𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum Mlm an yini lfy ???? Malam Dan Allah a taimaka min mijina ko kaɗan bashi da sha'awa Malam miye zanyi amfani dashi batareda yasaniba ko Wanda zaisha a tea haka Dan tunda ya yi aure ya juyamin baya ko abincina baici saidai tea Malam ataimaka min wajen 2yrs kenan Allah yaƙara basira.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumusslaam Warahmatullah.
A samu waɗannan mahaden
kamar haka:
1. Hulba.
2. Kirfa.
3. Alkurjal.
4. Abbahan.
5. Coffe na hausa (dan ƙamshi)
6. Lemon garas.
7. Minnanas.
8. Na'a na'a.
9. Habbatus sauda.
10. Tafarnuwa kamar sala 3.
11. Citta.
12. Kaninfari.
Da farko dai kisamu turmi ki haɗe su duka ki daka su zama gari, idan kuma za ki iya
amfani da su a haka, idan kinzo dafa shayi, sai ki dibi kowanne dai dai
gwargwadon yawan shayin (tea).
Sannan Sai ki samu ganyen shayi mai kyau ki hadesu
gaba ɗaya (ganyen shayi da waɗancan mahaden) ki dafa kamar yadda ake dafa shayi su tafasa sosai.
Idan kuma mai shan tea ne sosai kamar ni Sai a
hadesu a dakasu, sai ki auna ruwa dai dai flask ɗaya, ki zuba wanan garin da kika daka cokali 2 na shayi,
sanna ki barshi ya tafasa sosai , sai kabashi ya yi tasha, don indai ma'abocin
shan shayi, to yadaina shan shayi sai wanan haɗin, ko wane shayi yasha bazai ji daɗinsa ba.
Bayan nan wanan shayin yana maganin kasala, nauyin
jiki da kuma kuzari, da din da dawa yana rege kiba da tumbi, kuma har mata ma
za su iya sha. Allah ta'ala yasa mudace
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.