Ticker

6/recent/ticker-posts

Wasu Daga Cikin Kalmomin Hausa Da Suke Kokarin Bacewa Saboda Daina Ko Takaita Amfani Da Su

WASU DAGA CIKIN KALMOMIN HAUSA DA SUKEKE ƘOƘARIN ƁACEWA SABODA DAINA KO TAƘAITA AMFANI DA SU

1. Almuru

2. Fantimoti

3. Tsitaka

4. Matsefata

4. Kwararo

5. Balangada

6. Kwatsawa

7. Fatara

8. Sawu

9. Tobi

10. Guntsa

11. Rattaɓawa

12. Jewa

13. Sa'a (ta lokaci)

14. Fa'a

15. Ƙuloto

17. Ɗiɗɗila

18. Zulumbuwa

19. Reɗewa (pare)

20. Shuɗi

21. Rawaya

22. Tsingaro

23. Santola/Sanho

24. Tsako/Tsiyako

25. Somi/Somawa

26. Salka

27. Kuyanga

28. Ƙillewa

29. Ƙirgi

30. Dudduga

31. Tumurmusa

32. Kallabi

33. Sanwa

34. Sulluɓewa

35. Keso

Da dai sauran kalmomi makamanta waɗannan.

DALILAN DA KAN SA A DENA AMFANI DA WATA KALMA

Akwai dalilai da dama da suka jawo aka dena amfani da wasu kalmomi a Hausa kuma a kowane Harshe ma a duniya hakan ta kan faru sai dai su a ɓangaren su wasu kalmomin suna ɓata ne kuma ana ƙirƙirar wasu. Amma a Hausa ɓacewa kalmomin suke kuma ba a maganar samun wasu sabbi. Wasu daga cikin dalilan dena ko taƙaita amfani da wasu kalmomi sun haɗa da:

1. Samun wata kalma mai irin ma'anarta a cikin harshen: idan ya kasance akwai kalmomi guda biyu ko sama da haka masu ma'ana iri ɗaya sai masu magana da Harshen su fi amfani da wata sama da wata saboda ta fi sauƙi ko ta fi tsafta ko ta fi dacewa da zamani ko kuma ta fi sanuwa a tsakanin mutane.

2. Rashin buƙatar amfani da kalmar: wannan babban dalili ne da kan sa a dena amfani da wata kalma wanda idan abun ya yi tsawo za a iya mantawa da ita gaba ɗaya. Mutane kan yi amfani da kalmomi ne da suke da buƙata da su musamman buƙata ta yau ta da kullum ko kuma buƙata ta lokaci-lokaci. Misali akwai kalmomi da kullum a kan yi amfani da su kamar su kalmar 'wanka' ko 'abinci' ko ruwa da sauran su. Akwai waɗanda sai lokaci-lokaci ake amfani da su, misali lokacin bikin Sallah ko bikin aure da sauran su. Daga cikin irin waɗannan kalmomin akwai 'fata' ko 'hadaya' ko 'daba' ko 'haniniya' da sauran su. To idan ya kasance kalma ba ta cikin wannan ayarin akwai yiwuwar a dena amfani da ita.

3. Rashin sanin kalmar gaba ɗaya: wannan dalili ne da ko yanzu ya kan yi tasiri a tsakanin al'ummar Hausawa. Ga waɗanda suke koyar da Hausa a makarantu za su iya lura cewa yara masu tasowa da dama ba su san kalmomi da yawa na Hausa ba, waɗanda kuma ya kamata su san su. Hakan kuma bai rasa nasaba da mamayar da kayayyakin Bature suka yi mana wanda ya jawo dena amfani da da dama daga cikin kayayyakin gida. Saboda haka, idan abubuwa suka ci gaba da tafiya a haka akwai yiwuwar kalmomi da dama na Hausa su ɓace.

4. Ƙyamar Harshen Hausa da wasu Hausawa ke yi: har yanzu akwai Hausawa da dama da suke ƙyamar Harshen Hausa wanda na kan musu uzuri da rashin sani kuma abun da suke yi ɗin kuskure ne babba. Abun da Hausawa da dama ba su sani ba shi ne, a halin da ake ciki a Nijeriya yau ba Harshen da yake yaɗuwa kamar Hausa, ma'abota tafiye-tafiye da yawace-yawace a cikin ƙasar za su gaskata haka. Kuma haka abun yake a faɗin duniya gaba ɗaya. Saka Harshen Hausa da kafafen sada zumunta na zamani suka yi a jerin harsunan su zai gaskata haka. Yanzu a faɗin duniya akwai jami'o'i manya-manya da suke koyar da Hausa. Amma abun takaicin shi ne har yanzu akwai Hausawa da dama da kan ƙyamaci Harshen Hausa wanda hakan babban kuskure ne.

INA MAFITA?

Akwai hanyoyin da dama da za a bi wajen ganin an dawo da amfani da kowace kalma da ke ƙoƙarin ɓacewa, duk da hakan ba mai sauƙi ba ne, amma zai yiwu. Waɗanda za su fi taimakawa ta wannan fuskar su ne malaman makarantu da kuma malamai saboda su ne jama'a masu yawa suke sauraron su a lokaci guda. Ga wasu daga cikin matakan da idan an ɗauka za a farfaɗo da wasu kalmomin:

1. Yawaita amfani da kalmomin a maganganun yau da gobe: wannan ita ce hanya mafi sauƙi wajen ɗago da kalmomin da ke ƙoƙarin ɓacewa. Saboda duk lokacin da ka yi magana a ƙalla mutum guda ya ji abun da ka ce, shi ma kuma wani lokaci ya iya maimaita abun da faɗa ɗin wani ya ji ballantana idan masu ji ɗin suna da yawa. Saboda haka matakin farko  da za mu ɗauka shi ne mu yi ƙoƙarin dena amfani da duk wata kalma da ba ta Hausa ba a zantukanmu.

2. Shirya tarukan bita ga malaman firamare da ƙananan makarantun sakandare: wannan hanya ce mai kyau da idan an bi ta za a zaƙulo kalmomin Hausa da dama, saboda kowane malami da irin abun da ya sani ga kuma manyan malaman Hausa da za su gabatar da jawabai. A wurin irin waɗannan tarurruka za yi ƙoƙarin gano a ina matsala take kuma ta yaya za a iya magance ta.

3. Ba da ƙarfi ko muhimmanta Hausa a matakan farko na karatu: Yana da kyau hukumomi da cibiyoyin ilimi da tsangayun kwalejoji da jami'o'i da ƙananan makarantu su ba da ƙarfi ga darusan Hausa ta yadda harshen zai yi gogaiya da sauran kwasa-kwasai. Idan hukuma ce kuma za ta iya ɗaukar nauyin buga litattafai da dama waɗanda idan aka kawo su makarantu za a amfana sosai.

4. Duba yiwuwar tilasta wa ɗalibai karanta litattafai a takardance a matakan sakandare da gaba da sakandare: wannan matakin ɗaukarsa zai yi wahala amma idan za a ɗauka zai yi tasiri matuƙa. Da dama dsga cikin ɗalibai a dukkan matakan karantu ba sa son karanta littafi sai dai in ya zama dole wanda hakan ya nesanta su da ilimi mai yawa. Saboda haka idan zai yiwu malamai su tilasta wa ɗalibai karanta littafai ta yadda a cikin karatun nasu za su riƙa cin karo da kalmomin da ba su san su ba.

Tuni: Muna maraba da dukkan gyare-gyare dangane da wannan rubutu.

(m) Comr.  Suleiman Ahmed
22 ga Mayu, 2025.

Post a Comment

0 Comments