Ticker

6/recent/ticker-posts

Ba Fa Ruwan Wakokin RARARA Matsalar Tamu Ce!

BA FA RUWAN WAƘOƘIN RARARA, MATSALAR TAMU CE!

"Wannan kiɗa, kiɗa na mashaya, wannan kiɗan 'yan yanzu. Arna ku sha giya ku ci mushe, aljanna mai rabo ka sama!"- Haro mai waƙar Shaye-Shaye.

Matsalar ba ta waƙoƙin Rarara ba ce, matsala ce ta rashin tsaro da talauci da yunwa da mugun mulki da muggan shugabanni da talakawa da 'yan kasuwa da makamantan su, matsala ce ta ni da ku!

Waƙa sana'a ce, ba masallaci ko wajen wa'azin ƙasa ko taron saita tunanin al'umma ba ce, duk da za ta iya zama hakan in an so, to da ba a so ba, ku me ya hana ku ɗau gangar ko fiyanon ku yi wa'azin ko saita al'ummar ko daidaita tunanin, dole sai mawaƙi ɗaya ko wani mutum can ɗaya?

Matsalar ba ta jam'iyyu ba ce, matsala ce ta mutanen da ke cikin jam'iyyun da waɗanda ke biye masu har suke mana dodorido da rayuwa, har ba mu iya bambacewa tsakanin gaskiya da ƙarya. Ta yaya za mu ga mutum na ƙwarai a jiya, yau ya zama TSULA, kuma a zauna lafiya? Ta yaya wanda ya CI KUƊIN MAKAMAI zai dawo ya zama gwarzo, muna kuma shewa da arerewa? Ya za a yi BURGU da ya riƙa zai dawo cikin gona a ce yau ya koma ƊAWISU, sannan a ce wai ci gaba ake nema? Ba kwa jin cewa, gobe MAI MALFA na iya sanya jar hula ya zo Kano, a dama da shi har Ƙofar Kudu?

Matsalarmu ta kasancewa al'umma ce masu bauta da FUSKOKIN JANUS ne, shi ya sa rai ke ɓaci, zuciya ke kakkarwa, baki ke kumfa, idanun na yin ja, amma ba kataɓus!

Ta yaya ku da ke waƙen batsa, waƙen karuwai, waƙen giya, waƙen caca, waƙen ɓarayi, waƙen bambaɗanci kowane iri ku zo kuna cewa ƙasa ta lalace, al'umma na cikin tasku? Ku kuma waɗanne mala'ikun ne, daga ina kuka shigo wannan duniyar, wace nahiya ce kuka taso a cikinta da kuke hawa can tudu don ganin laifin wasu, bayan kun yi shame-shame a bisa tudun ɓarna?

Laifin ba na mawaƙi ba ne! Ta yaya zai zama laifi don mutum ya ajiye muku madubi ku ga yadda rayuwarku take; mashirmanta, marasa madafa da kan gado, algungumai, macuta, maɓarnata, masu sayar da gobensu saboda taliya da rashin sanin makama? Zagin madubin ko fasa madubin ba zai taimaka ba, domin abin da kuke gani a ciki, shi ne a'ala! Ku canza fasalin fuskokinku, in sha Allah ba za ku ga muguwar fuska ba!

Matsalar tamu ce, kuma ko gobe aka zo da wata sabuwar fiƙira da fasaha da ayyanawa da ta sha bamban da siyasarmu ko aƙidarmu ko wani can da muke 'bauta' wa ko yake ɗaukar nauyin abin da za mu ci ko sha, za mu fara zare ido da jefa kakkausan zance, wai an manta matsalolin tsaro da yunwa da talauci ana ta waƙe waɗansu banzaye, ko?

Ina mawaƙan namu suke, ba sai na kira suna ba! Ina na PDP ko na Kwankwasiyya ko na 'yan ba ruwanmu ko na sa-kai, ko wasu da ke basirar tsarawa da rerewa, a fito mana, ai ga filaye nan, ga dawakai, me ake jira, dole sai Rarara zai gyara ƙasar shi kaɗai, saura me suke yi?

Idan muka tsaya bin gida-gida ko layi-layi ko sai mun ba ta wuta, ko wane ko wance kawai, to mu sani haka za mu ƙare a tudun mun- bani, ko mun ƙi ko mun so!

Daga Taskar:
Prof Malumfashi Ibrahim

Rarara

Post a Comment

0 Comments