Ticker

6/recent/ticker-posts

Gurbacewar Al’adun Hausawa Da Dabi’unsu Da Halayensu a Karninmu

Citation: Bunza, A.M. (2025). Gurɓacewar Al’adun Hausawa, Ɗabiunsu Da Halayensu a Ƙarninmu. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 4(1), 14-23. www.doi.org/10.36349/tjllc.2025.v04i01.002.

GURƁACEWAR AL’ADUN HAUSAWA, ƊABI’UNSU DA HALAYENSU A ƘARNINMU

Daga

Aliyu Muhammadu Bunza
Department of Nigerian Languages
Usmanu Danfodiyo University
Sokoto, Nigeria
mabunza@yahoo.com
08034316508

Tsakure

Al’ada Balarabar kalma ce da a sakamakon zamantakewa ko saduwar Balarabe da Bahaushe ta samu a harshen Hausa. Al’adunmu sun samu sauyi daga addinan da suka riski ƙasarmu guda biyu (Kiristanci da Musulunci). Haka kuma, sun gurɓace sanaddiyar Mulkin Mallaka da karatun Boko. Wayewar kan zamani na hanyoyin sadarwa na baka da rubutattu sun sa masassara ga al’adunmu. Cigaban mai ginar rijiya na hanyoyin sadarwa na ga-ni-ga-ka na rediyo mai hoto da finafinai, da wasannin kece raini da batsa sun yi wa al’adunmu rauni babba. Shirye-shirye da tsare-tsaren wayoyin hannu sun mayar da gaba baya; sun gurɓatar da kyawawan al’adunmu, muka koma gaba kallo baya da mamaki. Babban abin da ya kyautata al’adunmu na gado shi ne “gaskiya” abin da ya gurɓatar da su shi ne “ƙarya”. Ga alama, dabarar da muka fara yi ta leƙon al’adunmu na shekaranjiya, da shekaranjiya ban da jiya, domin gyara su a yau domin amfaninmu jibi da gata, su ne kaɗai dabarun gyaran gurɓatacciyar al’ada da inganta ta.

Gabatarwa

Hausawa mutane ne da suka mamaye duniyar ɗan Adam ga harshensu, sana’o’insu, zamantakewarsu, sarautunsu, da fasahohinsu. Daga cikin abubuwan da suka ɗaukaka Hausawa nan duniya akwai: Harshensu, da ɗabi’unsu, da ƙwazonsu na kare kansu da al’adunsu. Yadda ƙwazonsu ya ɗaukakar da su, aka san su a duniyar kowane zamani shi ya sa har yanzu ana koyi da su wajen neman cigaba ga kowane abu ake fuskanta a duniyar zamaninmu. Wannan ya sa duk abin da ya gurɓata duk wata hanyar ɗaukakar Bahaushe Hausawa na damuwa da shi, da ƙoƙarin jawo hankalin Hausawa a tabbata musu daga na gaba ake gano zurfin ruwa. Duk al’ummar da ba ta kula da sakarkacewar kyawawan al’adunta saboda sauyawar lokaci da zamani ba, ta taimaki kanta ga cigabanta da gudunmuwar magabatanta ba, tana cikin ƙalubale. Bisa ga irin wannan misali halayyar da al’adun Hausawa suke ciki a yanzu sun cancanci a nazarce su, a ga yadda za a fuskance su domin a ci ribar abubuwan da aka gada kaka da kakani.

Ma’anar Al’ada

Na so in ɗan taɓo ita kanta kalmar “al’ada”. Abin sani shi ne, kalmar ba ta Hausa ba ce, ta Larabci ce. Abokan zama da dama, da manazarta, idan an tattauna da su kan ma’anar “al’ada” za a ji sun ce:

a.      Halayyar rayuwa

b.      Ɗabi’un mutane

c.       Ayyukansu na al’ada da sauransu

Ga alama, kalmar da Hausawa suka fara amfani da ita a kan “al’ada” ita ce “gado”. Wataƙila saboda tsoron fassarar da waɗanda ake yi wa ita rashin fahimta shi ne ya sa aka fassara ta da “al’ada”. Gabanin Hausawa da baƙin al’ummomi da addinai da harsuna daban-daban za mu ji Hausawa na faɗar:

a.      Ƙira ya yi gado

b.      Masunci ne ga gado

c.       Bakano ne ga askar gado

d.     Ai gadon Musulunci ya yi

e.      Hausawa ba su gaji ƙarya ba gaskiya suka gada.

A taƙaice, za mu iya cewa:

Al’ada ita ce wasu abubuwa da muka gada kaka da kakanni. Sukan iya kasancewa dabarun zamantakewa, ko ayyukan aure, suna, da mutuwa. Haka kuma, yakan kasance abubuwan da aka gaji dokokin yin su, ko ƙaurace musu, ko jin kunya ga aikata su, ko samun godiya ga aikata su. Ana gano al’ada daga bakin masu ita ko ayyukansu.

Wane ne Bahaushe?

Gabanin mu leƙo al’adun mai al’adu, a al’adance ya fi dacewa mu san shi da bayyana yadda za a gane shi ko ga wanda bai san shi ba ne. Fitattun masana Hausa, da Tarihi, da Addini, da Ilmin Harsuna, da sauransu sun yi ƙoƙari a fannonin ƙwarewarsu su fayyace wane ne Bahaushe? Ƙoƙarin da suka yi shi ya ba da damar samun shafukan sake bitar ayyukansu da hanyoyin da ba su faɗaɗa ba a nazarce-nazarcensu. A taƙaice, za mu ce, duk wani ilmin gano wane ne Bahaushe? Dole sai ga Bahaushe za a iya gano shi a kuma tambaye shi tushensa da asalinsa. Zancen da zai fito daga bakin mai abu ya fi na kowa dacewa. Dr. Ibrahim Narambaɗa ya tabbatar da cewa:

Jagora: Ko an so ko da ba a so ba,

: Mai abu dai shi adda abinai.

Gindi: Shiri bajinin Mamuda,

: Abu na Namoda tsararre.

Bisa ga bitar binciken da masananmu suka yi za mu iya cewa:

a.      Bahaushe shi ne wanda ya yarda da Bahaushe ne kuma yana bugun gaba da zama Bahaushe

b.      A samu ga iyaye da kakani duk Hausawa ne

c.       Ba ya bugun gaba da wata ƙasa in ba ƙasar Hausa ba

d.     Yana da karin harshe daga cikin karuruwan harshen Hausawa

e.      Idan an same shi da askar fuskar Hausawa ya tabbatar da iƙirarinsa

f.        Samun sa baƙar fata dole ne, kasancewarsa farar fata ya ɓata dukkanin matakai (v) da suka gabata.

Ina ne Ƙasar Hausa?

Ƙoƙarin gano ƙasar Hausa zai taimake mu gano ina al’adun Hausawa da ɗabi’unsu suka mamaye da kuma yadda gurɓacewar wasu daga ciki ya kasance. A taƙaice, ƙasar Hausa ƙasa ce da take da ƙasashe manya da suka tabbatar da zamanta babbar farfajiya bisa ga kasancewar:

a.      Kano ƙasar Kanawa mai cibiya Kano

b.      Gobir ƙasar Gobirawa mai cibiya Sabon Birni

c.       Kabi ƙasar Kabawa mai cibiya Argungu

d.     Katsina ƙasar Zagezagi mai cibiya Zariya

e.      Zamfara ƙasar Zamfarawa mai cibiya Anka/Gummi/Gusau

f.        Yawuri ƙasar Yawurawa mai cibiya Yawuri (daga Birnin Yawuri)

g.      Daura ƙasar Daurawa mai cibiya Daura

h.      Maraɗi ƙasar Maraɗawa/Arawa mai cibiya Maraɗi

i.        Damagaran (akwai maganganu da yawa a kanta)

Waɗannan su ne ƙasar Hausa wurin da Hausawa suka kafa garuruwan da suke cibiyi ko su Hausawan ke sarauta ko harshensu ya mamaye harsunan da aka tarar a nan. To, mun ga Bahaushe da ƙasarsa sauran harshensa domin mu san yadda ake furta shi, ya aka gado shi, wannan kaɗai ya isa gano harshen Hausawa na asali.

Yaya Harshen Hausa Yake?

Bahaushe ga al’adarsa shi ya sa wa Hausa sunan harshen “Hausa”. Mai gadon harshe ya kira shi “Bahaushe”. Furucin magana da harshen a ce mishi “Hausa”. Fassarar wani harshe zuwa harshensa ya ce masa “Hausantawa”. Farfajiyar da sarakunan Hausa suke sarauta a ce mata “ƙasar Hausa”. Wanda ya zauni ƙasar Hausa ba ya jin harshen Hausa a kira shi da sunan “Ba Hausa”. Hausa harshe ne mai gajerun kalmomi da jimloli da keɓaɓɓun kalmomi ga sana’o’i da wasanni. Ga alama ya fi sauran harsuna da ke kusa da shi ƙirar wasali da baƙaƙe. Ga ɗan misali kamar haka:

a.      Wasula: a, i, o, u, e.

b.      Wasula biyu: ai, au, ui, iu (da wuya a same su ga wasu harsuna)

c.       Tagwayen baƙaƙe: kw, gw, gy, ts, ky, sh, fy

d.     Tagwaye masu ƙugiya: ƙy, ƙw

e.      Baƙaƙe masu ƙugiya: ɓ, ɗ, ƙ, ‘y

f.        Baƙaƙen karin harshe: ɗw, tc, tw, dw, rw, lw, hy, nw, sw

Kaɗan ke nan daga cikin haruffan da Hausa take da su da masana harshe na gado sai ‘yan harshen na asali ke iya furta su sosai. Haka kuma, daga cikinsu ake iya rarrabe karuruwan harshen Hausa.

Zamunan Ƙasar Hausa

Masana tarihi, da Hausa, da sauran ilmuka suna da irin kallon da suke yi wa zamunan ƙasar Hausa domin yin ƙoƙarin rarrabe yadda al’adu da ɗabi’un Hausawa suke juyawa daga wani zuwa wani wuri na cigaba ko faɗuwa, ko gurɓacewa. Yadda ƙasar Hausa take, za a ga zamunan da ta shimfiɗu ciki su ne:

1.      Zamanin farko: ɓullarsa, bayyanarsa da kafuwarsa

2.      Zamani na biyu: hulɗa da wasu ƙabilu makusanta

3.      Zamani na uku: haɗuwa da ƙabilu manisanta

4.      Zamani na huɗu: zamanin addinin Annabi Isa (AS)

5.      Zamani na biyar: zamanin addinin Musulunci

6.      Zamani na shida: zamanin mulkin mallaka

7.      Zamani na bakwai: Boko da wayewar kai

Kowanne daga cikin waɗannan zamuna bakwai da ƙasar Hausa ta ratsa ko suka ratse su akwai wasu al’adu da suka ci gaba da rayuwa, ko rage ƙarfi, ko masassara, ko rugujewa, ko taɓarɓarewa ba da sani ba, ko da sanin da ba a hango makircin da yake ciki ba. Zamanin farko fari ne fes daga Bahaushe sai Bahaushe. Zamani na biyu an sadu da Fulani, Dakarkari, Zabarmawa, Kyangawa, Adarawa, da sauransu. Zamani na uku, saduwa da Larabawa, Kanuri, Yoruba, Nufawa, Bambara da Shonghai (Mali), Asanti (Ghana) da sauransu. Zamanin addinin Annabi Isa (AS) an sadu da Arawa da Kyangawa. A zamanin da addinin Musulunci a ko’ina ya shiga ƙasar Hausa. Idan muka dubi zamani na shida na mulkin mallaka da zamani na bakwai na Boko da wayewar kai, nan maganganun da muke son mu faɗaɗa bincike suke.

Makarantun Ilmin Hausawa na Farko

Duk wani bincike, da karatu, da rubuce-rubucen da za a yi kan gurɓacewar al’adun Hausawa, da ɗabi’unsu, jiya da yau dole sai sun leƙo waɗannan makarantu za a tabbatar da su, ga makarantun:

1.      Tatsuniya

2.      Karin magana

3.      Salon magana

4.      Kirari

5.      Baƙar magana

6.      Waƙoƙin yara na baka

7.      Waƙoƙin zanga-zanga (na yara)

8.      Waƙoƙin yaƙe-yaƙe (na gari)

9.      Waƙoƙin aure (na yara)

10.  Waƙoƙin bukukuwa (yara da manya)

11.  Waƙoƙin mutuwa (na manya)

12.  Waƙoƙin daka (na mata)

13.  Waƙoƙin kishi (na mata)

14.  Waƙoƙin talla (na masu sana’a)

15.  Waƙoƙin baka (na manyan maza da manyan mata)

Waɗannan waƙoƙin da wasu nassoshin magana na Hausawa tun gabanin zamani na biyu Hausawa ke da su, kuma a nan aka ɓoye kyawawan ɗabi’u da ake hardacewa domin ganin an yi nasarar ɗabi’u na kirki da aka gada kaka da kakani.

Kyawawan Ɗabi’uƘyawawan Ɗabi’u na Kirki da Aka Gada Kaka da Kakanni

Manyan littattafan da aka karanta ko aka hardace a makarantunmu na gado sun haɗa da:

1.      Goyon bayan gaskiya da aiki da ita

2.      Nisantar ƙarya da faɗa da ita

3.      Rowa da nisantar tanisantarta

4.      Kyauta da kusantar ta

5.      Ɓanna da illolinta

6.      Tsaro da dabarar yin sa

7.      Haɗin kai da hidimarsa

8.      Girmamar da gabaci da magabata

9.      Kawar da laifukan sata da ƙazantu

10.  Kyautata ƙwazo da rushe ragganci

11.  Zumunci da muhimmancinsa

12.  Inganta harshe da adabinsa

13.  Tattalin arziki da muhimmancinsa.

Kaɗan ke nan daga ƙunshiyar abubuwan da muka tarar ga magabata, a yau suna batun ɓata mun kasa mu tsaya mu yi gyara. Magabatanmu sun san wannan gurɓacewa tun gabanin bayyanar ta a wannan zamani namu na cigaban ginin rujiya. Ji wannan saƙo ga Dr. Makaɗa Ibrahim Narambaɗa:

Jagora: Na hore ki gaskiya bari tsohon ƙarya,

Yara: Mai ƙarya munahuki Allah su yaƙ ƙi,

Jagora: Har yau ba mu ga in da an ka bi mai ƙarya ba,

Yara: Amma ita gaskiya gari da mutane tay yi,

Gindi: Gwarzon Shamaki na Malam toron giwa,Toron Giwa

            : Baban Dodo ba a tamma da batun banza.

A Bahaushiyar al’ada, babu abin da kan gyara mutane da al’adunsu, da addininsu, da zamantakewarsu, da tsaronsu, da cigabansu, da cin nasararsu, da ɗaukakarsu, sai gaskiya. Tunanin Bahaushe ya yi canjas da na sauran al’ummar duniya. Wanda duk ya ɗaukaka a duniya za a ga gaskiya ce ta ɗaukaka shi. Babu abin da ya gurɓata muna al’adunmu na gargajiya a yau illa ƙin ba gaskiya goyon baya. Dubi yadda karuruwan maganarmu na gyara muna al’adun zamantakewa da irinsu:

-          Gaskiya ina laifinki

-          Gaskiya mai korar ƙarya

-          Gaskiyar faɗa harsashe

-          Gaskiya dokin ƙarfe

-          Gaskiya sunan ta gaskiya

-          Gaskiya a ƙi ki, a so ki

Bin gaksiya ya ɗaukaka sarakunan da suka gina ƙasar nan, da gwarazanmu, da jagororinmu. Yau saɓa mata ya ɓata shugabancinmu na sarauta, da addini, da ilmi, da siyasa.

Ƙarya

Al’adunmu sun ƙi ƙarya, sun ƙi masu yin ta, ba su yarda hulɗa da ita da masu yin ta ba. A al’adance, duk wurin da ƙarya ta kutsa taɓarɓarewarsa ta tabbata. Ai don haka ne magabatanmu ke cewa:

-          Ƙarya fure take ba ta ɗiya (‘ya’ya)

-          Ramin ƙarya ba ya da zurfi

-          Gaskiya mai korar ƙarya

-          Ƙarya aka yi wa rijiya, ruwa na gulbi

Makaɗa Aliyu Ɗandawo ya jawo hankalinmu ga matsalar ƙarya a faɗarsa da yake cewa:

Jagora: Mai kurin biɗan faɗa

Yara: Bana an ba shi kashi

Jagora: Har na zaburo rabo

Yara: Sai naj ja da baya

Jagora: Nat tuna ƙaryar da yay yi min

Yara : Gara a ba shi kashi.

Gindi: Bai ɗau wargi ba Audu,

             : Mu je mu ga Madawaki.

Makaɗa Dr. Ibrahim Narambaɗa ya tabbatar mana damuna cewa ƙarya tana gurɓata komai na rayuwa, da addini, da iko, da sarauta, da siyasa, balle al’adunmu na gargajiya, ji yadda saƙonsa yake:

Jagora: Na bar ƙarya ko ina kiɗi,

: Na wuce ƙarya ko ina kiɗi,

: Nai sittin saba’in nika hwaɗa,

: Mai saba’in yai ƙarya,

: Ana ta zunɗe nai,

Yara : Ko yaran da ag garai,

: Duk wawwatce mishi sukai,

: Shina yawo shi ɗai ɓarau-ɓarau.

Gindi: Ya ci maza ya kwan yana shire,

: Gamda’aren Sarkin Tudu Alu.

Koyon gaskiya da nisantar ƙarya su ne al’adun da Hausawa suke koyar da yara su, a girma cikin saninsu sai a ɗaukaka a ɗaukakar da al’ada.   A kula, al’adar gaskiya, tana cikin tatsuniya, karin magana, salon magana, waƙe-waƙen yara da manya. Duk wani cigaba da aka samu na rayuwar al’ada gaskiya ta taimaka aka yi, cikas da aka gani cikin gurɓacewar al’adunmu a yau ƙarya ta cutar da mu.

Kyauta da Rowa

Gaskiya ta taimaka wajen inganta kyauta har Hausawa da al’adunsu suka rinjayi wasu al’ummomin da ke tare da su. Ai gaskiya ta koyar da kyauta ga ‘yan uwa, da iyalai, da abokan zama gaba ɗaya. Kyauta tana inganta tsaro da tattalin arziki, da haɗin kai, da cigaban al’umma. Dubi yadda Alhaji Gambo Fagada mijin Kulu ya kalli kyauta:

Jagora: Kyautar mai kuɗi yar taƙi ta,

: In an yi bukin dangi yanai ma,

: In an yi bukin salla yanai ma,

: Amma a ba ka yau, a ba ka gobe,

: Kuma jiɓi a ƙara ba a gaza ba,

: Wallahi ɓarawo ɗai ka yin haka,

: Ba da abinai na shi kai ba.

Ya tabbatar da cewa, Hausawa suna da al’adar kyauta ta fitar da ‘yan’uwa da abokan hulɗa ga wahala da rashi. Almubazzaranci kuwa ƙarya ta haddasa shi, domin ta kore kyautar da gaskiya ta turo. Tsofaffin taskokin adabi na baka da ƙasar Hausa ta fara amfani da su, su suka bai wa mawaƙan kowane fanni kayan aiki da suke amfani da su ga aiwatar da waƙoƙinsu kuma da abubuwa biyu aka yi amfani da su, “gaskiya” da “ƙarya”. Duk wata hanyar rayuwa su ne manya a ciki.

Dangantakar Al’adu da Addinai

Ga ƙolin binciken addinan da suka rayu ƙasar Hausa akwai na gargajiya da na Kirista da kuma addinin Musulunci da yake kan gaba. Na gargajiya babu takamaiman lokacin faruwarsa, sai dai a ce lokacin da ƙasar Hausa ta bayyana a bangon ƙasa. Addinin Kiristanci daga Masar ya fara kutso kai tun zamanin kasuwanci da sarautar Gobir da wasu sassan Gobir da Maraɗi. Addinin Musulunci kuwa ya yi shekaru da yawa da bayyana tun wajajen ƙarni na sha uku (13ƙn), wasu na ganin tun bayyanar Manzo (SAW). Duk yadda waɗannan abubuwa suka kasance sun yi ɗan tasiri cikin al’adun Hausawa, har wasu al’adu suka gurɓace. Babban abin nufi sun yi tasiri ga:

1.      Matakan rayuwa uku: aure, haihuwa da mutuwa

2.      Tasiri a rayuwar bauta musamman a kan bori da tsafi

3.      Sun yi tasiri a tsarin abubuwan ci da sutura

4.      Sun yi tasiri a rayuwar ladabi da biyayya na gargajiya wasu sun rushe wasu an yi gyara

5.      Sun yi tasiri a kan tsaro da ƙirƙiro dokokin zaman lafiya

6.      Sun yi canjaras ga gurbin gaskiya

7.      Sun haɗu tangam a kan gano ƙarya da ƙin ta.

Saukakkun addinai da suka sauƙa a ƙasar Hausa sun tsawatar a kan sata, da yaudara, da zina, da shaye-shaye, da cunkoson mata da maza, da kisan kai, da yaƙe-yaƙe. Addinan sun yi tasiri a kan al’adun tsage-tsagen fuska, da tsiraici da yin kaciya ga maza da mata, da barin gemu da saje, da auratayya musamman mata fiye da ɗaya. Tabbas! Al’adun da suka saɓa wa aƙidar addinin Musulunci, addinin Musulunci ya hana su yaɗuwa ga masu addinin sai aka kawar da su.

Al’adun Kyautata Zamantakewa

Ƙasar Hausa tana da tarihin yaƙe-yaƙe da yawa musamman in an dubi daular Kabi, da Gobir, da Kano, da Katsina, da dai sauransu. Ƙulla yaƙi da aiwatar da shi lalata tsaro ne da zaman lafiya. Don haka al’ada ta zo da wasar kore yaƙi da gaba mai suna “Tobasantaka”. Dubi wasan Katsinawa da Zagezagi, da ta Gobirawa da Fulani, da ta Kabawa da Fulani da dai sauransu. Da wasar tobasantakan jini, da ta ‘yan masu sana’ar da suka yi takin saƙa kamar mahauta da masunta. Yau tobasantakar dogo da gajere, takwaranci, kaka da jika, malamai da bokaye, auren zumunta da ire-irensu sun fara rafashewa saboda wayon cewa, wai an waye sai ɗabi’unmu na haɗin kai suke lalacewa. Dubi satar ‘yan’uwa ada ɗora kuɗin fansa, sanya da sa makamai a halaka abokan zama, ya haifar da wata sabuwar musiba da ta haifar da gaba tsakanin al’umma, musamman a arewacin Nijeriya.

Kafofin da Suke Gurɓata Al’adunmu da Lalata Su

Kafofin da suka fara yi wa al’adunmu ɓarna da gurɓatar da mu, ba mu kaɗai suka shafa ba; har sauran ƙabilunmu na Nijeriya sun shafa. Wasu abubuwa kamar don cigaba aka tarbe su, suka haifar da koma baya kamar:

1.      Karatun boko

2.      Kafofin yaɗa labaranmu na waje

3.      Kafofin yaɗa labarai na cikin gida

4.      Ƙungiyoyin wasannin kwaikwayo

5.      Ƙungiyoyin rawa da waƙe-waƙe

6.      Cibiyoyi finafinai

7.      Litttafai da mujallunmujallu na wasannin da ba al’adunmu ba, amma ana gudanar da su da harshenmu

8.      Ƙungiyoyin waƙe-waƙe da raye-rayen jam’iyun siyasoshi

Haɗa al’ummomi da yawa tare da gudanar da wasanni cikin harshenmu da al’adunmu

Waɗannan abubuwa (9) su suka fara taɓa al’adunmu aka fara gurɓata su sannu-sannu, har muka wayi gari yau cikin injimomin kwamfuta da wayoyin hannu da suka game duniya aka fito da hanyoyin sadarwa na:

1-      Facebook

2-      Instagram

3-      Whatsapp

4-      Tiktok

5-      Tik-tok

6-      Snap chat

7-      You tube

8-      Twitter

Babu wani hoto, da aiki, da labari, da tattaunawa, da kiɗa, da rawa, da waƙoƙi, da hulɗoɗin mutane, da yaudare-yaudare, da babu a cikinsu. Sun gurɓatar da ingantattun al’adunmu sun sa mu koyon miyagun al’adu.   A cikin waɗannan hanyoyin an koyar da yaranmu maza da mata:

1.      Shaye-shaye

2.      Tsiraici

3.      Ƙarya da yaudara

4.      Kisan kai na gayya

5.      Koyar da sace-sace

6.      Rashin ladabi da biyayya ga ma’aurata

7.      Keta haddodin addinanmu

8.      Koyar da yara bore da zanga-zanga

9.      Gina ƙiyayyar ƙabilanci

10.  Cire ɗa’ar yara ga iyayensu

11.  Mayar da ƙarya wata makarantar kanta.

A cikin waɗannan shirye-shirye aka raunanar da ɗa’a tsakanin ma’aurata a fito da ‘yancin mace fiye da na miji. A sakamakon haka, a Kaduna sarakuwa ta sayar da kanta ga ‘yan ta’adda don a yi wa mijin ɗiyarta tara ya tsiyace a sake kishiyarta. A Katsina, an nuna yaron da ya sayar wa ‘yan ta’adda mahaifiyarsa. Haka aka nuna yaron da ya kashe mahaifinsa a Bauchi ya ce, ya yi haka ne domin mahaifinsa ya samu shahada. A Neja yaro ɗan shekara (25) Abubakar Muhammad ya biya abokinsa (N110,000) su kashe mahaifinsa domin ya gaji dukiyar mahaifin mai yawa. Mahaifin ɗan shekaru hamsin da biyu (52) ne, kai tsaye aka kashe shi. Haka yaro ɗan shekara (23) ya kashe mahaifinsa a jihar Delta. Waɗannan bala’o’in duk cigaban zamani da waɗancan shirye-shirye ya haifar da su.

Shirye-shiryen sun ci nasarar cire wa matanmu al’adun jin kunya. Neman aure, da son aure, da ɗaura aure, da bukin aure, da kai amarya, da sada ta da ango, da hanyoyin ciyarwa, da shayarwa, an ɗebe al’adunmu.   Ga al’adar Bahaushe, mata ba su sa wando a matsayin suturar ƙasa, ba su sa hula, ba su sa riga bale tagguwa, ba su ƙawata fuska, ba su ƙawata yatsu da zobba. Yau sun koma kamar matan Indiyawa da Romawa. Mace da miji ba sa faɗan sa-in-sa gaban mutane, yau finafinanmu sun rusa wannan al’ada. Ladabin gaisuwa, da barka, da ban kwana, na matan Hausawa iri ɗaya na girmama maza. A yau, TikTok da Istagram da Feacebook sun gurɓace muna al’ada. Da za mu yi nazarin waɗannan labarai za mu tabbatar da zamani ya illantar da al’adunmu:

-          Rufin kan uwar daɗi

-          Gaba kallo baya da mamaki

-          Gwamma a bakin Ɗangambara

Rusar da kunya ga idanunmu musamman matanmu shi ne babbar yaudarar zamani ga ɓata kyawawan al’adunmu. Abin ban tsoro shi ne, da maƙiya sun ci nasarar kore kunya ga matanmu tarbiyar yaran da za a haifa ta taɓarɓare, al’umma kuwa ba ta san ƙarshen makomarta ba. Yaudarar da muka yi wa ma’abota al’ada managarciya ita ce, a tura musu al’adar da ba tasu ba wadda ta keta dokokin al’adunsu a ce, ita ce wayewa sai a rungume ta hannu biyu.

Musabbabin Gurɓacewar Al’adunmu

Babu al’ummar da masassarar al’ada bai shafa ba, hatta masu iƙirarin su ne wayo kuma gare su wayo ya fito. Duk da haka a wajenmu Hausawa manya abubuwan da suka gurɓace al’aunmu su ne:

1.      Mulkin mallaka

2.      Ilmin boko

3.      Ƙungiyoyin siyasa

4.      Finafinan da, da na yanzu

5.      Kafofin yaɗa labarai na baka da rubutattu

Turawan mulkin mallaka a ko’ina suke al’adunsu ne halartacciya wadda ta yi taƙin saƙa da ita haramtaciya ce matuƙar ba ta yi maraba da su ba. Ilmin Boko na ‘yan mulkin mallaka ne, ai da shi aka tsara tsarin mulkinmu da al’adunsu ya mamaye. Ɗan boko Hausawa sun ce, mai ganin uba nai wawa. Na bar masu karatu da fassara, siyasar ƙasarmu ta game dukkanin ƙabilar da ke cikin ƙasa. Kowane ɗan ƙabila ya samu shugabantar ƙasa da al’adunsa yake mulki talakawa su fara aron su. Finafinai tun fitowarsu ya zuwa yau, al’adun wasu ake talla don su shiga zuciyar al’adun waje suke talla. Na cikin gida kowa takansa yake yi kuma sun rinjaye Hausawa yawa. Dalilai na sama biyar duka, daga na (2-5) na (1) ne ya haddasa su. Gaskiyar yaran ƙasar Hausa da ke waƙar:

Jagora: Kai ku ɗaga ga ɗan doka,

‘Yan Wasa: Ba mu gudu sai mun ga Nasara.

 

Jagora: Jar hula ba iko ce ba,

‘Yan Wasa: Ko rawani ba iko na ba.

A taƙaice sun tabbatar da mu cewa, mulkin mallaka ya karɓe komai ga hannun sarakunanmu da ‘yan dokarsu (masu jar hula) da su masu rawuna. Ashe tushen suturarmu na iko su ne hula da rawani da riga don rusa wannan al’ada Turawa suka ƙago kayan aiki na mata da maza iri ɗaya da ‘yan sanda, da soja, da duk masu aikin tsaron ƙasarmu. Wane Bahaushen asali zai yarda da ɗiyarsa, ko matarsa, ko uwarsa, su sa wandon aiki, da ‘yar riga, ɗuwawu da nonna suna jijjiga gaba suna fassarar taho na shirya?

Hanyoyin da Za a Farfaɗo da Al’adunmu

Babu Bahaushen da zai musanta cewa, ba a zalunci Hausa a al’adance ba. A tarihance yau 2025 muna da shekara 65 daga samun mulkin kai da aka ba mu 1960. Kasancewarmu shekaru 65 ƙarƙashin maƙiyanmu ba mu san iya cutuwar da aka yi muna ga al’adunmu ba. Haka kuma, ba mu iya fayyace irin gurɓacewar da al’adun suka yi ba. A al’adance, Hausawa ba su da gajeren wondo, sai dai kirshe da yaba ko warki da zai rufe jiki zuwa guiwa tun gabanin kowane addini a ƙasarmu. Turawa suka kawo gajeren wando da Hausawa suka ƙi. Dubi waƙar mayaƙan Satiru 1906, a ƙasar Boɗinga, Ɗancaɗi da Satiru suna waƙa:

: Waziri ya daɗe bai zaka ba,

: Marafa ya daɗe bai zaka ba,

: Balle Nasara mai ɗan wando,

: Babban mutum da wandon yara,

: Ku sa kiɗi mazaizai mu gani,

: Ko can gida faɗa munka sani,

: Ba mu san gudu ba sai dai a mutu.

Don haka babbar hanyar kare al’adunmu da farfaɗo da su da ɗaukaka su ita ce inganta karatun Hausa. Na biyu, kiran taron ƙara wa juna sani. Na uku, shi ne, inganta al’adunmu musamman na sana’o’i. Na huɗu, a sa dokokin haramta shigo da finafinan batsa da ta’addanci kamar yadda Russia da Saudiyya suka yi. A nan Nijeriya, jihar Kano ta fara kafa irin wannan doka.

Sakamakon Bincike

Bincikenmu ya tabbatar da cewa, al’ada wata babbar ɗabi’ar rayuwa ce ta kowace al’umma. Duk da kasancewar sunan “al’ada” Larabci ne da ya taushe na Hausa “gado” za mu ce:

a.      Mulkin mallaka ya haddasa duk wani abu da ya taɓi al’adunmu, kuma ba a daina ba har yau (2025).

b.      Taɓarɓarewar al’adunmu matasa ya fi mamayewa tsofaffin da suke rage da sun wuce an gama da mu.

c.       Ƙabilancin ƙabilun da Hausa ta haɗe harshensu, da waɗanda ta fi yawa, da wanzuwa, na daga cikin abubuwan da suka janyo gurɓacewar al’adunmu.

Naɗewa

Hausawa sun ce, ba a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare. Al’adunmu su ne, harshenmu, halayyarmu, ayyukanmu da muka gada kaka da kakani, tunaninmu da hangenmu da suka bayyana a adabinmu. Babu shakka, duk al’ummar da take bangon ƙasa yau, al’adunsu na gado masu yawa sun ɓata, wasu sun gurɓace, wasu ko suna nan suna kai da kawo. Abin da ya kyautu shi ne, mu yi tunanin gina harshenmu da koyar da ilmi cikinsa kamar yadda ake yi a ko’ina duniya ba aron harshen Ingilishi da Faransanci a makarantunmu ba. Su me ya hana su aron wani harshe su koyar da yaransu? Ai cikin harsunansu ne suka turo muna abubuwan da suka yi wa al’adunmu alaƙaƙai. Wani fitacen mawaƙin tashe a ƙauyenmu yana cewa:

Jagora: Sai dai a hi mu kalangu da kurkutu,

Yara: Amma ba a hi mu daɗin baki,

Gindi: Bori goje kana da borin tashe.

Manazarta

Adam, Y. M. (Ed.). (2021). Hausa prose-fiction: A reader. Kano: Bayero University Press.

Adamu, A. U., Yusuf, M. A., & Umar, F. J. (Eds.). (2004). Hausa home videos: Technology, economy and society. Kano: Centre for Hausa Cultural Studies.

Adamu, M. (1975). Hausa factor in West African history. Zaria: Ahmadu Bello University.

Adamu, M. (1980). The Hausa and other peoples of Northern Nigeria, 1200-1600 A.H. Seminar paper. Zaria: Ahmadu Bello University.

Adamu, M. U. (2011). Sabon tarihin asalin Hausawa. Kaduna: Espee Printing and Advertising.

Ajayi, A. S., & Fabarebo, I. (2009). Oral traditions in Black and African culture. Lagos: Centre for Black and African Arts and Civilization (CBAAC).

Alao, A. (Ed.). (2011). Politics, culture and development in Nigeria: A Festschrift for Gabriel Olatunde Babawala. Lagos: Centre for Black and African Arts and Civilization (CBAAC).

Al-Hajj, M. (1968). A seventeenth-century chronicle on the origins and missionary activities of the Wangarawa. Kano Studies, 4.

Alkali, B. (1968). Hausa community in crisis: Kebbi in the 19th century (Master’s thesis). Ahmadu Bello University, Zaria.

Augi, A. R. (2021). The Gobir factor in the social and political history of Rima Basin (c. 1650 to 1808 A.D.). Makurdi: Aboki Publishers.

Bello, A. (1992). The dialects of Hausa. Fourth Dimension Publishers.

Bunguɗu, H. U. (2022). Waƙoƙin Amali Sububu. Zaria: Ahmadu Bello University (Supported by Tetfund).

Bunza, A. M. (2002). Yaƙi da rashin tarbiyya, lalaci, cin hanci da karɓar rashawa cikin waƙoƙin Alhaji Muhammadu Sambo Wali Basakkwace. Lagos: Ibrash Publishers.

Bunza, A. M. (2005). The place of culture in national development. Paper presented at the First Convocation Ceremony, Adamu Augi College of Education, Argungu.

Bunza, A. M. (2006). Gidan Gadon Feɗe Alada. Lagos: Tiwal Publishers.

Bunza, A. M. (2009). Narambaɗa. Lagos: Ibrash Publishers.

Bunza, A. M. (2010). In ba ka san gari ba saurari daka: Muryar nazari cikin tafashen gambo. Cairo: Elkods Printing House.

Bunza, A. M. (2023). Hausa a matsayin harshen uwa a farfajiyar karatun boko. Biram Journal of Contemporary Research in Hausa Studies, Maiden Edition. Kafin Hausa: Jami’ar Sule Lamiɗo.

Bunza, A. M., Ibrahim, S. S., & Usman, B. B. (Trans.). (2007). Daular Sakkwato (M. Last, Author). Lagos: Ibrash Publishing Company.

Dokaji, A. A. (1978). Kano ta Dabo Ci Gari. Zaria: NNPC.

East, R. M. (1932). Labaran Hausawa da maƙwabtansu. Zaria: NNPC.

Farguson, D. E. (1973). Nineteenth-century Hausaland: Being a description by Imam Imoru of land, economy, and society of his people (PhD thesis). University of California.

Haroun, K., & Nasiru, A. (Eds.). (2022). Women and their contribution to Hausa society. Katsina: Alqalam University.

Ibrahim, M. S. (1982). Dangantakar al’ada da addini (Master’s thesis). Bayero University, Kano.

Igwe, S. (2010). How Africa underdeveloped Africa. Port Harcourt: Prime Print Technologies.

Isa, M. A., Ibrahim, A. K., Junaidu, M., & Isma’ila, B. (Eds.). (2017). Kano: The state, society, and economy (1967–2017), 50th anniversary of the creation of Kano State. Kano: Century Research and Publishing Limited.

Koko, H. S., & Fatima, A. (Eds.). (2018). Taskar adabin mata. Sokoto: Annoor Multimedia Limited.

Labbo, U. M. (2015). Diplomacy and war in the Sokoto Caliphate. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

Madauci, I. (1968). Al’adun Hausawa. Zaria: NNPC.

Maishanu, I. M., Jafar, M. K., & Nazir, I. B. (Eds.). (2020). Zamfara and the challenges of socio-political transformation (1764–2019). Sokoto: Faculty of Arts and Islamic Studies.

Maishanu, I. M., Usman, M. T., & Gobir, Y. A. (Eds.). (2021). Transformation in Gobir Kingdom: Past and present. Sokoto: FAIS, International Conference Proceedings.

Mani, A. M. (1956). Zuwan Turawa a Nijeriya Arewa. Zaria: NNPC.

Nadama, G. (1977). The rise and collapse of Hausa states: A social and political history of Zamfara (PhD thesis). Ahmadu Bello University, Zaria.

Nasidi, Y., & Iyortange, I. (Eds.). (1997). Culture and democracy. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

Nedel, F. J. (1970). Hausawa da maƙwabtansu. Zaria: Gaskiya Corporation.

Safana, M. S. (2003). Gurbin gaskiya cikin adabin Hausa (Master’s thesis). Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

Sani, A.-U., & Bakura, A. R. (2023, December). Al’adun Hausawa a duniyar intanet: A san matsayin yau don a kyautata gobe. Zamfara International Journal of Humanities, 2(3), 82–92. https://doi.org/10.36349/zamijoh.2023.v02i03.010

Sani, A.-U., & Maikwari, H. U. (2019). Cuɗanyar aladu a Sabon Garin Kano: Wani misali na mun zo garinku mun fi ku rawa. EAS Journal of Humanities and Cultural Studies, 1(4), 240–245. https://www.easpublisher.com/get-articles/359

Sani, A.-U., Shehu, M., & Rambo, R. A. (2023). Bitar tasirin Musulunci a kan al’adun Hausawa na mutuwa. Scholars International Journal of Linguistics and Literature, 6(12), 498–502. https://doi.org/10.36348/sijll.2023.v06i12.007

Sani, A-U. & Maikwari, H.U. (2019). Cuɗanyar aladu a Sabon Garin Kano: Wani misali na mun zo garinku mun fi ku rawa. EAS Journal of Humanities and Cultural Studies, 1(4), 240-245. https://www.easpublisher.com/get-articles/359.

Sarkin Sudan, I. A., Yahya, I., & Muhammad, M. U. (Eds.). (2021). Matsalar tsaro a Arewacin Nijeriya: Matanin rubutattun waƙoƙin gasar (2021). Sokoto: UDUS Press Ltd.

Shehu, M. & Sani, A-U. (2018). Zamantakewar Hausawa jiya da yau. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), 6. 274-284. ISSN 2449-0660.

Usman, B. B., & Sani, A.-U. (2019). Gargaɗi ga kyautata zamantakewa: Faɗakarwa daga alƙalamin Isan Kware Ɗan Shehu. East African Scholars Journal of Education, Humanities and Literature, 2(10), 621–632. https://www.easpublisher.com/get-articles/950

William, S. I. (2007). Can our culture and traditions overcome corruption? Inhaus Services Limited.

Yahaya, I. Y. (1979). Oral arts and the socialization process (PhD thesis). Ahmadu Bello University, Zaria.

Yanɗaki, A. I., Jumare, I. M., & Usman, M. T. (Eds.). (2018). Mahdi Adamu in the practice of history: Hausaland and beyond. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

Post a Comment

0 Comments