Ticker

6/recent/ticker-posts

Ina Yin Tallar Kayan Abokina Ta Status, Ko Ya Hallata Na Kara Sama Da Yadda Yake Sayarwa

INA YIN TALLAR KAYAN ABOKINA TA STATUS, KO YA HALLATA NA ƘARA SAMA DA YADDA YAKE SAYARWA?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Abokina ne yake kasuwanci sai ina yimasa talla ta status, ya halatta idan za'a saye kayan nashi ta hannu na in kara sama da yadda yake sayarwa, sai ya kasance duk abin da ya hau ya zama nawa kaso?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Toh abunda za'a duba anan shine tsakanin me siyan da asalin me kayan wanene ya ɗaukeka aiki? Kaga ai me siya bashi yasa ka aikinba, shi me kayan kakewa aiki toh shi ze biyaka kuɗin aikinka. Dan haka be halasta ka ƙaraba akan kuɗinda ya gaya maka, sedai shi acikin ribarsa yarage wani abu yabaka.

Kokuma idan shine da ra'ayin kansa ya ce maka ga kayannan kowanne akan 1300 yake inkaga dama za ka iya ƙara naka akai, idan shi da bakinsa yafaɗi haka bakai kace yasa hakanba, A'a shine yaga yakamata ƙila asali 1500 yake siyarwa seya ce maka 1300 saboda yanaso ka ƙara taka 200 akai toh wannan babu lefi.

Kokuma tun da farko sekace masa zan dinga maka talla shin nawane kasona idan na samo me siya?? Amma haka kawai me siyan kaya be halasta kayi masa ƙariba alhalin bashine ya ɗaukeka aikinba.

WALLAHU A'ALAM

🏽Jameel Al-Hassan Haruna Kabo

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments