) na duniya. Fassara
ta farko ita ce wadda Sarki Mansur (961-976) ya yi a ƙarni na 10 da 12. Ya sa fitattun masana su fassara Tafsir
al-Tabari daga Larabci zuwa harshen Persian. Wasu masana na ganin akwai fiye da
Tafsiran Alƙur’ani 2,770.
Daga cikinsu guda 300 kawai aka wallafa. Tafsir na farko shi ne na Muhammad Ibn
Jafar al-Tabari (838-823) wanda ya rubuta Tafsir Al-Tabari. Rubuce-rubucen
Tafsir a duniya ya buɗe ƙofar hardar Alƙur’ani domin fitacciyar hanyar gudanar da tafsir ita ce
yin tafsirin Alƙur’ani da Alƙur’ani.
Fassarar Alƙur’ani a Harsunan Nijeriya
Nijeriya tana da harsuna 500 wanda ya sa ta kasance ƙasa mai harsuna daban-daban a duniya. Ingilishi ne
harshen iko amma manyan harsunanmu sun haɗa da: Hausa,
Yoruba, Igbo, Fulfulde, Ibibio, Kanuri da Tiv. Daga cikin Harsunanmu an fassara
Alƙur’ani da
yawa: A Hausa manyan da suka yi fassarar Alƙur’ani gaba ɗaya akwai:
1)
a.
Sheikh Abubakar Gummi
b.
Sheikh Nasiru Kabara
c.
Farfesa Bello Sa’idu
d.
Farfesa Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu
e.
Wani mafassari da bai faɗi sunansa ba
f.
Fassarar Jami’ar Masar
g.
Cikakkiyar fassara ta baki “Tafsiri/Fashin Baƙi".
2) Reverend Michael Samuel Cole, Alƙur’ani ni ede Yoruba, 1906 Published 1924, Fassara ta
farko a harshen Afirka, da rubutun bokon Yoruba ba Ajami ba.
3) Sheikh Murtala Chukwuemeka a cikin
harshen Igbo da rubutun boko Igbo ba Ajami ba.
4) Fassara cikin Kanuri Shetima Kawoi a
1950s cikin Ajamin Kanuri.
5) Fassarar Nupe Kuranu Tsatsana Ndagi Abdullahi cikin Ajamin
Nupe.
6) Fassarar Fulani (Fulfulde) King
Abdullahi Bin Abdal Aziz Al-Saudi ya wallafa shi cikin Ajami Fulfulde.
7) Aliyu Ibrahim S. Mainagge Fassarar Tafsiri Ibn Kathir
(2018).
8) Wannginoore Maanaaji Qu’laanu Nder Fulfulde (2011).
Gasar Karatun Alƙur’ani
Karatun
Alƙur’ani wata
ibada ce babba a addinin Musulunci. Yadda ya fara a zamanin Manzo (SAW) da
zamanin Sahabbai (RTAM) da baki ake karatu; da shi ake koyar da wanda ya
musullunta baki da baki. Da lokaci ya yi tsawo Musulunci ya barbazu a duniyar
mutane, salon koyar da karantar da Alƙur’ani ya bambanta daga wata ƙabila zuwa wata, ko daga wata ƙasa zuwa wata. A Nijeriya ta Arewa, musamman ƙasar Hausa ga matakin da ake hawa:
a.
Koyar da yaro ko
babba karatun hijihi 1-2 da ka
b.
Koyar da harufan
Larabci a rubuce daga malami daga farfaru zuwa babbaƙu.
c.
Koyar da karatun daga
rubutun da malami ya yi a allo zuwa hizo 2-5
d.
Koyar da yaro rubutu
da hannunsa daga hijihi 1-60.
e.
Koyar da karatun Alƙur’ani daga rubutun da aka yi wa Alƙur’ani kai tsaye (Taƙarali)
f.
Karanta Alƙur’ani daga
farkonsa zuwa ƙarshe ana
kallon nassoshi rubuce a littafi.
g.
Koyar da hardarsa daga farko zuwa ƙarshe tare da
kulawar malami.
h.
Tabbata ya iya harda kai tsaye babu kurakurai ya zama “Alarama”.
i.
Koyar da rubuta Alƙur’ani da
hannu ba tare da an ɗauko shi ba, wato da kai, an zama “Gwani” ke nan.
j.
Rubuta Alƙur’ani sau
bakwai babu kure ga kowane an zama GANGARAM. An ce akwai MAHIRU gaba, babu
tabbas.
k.
Shimfiɗa buzun koyar da Alarama da Gwani bita da biyar ƙididdigar Alƙur’ani.
Tarihin Karatun Alƙur’ani a Fagen Tantance Gwani
Taron
karatun Alƙur’ani a matsayin fagen fito da gwani fitacce a harda,
ba Nijeriya aka fara yin sa ba. An fara yin sa a Indonesia a shekarar 1940s,
aka yi shi a Malaysia 1961, a ƙasar Saudiyya
a shekarar 1980, ita ce musabaƙa ta 44, wato
an fara ta a shekarar 1980 a ƙarƙashin Ma’aikatar kula da harkokin Addini. Sai bayan
shekaru (6) aka fara musabaƙa a Nijeirya
wato 1986. Ga alama, tsoron da Musulmi suka ji na ganin ba a ba Alƙur’ani wani bagiren zama ba a tsawon ilmin boko, suke
ganin dole a yi fito-na-fito ga masu ƙoƙarin taushe Musulmi. Tabban! Ko ba a yaƙe mu da makamai ba, hana Alƙur’ani zama a zukatanmu wata nasara ce babba ga maƙiyanmu a kanmu. Harda tana da shekaru da idan aka zarce
su, da wuya ta zauna garau a ƙwaƙwalwa masu yin ta. Duk wani cigaba da wayewar kai, da
tsaro, da tattalin arziki, aka samu in babu Alƙur’ani ci baya zai biyo baya. Da za a samu mahardata
dubu (1000) aka bincika za a ga fiye da ɗari tara da
saba’in (970) tun suna yara suka koyi hardar suka same ta. Ai ƙwararrun malamai sun ce, ana iya hardace Alƙur’ani cikin shekara 2-5.
Tarihin
Musabaƙa a
Nijeriya
A nawa tunani tushen musabaƙa wasu dabaru ne da jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato. Ta ƙago domin ƙara haɗin kan
Musulmi, ƙarfafa harda
ga yara maza da mata, soke ta’addanci, farfaɗo zuciyar
Musulmi kada jihadi ya yi masa girshi, ɗaukaka
Nijeriya cikin duniyar zamaninta da sauransu.
Shekarun Musabaƙa a Tarihance
S/N |
Jiha |
Hijira |
Shekara |
Adadi |
1. |
Sokoto |
1006AH |
1986 |
3 |
2. |
Borno |
1407AH |
1987 |
1 |
3. |
Kano |
1408AH |
1988 |
3 |
4. |
Oyo |
1409AH |
1989 |
1 |
5. |
Bauchi |
1410AH |
1990 |
3 |
6. |
Plateau |
1411AH |
1991 |
1 |
7. |
Lagos |
1412AH |
1992 |
2 |
8. |
Katsina |
1413AH |
1993 |
3 |
9. |
Niger |
1414AH |
1994 |
1 |
10. |
Kaduna |
1415AH |
1995 |
2 |
11. |
FCT |
1416AH |
1996 |
1 |
12. |
Ogun |
1417AH |
1997 |
1 |
13. |
Adamawa |
1419AH |
1998/1999 |
1 |
14. |
Kwara |
1420AH |
2000 |
2 |
15. |
Sokoto |
1421AH |
2001 |
3 |
16. |
Zamfara |
1422AH |
2002 |
3 |
17. |
Nasarawa |
1423AH |
2003 |
2 |
18. |
Yobe |
1424AH |
2003/2004 |
2 |
19. |
Kebbi |
1425AH |
2004 |
2 |
20. |
Kano |
1426AH |
2005 |
3 |
21. |
Bauchi |
1427AH |
2006 |
3 |
22. |
Kaduna |
1428AH |
2007 |
2 |
23. |
Edo |
1430AH |
2008/2009 |
2 |
24. |
Sokoto |
1431AH |
2010 |
3 |
25. |
Jigawa |
1432AH |
2011 |
2 |
26. |
Katsina |
1433AH |
2012 |
3 |
27. |
Zamfara |
1434AH |
2013 |
2 |
28. |
Jigawa |
14435H |
2014 |
2 |
29. |
Edo |
1436AH |
2015 |
1 |
30. |
Nasarawa |
1437AH |
2016 |
2 |
31. |
Kwara |
1438AH |
2017 |
1 |
32. |
Katsina |
1439AH |
2018 |
3 |
33. |
Gombe |
1440AH |
2019 |
1 |
34. |
Lagos |
1441AH |
2020 |
2 |
35. |
Kano |
1442AH |
2021 |
3 |
36. |
Bauchi |
1443AH |
2021/2022 |
3 |
37. |
Zamfara |
1444AH |
2022 |
3 |
38. |
Yobe |
1445AH |
2023 |
2 |
39. |
Kebbi |
1446AH |
2024 |
2 |
Sakamakon
Bincike
A
farfajiyar addinin Musulunci Alƙur’ani
shi ne Malamin Malanmai wanda duk bai fahince shi ba, ba Malan ba ne ko da ana
kiran sa UZTAZ. Kasancewar Alƙur’ani
tsare a zukatan muminai shi ya hana addininsu ya rafashe. A tarihin tattara
masu addini kowa ya fara karanta addininsa ko ya rena saƙonsa, ina jin a ƙasar Indiya aka fara shi shekaru masu
yawa tun Musulmi ba su yi tunanin tsara musabaƙa ba. An ce, ba su taɓa sa Musulmai ba, sai shekarar aka kira Musulmi
su zo su cika tattare da ba su da yawa a Indiya. Da aka zo suka ce Musulmi ya
fara. Ya hau ya fara da “Suratul Rahman”, da ya kamma kowa ya zauna. Aka kira
na gaba ya ce, wallahi ba zai je a yi dariyarsa ba. Wannan ya sa wasu suka
shiga Musulunci kai tsaye. Wannan ya sa na gano MUSABAƘA wani karatu ne mai koyar da mai
karatu, da maras karatu, karatu. Allah Ya yi muna jagora.
Naɗewa
Ɗaya
daga cikin zambar da Mulkin Mallaka ya yi muna shi ne, haɓaka karatun boko da rusa karatun Alƙur’ani don kar a yi jihadi da su. A
halin da muke ciki yanzu gudunmuwar Alƙur’ani ga rayuwarmu ya fi na boko.
Ta’addanci, da yaƙe-yaƙe, da rushewar tarbiya, da sace-sace, da
yaudara, da ƙabilanci,
da girman kai jahiltar Alƙur’ani
ya haddasa su. Babban mataki da ya kyauta mu ɗauka shi ne, a fere wa Alƙur’ani babban wuri cikin manhajar koyar
da yaranmu tun daga Firamare har ya zuwa Jami’a. Matuƙar ba a yi fito-na-fito da makircin
bokon Ingilishi ba, zaman lafiya ya ƙare a rayuwarmu. Alah Ya yi mana jagora.
Amin.
Manazarta
Adamu, M. (1978). The Hausa factor in West African
history. Zaria: ABU Press.
Ajayi, J. F. A. (1967). One thousand years of West African
history. Ibadan: University Press.
Algar, H. (1980). The Islamic revolution in Iran.
London: Open Press University.
Ali, A. Y. (1968). Translation and commentary of the Holy
Qur’an. Leicester: Islamic Foundation UK.
Bello, M. (1964). Infaq al-Maisur. Cairo:
Dar wa Matba al-Sha’aby.
Buhari, I. (1986). Sahih Albukhaari. Lebanon:
Dar-al-Arabia.
Bunza, A. M. (2023). Bahaushen Salo na
Taskace Alƙur’ani da Kiyayeshe.
Takarda a Makarantar Yara
Mahardata Bunza.
Bunza, A. M. (2024). Karatun Allo Ƙasar Hausa. Takarda, Makarantar Atta’aa’unu Jega.
Clarke, P. B. (1982). West Africa and Islam.
Scotland: Thomson Litho Ltd.
Dokaji, A. M. (1978). Kano ta Dabo Ci Gari.
Zaria: NNPC.
Gada, A. M. (2000). Islamic scholarship in Hausaland from
16th to the 18th C: A case of Katsina, Gobir, Zamfara and Kebbi
(PhD thesis). Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
Gumbi, M. S. (1986). Rayuwar Sheikh Abubakar Mahmud Gumi.
Kaduna: N.N.P.C. Nigeria.
Ilori, A. A. (1978). Al-Islam in Nigeria.
Muhammad, A. Y. (2003). Ilm-Al-Tajwid and Qur’anic recitation
competition in Northern Nigeria (PhD thesis). Usmanu Danfodiyo
University, Sokoto.
Palmer, H. R. (1967). Sudanes memoire (Vol.
III). Frankeass.
Redha, M. (2006). Imam Ali Ibn, Abu Talib the fourth
Caliph. Lebanon: Daarul al Kutbul Ilmiyya.
Tsiga, I. A., & Adamu, A. U.
(Eds.). (1997). Islam and
history of learning in Katsina. Ibadan: Spectrum Books Limited.
Zaharadden, M. S. (n.d.). The place of
mosque in the history of Kano. In Studies
in the history of Kano.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.