Ticker

6/recent/ticker-posts

Sharadi A Cikin Kasuwanci

SHARAƊI A CIKIN KASUWANCI:

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum, da fatar malam yana cikin ƙoshin lafiya. Mutum ne ya bani kuɗi in yi kasuwanci amma da sharaɗin duk wata ga abin da zan rinƙa ba shi, shin malam wannan ba riba ba ce? Allah ya saka wa malam da Gidan Aljannar Fardausi. Ameen.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Allah ya saka mana gaba ɗaya.

Malamai sun yarda cewa: Wani ya bayar da kuɗi, wani kuma ya riƙa yin kasuwanci, a ƙarshe kuma su riƙa raba ribar da aka samu da gwargwadon yadda suka yi sharaɗi tun farko a tsakaninsu daidai ne. Wannan ne suke kira: MUDAARABAH.

Amma a irin wannan halin da ake tambaya a kansa, inda ba a san nawa ne ribar da aka samu ba, sai dai kawai duk wata mai kuɗi ya riƙa zuwa yana karɓar wani adadi da aka yi amince a kansa tun farko, ban san madogarinsa a shari’a ba. Musamman ma da yake a cikinsa akwai cutarwa da takurawa ga mai gudanar da kasuwancin, domin ai bai san ko riba za a ci ko kuwa faɗuwa za a yi a cinikin wannan watan ba. Idan kuma mai kuɗin ya cigaba da karɓar kuɗi duk wata, za a wayi gari kenan uwar kuɗin da aka fara kasuwancin ma da shi ya kare! Zai kuma iya yiwuwa a riƙa samun riba mai yawa a cikin kasuwancin ta yadda mai kasuwanci ne zai cigaba da samun faida, shi kuma mai kuɗin zai riƙa cutuwa. A ƙarshe ya zo yana cizon yatsa.

Abin da ya fi dai kawai sai su zauna su sake tsarin don ya dace da koyarwar addini. Ko da ɗaya bisa goma (1/10) na ribar ce mai kuɗin zai riƙa karɓa ya bar wa mai kasuwancin tara bisa goma (9/10) ya fi daidai, insha’Allah. Ba za a ce wannan riba ba ce. Abin dai da ya yikusa da wannan a babin riba shi ne abin da malaman fiƙhu suke kira: RIBAL ƘARDI, watau: Riba na Bashi. Shi ne mutum ya bayar da bashin da a ƙarƙashinsa zai samu wani amfani, kamar yadda suke cewa:

ﻛُﻞُّ ﻗَﺮْﺽٍ ﺟَﺮَّ ﻧَﻔْﻌﺎً ﻓَﻬُﻮَ ﺭِﺑﺎً

Duk bashin da ya janyo amfani, to riba ne.

Sai dai kuma a fili yake cewa wannan ba bashi ya bayar ba, yarjejeniyar ciniki ce ba a ajiye ta yadda ya dace ba.

Wal Laahu A’alam.

Muhammad Abdullaahi Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments