Ticker

6/recent/ticker-posts

Dalilin Kiran Ibrahim Da Inkiyar Maigandi

KO ME NE NE DALILIN KIRAN MAI SUNA IBRAHIM DA ALKUNYAR "MAIGANDI" A YANKIN SAKKWATO, NA GURAGURI A YANKIN ZAMFARA, MAI KAITA A YANKIN KATSINA?

A Ƙaramar Hukumar Mulkin Raɓah ta Jihar Sakkwato akwai garin da ake kira Gandi wanda a nan ne  hedikwatar gundumar Gandi.

 Wannan gari ya samo asali ne daga zaman Ribaɗi na masu Jihadin jaddada addinin Musulunci da Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi ya jagoranta a farko farkon ƙarni na 19 har aka samar da Daular Usmaniya.

A lokacin mulkin Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan  Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio(1817-1837) ne aka naɗa ɗansa Malam Ibrahim a matsayin Sarki a wannan gari na Gandi.

Zamansa a Gandi ne ya haifar da kiransa "Maigandi" / "Mai Gandi" a matsayin alkunya wanda tun daga lokacin ne wannan suna ya zama alkunyar /laƙabin duk mai suna Ibrahim musamman a yankin Tsohuwar Jihar Sakkwato (Sokoto da Kebbi da Zamfara na yau).

A shekarar 1950 Ɗangaladiman Shinkafi Ibrahim ya zama Dagacin Shinkafi da laƙabin Sarautar Magaji, wato Magajin Shinkafi, ya yi mulki har zuwa rasuwarsa a shekarar 1990( Shinkafi a halin yanzu hedikwatar Masarauta ce mai daraja ta biyu kuma ita ce hedikwatar Ƙaramar Hukumar Mulkin Shinkafi a Jihar Zamfara).

Yana da amini /ɗan uwa da ake kira Malam Jibril dake da Sarautar da ake kira "Guraguri" anan Shinkafi.

Shi Guragurin Shinkafi Malam Jibril ya fito daga tsatson wani Mujahidi ne da ya taka rawar gani a jihadin jaddada addinin Musulunci na Daular Usmaniya da ake kira Malam Muhammadu Tukur da aka fi sani da Malam Tukur Ɗan Binta ko Malam Tukur na Matuzgi.

A farko farkon mulkin Magajin Shinkafi Ibrahim sai Makaɗa Alhaji (Dr.) Ibrahim Buhari Abdulƙadir Mai Dangwale Narambaɗa Tubali ya yi masa Waƙoƙi da dama cikin su kuwa har da wadda yake danganta sa da Guraguri Jibril ko Jibril Guraguri inda yake cewa "Ibrahimu na Guraguri, mai Shinkahi bajinin Zagi, mu dai Allah ya bam muna kayaa".

Sanadiyar yaɗuwar wannan Waƙa  a yankin Zamfara sai aka samu alkunyar "Na Guraguri" ga duk mai suna Ibrahim musamman a yankin.

 

Marigayi Mai Martaba Sarkin Katsina Malam Ibrahim ɗan Sarkin Katsina Malam Muhammadu Bello ɗan Sarkin Katsina Malam Umarun Dallaje wanda ya yi Sarauta daga shekarar 1870 zuwa 1882 ne sanadiyar samar da alkunyar "Mai Kaita" ga mai suna Ibrahim a yankin Katsina.

Marigayi Mai Martaba Sarkin Katsina Malam Muhammadu Bello ɗan Sarkin Katsina Malam Umarun Dallaje ya auro Mahaifiyar Marigayi Mai Martaba Sarkin Katsina Malam Ibrahim wato Malama Habi/Habiba(Ɗiyalle)  yar Malam Muhammadu Mai Gyaza daga garin Kaita.

A lokacin da Malam Ibrahim ɗan Sarkin Katsina Malam Bello ɗan Sarkin Katsina Malam Umarun Dallaje ya zama Sarkin Katsina sai ya dinga ziyartar garin  Kaita akai akai har ma ya gina gida a can inda yake zama idan ya je irin wannan ziyara.

A ƙarshe ma a garin na Kaita ne ya yi wafati kuma a cikin wannan gida da ya gina aka yi masa hubbare (makwanci).

Sanadiyar nuna irin wannan ƙauna zuwa ga wannan gari na Kaita da jama'ar Ƙasar da Mai Martaba Sarki Ibrahim ɗan Bello ɗan Malam Umarun Dallaje ya nuna sai al'ummar yankin suka dinga raɗawa akasarin 'ya'yansu maza suna Ibrahim da alkunyar "Mai Kaita" domin girmamawa.

Allah ya jiƙan magabatanmu ya sa mu wanye lafiya mu cika da kyau da imani, amin.

Malam Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji,
Jihar Zamfara, Nijeriya.
Laraba, 28/05/2025.

Post a Comment

0 Comments