Ticker

6/recent/ticker-posts

Maganin Kaikayin Gaba

MAGANIN ƘAIƘAYIN GABA

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mallam ALLAH ya saka da mafificin alkhairi bisa taimakon da kake wa al’ummar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam game da abin da ya shige mana duhu na addini da ma na lafiyar mu. Mallam don Allah taimako nake nema, Mata ke fama da kaikayin gaba, a da ciwon Mara ke yawan damunta amma yanzu ya dena sai kaikayin gaban kuma tana complain cewa wannan yar fatar ta cikin farjin ta ke kaikayin, gashi kuma tana da ciki wata 5, amma mallam tun da nake da ita ban taɓa jin daɗin saduwa da ita ba sai nazo yin inzali nake ji. Mallam ataimaka don naga ta fara shiga damuwa. Sannan kuma mallam ina bukatar shawarwari game da abubuwan da ya kamata in haɗa mata don karin lafiya gareta da jaririn dake cikinta. Nagode Allah Ya jikan mahaifa.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullah wa barakatuh.

Matsalar kaikayin gaba yawancin mata da yawa suna fama dashi, kuma yana da dalilai masu yawa da suke kawoshi. Misali Kamar:

1. Rashin Tsafta ce wajen ko askeshi akan kari.

2. Yawan yin tsarki da ruwan sanyi marar tsafta.

3. Sanya wando mai damshi.

4. Wanke gaba da sabulu.

5. Shan magunguna waɗanda ba’a tabbatar da sahihancinsu ba.

6. Matsalar Shafar Aljanun Soyayya (JINNUL ASHIƘ).

Yawancin lokaci irin wannan larurar tana da wuyar magani agun likitocin Zamani. Musamman ma idan Aljani ke kawota. Dole sai anyi maganin Aljanin, an kamashi a umurceshi ya ɗauke ajiyar da ya yi awajen. Amma dai koma mene ne musabbabin abun, ga wasu magunguna nan masu inganci a jarraba. insha Allahu za’a dace:

1. APPLE VINEGAR (KHAAL TUFFAH) : Arika haɗashi da ruwan dumi ko kuma hakanan yadda yake, ana chuda wajen, anan watsawa sosai.

2. INGANTACCEN GARIN HULBA : Arika dafawa cokali 3 ruwa kofi biyu, ahaɗa da cokali biyar na Khal Tuffah ko farin Khal (White Vinegar). Idan ya dahu sannan a surka ruwan arika shiga ciki ana dumama wajen. Bayan nan a shafa Man Hulba ko Man Na’a-Na’a, ko Man habbatus sauda mai kyau. ko kuma a sanya turaren Farin Miski. Insha Allahu za’a dace.

3. MUMTAZ : Wani magani ne wanda ZAUREN FIƘHU ya haɗashi musamman saboda mata waɗanda sukayi haihuwa da yawa. Yana tsuke mace, kuma yana maganin kaikayi da kurarrajin gaba. Da kuma bushewa ko jin zafi yayin saduwa. Idan an sameshi ana iya yin Matsi dashi sai bayan Awa guda ko awa biyu aje awankeshi da ruwan dumi. Za’a cigaba dayi har tsawon sati uku. Insha Allahu za’a samu waraka daga matsalar.

Waɗannan shawarwari da magunguna an samosu ne daga Zauren Fiƙhu, Shafin Ma’aurata. Sannan a sani cewa magungunan gargajiyane. Idan bayan kwana 2 ba’a samu sauki ba to a garzaya Asibiti.

WALLAHU A’ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments