Citation: Inusa, S. (2025). Nazarin Rikiɗar Wasu Sautukan Harshen Ngizim Zuwa Hausa. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 4(2), 10-18. www.doi.org/10.36349/tjllc.2025.v04i02.002.
NAZARIN RIKIƊAR WASU SAUTUKAN HARSHEN
NGIZIM ZUWA HAUSA
Daga
Sa’adu Inusa
Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, Katsina
Email: saadgash@gmail.com
Phone: 08036768267 or 08022701031
Tsakure
A duk lokacin da aka samu wata
cuɗanya ta mu’amala tsakanin harsuna
mabambanta guda biyu, akan samu harshe mafi tasiri a tsakaninsu. Irin wannan dangantaka
ta tsakanin harsuna, ita takan sa harshe mafi tasiri ya yi naso har ya kawo wasu
sauye-sauye a wani ɓangare na harshe abokin mu’amalarsa mai ƙarancin ƙarfin tasiri. Harshen Hausa da
na Ngizim, harsuna ne da suke da ƙullalliyar alaƙa ta asali ɗaya da kuma ta mu’amala bisa tsarin
zamantakewa. Manufar wannan bincike ita ce, nazartar irin rikiɗar da wasu sautukan Ngizim sukan
yi ta hanyar narkewar furucinsu na asali zuwa wasu na daban a Hausa. Dangane da
hanyoyin gudanar da binciken, an yi amfani da dabarar tatsar bayanai daga ‘yan asalin
harshen Ngizim ta hanyar sauraron maganganunsu a muhallai daban-daban da kuma karantawa
daga wallafaffun littattafai da takardu na masana domin tantancewa da ma kafa hujja
a kan bayannan da aka tatsa. Haka nan, Ra’in Tsarin Sauti Ɗan Tsirau (Theory of Generative Phonology) na Chomsky da Halle,
(1968) da kuma Ra’in Cuɗanya (Contact Theory) na Uriel Weinreich (1953) su aka yi
amfani da su a matsayin ra’in da aka ɗora binciken a kai. Bugu da ƙari, binciken ya gano cewa, wasu
keɓaɓɓun sautuka a harshen Ngizim kamar
/ə/ da /dl/ da /tl/ da kuma /zh/
suna rikiɗa zuwa wasu sautuka na harshen
Hausa sakamakon ƙarfin tasirin da harshen na Hausa ya yi a kan na
Ngizim.
Fitilun Kalmomi: Rikiɗa, Tsarin Sauti, Tasiri, Cuɗanya, Furuci
1.0 Gabatarwa
Harshe abu ne wanda yake rayuwa
kwatankwacin rayuwa irin ta ɗan’adam. Hakan yana nuna cewa rayuwar harshe ba ta yiwuwa sai da ta
ɗan’uwansa, kuma yakan rayu tsawon
wani lokaci sannan yakan iya mutuwa. Sai dai, harshe ba ya mutuwa irin ta fuju’a
kamar yadda take kasancewa a rayuwar ɗan’adam. Mutuwar harshe takan faru ne mataki-mataki,
har mai aukuwa ta afka masa baki-ɗaya (Mutuwa) (Crystal, 2000). Saboda haka, a duk
lokacin da aka samu wata cuɗanya ta mu’amala tsakanin harsuna mabambanta guda biyu, akan samu harshe
mafi tasiri a tsakaninsu. Irin wannan dangantaka ta tsakanin harsuna, ita takan
sa harshe mafi tasiri ya mamaye abokin mu’amalarsa mai ƙarancin ƙarfin tasiri wanda sannu a hankali
yana kai ga sauyin harshe. Bayan wani ɗan lokaci, wannan matsin lamba ta sauyin harshe
tana haifar wa wannan harshe mai ƙarancin ƙarfin tasiri ya fuskanci barazanar
mutuwa har ma ya kai ga mutuwar kacokam. Ita kuwa barazanar mutuwar harshe a halin
yanzu, al’amari ne da yake cigaba da ɗaukar hankalin masana da manzarta kasancewarta matsala
ce da take cigaba da ruruwa kamar wutar daji. Crystal (2000), ya bayyana cewa cikin
sama da harshe 6,000 da ake da su a duniya, guda 600 ne kacal suka hau tudun-mun-tsira.
Wannan yana nuna cewa, barazanar mutuwar ƙananan harsuna musamman waɗanda manyan harsuna suka yi irin
wannan tasiri a kansu, matsala ce da ta ratsa kusan kowane lungu da saƙo na duniya. Amma duk da haka,
masu ruwa da tsaki ba su ba wa wannan matsala ta mutuwar harsuna irin kulawar da
ta dace da ita ba domin ceto su waɗannan ƙananan harsuna daga wannan barazana.
Saboda haka, cikin sama da harshe 400 da muke da su a Nijeriya, ƙananan harsuna da dama suna fuskantar
wannan barazana ta rage ƙarfin amfani da su, wadda ta jefa su cikin barazanar mutuwa, ciki har
da harshen Ngizim a Jihar Yobe. Irin wannan alaƙa ta tsakanin manya da ƙananan harsuna, ita ake ganin
ta haifar da rikiɗar da wasu sautukan harshen Ngizim
suke yi ta hanyar narkewa su bi tsari da kuma furuci irin na wasu sautukan Hausa,
kamar yadda maƙalar ta ƙudiri aniyar dubawa. Domin masu iya magana sun ce "somin hauka,
zubar da yawu". Kalmar tasiri a nan, tana nufin yin rinjayen da harshen Hausa
ya yi a kan harshen Ngizim ta fuskar amfani da shi wajen mu’amala. Harshen Ngizim,
kamar harshen Hausa, harshe ne daga harsuna iyalan Cadi ta yamma a ƙarƙashin wani babban gidan harsuna
na Afirika da Asiya (Afro-Asiatic). Dangane da cuɗanya tsakanin Hausawa da Ngizimwa kuwa, ta samo asali ne tsawon
shekara kamar ɗari da suka wuce sakamakon zuwan Hausawa garin
Pataskum domin kasuwancin gyaɗa, Laver,
(1976) a cikin Abubakar, (2015).
3.0 Tsarin Sauti
Wannan wani
fage ne na nazari da ya shafi yadda harshe yake harhaɗa sautukansa na magana cikin wata keɓaɓɓiyar ƙa’ida. Saboda haka, a duk wani sautin
magana na kowane harshe akan yi amfani da mafurta mai motsi ko marar motsi yayin
samar da shi. Alal misali a harshen Hausa, yayin furta sautin /d/ tsinin harshe;
a matsayin mafurta mai motsi, take haɗewa da hanƙa; a matsayin mafurta marar motsi,
sannan sai a samu tsukewar tantanan maƙwallato domin kasancewar sautin
mai ziza ne.
Dangane da wannan, masana sun
tofa albarkacin bakinsu kamar yadda Sani, (1999) ya nuna cewa tsarin sauti yana
ɗaya daga cikin fannoni daban-daban
da suka danganci kimiyyar harshe. Sannan ya ƙara da bayyana cewa tsarin sauti
ya shafi yadda harshe yake harhaɗa sautukansa bisa ƙa’ida ya samar da ma’ana. Shi
ma Crystal, (2008) ya kalli tsarin sauti a matsayin ɗaya daga cikin rassan kimiyyar
harshe wanda ya shafi yadda mutum yake sarrafa sautuka a bakinsa.
3.1 Sautukan Harshen Ngizim
Harshen Ngizim yana da adadin
sautukan magana mabambanta waɗanda aka shigar a matsayin jagorori na ƙamusun da harshen yake amfani
da su guda talatin da uku (33). Wannan adadi shi ne wanda binciken Schuh, (2004)
ya tabbatar da su kamar haka: /ə/, /a/, /b/, /ɓ/, /c/, /d/, /dl/, /ɗ/, /e/, /f/, /g/, /h/, /i/, /j/, /k/, /l/, /m/,
/n/, /o/, /p/, /r/, /r/, /s/, /sh/, /t/, /tl/, /u/, /ɓ/, /w/, /y/, /‘y/, /z/, /zh/.
Saboda haka, cikin wannan adadi na sautuka da aka ambata, an samu wasula guda 6
kamar /ə/, /a/, /e/, /i/, /o/ da /u/ waɗanda aka yi amfani da su a matsayin
jagorori cikin ƙamusun.
3.1.1 Jadawali na I: Misalan Kamancin Baƙaƙen Hausa
Da Na Ngizim Cikin Kalmomi
1. |
/b/ |
bango: |
wall |
/b/ |
bo:nè |
wàhalà: |
difficulty
|
2. |
/ɓ/ |
ɓatà: |
lost |
/ɓ/ |
ɓə̀ɓə̀lu |
ɓulɓùla: |
flow out
|
3. |
/c/ |
càrbi: |
rossery
|
/c/ |
cìmu |
rufè: |
close |
4. |
/d/ |
da:ma |
right |
/d/ |
darò:ta: |
riƙè: |
retained |
5. |
/ɗ/ |
ɗa:kì: |
room |
/ɗ/ |
ɗu:ya:k
|
kò:go: |
cave |
6. |
/f/ |
fita |
get out
|
/f/ |
fùwu |
sàuka |
get down
|
7. |
/g/ |
gànga: |
drum |
/g/ |
gə̀rìɗ |
kò:go: |
cave |
8. |
/gw/ |
gwa:ɓi: |
huge |
/gw/ |
gwamàk |
rà:go |
ram |
9. |
/h/ |
hannu: |
hand |
/h/ |
hù:mà |
hammà:
|
yawning
|
10. |
/j/ |
jìki: |
body |
/j/ |
jəgə̀na: |
kuncì: |
cheek |
11. |
/k/ |
ka:mà: |
catch |
/k/ |
kàsàktu
|
yàrda |
consent |
12. |
/kw/ |
kwa:kwà: |
coconut |
/kw/[1] |
kwàryu |
ca:ra: |
crow |
13. |
/l/ |
lallèe |
henna |
/l/ |
lifə̀r |
shàiɗan |
devil |
14. |
/m/ |
matsàa |
sƙueeze |
/m/ |
mugùrə̀m |
tàusàyii |
mercy |
15. |
/n/ |
neesà |
far |
/n/ |
nənuwaa |
inuwàa |
shade |
16. |
/r/ |
rabàa |
separate |
/r/ |
ràruu |
kiràa |
call |
17. |
/r/ |
kàrtaa |
scratch
|
/r/ |
raadləmà |
reediyòo |
radio |
18. |
/s/ |
saanìyaa |
cow |
/s/ |
sàamaɗàri |
shàazumamì |
sugar ant
|
19. |
/sh/ |
shìnkaafaa |
rice |
/sh/ |
shau |
kaashii |
excrement |
20. |
/t/ |
tàfi |
go |
/t/ |
tuubì |
tuuba |
repentance
|
21. |
/w/ |
waaƙàa |
song |
/w/ |
wùsu |
kumbùraa |
swell up |
22. |
/y/ |
yankàa |
slaughter |
/y/ |
yinɗà |
rantsuwaa |
oath |
23. |
/’y/ |
‘yan’uwaa |
relatives |
/‘y/ |
‘yawu |
hàifaa |
give birth |
24. |
/’/ |
ɗa'àa |
discipline |
/’/ |
o'o |
aa’àa |
no |
25. |
/z/ |
zaunàa |
sit down |
/z/ |
zə̀gar |
arèewa |
north |
(Newman, 2007)
A wannan jadawali na farko, an
nuna irin baƙaƙen da harshen Ngizim yake amfani da su wajen samar da kalmominsa na
yau da kullum. Haka nan, a ɗaya ɓangaren an yi ƙoƙarin kawo makamantan waɗannan baƙaƙe, waɗanda Hausa ita ma a nata ɓangaren, take amfani da su wajen
samar da nata kalmomi. Cikin wannan jadawali, an samu baƙaƙe mabambanta guda 25 waɗanda harshen Ngizim da na Hausa
suka yi tarayya a kan su tare da misalan kowane baƙi cikin kalmomi.
3.1.2 Jadawali na II: Misalan Kamancin Wasulan Hausa Da Na Ngizim Cikin
Kalmomi
SN |
Sauti |
Kalma (Hausa) |
Ma’ana |
Sauti |
Kalma (Ngizim) |
Hausa |
Ma’ana |
1. |
/a/ |
àgògo |
watch |
/a/ |
àgwai |
ƙwai |
egg |
2. |
/aa/ |
faatàa |
skin |
/a:/ |
àalân |
tuutàa |
banner
|
3. |
/ai/ |
Àikee |
sent |
/ai/ |
àiwà |
duhùu |
darkness
|
4. |
/au/ |
audùgaa |
cotton
|
/au/ |
àuɗu |
kabàrii |
grave |
5. |
/e/ |
eh |
yes |
/e/ |
deedù |
kawo |
bring |
6. |
/e:/ |
Teelàa |
tailor |
/e:/ |
rèetà |
rabàa |
divide |
7. |
/i/ |
imaanìi |
blief |
/i/ |
iyàaka |
iyàakaa |
boundary |
8. |
/ii/ |
kiifii |
fish |
/i:/ |
giinà |
rìgìngìnee |
lying on
the back |
9. |
/o/ |
shigoo |
enter |
/o/ |
o'ò |
aa’àa |
no |
10. |
/oo/ |
koofìi |
cup |
/oo/ |
daròota: |
riƙèe |
retained
|
11. |
/u/ |
Ùbaa |
father |
/u/ |
ùzər |
karfàa |
of bad
luck |
12. |
/uu/ |
buutàa |
cattle |
/uu/ |
dùuzhi |
muujìyaa |
owl |
(Newman, 2007)
Amma a wannan jadawali na biyu,
nuna irin wasulan da harshen Ngizim yake amfani da su wajen samar da kalmominsa
na yau da kullum aka yi. Bayan haka, binciken ya yi ƙoƙarin kawo makamantan waɗannan wasula, waɗanda hatta a Hausa ana amfani
da su wajen samar da kalmomi. Kamar yadda jadawalin ya nuna, an samu wasula mabambanta
juna guda 12 waɗanda harshen Ngizim da na Hausa
suka yi tarayya a kan su tare da misalan kowane wasli cikin kalmomi.
3.1.3 Jadawali na III(a): Misalan Sautukan Hausa Waɗanda Babu Su A Ngizim Cikin Kalmomi
Lamba |
Sauti |
Kalma (Hausa) |
Ma’ana |
1. |
/fy/ |
fyàaɗee |
rape |
2. |
/ts/ |
tsaatsàa |
rust |
3. |
/ƙ/ |
ƙàraamii |
small |
4. |
/ky/ |
kyâu |
beauty |
5. |
/ ƙy/ |
ƙyànƙyasàa |
hatching |
6. |
/gy/ |
gyaaraa |
repair |
7. |
/ƙw/ |
ƙwàara |
cheat |
8. |
/л/ |
hanyàa |
road |
9. |
/ŋ/ |
gàngaa |
drum |
10. |
/ui/ |
guiwàa |
knee |
(Newman, 2007)
To amma wannan jadawali na III(a)
cikin wannan bincike, shi kuma nuna irin sautukan da akan iya samu a harshen Hausa
jadawalin ya yi. Bugu da ƙari, an nuna misalan irin waɗannan sautuka cikin kalmomi dalla-dalla domin haskakawa.
Amma duk da yadda binciken ya kawo misalan irin waɗannan sautuka, an samu wani daga
cikinsu, wato wasalin /ui/ wanda ko a harshen Hausa wasu masana suna tababar kasancewa
ɗaya daga cikin wasulan na Hausa.
3.1.3 Jadawali na III(b): Misalan Sautukan Ngizim Waɗanda Babu Su A Hausa Cikin Kalmomi
SN |
Sauti |
Kalma (Ngizim) |
Hausa |
Ma’ana |
1. |
/ə/ |
àzəm |
cìyaawàa |
grass |
2. |
/dl/ |
dlàgdu |
ràatsee |
move aside |
3. |
/tl / |
tlàkàtu |
laalàace |
spoiled |
4. |
/zh/ |
zhà |
yaaƙìi |
war |
5. |
/p/ |
pə̀lùutu |
ragèe |
reduce |
Sannan binciken a cikin wannan
jadawali mai lamba ta IIIb, ya nuna wasu keɓaɓɓun sautuka na harshen Ngizim wanɗanda babu su a Hausa kasancewar
kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi idan aka kwatanta da irin sautukan wasu harsuna.
4.0 Manufar Bincike
Babbar manufar wannan bicike ita
ce, bayyana al’amuran da suka shafi rikiɗewar wasu sautukan harshen Ngizim zuwa wasu sautuka
na Hausa. A ƙarƙashin wannan babbar manufa, takardar ta yi bayanai tare da misalai a
kan muhallai da kuma dalilai da suke sa wasu mabambanta sautukan harshen Ngizim
suke canza lafazi su koma wasu sautuka na daban da suka fi zama na harshen Hausa.
5.0 Hanyoyin Gudanar Da Bincike
Yayin
tattara bayanan gudanar da wannan bincike, an yi amfani da muhimman hanyoyi guda
biyu. Da farko, an samu bayanai daga tushe (Primary Data) ta hanyar shiga a dama
da mai bincike da kuma sauraro a fakaice na hirarraki tsakanin al’ummar Gizimawa
domin lura da yadda suke furta wasu sautuka na harshen yayin zantuttukansu na yau
da kullum. A irin waɗannan muhallai
na tattaunawa tsakanin ‘yan asalin harshen Ngizim; kamar gida da kasuwa da masallaci
da makaranta, an ziyarce su a unguwanni daban-daban na garin Pataskum da kuma ƙyauyukan da suke wajen garin. A irin wannan tattaunawa, an
zaɓi mutum 15 tsakanin
maza da mata daga shekara 15 zuwa 55. A yayin zaɓin waɗannan mutane, an yi amfani da dabarar zaɓi na Kan-Mai-Uwa-Da-Wabi wanda ya shafi tsari
na ɗauki ɗaiɗai na mutanen da aka yi nazari a harshen nasu (Ngizim). An
yi haka ne da nufin tattaunawa da su da kuma sauraron hirarrakinsu domin zaƙulo irin waɗannan sautuka da suke rikiɗa su canza lafazi domin nazarinsu a muhallai daban-daban.
Sai kuma hanya ta biyu, a nan binciken ya karanta daga wallafaffun takardu masu
nasaba da tsarin sauti kamar Newman, (2000) da Sani, (2011) domin kafa hujja yayin
nazartar tararrun bayanan binciken.
6.0 Ra’in Bincike
Akwai ra’o’i da dama waɗanda akan iya amfani da su wajen
nazarin wannan bincike, walau a ɗaiɗaikunsu ko kuma ta hanyar gwama su a lokaci guda.
Saboda haka, binciken ya zaɓi yin amfani da ra’o’i guda biyu, wato Ra’in Tsarin Sauti Ɗan Tsirau (Theory of Generative
Phonology) na Chomsky da Halle (1968) da Ra’in Cuɗanya (Contact Theory) na Uriel Weinreich (1953). An yi hakan
ne saboda ganin cewa dukkanin ra’o’in guda biyu kowane mizani ne na awon wannan
bincike a nasa ɓangaren. Wannan ikirari, Kenan (2008) ya tabbabtar da shi a cikin
Abdurrahaman (2019) inda ya nuna cewa, “Ra’i zaren tunani ne wanda za a iya yin
amfani da shi domin nuna irin abubuwan da ke aukuwa a duniya. Wato dai Ra’i, wani
al’amari ne da ake amfani da shi, a cikin bincike na ilimi wanda yake taimakawa
a cim ma samun kyakkyawan sakamakon bincike.
Ra’in Tsarin Sauti Ɗan Tsirau (Theory of Generative Phonology) na Chomsky da Halle
(1968) ra’i ne da aka yi amfani da shi domin haska wannan bincike wajen samun madogara.
Ra’in ya samu goyon bayan masana da dama irin su Greenberg (1970) da Stephen da
Anderson (1985) da Ladefoged (2001) da Scobbie da Smith (2006), da makamantansu.
Dangane da alƙiblarsa kuwa, ra’i ne da yake bayanin yadda ake samun sautuka a harshe
suke tsira daga wasu mabambantan sautuka. Haka nan, ra’in yana bayyana irin matakai
da sauye-sauyen da sautukan da suka tsira suke hawa, ta fuskar ƙirar ɓoye da ta sarari (underlying and
surface representation). Manufa, ra’in yana nuna mabambantan matakan da aka samu
sauyawar kalma tare da bayanin irin abin da ya faru a kowane mataki. A nan ne ake
fayyace zahirin yadda kalma take a fili; wato mataki na ƙirar ɓoye, sannan a zahirin yadda al’umma
suke furta kalma da kuma yadda suke sauraron ta. Bayan haka, ra’in ya yi bayanin
yadda ake amfani da matakai guda biyu na tantance matsayin sautuka ta amfani da
alamar tarawa ko ɗebewa (+/-) domin fito da sifofi
ko sigogin sautukan da ake magana a kan su.
A ɗaya ɓangaren kuwa, Ra’in Cuɗanya (Contact Theory) na Uriel Weinreich (1953) ra’i ne da aka yi amfani da shi a kan harshen nan na nahiyar Turai; wato Norwegian da Amurka. Daga cikin ƙudurorin ra’in, akwai cuɗanyar harsuna daga sassa daban-daban, wanda hakan kan haifar da tasirin harsuna bisa juna, ko kuma wani harshe ya yi tasiri bisa wani ko wasu. Bisa irin wannan dalili na cuɗanya tsakanin harsuna har takan sa a samu aron kalmomi a tsakaninsu. Manazarcin, ya ci gaba da bayyana ƙudurorin ra’in kamar yadda yake cewa, cuɗanyar harsuna na samar da yin amfani da “Creole” da kuma Buroka a tsakanin al’ummu masu mu’amala. Har ila yau, daga cikin ƙudurorin ra’in, akwai sirki da hargitsa balle, wato sirka kalmomin wani harshe a cikin wani domin isar da saƙo. Bayan haka, manazarcin ya tabbatar da wannan ikirari nasa ta hanyar nuna yadda harshen Chana da na Japan inda ake samun sirka kalmomi harshen Chana a cikin harshen Japan a lokutan cuɗanya. Wannan ra’i na cuɗanya ya samu goyon bayan manazarta irin su Haugen (1972) da Wardhaugh (1972) waɗanda suka yi bayanin yadda harsuna suke cuɗanya da junansu ta hanyoyi daban-daban. Hakan yana ƙara tabbatar da cewa akan samu cuɗanyar harsuna mabambanta a wuri guda wanda yakan kai ga tasirin wani harshe a kan wani ta fuskoki daban-daban. Bisa wanan dalili ne ra’ain ya samu karɓuwa wajen masana da manazarta wanda har a nan cikin gida an ɗora shi a kan wani nazari na Yakasai (1999) wanda ya bayyana yadda cuɗanya ta wakana tsakanin harsuna daban-daban a kan iyakar garuruwan Ƙonni da Illela da suke ƙasashen Nijar da Nijeriya.
7.0 Nazarin Rikiɗar Sautuka a Harshen Ngizim
A nan, muƙalar ta nuna yadda akan samu sassauyawar
sautuka ta fuskar lafazi sakamakon tasirin wasu sautuka ‘yan uwansu waɗanda suka haɗa muhalli ɗaya a cikin kalma. Irin wannan
tasiri na harshen Hausa a kan harshen Ngizim wajen rikiɗar sauti, yana samuwa ne saboda
kowane harshe da haɓarsa yake tagumi a fagen tsarin
sauti. Manufa, Hausa tana rinjayar keɓaɓɓun sautukan Ngizim ne wajen daidaita su da nata
domin samun sauƙin furta su ga ‘yan asalin harshen na Ngizim sakamakon wannan tasiri
na zamantakewa da al’ummar Hausawa. A ƙarƙashin wannan, maƙalar ta kawo misalan sautukan
cikin kalmomi tare da bayanin ƙididdigarsu ta hanyar amfani da alamomin tsarin
sauti gami da ma’anoninsu kamar haka:
7.1 Rikiɗar Sautin Wasalin /ə/
Dangane da irin bayanin da ya
gabata nan sama, wannan muƙalar tana nuna cewa wasalin /ə/ na harshen Ngizim yana rikiɗa ya koma furucin wasulan [i]
da [u] a Hausa, gwargwadon irin harafin da ya biyo bayan wasalin na /ə/. Duba waɗannan misalai:
Lamba |
Ngizim |
Hausa |
Ma’ana |
1a. |
Ƙirar ɓoye Ƙirar sarari/lafazi məya |
bàakii |
mouth |
1b. |
cəmà |
rufèe |
to close |
1c. |
fəɗu |
huɗu |
four |
1d. |
məwà |
rinàa |
distain |
1e. |
wən |
ɗaa |
son |
1f. |
wənu |
kwana |
spend the
night |
1g. |
wəndùwà |
gidaa |
compound |
Binciken a wannan rukuni, ya kawo
misalai daban-daban dangane da rikiɗar sautin wasali /ə/ na harshen Ngizim. A misalai
masu lamba ta 1a-c, an nuna yadda wasalin tsakiya tsaka-tsaki maras kewaye /ə/ yake rikiɗa ya koma furucin wasalin sama
na gaba maras kewaye [i] a muhallin tsakiyar kalma kamar yadda ƙa’idar take nunawa a nan ƙasa:
Haka nan,
a sauran misalan masu lamba ta 1c-1g da suke sama, su ma sun nuna yadda wasalin
na tsakiya tsaka-tsaki maras kewaye /ə/ a harshen Ngizim yake rikiɗa ya koma furucin wasalin ƙurya na sama mai kewaye [u] a
muhallin tsakiyar kalma kamar yadda ƙa’idar ta nuna nan ƙasa:
7.2 Rikiɗar Sautin Baƙin /tl/
A nan, sautin /tl/ na harshen
Ngizim yakan tasirantu da furucin [
Lamba |
Ngizim |
Hausa |
Ma’ana |
2a. |
Ƙirar ɓoye Ƙirar sarari/lafazi tlaaɗà |
ƙàiƙàyii |
itch |
2b. |
tlàkàtu |
laalàacee |
spoiled |
2c. |
tlau |
taashì |
stand up |
2d. |
tlaàwùrtu |
hàukaa |
madness |
2e. |
tlùwai |
naamàa |
meat |
2f. |
tluùmà |
yaayì |
trash |
A waɗannan misalai masu ɗauke da lamba ta (2a zuwa 2f) sun nuna yadda sautin baƙi ɗanjirge maras ziza /tl/ a harshen
Ngizim yake rikiɗa ya koma furucin ɗan bayan hanƙa zuzau maras ziza [
7.3 Rikiɗar Sautin Baƙin /zh/
A wannan
rukuni kuma, sautin /zh/ na harshen Ngizim yakan rikiɗa ya koma furucin [ʤ] na Hausa saboda tasirin harshen
Hausa a kan Ngizim. Binciken ya nuna irin wannan sauyi cikin wasu kalmomi kamar
haka:
Lamba |
Ngizim |
Hausa |
Ma’ana |
3a. |
Ƙirar ɓoye Ƙirar sarari/lafazi zhəbjəəp |
taanaa |
earthworm |
3b. |
zhà |
yaaƙìi |
war |
3c. |
zhabùwà |
zumàa |
honey |
3d. |
zhànyi |
luudàyii |
ladle |
3e. |
zhìgom |
jaarùmii |
brave man |
3f. |
zhiməɗ |
ƙàshin baayaa |
vertebrate |
3g. |
zhìrau |
kunyàa |
modesty |
Kamar dai
a rukunin da ya gabata, a nan ma binciken ya nuna yadda sautin baƙi baganɗe zuzau mai ziza /zh/ na harshen
Ngizim yake rikiɗa ya koma furucin ɗan bayan hanƙa ɗan atishawa mai ziza [ʤ] a muhallin farkon kalma kamar
yadda misalan suka nuna. Haka nan, an nuna yadda lafazin kalmomin suke a ƙirar ɓoye sannan aka nuna yadda suka
koma bayan rikiɗar lafazin nasu a ƙirar sarari cikin kalmomi daban-daban
daga 3a-3g. Bayan haka, binciken ya nuna yadda rikiɗar sautin take a wannan rukuni
ta hanyar amfani da alamomi kamar haka:
7.4 Rikiɗar Sautin Baƙin /dl/
A wannan rukuni ma, sautin /dl/
na harshen Ngizim yana rikiɗa ya koma sautin /d/ kamar yadda furucinsa yake a harshen Hausa. Binciken
ya nuna irin waɗannan misalai cikin kalmomi ta
hanyar bayyana sigarsu a ƙirar sarari da ƙirar ɓoye kamar yadda aka nuna nan ƙasa:
Lamba |
Ngizim |
Hausa |
Ma’ana |
4a. |
Ƙirar ɓoye Ƙirar sarari/lafazi dləgdu |
fansaa |
ransom |
4b. |
dləgəmau |
ràaƙumii |
camel |
4c. |
dləgàyu |
maƙàlee |
become lodged |
4d. |
dləgiɗ |
màkaahòo |
blind person |
4e. |
dlə̀mà |
gud |
donation |
4f. |
dlə̀màtu |
ɓaacì |
spoiled |
4g. |
dləra |
ciiwòo |
pain |
Bisa la’akari
da bayanai gami da misalan da aka gabatar tun daga lamba ta 4a zuwa ta 4g ƙarƙashin wannan rukuni, an ga yaddda
binciken ya nuna rikiɗar sautin baƙi ɗan jirge mai ziza /dl/ na harshen
Ngizim zuwa bahanƙe tsayau mai ziza [d] a muhallin farkon kalma. Haka nan, an nuna yadda
rikiɗar sautin take a wakana a wannan
rukuni ta hanyar amfani da alamomi kamar yadda aka nuna nan ƙasa:
8.0 Sakamakon Bincike
Dangane da
yadda binciken ya nazarci tararrun bayanansa, an gano cewa lallai lafazin wasu sautuka
sukan rikiɗa zuwa wasu sautukan Hausa musamman
sakamakon tasirin harshen Hausa a kan na Ngizim. Daga cikin sautukan da abin ya
shafa akwai wasalin tsakiya tsaka-tsaki maras kewaye /ə/ a harshen Ngizim yana rikiɗa ya koma furucin wasalin sama
na gaba maras kewaye [i] a muhallin tsakiyar kalma kamar yadda aka misalta a baya.
Haka nan kuma, wannan wasalin tsakiya tsaka-tsaki maras kewaye /ə/ a harshen Ngizim, yana rikiɗa ya koma furucin wasalin ƙurya na sama mai kewaye [u], shi
ma a muhallin tsakiyar kalma. Bayan haka, biniciken ya ƙara gano cewa, sautin baƙi ɗanjirge maras ziza /tl/ a harshen
Ngizim yana rikiɗa ya koma furucin ɗan bayan hanƙa zuzau maras ziza [
9.0 Kammalawa
Bisa la’akari
da irin bayanan da wannan takarda ta nazarta, an ga yadda ta fito da rikiɗar wasu sautukan harshen Ngizim
su koma furucin wasu sautuka na daban a harshen Hausa. Takardar ta gano hakan ne
ta la’akari da irin ƙarfin tasirin da harshen Hausa yake da shi a kan na Ngizim musamman
ta fuskar furuci. Domin kuwa a iya sautukan
harshen Ngizim da binciken ya nazarta, sautuka ne da babu su a harshen Hausa. Saboda
haka, binciken sai gano cewa harshen Hausa ya yi amfani da ƙarfin tasirinsa ne a kan Ngizim
wajen mayar da furucin sautukan daidai da na Hausa ta la’akari da irin sautukan
da suke da kamancin furuci da na Hausa. Tasirin kuwa kamar yadda binciken ya tabbatar,
ya samu ne a sakamakon hulɗa ta mu’amala a tsakanin ƙabilun guda biyu (Hausa da Ngizim)
wanda ya samo asali daga zamantakewar wuri guda tsakanin ƙabilun musamman a garin Pataskum na jihar Yobe.
Manazarta
Abdullahi,
M. I. (2005). Tasirin harshe da al’adun Hausawa
kan kabilar Gwari a garin Minna. [Kundin digiri na biyu]. Jami’ar Usmanu Ɗanfodio.
Abubakar,
A. (2001). An introductory Hausa morphology.
Faculty of Arts, University of Maiduguri Nigeria.
Ado, A. (2020).
Dabarun gudanar da bincike na ilimi a kan
Hausa. Government Printing Department.
Batibo, H.M.(2005).
Language decline and death in Africa.
Cornwell, Cornwell Press Ltd.
Chomsky,
N. & Halle, M. (1968). The sound pattern
of English. Harper and Row. https://www.googlescholars.com
Crystal,
D. (2000). Language death. Cambridge University.
Crystal,
D. (2007). How language works. Canada: Penguin Group Crystal, D. (1) .C DUA The Enclopedia of languages and linguistics.
Greenberg,
J.H. (1966) The Language of Africa. The
Hague Mouton.
Greenberg,
J.H. (1970a). Some generalization concerning glottalic consonants, especially implosives. International Journal of Linguistics, 36(2).
Hans Walff Memorial Issue: Fascicle II. https://jstor.org/10/stable/1264671
Greenberg,
J.H. (1970b). The languages of Africa, (third
edition). Indiana University Press.
Grema, M.
(2018). Linguistic borrowing: A study
of Hausa loan words in Kanuri [Unpublished doctoral dissertation]. Bayero University
Kano.
Inusa, S.
(2018). Kwatancin wasun bayanau a nahawun Hausa da na Badanci. [Kundin digiri na
biyu]. Jami’ar Ahmadu Bello Zaria.
NERDC, (2008).
Report on the sociolinguistic survey of language
use and diversity in Nigeria. Sheda-Abuja: NERDC Press.
Newman, P. (2000). The Hausa language: An encyclopedic reference grammar. Yale University
Press.
Newman, P. (2007). A Hausa-English dictionary. Yale University Press.
Salim, B.
(1981) Linguistic borrowing as eɗternal evidence in phonology: The assimilation of
English loanwords in Hausa [Unpublished doctoral dissertation]. University of New
York.
Sani, M.A.Z.
(2011). Gamayyar tasrifi da tsarin sautin
Hausa. Ahmadu Bello University Press.
Wakili, B.D. (2009). Bade-English-Hausa Dictionary.Potiskum: Ajami
Press Limited.
Weinreich, A. (1953).Language
in contact. New York: Linguistics circle The Hougue: Mouton.
Yakasai, S. A.
(1999). Language accross two boarders: A socio linguistic studies of Hausa in Ƙonni and Illela
boarder towns. [Unpublished
doctoral dissertation]. Bayero University
Kano.
[1]. Wannan sauti na
/kw/ da takwaransa na /gw/ ba su fito a matsayin jagorori na ƙamusun da muƙalar ta yi amfani
da ita ba, wato Schuh, (2004). Sai dai, muƙalar ta nuna su ne a matsayin wasu sautuka da harshen na Ngizim ya yi
amfani da su a wasu kalmominsa kamar yadda aka misalta.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.