Ticker

6/recent/ticker-posts

Hanya Mai Hada Zumuntar Dole: Tsokaci Kan Dangantakar Sana’ar Jima da Wasu Sana’o’in Gargajiya Na Hausawa

Citation: Ibrahim, A. (2025). Hanya Mai Haɗa Zumuntar Dole: Tsokaci Kan Dangantakar Sana’ar Jima da Wasu Sana’o’in Gargajiya Na Hausawa. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 4(1), 24-34. www.doi.org/10.36349/tjllc.2025.v04i01.003.

HANYA MAI HAƊA ZUMUNTAR DOLE: TSOKACI KAN DANGANTAKAR SANA’AR JIMA DA WASU SANA’O’IN GARGAJIYA NA HAUSAWA

Dr. Aminu Ibrahim
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, Katsina
Email: Ibrahim.aminu@umyu.edu.ng
GSM: 08067795891

Tsakure

Dangantaka a tsakanini sana’o’in gargajiyar Hausawa alaƙa ce da ta haɗa sana’o’in ta fuskoki da dama musamman ta yadda suke gudana da kuma yadda hakan yake taimakawa wajen motsa da tafiyar da tattalin arziƙin al’umma. Cikas ga irin waɗannan alaƙoƙin da ke tsakanin sana’o’in Hausawa musamman na gargajiya kan iya durƙushe ko hana gudanuwar wasu sana’oi’in, wanda hakan kan iya haifar da masassara ta tattalin arziƙin al’umma. Babbar manufar wannan muƙala ita ce a yi duba tare da nazarin dangantakar da ke tsakanin sana’o’oin gargajiyar Hausawa da kuma yadda hakan yake taimaka masu wajen biyan buƙatun al’umma. Fito tare da nazarin dangantakar shi zai bayar da damar fahimatar yadda kowace sana’a take dogarau da wasu wajen aiwartar da aikace-aikacenta na yau da kullum. An yi amfani da hanyoyi da yawa wajen tattaro bayanan da suka taimaka wajen rubuta wannan muƙalar da suka haɗa da hirarraki da masu gudanar sana’o’in gargajiya daban-daban. Haka kuma, an tuntuɓi masana, musamman masana al’adu da tattalin arziƙi. Har wa yau, an nazarce rubuce-rubucen da wasu masana suka yi a kan sana’o’in gargajiyar Hausawa. An aza muƙalar a bisa ra’in Alfanun Sassan Al’ada (Functionalism Theory of Culture) don fayyace batutuwan da binciken ya ƙunsa. A ƙarshe, sakamakon binciken ya nuna yadda sana’o’in gargajiya suke tamkar jini da tsoka a tsakankaninsu.

Fitilun Kalmomi: Dangantaka, sana’o’i, gargajiya

1.0 Gabatarwa

Wannan muƙala mai taken “Hanya Mai Haɗa Zumuntar Dole: Tsokaci Kan Dangantakar Sana’ar Jima da Wasu Sana’o’in Gargajiya Na Hausawa” tana ƙunshe da nazari ne a kan dangantakar da sana’o’in gargajiyar Hausawa suke da shi ta fuskar yadda suke gudana ko aiwatar da ayyukansu. A iya kallon wannan dangantaka a matsayin alaƙa ta ƙuƙut wadda ta samar da yanayi irin na-cuɗe-ne-in-cuɗe-ka a tsakanin sana’o’in gargajiya na asali da ake samu a ƙasar Hausa. Ba a yi laifi ba idan aka ce sana’o’in gargajiya na jingine da juna ne ta yadda ɗaya ba zai iya gudanar da ayyukansa ba tare da taimakon wasu sana’o’in ba. Idan aka samu rashin gudanuwar wasu sana’o’i, haka na iya haifar da cikas ko ma rashin gudanar wasu sana’o’in. A dalilin haka ne ake kallon sana’o’in gargajiya a matsayin “tsintsiya maɗorinki ɗaya.” Har wa yau, ana kallon waɗannan alaƙoƙi a matsayen abubuwan da suka sanya sana’o’in a ƙarƙashin inuwa ɗaya, kuma suka zama tamkar zaren carbin da ya haɗa ‘ya’yanta a waje guda. Haka kuma, wannan zumunci ne ya sa duk abin da ya taɓa sana’a ɗaya lalle yana iya haifar da matsala ga saura, ko dai ta kai tsaye ko kuma ta a kaikaice.

2.0 Ra’in Bincike

 An yi amfani da Ra’in “Alfanun Sassan Al’ada” (Functionalism Theory of Culture) wajen gudanar da wannan bincike. An samar da ra’in ne ta kallon yadda al’umma ke zaune a wuri guda, kuma an dubi sassan al’adun mutanen da kuma yadda sassan suke dogara da juna wajen yin aiki. Wannan ra’i ya samu ne sakamakon tarken da masana da manazarta suka yi a kan ra’in “Tsarin Sassan al’ada”. An tsirar da ra’in ne sakamakon wata sabuwar fahimta da wani masanin ra’i mai suna Charles Darwin ya yi a kan yadda abubuwa suke a tsare, kuma suke taimakon juna wajen gudanar da aikace-aikacensu. An fara nazarin tsarin zamantakewa da al’adu da kuma ɗabi’un mutane a shekarar 1939 a makarantar Praque ta ƙasar Faransa. Akwai kuma masu ra’ayin cewa an fara wannan nau’in nazarin a farko-farkon shekara ta 1960 a babban birnin ƙasar Faransa, watau Paris (Ado, 2019:33).

Akwai sana’o’i da dama da Hausawa suke gudanarwa a yankunan da suke zaune, domin tafiyar da rayuwarsu, kuma sana’ar jima na daga cikinsu. Sana’o’in gargajiya da Hausawa ke aiwatarwa suna da hanyoyi da kuma ɓangarorin da ke tafiyar da su. Dukkan sassan sana’o’in gargajiya na dogara da juna wajen tafiyar da aikace-aikacen da suka shafe su. Har ila yau, sana’o’in Hausawa na gargajiya na a bisa wani tsari, kuma gwargwadon yadda kowace sana’ar ke bayar da gudummuwa wajen tafiyar da al’ummar ga baki ɗaya gwargwadon matsayin da take da shi a cikin tsarin zamantakewar al’umma. Kowace sana’a tana da muhallin da al’ada ta ba ta, kuma in aka samu wadda ta kasa sauke nauyinta, kamar yadda ya kamata, to, hakan na iya haifar da cikas wajen gudanar da wasu sana’o’in. Kamar yadda aka sani, sana’o’in gargajiyar Hausawa yawa gare su, kuma dukkansu suna jingine ne da juna wajen aiwatar da aikace-aikacensu. Sana’ar jima da za a yi nazari a kanta, ta dogara da wasu sana’o’i, kamar yadda ita ma wasu suka dogara da ita wajen gudanar da aikace-aikacensu na yau da kullum.

3.0 Waiwaye a kan Ma’anar Jima

Ƙamusun Hausa na CNHN (2006:217) ya fassara jima da “sana’ar fid da gashi daga jikin fata.” Idan aka dubi wannan ma’anar da idon basira, za a iya kwatanta sana’ar jima da aikin raba gashi daga fatar dabba da aka yanka. Irin wannan hidima da ake yi wa fatu ta aiwatar da dabaru ko hikimomin gargajiyar Bahaushe, domin sa fata a cikin yanayin da ake so, shi ake ce wa jima. Wannan bayani da Ƙamusun ya yi a kan sana’ar jima bai wadatar ba, domin a dunƙule ya bayar da shi, sai dai ya agaza sosai wajen sanin abin da ake nufi da jima.

An kuma samu wata ma’anar da wani masani ya bayar a kan ma’anar jima. Ga abin da ya ce:

Jima sana’a ce da ta fuskanci sarrafa fatar dabba. Wannan kuwa yana nufin bin waɗansu hanyoyi, domin raba fata da gashin da ke jikinta, a kare ta daga lalacewa a wani wuri keɓaɓɓe inda ake aikata fatun wanda ake kira majema. Ana sayo fatun ne daga hannun mahauta da ‘yan farauta da ‘yan su. Irin fatun da ake sayowa daga hannun mahauta kuwa, su ne kamar su fatun shanu da awaki da na tumaki da na raƙuma da sauransu, ana kiran waɗannan fatun namun gida (Auta, 2006:197).

Masanin ya dubi jima ne a jiya, watau bai kawo wani abu da yake da alaƙa da zamani ba. Kamar yadda aka sani, babu wata sana’ar gargajiya da zamani bai shiga ya yi tasiri a cikinta ba. Gaza gabatar da bayanai na yadda zamani ya shiga a cikin sana’ar, shi ne ya haifar da babban giɓi ga ita ma’anar.

Sharifai (1990:69) ya fassara sana’ar jima a cikin wani aikinsa da ya yi da:

“Wata sana’a ce da ake aiwatar da ita da fatar dabbobi, inda ita wannan fata za a iya gyara ta a ɗebe gashinta, a mai da ita wani launi kamar ja, ko baƙa, ko shuɗiya, ko rawaya, ko mai ruwan tsirya (koriya), ko kuma a bar ta haka fara da sauransu. Ana kuma iya jeme ta ba tare da an ɗebe gashin ba, don ta yi laushi. Ita kuma wannan fata ana mai da ita mai laushi da taushi don samun sauƙin sarrafawa wajen amfani da ita.”

Idan aka aza wannan ma’ana a bisa faifan nazari, za a fahimci cewa, ma’anar na ƙoƙarin fito da cikakken hoto da ya haɗa dukkan muhimman batutuwan da sana’ar ta ƙunsa. Sai dai kamar yadda ma’anar ta nuna, ba a dubi yadda zamani ya yi tasiri a kan sana’ar ba. An dai fito da bayanai na yadda ake sa fatu a cikin kyakkyawan yanayi ta hanyar gyara. Haka kuma, an ga yadda ake amfani da hikimomi wajen sauya wa fatu launi a gargajiyance. Idan aka yi duba da ma’anonin da aka gabatar, ana iya fassara sana’ar jima da dukkan wani ƙoƙari na gyara fata. Har ila yau, hidimomin da ake yi wa fatu sun haɗa da, cire gashi da kuma raba fatu da wari, domin su amfanu a yayin sarrafa su a wasu aikace-aikacen fatu.

4.0 Sana’a

CNHN (2006:387) ya bayyana kalmar sana’a da, “Aikin da mutum yake yi don samun abinci.” Idan aka dubi wannan ma’anar da ƙamusun ya bayar, za a fahimci cewa, sana’a ita ce duk wani abu da za a yi da hannu ko wani sashe na jiki, domin neman kuɗi ko abinci. Waɗannan aikace-aikace da ake yi da sunan sana’a, ana koyan su ne, watau sai an tarbiyyantar da mai koyo bisa tsare-tsaren sana’ar tare da ba shi horo na tsawon lokaci, kuma sai in ya iya, sannan zai iya cin moriyarta. A irin waɗannan sana’o’i da mutane suke yi ne, ake samun ‘yan gado da kuma ‘yan haye, watau waɗanda suka koya, kuma suka iya, amma ba gado suka yi uwa da uba ba.

5.0 Gargajiya

Kalmar gargajiya kamar yadda Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero ya bayyana, ya fassara ta da, “Ɗabi’a ko wani kaya irin na zamanin da” (CNHN, 2006: 159). Wannan ma’ana tana nuni da duk wani hali ko wasu kayayyaki da ake dangantawa da mutanen da suka rayu a baya, watau tun a zaman farko. A iya cewa duk wani abu da jama’a suka gada daga wajen magabatansu da suka shuɗe da suka haɗa da kaya ko hanyoyin rayuwa da ƙila har yau wasu ke amfani da su ba tare da wani cikakken sauyi ba, to su ake kira da gargajiya. Bunza (2006: xxxii) ya ƙara tabbatar da wannan batu ta bayyana asalin samuwar kalmar, domin ya nuna cewa kalmar ta samu ne daga kalmar gado, inda ta rikiɗa ta koma gadajje, wanda kuma daga bisani ta koma gargajiya.

6.0 Zumunci

CNHN (2006:496) ya fassara kalmar zumunci da, “Kyakkyawar dangantaka ta jini ko ta aure ko kuma ta abota tsakanin mutum da mutum.” Wannan ma’ana da ƙamusun ya bayar yana nuni da alaƙa da jini ko aure ko abota ko kuma maƙwabtaka kan haifar, waɗanda ke sa a samu taimakekeniya a tsakanin su mutanen tare da kawo wa juna ɗauki a duk lokaci da ɗayansu ya buƙata. Bargery (1993:1146) ya bayyana kalmar da, “Relationship by blood or by marriage”. Wannan gudummuwa da Bargery ya bayar ba ya da wani bambanci da ma’anar da aka yi tsokaci a kanta a baya, domin duk suna magana a kan abu guda ne. Dukkan ma’anonin biyu sun fassara kalmar zumunci da alaƙa ko dangantaka da ke tsakanin mutane, wanda ke kusantar da su a matsayin dangi ko ‘yan’uwa.

7.0 Dangantaka a Ma’aunin Nazari

A Ƙamusun Hausa na jami’ar Bayero, an fassara kalmar dangantaka da, “Yan’uwantaka” (2006:95). Haka shi ma Bargery (1993:217) ya fassara dangantaka da, “Relationship,” watau ‘yan’uwantaka idan aka fassara kalmar ya zuwa Hausa. Idan aka dubi waɗannan ma’anonin da ƙamusoshin biyu suka bayar za a fahimci cewa ba wani abu ba ne dangantaka illa ‘yan’uwantaka. Wannan ‘yan’uwantaka za ta iya samuwa ne ta dalilin jini ko auratayya ko kuma maƙwabtaka, kuma suke haifar da dangantaka. Wannan dangantaka ta ‘yan’uwantaka tana taimakawa wajen ƙarfafawa da kuma taimakon juna ta fukoki da dama. Taimakon na iya kasancewa ko dai ta fuskar tattalin arziƙin ko ta tsarin zamantakewar al’umma, kamar su buki da gayya da tallafa wa gajiyayyu, wanda haka yana taimakawa wajen ƙarfafa da yauƙaƙa zumunci da kuma haɗin kan mutane.

8.0 Dangantakar Sana’ar Jima da wasu Sana’o’in Gargajiyar Hausawa

Wasu sana’o’in gargajiyan da al’ummar ƙasar Hausa suke gudanarwa suna da dangantaka da juna tamkar dai yadda ƙullin sarƙa yake a jere, watau suna jinginuwa da juna ne a wajen aiwatar da aikace-aikacensu. Irin wannan yanayin ne yake sa a kasa gudanar da wata sana’ar yadda ya kamata, saboda rashin agajin wata sana’ar. Akwai wasu sana’o’in da kwata-kwata, ba sa motsawa sai da taimakon wasu sana’o’in na daban. Akwai yanayin da ake samu, inda wasu sana’o’in suke samar wa wasu kayayyakin aiki na gudanar da su. Wasu sana’o’in ke taimakawa wajen raba wasu da kayyayakin amfanin da suka samar, wanda in ba su yi haka ba, to hakan na iya nakkasa ko ya sanyaya guiwar su. Haka kuma, ba za a samu yanayin ciniki ba; kuma tattalin arzikinsu ba zai riƙa juyawa ba. A iya cewa, sana’o’in gargajiyar Hausawa bai ɗaya suke tafiya, kuma kowane yana taka rawa wajen rayar da waɗansu sana’o’in. Wannan shi ke nuna cewa, dukkan sana’o’i musamman na gargajiyar Hausawa, na buƙatar juna wajen ci gaba da wanzuwa, kuma abin dogaro ga masu yin su. Sana’ar jima, kamar sauran sana’o’in Hausawa, su ma suna jingine da wasu, kamar yadda wasu ke jingine da ita. Aikacen-aikacen da majema suke yi da kuma kayan amfani da suke samarwa, yana taimakawa wajen aiwatar da wasu sana’o’in na daban. Ga bayanin yadda dangantakar wasu sana’o’in gargajiyar Hausawa suke da sana’ar jima.

8.1 Jima da Ƙira

Sana’ar ƙira da masu iya magana suke yi wa kirari da,” Ƙira dakan maza, ga na safe, ga na maraice”[1], sana’a ce ta ƙarfe kuma daɗaɗɗiya a ƙasar Hausa. Sana’a ce ta sarrafa ƙarfe, domin samar da kayayyakin amfanin jama’a, musamman na gida da kuma na gudanar da waɗansu sana’oin. Wannan sana’ar ta ƙira tana taka rawa wajen rayar da waɗansu sana’o’in gargajiyar Hausawa. Haka kuma, a iya cewa su ne suke tallafe da ƙashin bayan wasu sana’o’in. Yana da matuƙar wahala a samu sana’ar da maƙera ba su bayar da gudummuwa a cikinta ba, wadda gudummuwar da suke bayarwa, ita ta tabbatar da ci gaba da wanzuwar wasu sana’o’in. Babu wani takaimamman lokacin da masu wannan sana’ar ke gudanar da sana’arsu, watau suna iya gudanar da wannan sana’a a kodayaushe, amma sun fi yin ta da safe da kuma rana. Bisa ga al’ada, kamar sauran masu sana’o’in gargajiya na Hausawa, su ma maƙera sukan ɗan ɗaga wa sana’ar a lokacin damina, domin su noma abincin da za su ci a shekara. Ga abin da wani masanin ya ce game da sana’ar ƙira tare kuma da yanaye-yanayenta:

Ƙira sana’a ce wadda aka fi yi a lokacin rani, domin tanadar kayan noma, amma duk da haka ana yin ta a kowane lokaci na shekara, domin samar da kayan amfanin gida na yau da kullum. Maƙera sun kasu zuwa kashi biyu: akwai maƙeran baƙi da na fari. Maƙeran baƙi su ne suke tono tama su kuma narka ta, don ta zama ƙarfe, wanda suke amfani da shi domin yin nau’o’in kayan ƙira. Ire-iren kayayyakin da maƙeran baƙi suke yi sun haɗa da fartanya da masassabi da gatari da lauje da sungumi da adda da sauransu domin yin ayyuksan noma. Haka kuma, suna ƙera takubba da gariyo da tsitaka da masu da kibau da sauran kayayyakin da ake amfani da su wajen yin farauta da yaƙi. Bayan waɗannan suna yin kalaba da ƙanana da manyan wuƙaƙe waɗanda ake amfani da su wajen yin ayyukan cikin gida na yau da kullum (Sallau, 2010: 21).

Idan aka yi duba da waɗannan bayanan da masanin ya bayar a kan sana’ar ƙera, za a ga cewa sana’a ce ta tu’ammali da ƙarfe, watau sana’a ce ta sarrafa ƙarfe. Haka kuma sana’a ce da masu yin ta suke samar da kayayyakin amfani da na aiki ga sauran masu sana’o’in. Wannan sana’ar kamar yadda aka gani, sana’a ce da ake iya gudanar da ita a kowane lokaci da masu sana’ar suka samu zarafi. Haka kuma, masanin ya raba sana’ar ya zuwa gida biyu, inda ya ce akwai maƙeran baƙin ƙarfe da kuma na farin ƙarfe.

Idan ko aka dubi alaƙa ko dangantakar da take tsakanin sana’ar jima da na ƙira, za a ga dangantakar ba ta wuce ta yadda kowanensu yake taimakawa wajen samar da kayayyakin aikin da kowane ke amfani da su wajen gudanar da sana’arsu ba. Wannan abu shi ne babban abin da ya haɗa sana’o’in biyu, kuma suna cin moriyar juna ta wannan fuskar, kuma idan aka kuskura ɗaya bai sauke nauyinsa yadda ya kamata ba, hakan na iya haifar da cikas ga ɗayan sana’ar. Idan muka dubi majema, za mu ga cewa su suke samar da jemammiyar fata da ake haɗawa a samar da zuga-zugi da maƙeran suke amfani da shi wajen hura wutar da ake narka ƙarafa da ita. Kamar yadda aka sani, zuga-zugi na ɗaya daga cikin kayan aikin da ƙira ba zai taɓa yiwowa sai da shi ba, domin shi ke samar da wuta wajen narka ƙarfe. Haka su ma maƙeran, su suke samar da wasu kayayyakin aikin da majema suke amfani da su wajen gudanar da aikace-aikacensu na jeme fatu. Kayan aikin jimar da maƙera suke samarwa, sun haɗa da, kartaji da majema suke amfani da shi wajen raba fata da gashin da yake jikinta. Haka kuma, da kartajin ne ake amfani wajen yin kannin fata, watau kankare ragowar nama da yake maƙalewa a cikin fata. Haka kuma, maƙera suke samar da wuƙa da almakashin da majema suke amfani da su wajen daidaita fatu. Idan aka yi duba, ana iya cewa sana’o’in guda biyu, sun kasance suna taimakon juna wajen samar da kayayyakin da kowanensu yake amfani su wajen gudanar da ayyukansu, kuma tabbatuwar haka, shi ne ya ƙara tabbatar da yadda sana’o’in suke jinginuwa da juna wajen yin sana’o’in a cikin sauƙi ba tare da cikas ba.

8.2 Jima da Fawa

Sana’ar Fawa wadda masu iya magana suke yi wa kirari da, “Ciniki ɗai rana, in ta kwana ta ɓaci.”[2] Sana’a ce ta saye da sayar da nama. Masu sana’ar ake cewa rundawa, watau su ne suke nemo dabba, ko a kawo masu su saya, sannan su yanka su sayar wa al’ummar gari. Sana’ar fawa kamar sauran sana’o’in da aka sani na asali a ƙasar Hausa, daɗaɗɗiyar sana’a ce, kuma masu yin ta amintattun al’ummar gari ne. Ba sa yanka dabba sai wadda suka yarda da lafiyarta, watau ba irin wadda za ta cutar da lafiyar mutane ba, kuma ba sa sayar da mushe, watau naman dabbar da ta mutu. Rundawa suna taka rawa wajen wadata mutane da naman da za su ci. Haka kuma, masu wannan sana’ar, su suke gyara wa mutane nama, watau yanka da fiɗa, da raba nama da ƙashi da sauran hanyoyi na sarrafa nama, kamar sayar da gasashen nama da tsire da kilishi, ko kuma balangu. Ga yadda wani masanin ya fassara sana’ar fawa:

Sana’a ce da ta jiɓinci sarrafa naman dabbobi, wato yanka su da gyara naman da sayar da shi ga mabuƙata. Mai yin wannan sana’a shi ake kira mahauci. Mahauci shi ne wanda aikinsa ya gyara dabba bayan an yanka ta, ya fitar da ƙashi daga tsoka ya rarraba shi gwargwadon yadda ake buƙata. Shi ne kuma yake sayar da da naman, a ɗanyensa ko bayan ya gasa ga mabuƙata masu saye (Tukur, 1994:38-39).

Idan aka yi duba da wannan fassarar, za a ga cewa, mahauci shi ne wanda aka sani da sana’ar fawa wadda take na saye da gyara nama, kuma sukan tsabtace nama su gyara shi gwargwadon buƙatar mutane. Haka kuma, yana samo dabba ya yanka ta, sannan ya sayar da naman, wasu a ɗanyensu zai sayar da su, a yayin da wasu sai ya sarrafa su zuwa yadda masu saye ke buƙata. Bayan wannan aikin da al’ada ta ba su, kuma aka san su da ita, su ne kuma mutane suke nema, don su gyara masu dabbar da suka yanka, domin ci, ko kuma don wani buki ko wani abu na daban. Har ila yau, ana kiran su don su yanka dabbar da suka fahimci za ta gaza. Akwai ‘yan gado waɗanda su gadon sana’ar suka yi daga iyaye da kakanni, kuma ana samun ‘yan haye, watau waɗanda ba gado suka yi ba, illa dai sun shigo cikinta ne, don su ci abinci.

Idan aka waiwayi dangantakar da take tsakanin sana’ar jima da ta fawa, za a ga cewa suna da alaƙa mai ƙarfi, kuma a tare suke tafiya. Akwai rukunin wasu mutane a cikin al’umma da har gobe, ba za su iya rarrabe tsakanin majemi da mahauci ba, watau suna kallon dukkan mahauci majema ne, don ganin yadda suke amsar fatun dabbobin da suka yanka a matsayin tukuicin aikin da suka yi, ko kuma su saya. Har gobe, mahauta mutane suke kai wa fata, domin su saya, kuma suna sayen ta yadda suka ga dama, kuma haka mutane suke sakar masu, domin in ba su saya ba, ba su da inda za su kai ta, su sayar. Su kuma rundawa in sun sayi fatun, majema suke sayar mawa. Haka kuma, suna a matsayin waɗanda suke samar wa majema fatu, kuma suna taka rawa wajen fitar da fatun ta hanyar fiɗa daidai da yadda majema suke buƙata. Fatun da aka samo daga hannun rundawa suna yin daraja sosai ga majema, domin gwanancewarsu a wajen fiɗa. Haka kuma, su majeman ne suke raba rundawa da fatun da suka samo, ko suka sayo, kuma in ba wurin su ba, su ma rundawa ba su da yadda za su yi da fatun, ko su kai a shigar da su da daraja. A kan wannan dalilin ne ya sa suka tsiri wasan barkwanci a tsakaninsu, wanda kowane yake ganin in babu shi, ɗayan ba zai iya tsayuwa da ƙafafunsa ba. Bugu da ƙari, kowanne na tinƙaho a matsayin shi ne ubangida.

8.3 Jima da Dukanci

Sana’ar dukanci, sana’a ce ta sarrafa fata bayan majema sun gama gudanar da nasu aikin. Dukawa tamkar jini da tsoka suke da majema. Dukawa suke sayen jemammun fatu daga wajen majema su juya su ya zuwa wasu kayayyakin amfani irin su jikka da takalma da sauran kayayyakin amfani na gida da dai sauransu. Dukanci daɗaɗɗiyar sana’ar gargajiyan Hausawa ce, kuma yana da matuƙar wahala a iya faɗin lokacin da Hausawa suka fara wannan sana’ar, sai dai a yi kintace. Akwai masu ra’ayin cewa, an fara sana’ar ne tun lokacin da Hausawa suka fara farauta. Farautar dabbobi da kuma yadda suke amfani da fatu wajen neman mafaka daga yanayi na sanyi da kuma suturce jikin, wanda sannu a hankali suka gano wasu dabaru na sarrafa fatun ya zuwa wasu abubuwan, domin biyan buƙatun kansu. Sallau (2010: 20) a cikin littafinsa ya bayar da ma’anar da cewa:

Dukanci sana’a ce wadda ake sarrafa fata don mayar da ita wani abu na amfanin yau da kullum. Ire-iren abubuwan da dukawa suke yi sun haɗa da jikkuna da takalman fata da igiyar linzamin doki da burgami da zabira wadda ake zuba kayan wanzanci da jikkar zuba wa dawaki dawa da dussa. Haka kuma, suna yin warki da gafaka da tandun kwalli da kuben wuƙa da na takobi da sauran abubuwa da daman gaske (Sallau, 2010: 20).

Masanin ya dubi sana‘ar dukanci da sana’ar da ake amfani da fatu wajen yin kayayyakin da suka haɗa da kayan amfanin mutane irin na yau da kullum. A ƙarshe, ya dubi dukawa a matsayin waɗanda suke taimakawa wajen rayar da tattalin arzikin Bahaushe. Irin wannan gudummuwar da suke bayarwa, shi ne ya tabbatar da ƙololuwar ci gaban da Bahaushe ya kai a duniyar sana’o’i na fasahar hannu.

Idan ko aka dubi dangantakar wannan sana’ar ta dukanci da kuma ta jima, za a ga dangantakarsu ta fi ƙarfi fiye da ta sauran sana’o’in da ake alaƙantawa da kowane. Dangantakar da take tsakaninisu ta fi gaban a misalta, domin ana yi wa sana’o’in kallon Hassan da Hussaini, saboda yadda ƙarfin dangantakarsu take. Tabbas! Sana’ar jima ba za ta wanzu a cikin sauƙi ba, ba tare da wanzuwar dukawa ba, su ma dukawan haka. Baduku ne suke raba majemi da fatar da ya jeme, wataƙila a iya cewa ba don baduku ba da majema sai sun rasa yadda za su yi da fatun da suke gyarawa. Su ma dukuwan, in majeman ba su jeme fatu ba, lalle ba za su samu fatun da za su sarrafa ya zuwa wasu kayayyakin da jama’a suke buƙata ba.

8.4 Jima da Kiwo

Kiwo sana’a ce ta kiwata dabbobin gida manya da ƙanana, domin a rene su, su girma, kuma a sayar ko a ci, don a biya buƙatun rayuwa. Bisa ga al’ada, akwai nau’ukan kiwo da aka keɓe wa maza, akwai kuma waɗanda aka keɓe wa mata. Haka kuma, akwai inda suka yi tarayya. Kiwo sana’a ce da take dogara a kan karɓa, watau mutanen da kiwo ya karɓa, a yayin da wasu sana’ar ba ta amshe su ba. Akwai masu sa’ar gaske a sana’ar, inda za a ga dabbobin da suke kiwo suna hayayyafa suna ƙara yalwa. Idan aka fahimci haka ga mutum, sai a ce kiwo ya karɓe shi. Kiwo, kamar sauran sana’o’in gargajiyan Hausawa, daɗaɗɗiyar sana’a ce, da Hausawa suka fara ta tun lokacin da suka fara zama a wuri ɗaya, domin gudanar da rayuwarsu. Kowane gida a ƙasar Hausa, da nau’in kiwon da suke yi, haka kuma, a iya cewa sana’a ce ta gama-gari. Sallau ya bayyana kiwo da sana’ar da:

Hausawa ke tsare dabbobi da tsuntsaye a gidajensu ta hanyar ba su abinci ko kuma a kora su zuwa daji don su ci abinci a can. Ire-iren dabbobin da Hausawa suke kiwo sun haɗa da shanu da tumaki da awaki don cin namansa da kuma sayarwa. Haka kuma, ana sayar da fatunsu da ƙiragansu don yin amfani da su. Ana kuma ɗaukar kashin da suka yi don kai wa gona a matsayin takin da zai ƙara wa gona albarkar ƙasa. Bayan waɗannan dabbobi, Hausawa na kiwon dawaki da alfadarai, don hawa na ƙawa da jin daɗi, ana kuma kiwon jakkai don ɗaukar kaya da yin wasu ayyuka irin su fatauci. Ire-iren waɗannan dabbobi dukkansu ana kiran su da sunan dabbobin gida (Sallau, 2010: 15).

Wannan bayanin ya bayyana sana’ar kiwo da sana’ar killace dabbobi a wuri guda ana ba su abinci ko a riƙa kora su daji ko wurin kiwon da za su samu abinci. Ya ƙara bayyana yadda sana’ar take samar da naman ci ga al’umma da kuma fatun da ake samarwa, domin a samar wa majema da dukawa kayan aiki. Haka kuma, kiwon da suke yi, shi ne yake samar da takin da ake amfani da shi a gonakai. Sana’a ce da take tallafar wasu sana’o’in, ta hanyar samar masu da abubuwan da masu sana’o’in suke buƙata wajen tafiyar da sana’o’insu.

Ta fuskar dangantakar da take tsakanin jima da sana’ar kiwo kuwa, a iya cewa masu sana’ar kiwo ne suke samar da dabbobin da ake yankawa, har mahauta su gyara, sannan majemi ya samu fatun da zai yi amfani da su wajen gudanar da tashi sana’ar. Tun daga matakin kiwo, ake samar da fatu ingantattu masu kyau da za su sarrafu yadda ake so a wajen aikace-aikacen jima. Sai mai kiwo ya yi sana’arsa yadda ya dace, sannan dabbar za ta yi isasshen nama da mahauta ke so, sannan a samu fata mai rai da lafiya da za ta jure wa aikin jima. Wannan ya ƙara tabbatar da rawar da masu kiwo suke takawa wajen wanzuwar wasu sana’o’in wanda jima tana daga ciki. Haka kuma, kasancewar wanzuwar sana’o’i irin su jima da wasu, su ne suka ƙara sa wa sana’ar kiwo ta ƙara armashi da kuma yalwa ta fuskar ƙaruwar riba, saboda babu abin yadawa a sana’ar, tun daga matakin samar da nama da mahauta suke buƙata da fatu da majema da dukawa suke so, don yin sana’o’insu har ya zuwa ga manoma da su ma suke samun takin da suke amfani da shi wajen inganta ƙasar gonakinsu da kuma ƙaruwar albarkar gonar.

8.5 Jima da Wanzanci

Wanzanci da masu hikimar zance suke yi wa kirari da,”Babba da rataye, yaro da rataye, na Inna kashin shanu, da dariya kukan yi mugunta”[3]. Daɗaɗɗiyar sana’a ce a ƙasar Hausa. Sana’a ce ta aske gashin kai a yayin da aka buƙaci hakan. Kodayake, sana’ar wanzanci ba ta taƙaita ga aski kaɗai ba, har wasu aikiace-aikacen suke gudanarwa ga al’umma, da suka haɗa da yin kaciya ga yara ƙanana da kuma yin ƙaho, domin fitar da mataccen jini a jikin mutane. Haka kuma, su ke yin tsaga kowace iri, da ta ɗebe ciwo, da targaɗe, da na shasshawa, da ta al’ada, watau ta kumatu da ta jarirai. Sana’a ce mai asali wanda masu yin ta sun shahara ƙwarai a cikin al’umma. Sana’a ce ta gado da take tattare da fasahohi da kuma hikimomin da suke da matuƙar wahala a iya bayyana wa wanda bai jiɓanci sana’ar ba. Ana samun ‘yan haye, watau waɗanda ba gado suka yi ba, watau su sun koyi sana’ar a wajen ‘yan gado ne. Haka kuma, sun koya, kuma sun iya. Komin yadda ɗan haye ya koyi sana’ar, kuma ya iya, ba zai kai wa ‘yan gado ba. Sallau ya bayyana asalin sana’ar da:

Sana’ar wanzanci ta samo asali ne ta la’akari da buƙatun rayuwar ɗan adam. A dalilin tasowar buƙatu, sai ya ƙirƙiro wa kansa hanyoyin da zai warware su. Ta irin wannan hanya ce, saboda samuwar gashi a ka, ya sa mutum tunanin neman hanyar da zai rage shi ko rabuwa da shi, domin ya sami sauƙi ya kuma ji daɗin rayuwarsa. A taƙaice, a iya cewa, ta wannan hanya ce sana’ar wanzanci ta samo asali har ta bunƙasa ya zuwa matakin da take a yanzu inda har wasu zuri’o’i suka mayar da ita sana’ar gado (Sallau, 2010: 37).

Wannan masanin ya bayyan yadda sana’ar wanzancin ta samo asali da kuma yadda buƙatuwar mutane ta rabuwa da gashi da yake taruwa a ka, ya sa sana’ar ta samu, saboda dai biyan wannan buƙatar. Sana’a ce wadda take da waɗanda ake ce wa ‘yan gado kamar dai yadda aka gani a cikin bayanin matanin da ya gabata, sannan su ne suke gabatar da sana’ar ga al’umma a duk lokacin da aka buƙace su da su gudanar da ita. Wannan yanayin ya sa kowane gida a da, da ma yanzu, a wasu gidajen Hausawa, suke riƙe da wannan tsohuwar al’adar, inda suke da wanzaman da suka ɗora wa wannan hidimar, kuma suke aiwatar da ita a gare su a duk lokacin da buƙatar hakan ta tashi. ‘Yan gadon sana’ar wanzance ne aka sani da wasu tarin sirrin sana’ar wanda da su ne suke bambanta da waɗanda ake yi wa kallon ‘yan haye waɗanda suka shigo domin su ci abinci. Wannan sana’ar na buƙatar gwanancewa kafin a fara cin moriyar ta, kuma shiga ba tare da an san aiki ba, ka iya haifar wa mai sana’ar da gaza cin moriyarta.

Dangantakar sana’ar wanzancin da ta jima bai wuce ta kayan aikin da majema suke samar wa wanzamai ba. Majema ne suke gyara fatun da ake amfani da su wajen yin zabirar da wanzamai suke amfani da ita wajen adana kayayyakin aikin wanzancin irin su aska da kwanon aski da ƙoshiya da fatar washin asaken aski wanda dukawa suke yi. Su ma dukawa daga wajen majema suke samun fatun da suke sarrafawa ya zuwa kayan aikin da wanzamai suke amfani da su. Ire-iren waɗannan ayyukan ne da majema suke gabatarwa ga wanzamai duk da cewa ba kai tsaye suke gabatar da su ga wanzaman ba, amma a ƙarshe wanzaman suke amfana da su. Su ma majema suna amfana da ayyukan da wanzamai suke gudanarwa, domin su ma suna daga cikin rukunnan mutanen da wanzamai suke yi wa hidima.

8.6 Jima da Farauta

Farauta sana’a ce da wasu rukunnan mutane suke yi, domin neman abinci. Wannan sana’a ce ta shiga dazuka, don farautar namun daji, ko kamo su ko harbo naman daji. Ana iya cewa, sana’a ce ta fafatukar neman namun daji a dawa, musamman a lokaci da ba na noma ba, wanda akasarin masu farauta suke fita, domin neman naman da za a ci. Haka kuma, wasu kan shiga can cikin ƙuryar daji, in da ba gari ko gonakai kusa, su nemi namaun dajin. Su kuma irin waɗannan ko cikin damina ne, suna fita, kuma ba su da wata sana’a da tafi ta. Daga mafarauta majema suke samun wasu fatun da suke saya, kuma su jeme saboda mabuƙata. A wasu lokutta kuma mutane ne suke ganin irin fatun daga wajen mafarautan, sai su saya su kai a jeme masu, domin biyan wasu buƙatunsu na musamman. Mutane sukan nemi fatun wasu dabbobin ko wani sashen nasu, domin yin magungunan neman lafiya ko na kariya. Wasu kan buƙaci wasu fatun kamar na zaki ko damisa ko na raƙumin dawa, domin kwalliya. Haka kuma, fatun da mafarauta suke samowa, ba sa zama a yanayin da za a iya aje su, domin kwalliya, har sai an kai wa majema sun gyara, watau sun aiwatar da dukkan matakan da ake aiwatarwa ga fatar da ake son a jeme. Ba a fitar da gashin dabba daga irin waɗannan fatu, domin barin su da gashinsu yana ƙara masu daraja, da kuma ƙima. Ba majema su sarrafa su ta yadda ya dace, shi ne ke sa su yi ƙwari kuma su yi shekaru ba tare da sun lalace ba.

 Dangantakar da take tsakanin majema da mafarauta sananniya ce, saboda yadda suke cin gajiyar juna, musamman idan aka yi duba da irin rawar da kowane yake takawa. Sanin kowa ne cewa a wurin mafarauta majema suke samun wasu nau’ukan fatun da suke jemewa, kamar fatun manyan macizai da na zakuna da na damisa da sauran namun dawa waɗanda dole sai ga mafarauta ake iya samun su. Haka kuma, ga majema kaɗai mafarauta suke iya shigar ko sayar da fatun da suka samo a wurin farauta a cikin mutunci, domin su suka san darajarsu.

8.7 Jima da Su

Sana’ar su da masu hikimar harshe ke yi wa kirari da, “Su cinikin ɗa da ɗa, su cinikin ɗan halal, shege ko ya soma ya fasa[4],” daɗaɗɗiyar sana’a ce wadda Hausawa suka gada tun daga iyayen da kakanni. Sana’a ce mai cike da fasaha da hikima, wanda duk mai son yin ta, sai ya koya. Akwai ‘yan gado waɗanda suka gaje ta kai tsaye daga iyayensu, kuma akwai shigaggu, watau waɗanda suke ‘yan haye. Ana iya danganta wannan sana’a da sana’ar farauta, amma ta cikin ruwa. CNHN, (2006: 399) ya fassara su da, “Farautar kifi a ruwa.” Wannan fassara da ƙamusun ya bayar a kan kalmar, za a fahimci cewa ya danganta ta da aikace-aikacen da suka jiɓanci farautar namun ruwa, musamman kamun kifi da sauran dabbobin ruwa da ake farauta don ci da kuma wasu buƙatu na musamman. Har ila yau, marubutan littafin Labaru Na Da Da Na Yanzu sun ce: “Su wata irin farauta ce ta ruwa wadda ake yi, ana kamun kifi da waninsa” (NNPC, 1968: 20). Kamar dai yadda Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero ya bayyana kalmar, su ma waɗannan marubuta sun danganta sana’ar da farauta ta cikin ruwa da ake yi don kamun kifi da sauran namun ruwa.

Masana sun ta kawo ra’ayoyi mabambanta dangane da tarihin samuwar sana’ar su, amma ra’ayi mafi fice daga cikin ra’ayoyin shi ne wanda Sharifai ya ruwaito a cikin kundinsa da ya gabatar, domin neman digiri na biyu inda bayyana cewa sana’ar ta samu ne tun a zaman farko. Ga abin yake cewa:

Wannan sana’a (su) ta faru ne a sakamakon fafutikar da ɗan’adam yake yi don neman biyan buƙatunsa na rayuwa kamar abinci da muhalli da sutura da ‘yanci da tsaro da motsa jiki da nishaɗi da hutu”. Amma wasu suna ganin asalin wannan sana’a shi ne lokacin da ɗan’adam ya fara zama a guri guda, namun daji suka fara yi masa nisa, sai Allah ya ɓullo masa da wata hanyar ta samun nama, wato kifi. Yadda aka gano wannan shi ne lokacin damuna ruwa kan taru a cikin ramuka, idan kuma damunar ta wuce sai wannan ruwa ya kafe, idan ya kafe sai kawai a ga kifaye, mutane su yi ta kamawa. Kowace shekara haka har jama’a suka sami dabarar kwashe ruwa daga ramukan nan da ruwa kan taru, idan sun ga ruwa ya kusa kafewa. Ana nan ana haka hikima kuma na daɗa ƙaruwa suna ƙara fahimta, har Allah ya sa suka gane wasu hanyoyi da ‘yan dabaru ta hanyar yin amfani da wasu abubuwa don kamun kifi. Daga nan jama’a suka ga amfanin sana’ar (Sharifai, 1990: 46).

Idan aka yi duba da kyau, za a ga kamar dai yadda abin ya kasance ga sauran sana’o’in gargajiyar Hausawa, domin yana da matuƙar wahala a iya faɗin lokacin da Hausawa suka fara gabatar da sana’ar kamun kifi a yankunansu. Tabbas! Ba a yi kuskure ba idan aka ce sana’ar su ta samu ne daga lokacin da Hausawa suka fara kafuwa a wuri guda don tafiyar da rayuwarsu. Kamar yadda tarihin da Sharifai ya kawo, sana’ar ta samu ne a dalilin neman abincin da mutane suka yi a wancan lokaci na zaman farko. Sana’a ce wadda ta danganci farauta, amma ta cikin ruwa.

Sana’ar su na da dangantaka da jima, musamman ta yadda masunta suke samar wa majema da kayayyakin aikin, musamman fatu don gabatar da aikace-aikacensu gyara su da kuma sa su a yanayin da ake buƙata. Fatu na daga cikin manyan kayayyakin aikin da majema suke amfani da su wajen tafiyar da sana’arsu. Kamar yadda aka gani a ma’anar da marubutan Labaru Na Da Da Na Yanzu, suka bayar, sun bayyana cewa ba kifaye kaɗai masunta ke farauta ba, watau har da sauran namun ruwa, kamar su kada da dorinar ruwa da sauran manyan dabbobin da ake samu a cikin ruwa. Idan masunta suka samu nasarar kama irin waɗannan dabbobi sukan sayar da su kai tsaye, ko kuma su gyara su, su fitar da naman don ci da kuma sayarwa. Idan suka ɗebe naman, sukan sayar da fatun, musamman ga majema don su gyara su. Ta ɓangare majema kuwa, a iya cewa su ke raba masunta da fatun dabbobin ruwan da suka farauto. Yin haka yana taimakawa wajen ƙara yi wa masu sana’ar su ƙaimi tare da ƙara inganta tattalin arziƙinsu, wanda haka ka iya bunƙasa sana’ar tare da raya ta. Ta la’akari da tsokacin da aka yi, za a fahimci cewa kowanensu na dogara da juna ta fuskar tattalin arziƙi, kuma kowane na bayar da tasa gudummawa wajen tafiyar da aikace-aikacen juna.

9.0 Sakamakon Bincike

Bisa ga al’ada na kowane irin aiki, akwai batutuwan da suke biyo baya, watau bayan an kammala bincike, waɗanda suke zama sakamakon binciken da aka gano. Ana danganta sakamakon bincike da abin da mai nazari ya gano, kuma yake tamkar gudummawar da aka bayar ta fuskar ilimi. Wannan muƙala da aka rubuta ta gano abubuwa da suka haɗa da:

Da farko, sakamakon binciken ya nuna yadda sana’o’in gargajiyar Hausawa suke tamkar jini da tsoka ta fuskar dangantaka da ke tsakaninsu. Kowace sana’a tana jingine ne da sauran sana’o’in gargajiya da ake aiwatarwa a ƙasar Hausa. An kuma gano cewa duk sana’ar da aka gaza alaƙanta ta da sauran sana’o’in da Hausawa suke yi, za a dube ta a matsayin baƙuwar sana’a, watau sana’ar da ta shigo bayan da Hausawa suka haɗu da waɗansu al’ummomi na daban.

10.0 Kammalawa

Wannan takarda ta yi tsokaci ne a kan dangantakar sana’o’in gargajiyar Hausawa da kuma yadda zumuncin sana’o’in yake taimakawa wajen gudanar da aikace-aikacensu da kuma wanzuwarsu. Dukkannin sana’o’in da Hausawa suke yi a ƙasar Hausa, suna da matuƙar kusanci da juna ta yadda dole sai wasu sun sauke nauyinsu ta hanyar aikace-aikacensu, sannan wasu ke samun sukunin gabatar da nasu, wanda akasin haka ka iya durƙusar da wasu sana’o’in. Haka kuma, wannan zumunci na daɗa nuna yadda dukkan ilahirin sana’o’in gargajiyar Hausawa suke jingina da juna ta fuskar yadda suke gabatar da ayyukansa. An kawo wasu sana’o’in aka kuma yi ƙoƙarin fito da alaƙar da ke tsakaninsu da juna. Takardar ta nuna duk sana’ar da aka gaza samar mata da gurbi a wannan ma’aunin awo, to ana iya kallon ta a matsayin baƙuwa da baƙi ko zamani suka kawo.

Manazarta

Anagbogu, I. (1986). “The History of Indigenous Leather Industry in Sokoto And Kano, Northern Nigeria. 1903-1960” Ph.D. Thesis. Centre of West African Studies and Faculty of Arts. Birmingham: University of Birmingham.

Auta, A.L. (1986). “Jima Sana’ar Sarrafa Fata da Muhimmancinta a Ƙasar Hausa.” Kundin Digiri na Farko. Sashen Harsunan Nijeriya. Kano: Jamiar Bayero.

Bargery, G.P. (1993). A Hausa-English Dictionary and English-Hausa Vocubulary. Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited.

Bara’u, B. (2019). “Sana’ar Dukanci da Muhimmancinta a Ƙasar Zakka Jiya da Yau.” Kundin Digiri na Farko. Sashen Harsunan Nijeriya. Katsina: Jamiar Umaru Musa Yar’adua.

C.N.H.N. (2006). Ƙamusun Hausa. Kano: Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero

Garba, B.L. (2015). “Sana’o’in Hausawa na Zamani.” Kundin Digiri na Ɗaya. Sashen Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.

Rimmer, E.M da Wasu. (1966). Zaman Mutum da Sana’arsa. Zaria: Northern Nigeria Publishing Company.

Sallau, B.A. (2009). “Sana’ar Wanzanci da Sauye-Sauyen Zamani Jiya da Yau.” Kundin Digiri na Uku. Sashen Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.

Sanda, U.M. (1999). ”Sana’ar Su a Madatsar Ruwa ta Kainji.” Kundin Digiri na Ɗaya. Sashen Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Ɗanfodiyo.

Sharifai, B. I. (1990). “Take da Kirarin Sana’o’in Gargajiya: Nazarin Ma’anarsu da Muhimmancinsa Ga Rayuwar Hausawa.” Kundin Digiri na Biyu. Sashen Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.



[1] Domin ƙarin bayani a dubi kundin digiri na biyu wanda Sharifai (1990:98) ya gabatar mai taken “Take Da Kirarin Gargajiya: Nazarin Ma’anarsu Da Muhimmancinsu Ga rayuwar Hausawa” na sashen koyar da harsunan Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero.

[2] Domin ƙarin bayani a dubi kundin digiri na biyu wadda Sharifai (1990:84) ya gabatar mai taken “Take Da Kirarin Gargajiya: Nazarin Ma’anarsu Da Muhimmancinsu Ga rayuwar Hausawa” a sashen koyar da harsunan Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero.

[3] Domin ƙarin bayani a dubi kundin digiri na biyu wadda Sharifai (1990:31) ya gabatar mai taken “Take Da Kirarin Gargajiya: Nazarin Ma’anarsu Da Muhimmancinsu Ga rayuwar Hausawa” a sashen koyar da harsunan Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero.

[4] Domin ƙarin bayani a dubi kundin digiri na biyu wanda Sharifai (1990: 84) ya gabatar mai taken “Take Da Kirarin Gargajiya: Nazarin Ma’anarsu Da Muhimmancinsu Ga rayuwar Hausawa” a sashen koyar da harsunan Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero.

Post a Comment

0 Comments