𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum Tambaya ta ita ce, Ina yin online business, Ina siyar da kayan sawa na Mata, Amman bani ce da kayan ba, na wasu Yan kasuwa ne nake tallata musu sai na ɗora ribata akai. Idan an siya sai na cire ribata na tura musu da kuɗinsu.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Wannan nau'in kasuwancin naki bai halatta ta
wannan fuskar ba. Domin kuwa kina cin riba ne da gumin wasu, da jarin wasu,
kuma watakil ba tare da yardarsu ba.
Amma ga wata hanyar da za ki bi domin samun kuɗinki na halal kamar haka :
1. Kodai ki rika sayen kayan da kuɗinki, sannan ki rika tallatawa kina samun ribarki.
2. Ko kuma idan baki da halin yin hakan, to su
'yan kasuwar (ma'ana masu asalin kayan) kuyi yarjejeniya dasu akan adadin kuɗin da za su rika biyanki bisa jimillar kayansu da kika
tallata kuma aka saya ta hannunki.
Amma ɗora riba bisa abin
da asalinsa ba naki ba ne, kuma ba tare da cewa sayensa kikayi tun farko daga
hannun kampani ko dololi ba, wannan bai halatta ba.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.